Showing 66001 words to 69000 words out of 167047 words

Chapter 23 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

neman aiki sai dai duk inda taje ba'a daukarta aiki tun abun baya damunta yazo ya fara damunta tayi tunanin tayi chart din ammar ko zai taimaka mata dan haka ta shiga what's app dinta tayi masa sallama ya bude amman bai bata amsa ba. ta sake aika masa still ya bude amman babu amsa dan haka tayi tunanin kiransa WhatsApp call bai dauka ba sai ma sakonsa ta gani "lafiya !?kiran me kike min ?"Jikina na rawa ta soma typing "dan allah oga ammar kayi hakuri akan abinda nayi, yanzu nasan nayi kuskure mai girma "ta tura masa."


jin kad'an sai ga amsarsa ta shigo " bakiyi kuskure ba tukun sai anan gaba karki manta don't ever call me again or chart me "inna lillahi wa innna ilahi rajiun allah ka gani taimako nayi allah karka barni da iyawata kabi bayana akan dukkanin lamurana ."
tun daga wannan rana maryam bata kuma wani sukuni ko walwala ba ,har mamakin kanta takeyi dan bata d'auka abun zai dawo ya dameta ba kullum cikin damuwa take da neman aiki bata wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane halin da take ciki a gida sai dai kowa ya tambayeta sai tace bata da lfy ne aunty salma kam kirikiri take mata dariya tare da cewa "an gama boko anyi bautar qasa babu riba dole a zaman gida tare damu ."


azumi da nafilflii kullum cikinsu take domin allah ya kawo mata mafuta da samu aikin, abun duniya ya ishi Aunty dan yar magana da take ma yanzu ta rage  Ta sake dawowa shiru shiru ga rashin aiki ga aurenta da yaya sadam na matsowa ranar monday ta shirya zata neman aiki aunty tace kar taje koina "me yasa Aunty ?"bazan iya kije ki dawo baki samu ba ki kwanta rashin lafiya nafi bukatar lafiyarki akan aiki ida ma zaki iya muje Asibiti a duba min lafiyarki dan wannna ramar ta isheni" muryarta a sanyaye tace "nifa lfy ta kalau "ina wani lafiya ana ?Kiyi hakuri aunty ki barni naje ."


"Ni baki min laifin komai ba "to amman ai fushi kike dani Kiyi min addua ko zan samu aiki "kullum ina miki addaua amman dai yanzu kinsan kiyi wasa da damarki ta barwa subai'a aikinki ?nasani Kiyi min addua allah ya sake aramin wata damar "allah yasa a dace sai kin dawo allah ya tsare" jiki a sanyaye tace "ameen!"sannan ta fita yau din ma dai kamar ko yaushe bata samu tayi kukanta har idanunta suka kunbura damuwarta ta qaru wunin ranar cikin tsananin damuwa tayisa . yadda take cikin damuwa haka zuciyar ATA ta kasa samun sukuni duk inda ya motsa sai yaji zuciyarsa na luguden bugu da tunaninta duk inda ya motsa yana jinta a jikinsa da zuciyarsa ,wunin yau din wutar soyayyarta sai qaru yake a cikin zuciyarsa ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya yunkura ya mike tsaye daga zaunen da yake yana gyara zaman yar saman suit dinsa ."



Dakin dake manne acikin office dinsa ya shiga ya tsaya hannunsa d'aya rike da kugunsa yana qarewa makeken zanenta kallo "to ban zata daidai bane ko ya ?ya tambayi kansa yana zurfafa tunaninsa "amman kuma wannan fuskar nake gani acikin mafarkina "me zai hana kasa a nemo maka kwararrun masu zane su zana maka ita kaga nasu kwarewar ko akwai abinda zai bambamta da naka ?nan take ya amince da shawarar zuciyarsa ya fito yana kiran yaronsa seun cikin kankani lokaci ya shigo cike da girmamawa "yayi masa bayanin abinda yake bukata "amman sir me zai hana ka gwada masu zanen kamfaninka AGC mana "nasan dasu na buqaci wasu dabam ,kaje kayi abinda nasaka "okay sir ya juya da sauri ."yadda yake cikin damuwar rashinta haka itama ta kasance cikin damuwar maseefar rashin aikinta dake bibiyar rayuwata kukan data yini yi ne yasa kafin shida na yamman ranar jikinta yayi zafi tamkar garwashin wuta aunty ce tsaye akanta tana shafe jikinta da jikakke
towel byn ta bata magani tasha ."




Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 13


amatukar galabaice ATA ya qaraso gida zuciyarsa na hasko masa fuskar zanen mafarkinsa " mai yasa na qasa mantawa dake ?yayiwa kansa tmbyr yana shafa sumar kansa, gbdy yau din tunaninta ya hanani sukuni ya fad’a a fili yana fesar da numfashi mai zafi daga bakinsa ,qirjinsa kuwa banda bugawa da karfi babu abinda yake, ahankali ya shiga zagaye d’akin hankalinsa na sake tashi ,a tsakiyar d’akin ya tsaya rike da kugunsa yana ciza lip’s dinsa na qasa “mai yasa bazan manta daita na cigaba da rayuwata ba ?”ya wurgawa 'kwal'kwaluwarsa tmby " ban san me yasa nake ji araina kina cikin wannan duniyar ba yaja qaramin tsaki “what's wrong with my brain ?I have to stop all this nonsense.”ya fad’a yana cigaba da d’aga kafafuwansa. bayan kamar minti biyar ya tsaya cak yana sake kamo lips dinshi na kasa yana cizawa ahankali ahankali ya d’auki lokaci mai tsawo yana shawagi acikin d’akin sannan ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka ya fito ya sanya kayan marasa nauyi riga yellow mai hannun hamles da farin wondo iya gwiwa , ya samu waje ya zauna a bakin gado zuciyarsa na sake hasko masa fuskar zanensa.”



“ idan tunaninta ya sakashi gaba jin zuciyarsa yake kamar zata buga hakan yasa yaki sauka parlour ‘n gidan kamar yadda ya saba a duk sanda ya dawo .”tsaki yaketa já yana qarawa domin tunaninta na damun kwakwaluwarsa,idan a son ranshi ne baya son yana damun zuciyarsa da kowa i irin tunani yana nan zaune a bakin gado yayinda kafarsa daya ke kasan tayis d’ayan kuma ya tankwashe tare da dafe gaban goshinsa dake sara masa kad’an kad’an gefe guda kuma yana jin damuwar da ciwon abinda dakikiyar yarinyar nan tayi ,shi tunda yake babu wanda ya samu aiki da kamfaninsa yayi rejecting dinsa sai ita ,ai kuwa zata ga wahala ganin idanunta yana zaune maryam ta turo kofar d’akin ahankali ta shigo bakinta d’auke da sallama bai amsa mata ba haka zalika bai d’ago ya kalli inda take ba .”


kusan minti biyar tana tsaye tana qare masa kallo sannan yaji sautin muryarta a sanyaye “baby sannu da zuwa !”ta fad’a ahankali tamkar wacce mako shinta Ke ciwo “ya d’ago a natse ya kalleta sanye take cikin kananan kaya wondo da riga maron colour mai ratsen fari ajiki yayinda jikinta ke fitar da kamshi hannunta rike da wani had’ad’den tray. bai amsa mata ba ,ya d’auke kwayar idanunshi akanta zuwa wani bangaren yana jan tsaki dan ya tsani sunan baby din da take kiransa dashi ,bugu da qari bazai iya jurar cigaba da kallonta ba, dan babu macen data isa ya tsaya yana kallonta .” sa’banin ita daya rigada ya saba da kallo irin nata indai tana kusa dashi to fa dukkanin idanunta da natsuwarta suna kanshi ne “ bata damuwa da duk irin wulakancin da yake mata hassalima ya fahimci dadin kallonsa take ji dan ya santa farin sani babu yadda zaayi tana tsaye haka agabansa idanuwanta ba akanshi suke ba .”



