Showing 18001 words to 21000 words out of 167047 words
Chapter 7 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
tsakanina da allah kuma nuzla yaruwata ce da nake so da qauna "ahankali suka cigaba da tautauna akan abinda ya shafi matsalarsu ."
a round 6pm bayan sun tashi daga aiki ya kamo hanyar gida saboda yau agajiye yake sosai yana buk'atar hutu ba zai iya zuwa gidan mumy ba ko wajen nuzla."yana isowa yayi horn gateman ya bud'e masa ya shigo yayi parking sannan ya fito tana zaune parlour'n sanye da wasu kaya ba wanda ya barta dasu ba ,tana ganinsa ta mike da sauri ta rungume shi ajikinta sannu da zuwa "yauwa !" ya fad'a atakaice yana qoqarin zareta ajikinsa dan bazai iya misalta yanayin da yaji ajikinsa ba ."
zata amshi jakar hannusa ya hana ya shige d'akinsa d'akin tabi shi alokacin ya ajiye jakar hannunsa ta shigo ta tsaya gabansa zata kai hannuta jikinsa ya rike yana cewa "out pls "Kai tsaye fita tayi ranta a b'ace tamkar wacca akayiwa mutuwa, tana shiga dakinta kiran maryam ne ya shigo wayarta ahankali ta dauka kuka ta fashe mata dashi tana furta "sister zuciyarta ta fara min zafi ". duk hankalin mrym ya tashi tana tmbyrta "sister mun jefa rayuwarmu cikin qangin rayuwa kuka take sosai maryam na rarrashinta ."
*******
Mami ta kira ya'yanta mata kan tana neman su a washegarin ranar suka kamo hanya suka zo nan mami tayi masu bayanin abinda yasa ta kirasu batare da bata lokaci ba suka amince aunty khadija tace "ai idan bai yarda ba mami ki bud'e masa wuta ,uhm uhm !! aunty khadija kin fa san halinsa mu dai bi ahankali idan aka bishi ahankali zai iya amince wa "inji cewar zabiba "wannan zaa bi ahankali ai shikenan a kirasa " babu 'bata lokaci aunty shahida ta kirasa kasancewar weekend ce yana gida ya shigo cike da izza fuskar nan tashi a had'e tamkar ta zaki yana shan kamshi".
" adamu !"aunty shahida ta kira sunansa tare da mikewa daga zaunen da take ta jawo hannusa ta zaunar dashi bisa kujera itama ta zauna akan kujerar data tashi , cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoron abinda suke shirin fad'a masa ya kalli mahaifiyarsu kana ya juyo ya kalli aunty shahida ,yayinda gefen hangunsa aunty khadija ce wacce fuskarta tafi ta sauran hadewa sai zabiba ya zuba masu ido yana kallonsu da sauraronsu cikn yin kasa da murya aunty shahida ta soma magana "yaushe zaka tare a sabon gidanka musan ranar da maryam zata tare ?".
Gabansa ne ya shiga fad'uwa cikin tashin hankali yace "me yasa kuke da damuwa ne ?ya fad'a tare da jan sayayyen numfashi ya gyara zamansa yayinda ganadayansu har mami kacokan suka maida hankalinsu kanshi duk hankalinsu a tashe yake kar ya shigo masu da wata matsala ."wani numfashi ya sake saukewa kana ya cigaba da motsa lip's dinsa "da gidana da nan duk daya ne a wajena dan haka ta cigaba da zamanta anan kawai "cikin yanayi na tashin hankali suke kallon mami "mami kina jinsa kinyi shiru wannan wacce irin rayuwa ce shi babu wanda ya isa dashi sai abinda yaga dama zai yi "me maryam tayi maka daka zabi ka dinga wulakantata haka ?"inji cewar aunty Khadija ."
