Showing 42001 words to 45000 words out of 167047 words
Chapter 15 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
tashin hankali ita da kannenta wanda baki bazai fad'a ba tabbas rayuwarsu zata sake shiga cikin matsala babba yanzu saura abinda ya rage masu mahaifiyarsu ce itama kuma ba wani isashen lafiya gareta ba lallai suna cikin tsaka mai wuya basu da mataimaki sai allah shiyasa sunyi kuka kamar me maryama taje ta kuma ta tausaya mata matuka dan tana tausayin kanta amman idan ta tuna rayuwar subai'a sai taga gara ita akanta from rich to poor is not easy .”
a bayan can mahaifinsu mai arziki ne sai dai bai yiwa kanshi tanadin komai ba har zuwa lokacin da yayi accident ya samu matsala a bayanshi ."alokacin da yake tsaka da jinya sai yayi tunanin da zaman da yake na rashin sanin ranar warkewarsa mai zai hana bazai hada kwssamominsa da abokansa guda biyu ba tunda shi bazai iya komai ba su kuma daman ba wani samu suke ba kusan a karkashinsa suke samu alhj sani da alhj dan umma ,tofa tun daga wannan lokacin daya hadasu komai ya sauya agareshi domin kuwa babu abinda ya biyo baya sai danasani dan kuwa tunda suka fara samun kudi suka juya masa baya basuyi tunanin su taimaka masa ba.”
tun suna masa naci har yazo ya gagaresu sai rufin asiri allah mahaifinsu na cikin wannan halin mahaifiyarsa ta kamu da hawan jini ga diebites daman tana dashi , shekaru biyar yayi yana jinyar sai yau rai yayi halinsa aunty tazo da ummah zaune su subai da kanneta suke wajan gaisuwa amman da ka kalli fusk'okinsu kasan suna cikin rud'u da tashin hankali ."sai dai fatan samu sausauci daga Allah.”
Ranar asabar da misalin karfe tara na safiya bayan an shirya komai na bangaren umma tsaf yayinda aunty salma tayi duk wani shiri domin janye zuciyar yusif ta hanyar malaminta ya koma kan soyayyar daya daga cikin yayanta , kausar data gama gaisawa da umma ta fito neman maryama tana kwance acikin kalubalin rayuwa da yake zuwan mata lokaci lokaci ita gbdy ma data sanin girmanta take domin gara tana yarinya radadin rashin mahaifi ne kawai Ke damunta da kuma cin zarafin yan gidansu amman bata taba kwana da abinda Ke daga mata hankali har ya hanata runtsawa ba ."
Da gudu kausar ta fado kanta tana cewa masoyiya I miss you a lot duk da halin qunci da take ciki bai hanata nuna mata itama tayi farinciki da zuwanta ba "wallahi gidanmu kullum zanceki muke kowa mamaki yake wai yaya yusif yaga mace Kuma yana sonta har kuma ya kasa samun sukuni saboda ita tayi shiru kawai domin neman take ta daurawa zuciyarta damuwa acikin kahon zuciyarta domin dai ita tuni ta rufe babinsa da komai rayuwarta kawai take "dan Allah masoyiya ki tashi ki shirya yana parlour'n umma nasan ke kadai yake jira ."
Maganarta ta bata mamaki to idan haka ne ina batun baba gali da yace yusif din ya amince da auren shikura abbanau ya yarda da batun da baba yaje masa dashi maryama batayi nauyin baki ba kamar yadda ta saba tace “ai ina ganin Ke akwai abinda bakisani ba kausar ta kalleta cikin rashin fahimta tace "kamar me fa ?bayan tafiyarku baba yace sunyi magana da abbanku an maida wa yusif shukura amatsayina “kausar ta zaro ido tace "saboda ana hauka Ke waya ya fad'a miki wannna" baba !"