daga sannu da zuwan da tai masa bata sake ce masa uffan ba ta ajiye tray hannunta ta soma hidimar zuba masa abinci bayan ta gama zuba masa ta sake motsa bakinta “baby ga abinci “!still bai ce mata komai ba sai ma haushi da ta sake bashi ta cigaba da kallonsa dan kallonsa ba qaramin jefata cikin nishadi yake ba ,kamar ta bud’e baki ta tambayesa meke damunsa dan ta fahimci yanayinsa na yau ya canza fiyye da sauran lokutan daya saba kasancewa cikin miskilanci amman ta qasa tmbyrsa sbd gudun abinda zai je yazo .taga ya sake kallonta amman sai ta qasa d’auke idanuwanta akanshi duk da ta fahimci shi hakan yake buqata daga gareta .”madadin ta d’auke kwayar idanunta kamar yadda yake buqata sai ta durkusa gabansa ta d’auki glass cup ta had’a masa coffe ta mika masa “baby ga coffe ka sha nasan zaka fi buqatarsa “.



a matukar zuciye ya kar’bi cup din hannunta ya saita ta dashi zai kwata mata ruwan zafi tayi saurin zaro ido tare da yin gefe ,glass cup din ya samu bangon d’akin, nan take ya tarwatse a qasa , ya mike a fusace sauran kad’an ya taka wani bangaren na glass cup din dan har kafarsa ta sauka akan kwalba maryam ta saki qara mai sauti dole ya d’aga kafarsa Ya koma ya zauna tana dafe goshinsa .ahankali ta juya ta fita da sauri bata jima ba ta dawo ta durkusa ta tattara dukkan wajen ta mike tana dubansa “dan girman allah ka dinga bin komai ahankali kada kajiwa kanka ciwo “ ta furta cikin wata irin murya mai sanyi da tausasawa “muga kafarka allah yasa bakaji ciwo ba yaji tana fad’a “ya salam wannan wata irin mayya yarinya ce haka? ita sam bata damuwa da wulakancinsa ,har sai zuwa yaushe ne wuya zai sa ta gudu ta fita cikin rayuwarsa?”yana son ta gaji dan kanta ,yana son hakurinta ya qare ta gudu da kafafunta ba sai ya sallameta ba amman da alamun shine zai gudu ya barta .”



“bai ankara ba yaji ta kamo qafarsa data fi tunanin ita ce ta kusan taka kwalba ta sanya tafin hannunta karkashin tafin qafarsa ta soma murzawa ahankali “Alhamdulillah babu abinda ya sameka kamar wanda ya farka daga wani mummunar mafarki ya fixge qafarsa da mugun sauri yana huci. numfashi ta sauke ta mike tsaye idanunta na kanshi miniti biyu tsakani ta juya adaidai lokacin da wayarsa ta soma ringing ta d’an rage tafiyarta ya kai hannu ya d’auka ya manna a kunnensa “yaakayi ammar ?ya fad’a yana furzar da numfashi ,dan girman allah bana ce ka rabani da maganar yarinyar nan ba? na rantse da girman allah zamu samu matsala da kai mutuqar baka rabu dani ba ,makaho ne ko me ?maryam ta kasa cigaba da tafiya ta tsaya cak zuciyarta na karkarwa “eh haka né nasa a nemo min kwararun masu zane “ban gane na fara ganinta kafin na anemo masu zane ba ?”dan allah share yarinyar nan kwata kwata banason ganinta “wace yarinya ce wannan da yaya ammar ya damesa daita ?tayiwa kanta tmbyr yanayinta na canzawa lallai akwai buqatar taga wannan yarinyar .”