"ba maryam ya wulakanta ba ni ya wulakanta Ku rabu dashi kawai yayi abinda yake so rayuwa ce gani na da yake yi ne a duniya idan na mutu zanga wanda zai cigaba da wulakantawa "wani irin numfashi mai zafi ya fesar kana ya maida hankalinsa ga mami "ni ina jin ajikina mutuwa zanyi nan kusa , kawai bakincikina a yanzu bai wuce zan tafi na barku da matsala ba domin adamcy matsala ne arayuwarku "saurin runtse idanunshi yayi aunty khadija tace "ai shikenan idan ka kasheta gbdynmu zamuyi asa.."kafin ta qarasa ya jefa mata wani mugun kallo zuciyarsa na dukan tara tara idan akwai abinda ya tsani ji bai wuce mutuwar mahaifiyarsa ba "
"Kayi hakuri adam kayi abinda zai faranta ram mami kai kasan mami na matukar sonka dan allah ko sau daya ne ka faranta mata karka zo byn ka rasata kazo kana danasani, kazo kana son faranta mata babu hali kasani a yanzu ya kamata ka canza rayuwarka idan kaki farantawa mahaifiyarka rai ka sani alamuranka bazasu daidaitu ba zama su tabarbare ne zuciyarka zata qara bushewa ne matukar kaki amsar gsky ."
"Sai abu na gaba ka sani acikin biyayyar da zaka wa mahaifiyarka zai shigar da kai aljanna domin bazaka shiga aljjana ba sai mahaifiyarka ta d'aga maka kafa kuma zaka samu wannan damar ne idan ka faranta mata anan gidan duniya ."
yadda maganarta ke shiga kunnensa haka sautin kuka mami ke shiga, hankalinsa yay matukar tashi "ina ganin lokaci yayi da zan farantawa mahaifiyata domin samun rabauta "yana fad'ar haka basu jira jin abinda zai sake fad'a ba suka rungume shi suna jin wani farinciki na mamaye zukatansu yayinda duhun daya tsarke a zuciyar mami gabadaya ya yaye "da gaske ka amince zakayi rayuwa da mrym ?bai bude bakinsa ya amsa da "eh ko Aa ba amman aranshi ya amince ta tare a gidansa ".hakika ka faranta mana rai allah ya yaye maka dukkanin wata damuwa dake damunka yasa alkhairi arayuwarku "karku wani wahalar da kanku wajen min addua na amince ta tare ne kawai saboda sweetheart amman fa kusani idan dan farinciki akeyin aure ni bana cikin farinciki kuma babu wacce zan bawa farinciki yana gama fadar haka ya mike juya ya bar dakin ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 4
Kofar suka bi da ido cike da tsananin tashin hankali yayinda mami take kuka me karfi wanda ke fitowa daga cikin zuciyarta "me nayi wa adamcy da na cancaci wannan sakayyar bayan nayi masa komai a duniya .?"waigowa sukayi gabad'aya hankalinsu na qara tashi jin maganar mahaifiyarsu hankalinsu a tashe sosai duk sukai kanta cikin tsananin damuwa da tashin hankali "kiyi hakuri mami karki d'aga hankalinki tunda ya amince komai zai zo da sauki munyi miki alqawari muddin muna raye bazamu ta’ba bari wani mummunar abu ya faru da maryam ba ."
Hawaye yake zubowa daga idanun mami ta runtse idanunta gam tana jin wani iri a zuciyarta, zuwa wannan lokacin nadamar wannan auren ya shigeta" ina ma zata iya data bari adamcy ya sawakewa maryam kowa ya huta domin bata son mrym tayi rayuwar kunci a gidan aurenta ,kuma tasan babu tantama shi zatayi tunda gashi ya furta baya farinciki da auren dan haka babu wanda zai bawa farinciki tana tunani hawaye masu zafi na zubo mata ."
Kallon mami suke wacce ita kad’ai ta rage masu a duniyar yanzu idan akwai abinda suka tsana bai wuce ganin bacin ranta da ganin damuwarta ba hakuri da kwantar mata da hankali suka cigaba da yi inda mami tayi zurfi cikin tunanin yadda zatayi ta raba wannan auren ta huta sai dai gbdy ta rasa yadda zatayi "me zatace wa mutane?" duka aure bai wuce kwanaki goma zuwa shabiyar ba ace ta raba ai sai duniya ta zageta sam bama raba auren ne mafuta agareta ba .”