Sakina da shikura kuwa duk wani abinda ya Kamata aunty salma tayi masu wanda zasu jewa yusif dashi dan hK suka shirya cikin hadaddiyar kwaliya mai daukar hankali suka dauki abinda aka tanada domin shi suka nufi bangaren umma yana zaune jin tafiya yasashi fad'a da murmushinsa har wani mikewa yayi amman ganin sabanin abinda zuciyrsa Ke mararin gani ya dauke idanunshi daga kallonsu sukai sallama cikin siririyar murya tare da durkusawa suka ajiye mishi farati gabanshi suka zauna "ina kwana ya kuma hanya ?”ya dan kallesu "sannna ya tsaida kallonsa akan sakina yana cewa "kece sakina ?"
"Eh nice tayi mgnr tana sunkuyar da kanta "sannuku da kokari atare suka sakar masa wani kayataccen murmushi "me mukayi na Godiya batare da ya kalleta ba yace “ya cancanta na gode tunda kunyi aikin da baku ya kamata kuyi ba maryama ta baku wahala domin wannan aikinta ne tazo gareni da abinda zan saka abakina idan ma da hali ta ciyar dani” gbdy jikinsu yayi sanyi ta gyara zama "ai ya cancata muyi maka haka ya dan gyara zama sannna ya fuskancesu da wani iyayi da suke masa "akan me kenan ?sukai shiru hankalinsu ya soma tashi "tabbas wannan mutumin mai wuyar shaani ne idan da hali ma suce masa dan wulakanci, akace daya daga cikinmu zata iya maye gurbin maryama a wajenka ko baa fad’a maka bane .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 9
"Yusif ya d'an yi dariya kad'an sannan yace "saboda kuma kawai a garin mahaukata ake sai ku maye gurbinta? " maye gurbin maryama ko mace' yar kasar england ce maryama tafi gabanta awajena ." Jikin a sa'bule suka d'an yi shiru daga bisani shukura tace "amma baka san cewar akwai wanda yake son maryama ba har ma ana shirye shiryen kawo kudin auren ta?"wani mugun harara yusif ya buga mata yana d'aga kafad'unsa alamun ko ajikinshi ."
Ta sake bud'e baki zatai magana a fusace yace,"Ku dan Allah ban son sakarci da iskanci banza ku ta shi kuje ku sanar da maryama dominta kawai na zo gidan nan ba dan wasu 'yan iska ba ,ta yi sauri tazo ta samar da nutsuwa acikin raina ita kad'ai zuciyata Ke muradin son gani baku marasa kamun kai ba"
sakina da shikura sukai shiru suna kallonsa tare da jinjina girman wulakancinsa, yayinda zuciyar shukura ke qara lissafo mata abinda zata sake fad'a masa amman ta kasa domin tsoron amsar da yusif din zai bata "lallai wannan ba wanda zasu zo suyiwa wargi bane, dole sai mahaifiyarsu ta sake shiri akanshi atare suka tashi jikin babu kwari suka fice daga d'akin cike da 'bacin rai ."
Aunty salma na zaune tana tunanin ya yusif zai kar'bi ya'yanta sai gasu sun shigo mata rai 'bace ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike tsaye da sauri cike da fargaba duk da dai bata da já akan aikin malaminta tsayawa tayi tana kallonsu d'aya bayan d'aya kafin daga baya tace "yana ga kun dawo min jiki a sanyaye .?"
"wallahi mama wannan mutumin mugun d'an wulakanci ne na bugawa a jarida nan shukura ta zayyane wa aunty salma komai daya faru cikin 'bacin rai sakina tace ,"ni dai gsky mama ki hakura ki barwa maryama yusif ta aura tunda ya nuna ita din dai yake so bashi da abinda zai yi damu ita kuma shukura sai ta auri malam yahuza " .bayan aunty salma ta gama jin abinda ya faru tas da abinda sakina ta fad'a tace "bazaa hakura abar mata shi ba wannan auren muddin ina raye sai anyisa da d'aya daga cikinku ."
"to gsky mama ni dai banda ni sai dai ki aura masa shikura taje can su qarata dan bazan iya da wulakancinsa ba "na gode sosai yar'uwa dan dama zuciyata tana cikin d'ard'ar ne kar shirin mama yayi tasiri akanki gashi daman dani yafi dacewa tun dana d'aura kwayar idanuna akanshi na kamu da matsanancin qaunarsa "inji cewar shukura ".
