Showing 69001 words to 72000 words out of 167047 words
Chapter 24 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
qafafuwa umma da yaya sadam da habib na biye daita har bakin titi suka rakosu sai da suka shigarsu mota sannan suka dawo gida zaman jiransu ”.
Kai tsaye asibitin mayfear dake oke koto suka nufa umma tayiwa likita bayani yadda maryama take ji sannan likita ya bukaci ta basu guri fitar ummah yasa likita tambayarta yadda take ji “kasala nake ji sai qirjina dake min nauyi ga ciwon kai mai tsatsanani sannan zuciyata na min ciwo likita ya gwaggwadata sannan yace “kina yawon tunani ko ?tayi shiru tana nazarin maganarsa can tace “eh to bazaa rasa ba “.tunanin me kikeyi da qarancin shekarunki haka ?muryarta a raunane tace “ba komai ! ya kalleta na second biyu sannan ya d’auke kanshi yana rubuce rubuce tare da cewa “karya ne kina tunani domin tunani ne ke kawo duk abinda kika lissafa” shiru tayi ta rasa mai za tace likita ya dage lallai sai yaji damuwarta .”
numfashi ta sauke mai karfi tace “kawai d’an damuwar rashin samun aiki ne nan tayi masa bayani kad’an acikin damuwarta likita yace “to shikenan ki daina yawon tunani kisa allah a gaba ya rubuta mata magunguna suka koma gida da addua da rarrashin ummah da aunty tare da yaya sadam dan yanzu kullum yana tare daita yana bata kulawa har mamakinsa take kafin ya fita office zai shigo ya dubata haka idan ya dawo zai shigo daga shi har mahaifiyarsa suna bata kulawa wanda hakan yasa maryama ta dawo daidai ta cire zance samun aikinta aranta ta maida hankalinta akan zane .”ranar wata lahadi tana zaune a bangaren ummah suna hira suka jiyo sallamar subai’a ahankali ta d’ago idanuwanta ta saukesu akan kofar shigowa tana kallon subai’a tsaye, sanye cikin wasu hadaddun kaya riga da siket tayi rolling kanta da mayafi baki kafafunta sanye cikin baby shoe masu shegen kyau hannunta rike da leda kana kallonta zaka fahimci rayuwa ya sauya mata daman kuma idan Z&A suka d’aukeka aiki suna baka kudi masu yawa ka fara kimtsa kanka bare ita matsayin da take tasan zata samu da d’an yauwa .”
hakan nan taji wani abu ya tsarga mata da sauri tayi qoqarin kawar dashi acikin zuciyarta dake bugawa da karfi ta sakar mata murmushi wanda suka bayyana wushiyarta sama da qasa .”ummah ma ta saki fuska tana “cewa subai ce a gidanmu yau .”?marhabun lale da zuwa “cike da farinciki subai’a ta qaraso ciki ta durkusa har kasa gaban ummah tana cewa “nice ummah ina yini ?lafiya kalau subai ya mamanki da kannenki ya aiki kuma ?alhamdullahi mun godewa ta mike tsaye ta zauna kusa da maryama da idanunta ke kanta har lokacin ga wani murmushi da yaki daukewa akan fuskarta .subai ta kamo hannunta cikin nata “daga wajen aunty nake tace kina nan ya kike ya kwana biyu ?lafiya qalau subai’a nayi kewarki sosai ,wallahi nima kina raina kullum da tunaninki nake kwana nake tashi amman yanayin aikin dana iske a office babu sauki .”
maryama tayi murmushi tana cewa “wallahi subai’a idan na ganki cikin farinciki sai naji dadi a raina ”na gode kawata ina alfahari dake ta kalli ummah “umma ki tayani godiya a wajen kawata ta sadaukar min da aikinta “allah ya taimaka ai yiwa kai ne subai’a allah ya bata wanda yafi wannan amman maryamah ta nunawa duniya cewa ita mai qaunarki ce ummah ta furta tana dubanta .”Sosai kuwa ai bazan ta’ba mantawa daita arayuwata ba allah ya bar mana zumunci mu har ya’ya na haifi mace ta haifi nmj mu had’asu aure ummah tai murmushi “to allah yasa muna da rai da lafiya maryama ta mintsine cinyar subai’a tana cewa “dan son kai kece zaki haifi nmj ni kuma mace salon ki dinga kwacewa d’ana yan kudadensa subai’a ta sosa inda maryama ta mintsineta tana dariya “to shikenan ni na yarda zan haifi nmj ai duk ya’yana né atare suka rungume juna cike da farinciki .”