ahankali suka cigaba da tautauna can yace “dolen dolalo muna nan a yadda muke taki zuciya ta gudu ,wallahi ban soma jin komai akanta ba kuma bana fatan na so wannan yarinyar “ wannan magar da yayi ce tayi sauri dawo daita daga d’an tunanin da kwakwaluwarta ta tafi na wuncin gadi .jiki a sanyaye ta cigaba da sauraronsa “kai fa na fahimci baka son kaga ina cikin kwanciyar hankali ,wannan ba matsalata bace dan ni har yanzu ban maidaita matsayin mata ba ita ..”tun kafin ya qarasa ta fice da sauri idanunta na kawo ruwan hawaye bata san me suka cigaba da tautauna ba “amman kalma d’aya zuwa biyu suka fi tsaya mata a kahon zuciya “bai sonta da kuma tayin auren da yaya ammar yake masa “anya kuwa bazata kai qarar yaya ammar wajen mami ba ta taka masa burki ?akan wani dalili zai dinga tursasa mata miji alhalin tana iyakar qoqarin taga ta shawo kansa sun zauna lfy?amman kuma da tayi tunanin hakan zai iya janyo mata gagarumin matsala da shi ta fasa gara ta nemi yaya ammar din tayi magana dashi .”



Bayan awa d’aya da wasu mintuna ta sake dawo d’akin ahankali ta qaraso ta tsaya nesa kad’an dashi ta d’auki kallonsa gabad’aya yanayinsa ya koma na damuwa ,ta kalli abinci data kawo masa ga dukkanin alamun bai ci ba ,amman dai ta bud’e taga bai ci din ba kamar yadda tayi zato har yayi sanyi “me yasa bazaka barwa allah komai ba ?ka sani duk duniya nan idan suna son zamammu ma’aurata ida allah bai hukunto hakan a tsakaninmu ba bazai kasance ba ,haka duk kinka da auren nan idan allah yaso mutuwa ce zata raba mu .idan kuma allah yayi iya rabon zama ne atsakaninmu dole za rabamu karka manta yadda baka son auren nan amman allah ya qaddara sai da akayi .”



Tai shiru tana dubansa sam bashi da alamun zai kalli inda take bare yace wani abu ,tunani rayuwarsa kawai yake ta ina zai cigaba da zama daita bai ta’ba jin komai akanta ba ,shikenan mafarkinsa ya kasance karya ne kamar yadda aka sha fad’a masa dan da gaskiya ne yadda yake qoqarin neman princess daya sameta “nasan na dameka da magana kayi hakuri sannan dan allah kaci abinci .”shiru ne stil ya biyo baya bata ji komai aranta ba dan wannan yana cikin halinsa rashin son magana ta numfasa tana cigaba da kallonsa idanunta cike da ruwan hawaye .“dan allah kayi hakuri kaci wani abu ,rashin cin abincinka zai iya haifar maka da mummunar damuwa kuma bashi bane mafuta agaremu dan allah kaci wani abu tayi mgnr muryarta can kasa sannan cike da rawa .”


sai lokacin ya cire hannuwansa dake sarke cikin juna ya d’an kalleta ,gabad’aya ta dawo kalar tausayi amman ko kad’an bai ji wannan tausayin ba acikin ransa .”har sanda ta cigaba da magana “nasan baka yarda da wannan aure ba ,sannan baka sona amman at least dan allah ka boye wannan rashin qaunar da kake min a idanun mutane, idan ya zama dole sai ka nuna ka nuna shi atsakaninmu ,saboda samun kwanciyar hankalin mami ,aunty shahida da sauran yan’uwana bana son na gansu cikin damu “.“I can’t do it and I can’t accept this marriage ban tsara rayuwata dake ba gbdy bakya cikin tsarin rayuwata.” ya katseta ta hanyar fad’ar haka “why sweetheart ?” me yasa kike son tursasa zuciyata?shiru tayi tare da runtse idanuwanta hawayen dake boye cikin kwarnin idanunta suka samu nasara zubowa,ba tayi yunkurin sake cewa komai ba ta bude kular abinci ta zuma masa wani ta mika masa “ya adam eat your food zan juri komai amman bazan iya jurar rashin cin abincinka ba .”


kin amsar plet din hannunta yayi dan baya ji zai sauko haka cikin sauki ya rungume aurenta never yatsan hannunsa ya kai ya nuna mata bakin kofar fita “please leave i don’t want to see your face “ya furta a tsawace “ya Allah ta furta a fili tana sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta cigaba da kallonsa fuskar nan nashi a d’aure kamar koda yaushe,”amman yaya ..”I said leave …”ya sake nuna mata hanyar fita daga d’akin maryam kam gbdy ta rikice ta rasa abinda zatai jiki a sanyaye ta mike har tayi taku biyu tajiyo sautin muryarsa a kasalance tankar bashi ya gama rashin mutun ci ba “ki d’auke wannan banzar abincin naki !” lumshe idanunta tayi tana mai had’eye kololun bakincikin daya tokare mata qirji ta dawo ta durkusa ta d’auki tray ta fito ta shiga d’akinta .”