"yauwa shukurata nasan bazaki ta'ba bani kunya ba daman kuma kamaninmu d'aya "haka ne kuma dole halinku yazo d'aya ba" sakina ta fad'a acikin ranta sannan fili tace "yar wahala sai kije kiyita fama amman kisani bazaki ta'ba daraja acikin idanunshi ba karshe ma ki qarasa rayuwarki a wahala "tana gama fadar haka tasa kai ta shige d'akinsu ta barsu tana jin babu dadi aranta duk da ahalin yanzu babu wani shakuwa da soyayya a tsakaninta da maryama amman a wasu lokutan tana jin babu dadin abinda mahaifiyarta take mata ."
"Kece yar wahala daga nace ina son shi sai Kiyi min mummunar fata in sha allahu akanki zai qare "aunty salma taja hannun shukura zuwa cikin d'akinta tana cewa "manta da sakina muyi abinda Ke gabanmu "ta saki hannunta ta qarasa gaban wasu kwanuka
ta bud'e d'aya daga ciki ta d'auko tandun kwalli ta mikawa shukura tana cewa "ungo nan shukurata maza ki shafa wannan kwallin à idanunki" shukura ta kar'ba ta soma qoqarin shafawa yayinda aunty salma ta juya da sauri ta sake d'auko wani qaramin gwan gwani wanda Ke d'auke da wani bakin magani ta sake dawowa inda shukura take tsaye ta miko mata hannunta d'aya tana cewa "bani kwalli ki bani tafin hannunki idan yasan wata ai bai san wata ba zai san dani yake ".
Cike da farinciki shukura ta mika mata tandun kwallin sannan ta mika mata tafin hannunta kamar yadda ta buqata cikin sauri ta zuba mata bakin maganin tana cewa "ki fad'i sunansa sau uku sannan ki fad'i duk abinda kike son yayi miki idan kin isa gabansa ina mai tabbatar miki bazai sake miki mutsu akan komai ba sai akan abinda kika fad'a masa zai yi aiki dashi kuma zai bi umarninki ."
nan da nan shukura tayi abinda aunty salma ta umarceta"ki lashe kije zaki ga irin tarbar da zai miki sannan zaki ga irin tarbar da zai yiwa maryama zabinsa ,matsawar kika ga tarban da yayi miki bai miki ba ko ya had'a da tozarci ko cin fuska karki 'bata ranta ki dawo kawai amman kuma wallahi wallahi sai nayi masa abinda sai ya wulaqanta akan soyayyarki sai ya dawo yana kuka akanki, ke sai yayi sambatu akanki sai ya fifitaki akan uwar data kawo shi duniya ".
"yauwa mamana shiyasa nake mugun sonki allah dai ya bar min mamana ."maza kije garesa cike da Kamala da mutuntaka da kamewa ki shirya duk wasu kalamai masu sanyi da sanyaya zuciya da zakiyi amfani dashi allah ya bamu sa'a wani irin numfashi shukura ta sauke tare da rungume aunty salma ajikinta tana furta "ameen !sannan ta saketa ta juya da sauri ta bar d'akin ta nufi d'akin da yusif yake ."
ahankali ta shiga d'akin bakinta d'auke da sallama yana nan zaune kamar yadda suka fita suka barshi sai dai idanunshi a runtse suke suna kallon saman d'akin sallamar daya ji anyi ne yasashi bud'e idanu tare da sauke idanuwanshi abakin kofar d'akin suka sauka akan shukura dake tsaye tana kallonsa fuskarta cike da fara'a do cikin ido suke kallon juna ."
Wasu abubuwa ya dinga ganin suna fitowa daga cikin kwayar idanunta suna shiga nashi nan da nan ya gyara zamansa sosai yana cigaba da kallonta cikin wani irin farinciki mara misaltuwa tamkar lokacin ya fara ganinta arayuwarsa cike da tsananin farinciki yace "ya kika tsaya qaraso gareni zuciyata Ke take muradin son gani "cike da karairaya shukura ta dinga taku har ta qaraso ta zauna kusa dashi ya zuba mata ido kawai yana sakar mata tsadadden murmushinsa cikin shukin qaunarta daya ji daga sama "yaya yusif !"