bayan su natsa maryama ta mike ta kawo mata ruwa da abinci tare da janyo ledar data shigo dashi tana cewa “kawata me kika kawo min né ?subai’a tace “bud’e kigani” ta bud’e mayuka ne set da turaruka masu yawa har da pad aciki ta saki murmushin jin dadi“tun kafin maryama tayi mgn tace” duk naki ne kawata .maryama ta dan zaro ido “kai subai’a na kuwa go ..”no maryama kin wuce haka a wajena me ma nayi miki da zaki gode min ?maryama ta mikawa umma ledar ta duba itama godiya tayi kuma yabawa subai’a sosai .”ahankali subai’a take cin abinci suna hira da maryama a qalla sun d’auki minti talatin zaune cikin parlour’n umma sannan subai’a ta kalli maryama a karo na sau babu adadi “kawata kinsan karfin zuwanah yau din nan kuwa ?maryama ta girgiza mata kai alamun a’a.”
“mr ATA mai kamfaninmu yana buqatar kwararrun masu zane a kamfaninsa na AGC shine nace nazo na fad’a miki ko zaki shiga tsawu masu neman aiki akarkashinsa?”why not ?me nake jira ?to ai kuwa sai shirya zuwa da samfurin zanenki kiyi sumit ta haka ne zaa tantance sosai tayi mata qarin bayanin yadda tsarin yake “kai gsky kawata naji dadin wannan labarin da kika zo min dashi na gode sosai,dan allah ki daina ai babu wannan tsakaninmu “na ma yi tunanin ko mr ammar ya fad’a miki ,wallahi ko d’aya bai fad’a min ba ai fushi yake dani .”fushi kuma ?”akan me zai yi fushi da yar gaban goshinsa ?
“manta dashi kedai thank you so much I really appreciate “ko akan kin bar min aiki ?kai nasan ma saboda shine yake fushi dake ,”nace ki manta dashi muyi wata hirar yadda maryama ta tsinci kanta cikin farinciki haka ma ummah har murnata taso tafi ta maryama sosai ta sake sakankancewa da subai’a lallai itama kawar arziki ce daman sai hali yazo d’aya ake kawance ummah ta tashi ta shiga ciki domin ta basu waje .”hira ce ta barke sosai atsakaninsu sosai maryama taji dadin zuwan subai’a sunyi hira mai mahimanci da subai’a dan bata boye mata komai ba akan aurenta da yaya sadam aiko tayi murna tare da mata fatan alkhairi” sai laasar sannan subai’a ta mike tayi masu sallama ta kama hanyar zuwa gida.”
Zaune maryama take a d’akinta tayi nisa a zanen samfurin da zata gabatar a A.G.C ta jiyo sautin muryar aunty tana kiran sunanta “Ina zuwa aunty “ sai dai shiru bata mike ba ta cigaba da zanenta aunty ta shigo d’aki ta mika mata cup din tea” na gode my world best kamr Kinsan ina bukata “ don’t worry my life is for my princess. aunty ban san irin son da nake miki ba wallahi ina jin kamar na fasa auren nan na cigaba da zama dake .”thank you so much my princess nima zanyi kewarki sukai shiru na wani lokaci yayinda maryama ta cigaba da zane .”
“ maryama !”
da sauri ta d’ago daga abinda take ta tattara hankalinta dan duk sanda mahaifiyarta ta kirata da wannan sunan abu ne mai mahimanci zata fad’a mata “nan kusa zakiyi aure my princess Kinsan rayuwar gidan aure ba kamar rayuwar gidan iyaye bane ina son ki sawa ranki cewar lallai sai sadam ya yarda zakiyi aiki sannan ki amince da aurensa da zuciya d’aya sannan ki sonshi har cikin zuciyarki .”
Maryama tayi shiru tana cigaba da kallon mahaifiyarta .”me zai hana ki hakura ki ajiye aikin ki rungume rayuwar aurenki “wani dogon naunayen ajiyar zuciya ta sauke “aunty kina son aurena da yaya sadam kusan duk kinfi sonshi akan sauran wad’an da suka nemi aurena a baya ?”sosai kuwa my princess ina son ki auresa , mahaifiyarsa ta taimaka min arayuwa ,mahaifiyarsa mutunce da kirkinta ya wuce misali ,bancin allah da ita da yanzu ban san makotana acikin gidan ba ,ta tsaya min ta tsayawa ya’yana ta yanto min ya’yana daga bauta nasan bakisan dalilin da yasa aunty salma da hassana suka daina bautar dake ba ?itace silar wannan ta kwatar min ‘yancinki wallahi ko yanzu na mutu nasan ruhina zai samu salama tunda gabadaya kulawarki zata koma qarqashinta .” ta qarasa maganar hawaye na cika idanunta .”