Tana cikin wannan tunanin suka dafata suna kiran sunanta a matukar rud'e suna hawaye da sanyin jiki ta dawo hankalinta tare da kallonsu d’aya bayan d’aya itama mami hawaye ne ke zuba a nata idanun, ta kamosu jikinta ta damke hannuwansu duka cikin nata tace "duk naji hakurinku kuma na..na hakura na gode Kwarai da gaske allah yayi maku albarka allah ya raya maku ya'yanku ,yadda kuka min kuma allah yayi maku haka ina alfahari daku nasan ko bayan raina zaku duba bayana allah ya tayaku kula da rayuwar dan'uwanku kuyi masa addua in sha allahu ba zai cigaba da wannan rayuwar ba zai canza ."
Cikin rauni ta cigaba da mgn "bana son kuyi fushi dashi ina son ku cigaba da yi masa nasiha da adddu’a dan allah karkuyi fushi dashi kunji ya'yana allah yayi maku albarka yayiwa rayuwarku data ya'yanku albarka shima allah yayi masa albarka da rayuwarsa na yafe masa duka laifukan da yayi min wanda na sani da wanda ban sani ba daga haka tayi shiru tana goge hawayen idanunsu amman tamkar sake qara masu take sam sun kasa cewa komai su dake rarrashinta sai gashi ta dawo tana rarrashinsu tare da jaddada masu adamcy bashi da laifi duk laifinta ne data hada auren kuma tayi nadama
sannan ta bukaci suyi wa mrym nasiha akan yadda zata janyo hankalisa “nan suka cigaba da tautaunawa kowacce daga cikinsu na qoqarin sake kwantarwa da mami hankali ."
"Karku damu komai ya wuce idan allah ya kai mu jibi da yamma sai kuzo ku kai maryam gidanta "amman mami dan allah ki daina sakewa adam dayawa tunda Kinsan halinsa zuma ne sai anci sa da wuta dan wallahi mu bazamu ta'ba daga masa kafa ba muddin muka ga abinda bai mana ba na tozarci ko cin fuska akan mrym allah bazamu barshi ba dan bazamu yarda ya wulakanta maryam ba “. inji cewar Aunty khadija mami tayi murmushi irin nasu na manya kana ta soma magana a natse "Allah dai ya shirya mana shi ,mu dai cigaba da yi masa addua da kuma fatan alkhairi arayuwar aurensu ,babu yadda allah baya juya alamarinsa sai kuga komai ya daidaita a tsakaninsu “wannan haka ne allah yasa mu dace "kuyi qoqarin sheidawa maryam domin tayi nata shirin ."
A bangaren maryam kuwa wani farinciki ta tsinci kanta ciki lokacin da aka sheida mata ata ya amince dan bata yi zaton zai yarda da tarewarta ba , a zatonta lamarin zai zo da gardama ,bayan ta koma d’aki alqibila ta fuskanta tare da yin sujudul shukur cike da yalwataccen farinciki da yasa hawayen farinciki zubo mata ,alhamdulillah wannan maganar itace mafi dadin acikin dukkanin abinda ya shafi rayuwata hakika mami kin gama min komai arayuwata cike da farinciki ta kira nana hauwa'u ."
Tana d’auka taji ta sauke ajiyar zuciya sannan ahankali ta kira sunanta a can qasan makoshi wanda ya d’an d’aga hankalin maryam tace"sister lafiya ?a kasalance tace "lafiya sister bacci na tashi ya kike ?ta lumshe idanunta cike da jin dadi take fad'a mata batun tariya ranar asabar nana hauwa'u tayi murmushi jin dadi tace "to sister sai fa kin qara da hakuri akan wanda kike dashi coz gidan aure sai da hakuri it’s not easy auren mijin da bai sonka domin duk abinda zakayi bazaka ta’ba burgeshi ba ."