Ta kira sunansa cikin wata irin murya idanuwanshi kawai ya zuba mata batare da yace mata komai ba " akace daya daga cikinmu zata maye maka gurbin maryama a wajenka me ka gani ."?murmushi yayi kawai "gabanta ya shiga fad'uwa amman data tuna irin tarban da yayi mata a yanzu sai taji wani sabon gwarin gwiwa ya shigeta "ina son na maye gurbin maryama acikin zuciyarka me zaka iya cewa ?"ai wannan ba komai bane na amince dake dan ma kin fita dacewa dani ".
ta lumshe idanunta kana tace "amman kace domin maryama kawai kazo gidan nan ba dan wasu yan iska ba ?tayi masa tambayar tana mai kafesa da idanunta yayi shiru yana kallonta qirjinsa na wani irin bugawa da karfi "maryama kad'ai zuciyarka ke muradin son gani bamu marasa kamun kai ba ?ya kai hannusa ya riko hannunta gam cikin nashi yana matsewa "yaushe na fad'i haka ?ni babu wacce zuciyata ke muradin gani sai ke murmushi tayi kawai aranta tace "aiki yayi tasiri kanan "ta qara damke hannunsa dake cikin nashi "baka ci komai da'aka kawo maka ba".
"na koshi domin ganinki ma kawai ya kosar dani "ya fad'a a daidai lokacin da kausar ta shigo hannunta rike dana maryam ."wani irin bugu zuciyar kausar yayi da karfi sakamakon ganin yanayinsu dan ita maryama daman ta rigada ta cire samunsa acikin ranta ganinsu haka ma bai d'aga mata hankali ba ."
cikin wani salon jan hankali shukura ta tsura masa ido tana kallon kwayar idanunshi tana jin wani irin shaukin sonshi na ratsata yayinda maryama ta zame hannun ta cikin na kausar ta samu waje ta jingina bayanta da bangon d'akin Tare da sunkuyar da kanta kasa tana kallon zara zaran yatsun kafafunta dan bata son ganinsu bancin darajan kausar ma da ko hanyar d'akin bazata biyo ba ."
cike da tashin hankali kausar tace "yaya meye haka kuma ?"mai nayi kausar ?shima ya tambayeta yana jin kamar ana soka masa allura a gabad'aya ilahirin jikinsa "jikin maryama ya qara yin sanyi rauninta ya soma bayyana idanunta suka fara ciccikowa da ruwan hawaye "shikenan shima an gama dashi "ta fad'a acikin zuciyarta "dan Allah malama ki sakar masa hannu"kausar ta fad'a tana zabga mata harara shukura tayi murmushin mugunta tana zare hannunta cikin nashi tsaki kausar taja sannan ta soma zayyane masa duk abinda maryama ta fad'a ".
Amman da mamakinta sai ji tayi yace "sai me idan ta fad'a miki haka ?ta sake kallonsa a matukar tsorace tana cewa "yaya me kake nufi da fad'ar haka ?ina nufin yanzu shukura nike so kuma ita zan aura "ya salam yaushe wannan alamarin ya faru ?amman ko akan hanyarmu ta zuwa nan babu wannan tsarin a zuciyarka ? maganar maryama kake tayi babu tsarin auren wata shukura arayuwarka "to yanzu na canza raayina ita nake so kuma ita zan aura " a kan me ma zan auri wannan yarinyar? ya fad'a yana nuna maryama da babban yatsan hannunsa ."
"kausar ta rikice ta gigice ta waiga ta kalli maryama dake tsaye shiru tana ciza lips dinta na kasa "haba yaya me yasa zakayi haka ?me yasa zaka sa'ba alkwarin da kayiwa mumy ?me yasa ka furtawa maryama cewar kana sonta zaka aureta yanzu kuma kazo da wata magana da hankali bazai d'auka ba "why why !!? yaya dan allah karkayi haka,ka dawo haiyacinka karka yiwa maryama haka tayi maganar cike da tashin hankali idanunta na kawo ruwan hawaye ."