A fusace ta dangwarar da tray a qasa ta d’auki wayarta ta soma neman layin mahaifiyarta kira d’aya ta d’auka “Umma akwai matsala fa, ta fad’awa mahaifiyarta haka cikin tashin hankali da kidema.” “Akwai matsala kamar ya“?”yaya Adam fa yau ma bai ci abincin ba ,coffe ma dana had’a masa ya kwa’be ban san me zan yi ba kuma “ta fad’a tana maida dubanta ga kofar shigowa d’akinta cikin alamun damuwa sakamakon jiyo motsi muryarsa can qasa tace “ummah ina zuwa naji kamar motsinsa ta bud’e kofa ta leko shi din ta hango yana taka step da kyar kamar mai tausayawa step , wani dogon ajiyar zuciya da numfashi ta sauke alokaci d’aya “shine ya fito”ta fad’a tana komawa cikin d’akin “okay karki damu kullum idan zaki masa tayin abinci ki tabbatar kin saka masa wannan magani ni dai burina yaci ko spoon d’aya ko ya sha acikin abun shansa ,wallahi maryam a yadda nake jin bakincikin abinda wannan mijin naki yake miki matsawar bai zama naki ba zan iya kawar dashi daga doron duniya cikin ruwan sanyi kowa yayi asara ,muddin bazaki mallakesa ba gara kowace mace ta rasashi .”



da tarin mamaki maryam ke sauraron mahaifiyarta bakinta na rawa tace “a’a ummah banason!banason na rasa shi “tô meye amfanin ke baki samesa ba wata can tazo daga sama ,bari na fad’a miki abinda baki san na sani ba na samun labarin yadda yake son yarinyar mafarkinsa kuma kullum burinsa da adduarsa akanta ne .”ummah ta d’an yi shiru yayinda maryam cike da mamaki tace”wa ya fad’a miki haka ?”bangane waya fad’a min ba maganar duniya yana boyuwa né ko kin d’auka duk abinda ke faru bani da masaniya né ?tun daga lokacin da kka furta min kina son adam na maida hankalina kacokan akan sanin halin da Kike ciki dashi karon kanshi adam din ,dan haka idan bakya son ki rasashi kiyi duk dabarar da zakiyi yaci maganin nan ya zamo naki ke kad’ai ,ina son ki juya adam ,ina son ki saukewa adam jin kanshi ina son duk sanda zan shigo lagos jiniyar motocinsa né zasu tarbeni ,ke ina son na shigo gidansa cikin nuna isar ni uwar matarsa ce “.sun d’an jima suna tautaunawa umma na koyar daita hanyoyi da dabaru tare da yadda zata kwantar da kai ta samu yaci abincinta .”



Kwanaki biyu kenan aunty ta rasa gane kan maryama haka umma da habib har ma da sadam sosai suka d’aga hankalinsu dan haka ranar monday tun da safe umma ta shigo bangarensu tace ta shirya suje asibiti maryam ta kalleta a marairaice tace “lafiyarta kalau fa !umma tace “ke dai ki shirya muje a duba min lafiyarki hankalina yaki kwanciya, dan wannan rashin lafiyar bata rashin samun aiki bane kawai akwai abinda ke damunki “.maryama ta mike da kyar ta shirya cikin doguwar riga milk colour tayi Roling din kanta da mayafin doguwar rigar ta sanyawa qafafunta takalmi flat.” ita dai aunty idanu ta zuba masu har suka fice maryama naja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login