“A tunanina idan akayi aure shikenan kusancinka da miji kan sashi ya canza ashe ba haka ba, sai yanzu nake ganin gskyrki da kike kin auren yaya adam hakika shawo Kan yaya hisham ya gagareni bare ya adam” you're my life sister i love you so much duk duniya yanzu kece kawai wacce zan iya fad’awa damuwata ,ina shakar bakinciki a gidan yaya hisham most especially akan nuxla “ ni ban hanashi aurenta ba bare ma ban isa na hanashi ba, kawai ni abinda nafi buqata daga garesa ya kwantar min da hankalina shine kawai abinda nike so amman yaki kullum cikin d’aga min hankali yake ,ga yawon wayan da suke daita wani lokaci har asuba .”
“abinda ya bani mamaki daman nuzla tana son yaya hishsm ne? “ kamar tana son shi sister “idan tana son shi me yasa ta gudu ta barshi?"allah masani nima haka nagani abun nasu har da gayya amman ni na mika lamarina ga allah kullum shi nake roka ya zaba min abinda yafi zama alkhairi “ajiyar zuciya maryam ta sauke dan tuni farincikinta ya gushe ahankali kuma take jin wani irin tsanar nuzla na shigarta domin duk abinda zai damu sister ya dameta kuma zata iya yin komai akai "bari na fad'a miki irin abubuwan da nakewa yaya hisham da basu yi tasiri ajikinsa ba amman ki gwada yi wata kila yayi tasiri ajikin yaya adam "ki rufa min asiri sister kema kin kasa shawo Kan yaya hisham bare ni?
“ zaki iya nima da babu digon soyayyarsa nayi bare ke da na fahimci tsananin son da kikewa yaya."
“Kai sister !kai sister ko gsky "baki bazai iya misalta irin son da kike masa ba you just keep it in your mind naunayen ajiyar zuciya ta sake saukewa tace "haka ne sister ina tsananin son shi kuma bana jin zai daina wannan son har zuwa lokacin da numfashina zai bar jikina shine kad’ai muradin raina zan zauna dashi a kowani hali wannan alqawar ne “ shiru nana hauwa'u tayi tana sauraron bayaninta “uhmm ai nasani gbdy yayana ya tafi da komai naki ya bar min saura ."harara maryam ta sakar mata kamar tana gabanta stil fuskarta dauke da murmushi ta cigaba da magana "sister ko bai sona na kasance dashi hakan zai dangwamar dani cikin farinciki ko bazai soni ba zan rayu dashi ."
“Ina rokon allah idan har dole dayanmu ne zai samu farinciki samun soyayyar gidan aure to ya zamanto kece zanji dadi zanyi farinciki domin kece kike tare da abinda kike so ni kuma daman banyi aure dan soyayya ba ,”ni kuma ina rokon allah dukkaninmu mu dace mu samu soyayyar mazajenmu so na har abada “mrym ta qarasa mgnr tana hawaye yayinda itama nana hauwa'u hawaye take zuciyar kowacce na cike da tunani .”maryam na tunanin halin da zata shiga a gidan aurenta yayinda nana hauwa’u ke tunanin halin da take ciki a gidanta sun jima suna waya nana hauwa'u na fad'a mata abubuwan da zatayi domin janyo hankalin yayanta sannan sukai sallama.”
Maryam ta zauna shiru tana mamakin hakurin nana hauwa’u zata iya hakuri akan komai na gidan miji amman banda hakuri akan wata ko bata dauki mataki akan miji ba lallai zata dauka akan duk wacce zata ra’bi mijinta ,mijinta nata né ita kad’ai dan haka babu wacce zata daukarwa rainin” ta dade zaune tana saka da warwara kafin daga bisani ta mike ta nufi d’akin mami inda su aunty shahida suke,jiki a sanyaye ta tura kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama gbdynsu suka maida hankalinsu gareta cike da girmamawa tace “aunty shahida me zaa daura maku ?.”