"Duk yanzu na daina jin komai akanta sai dai ko a cikin masu mana aiki a gidanmu zan bawa wani shawarar ya auri wannan yarinya,amman yanzu sai shukura itace zabina a halin yanzu ma na kagauta na d'auketa daga wannan gidan dan ta fi karfin zamansa ita din ta dabance acikin zuciyata Ina kallonta ina jin farinciki araina "
hawaye dake makale acikin idanunta maryama suka zubo akan kuncin tayi sauri tasa hannunta ta goge yayinda zuciyar shukura tayi mata sanyi ta qara tabbatarwa kanta aikinsu yayi tasiri akanshi ta d'auko ruwan lemu ta tsiyaya a cup ta mikawa yusif tana cewa "ungo sha kaji sanyi aranka "yasa hannu ya kar'ba yana sakar mata murmushi cikin tsananin tashin hankali kausar tace "karka sa'ba alkwarin daka d'auka ,da maryama kawai kafi dacewa ba da wata shukura ba ka bud'e idanunka da kyau please ."
cikin wata irin murya mai sanyi da tausasawa maryama tace "kausar karki d'aga hankalinki dan baya cikin hankalinsa da natsuwarsa hasalima bazai ta'ba fahimtarki ba a halin yanzu ,kiyiwa danuwanki addua dani da shukura duk abu d'aya ne bazan ta'ba bakinciki dan yusif ya canza ni da shukura ba fatana allah ya basu zaman lafiya tana cikin fad'ar haka taji an fasa kuka abayanta mai kukan tana fadin" lahaula wala kuwwata inna lillahi wa inna ilahi rajiun wannan wani irin massefa ne haka ?
Duk suka juya umma suka gani tsaye cikin matsanancin tashin hankali "Shukura me maryama tayi miki kike shiga rayuwarta ?amman Kisani allah baya bacci kuma zai saka mata da kyakkyawan sakayya Ke kuma zaki ga muguwar sakayya dake da uwarki "idanu kawai yusif ya zuba mata ya kasa cewa komai "kiyi mata na malam yahuza ta hakura ta bar miki shi yanzu kuma yusif din kike so ?".
"umma gashi nan ki tambayesa bani nace ina sonshi ba shine da kanshi ya canza dani " yi min shiru munafukar allah daga Ke har uwarki zaku girba abinda kuka shauka ,da izinin allah sai maryama ta samu wanda yafi yusif komai kausar ta bukaci umma tayi mata qarin bayani akan mlm yahuza batare da 'bata lokaci ba ta zayyane mata komai ."
"uhmm lallai maryam kina cikin tashin hankali allah ya fitar dake kawai zan iya cewa sannan ta cire wayarta daga cikin fost dinta ta kar6i mukullin mota daga hannun yusif ta fice waje tana neman layin mumy yusif ya cigaba da yin shiru maryama ta juya jiki a sanyaye ta bar d'akin tana goge hawaye haka zalika umma kasa cigaba da tsayuwa tayi zuciyarta na tafarfasa ta shige d'akanta tana kuka ."
yaya sadam dake tsaye yana waya ya hango fitowar maryama tana tafiya tana goge hawaye ya bita da kallo Kamar ya tsaidaita yaji damuwarta sai kuma ya rabu daita da zumar zai nemeta daga baya ya cigaba da wayar da yake cikin haka kiran umma ya shigo wayarsa daman what's app call yake ."ya katse kiran domin ya d'auki kiran ummah kiran ya katse ya lalubo qaramar wayarsa yayi mamakin ganin missed call dinta dayawa ashe a silet yake "
ya kirata dan baya son ya shiga sai ya gama wayar da yake ,tana d'auka yaji muryarta can qasa tana kiran sunansa ya amsa yana tambayarta "lafiya ummah naji muryarki haka ?tace sadam kana ina ne ?ina cikin gida " tace ka shigo yanzu yanzu "okay! kawai ya fad'a ya soma tafiya cikin sauri ya shigo d'akinta."ya garasa