Aunty shahida tayi murmushi kana ta dubi sauran yan’uwanta tace “ me zaku ci ? duk abinda zaki ci shi zamu ci “okay mrym kin iya fankaso?mrym tayi shiru na second biyu sannan ta gyada mata kai alamun” eh! “tô kiyi mana fankaso na kwana biyu ban ci ba ,suma kuma nasan zasu ji dadi ahankali tace “tô !ta juya ta bar d’akin zuwa kitchen tana kiran masu aikin gidan cikin kankanin lokaci suka bayyana agabanta nan ta fad’a masu abinda take son su tayata ita kuma ta soma qoqarin kwa’ba fulawa duk abinda mrym tayi ranar cikin sanyin jiki tayisa tare da tunanin halin da nana hauwa’u take ciki .”
Washegari da misalin karfe shida na yamma ATA ya tashi daga bacci wanda ya soma tun karfe biyu dan baccin ne ma ya dawo dashi gida, mika yayi tare da salati sannna ya sauko daga shi sai boxer ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya fito kugunsa d’aure da towel yayinda hannunsa ke rike da wani qaramin towel yana goge sansar jikinsa bayan ya gama ya feshe ilahirin jikinsa da body spray sannan ya qarasa inda kayansa yake ya dauko blak and whit rigar mai hade da wula ya saka yayi kyau sosai tamkr wani matashi d’an shekara talatin a duniya ya gabatar da sallah la’asar ya fito parlour ’nsa ya bud’e fridge ya dauki holladia milk mai sanyi ya sha sannan ya sauko daga samansa ya nufi gurin mami yana qarasowa ta ajiye jaridar hannunta tare da mika masa hannu.”
ya qaraso ya zauna kusa daita kallonsa tayi cike da kulawa "shigowata uku ina duba ka baka tashi ba daman tun da naga irin kwanciyar da kayi nasan ka gaji domin bacci kake mai tattare da stress ."
numfashi kawai ya sauke batare da yace komai ba "muje kaci abinci kallonta yayi cike da qauna aransa ,yace "sweetheart na sha hollondia milk bana jin yunwa yanzu may be kafin na kwanta yayi mgnr yana zuba mata kwayar idanunshi ."adamcy nah !
ta kira sunansa yaji wani faduwar gaba dan duk sanda ta kirasa haka yasan akwai damuwa.”
"dan allah mar.."no sweetheart karki ce wani abu yanzu we 'll talk later amman right now karki ce min komai akanta dan allah ki barni na huta da mgnrta haka ,kullum magana daya kmr wata zinariya "yayi mgnr cikin fushi murmushi tayi tana dungure masa kai "bazaka bari nayi maka nasiha ba "wani nasiha kuma sweetheart ?nasihar da acikinta muka tashi idan ma nasihar ce ita ya kamata kiyiwa nasiha dan ni dai kinsan bana son qazanta a gidana , ina buqatar kamshi akoina na shiga bana son shirme da hauka agidana “ya qarasa mgnr tare da yi shiru "sai me kuma ?thats all I need bayan wadan nan bana buqatar komai ."
"shi gyara shim....fi...da.." rawar da muryarta ta fara da in ina saboda kallon daya tsareta dashi yasa da kyar ta samu zancen ya kai qarshe tace “me yasa kake kallona haka kmar zaka cinyeni ?”allah adamcy zaka iya kashe mutun da kallon nan naka ,mutun sai mugun kallo “lumshe tsumammun idanunshi yayi tare da riko hannunta daya cikin nashi yace "sorry sweetheart ban fahimci abinda kike nufi bane shi yasa kika ga ina miki kallo haka "ajiyar zuciya ta sauke tace " ina son jikoki daga wajenka shine maaanar gyara shimfida dan karka ce zaka ki hada shimfida daita ".ta qarasa mgnr tana dubansa .”
"Sweetheart iya jikokin da kike dasu sun isheki haka ba sai kin samu qari daga gareni ba”