shiru sukai gbdy babu wanda yace uffan daga aunty har marayama kafin daga bisani maryama tace “ amman aunty taya zan bar aikina dana rayu dashi idan ma na hakura da aikin office aikin zane fa ?ban san ya zanyi ba bayan rayuwar nan babu tabbas “ amman shikenan aunty karki damu zanyi komai akanki haka qaddara rayuwata tazo yaya sadam yazo cikin rayuwata ba dan ina sonshi ba na sasadaukar da rayuwata zan auresa yanzu kuma ya zo ya rusa min komai nawa ,gbdy yayi distroyen rayuwata matukar bai barni nayi aikina ba “ta ajiye pencil din zanenta tasa hannunta tai tagumi tana kuka.”kuka take sosai har da sheshekan nan da nan hankalin aunty ya tashi “ki daina kuka please!” me zanyi aunty ?”me zanyi daya wuce kuka tund bazan iya ja da dukkanin umarninki ba “.
hawaye ya zubo ma aunty ,lokaci daya ta tuno mahaifinta da mahaifiyarta irin gwagwarmayar da suka sha akan karta auri mahaifinsu amman taki masu biyayya ita kuwa wani aikin alkhairi ta ta’ba yi arayuwarta da allah ya bata ya’ya kimtsasu masu gudun ‘bacin ranta ?tayiwa kanta tambaya tana mai fashewa da kuka” nan kuma hankalin maryama ya qara tashi ta kai hannu tana goge mata hawaye “please aunty ki daina kuka akaina wallahi duk abinda kike so shi zanyi bazan ta’ba bata miki rai ba “ zan miki biyayya amman ina neman alfarmar agurinki ?aunty ta kamo hannunta ta rike gam cikin nata “komai kike so my princess zanyi miki shi “ki kai mu wurin danginki ina son naga family’s dinki ki amince aunty dan allah ko sau d’aya ne mu sansu .”numfashi aunty ta fesar kawai tana runtse idanunta “ bilkisu rayuwa babu tabbas ki koma ga iyayenki ki rungume iyayenki da qaddararki bawa baya wuce qaddarasa na ari bakin gbdynmu ki yafemu bilkisu muma bamusan qaddararki bace auren hussein ,da dukkaninmu muyi biyayya ga allah ,da bamu jayayya ba hukuncin allah ba, ina mai baki hakuri kiyi hakuri ki dawo garemu allah kuma ya baki ikon cinye jarabawarki maganar babbar yayarsu kenan wacce suke uba d’aya alokacin da take chart din zuciyarta a bushe take bata jin zata koma garesu amman yanzu ita kanta tana kewarsu .” tana son zuwa garesu amman bata san me zata tarar daga iyayenta ba ,”aunty kin min alkwarin zamuje kafin bikina ?ta gyada mata kai tana dubanta ,maryama ta matso kusa da mahaifiyarta tana goge mata hawaye” ina sonki mamana “nima ina sonki sarauniyata “ta fad’a tana shafa sumar kanta da suka zubo zuwa gadon bayanta .”
******
Zaune ATA yake a parlour’nsa tare da abokansa kuma yan’uwansa shawul,mb da salim hira suke amman shi jifa jifa yake sanya masu baki “qarar takun takalmin maryam ne ya janyo hankalinsu wani hill ne mai shegen tsini tasa wanda ya qara mata tsawo daman kuma haka gabad’aya takalmanta suke bata da silipas sai na yawo acikin gida da bayi sarai ATA yaga tahowarta ta qasan idanunshi itama ta lura da hakan amman kuma sai take ganin kamar ba gaske bane , dan yadda yayi din bazaka ta’ba cewa ya kalleta ba .a natse ta qarasa saukowa fuskarta a sake ta gaishe dasu “sannuku da zuwa ina yininku ko ina kwana zance dan ban duba lokaci ba na sauko ?lallai yar mami kinji dadin aure to ina yini muke “inji cewar mb shawul yace “wannan mijin naki ne zai yarda azo masa gida da safe ai wallahi da sai ya tafattakemu.” gabad’ayasu suka dariya ta d’an saci kallonsa taga ko kallonsu bai yi ba danne danne kawai yake a wayarsa tace “a’a karku yiwa mijina sharri babu wani fatattakarku da zai yi ta fad’a sannan ta samu waje ta zauna kusa dashi sukayi mugun daf da juna da zata qara taku guda zata iya masauki a faffad’an qirjinsa shawul ya kalli salim yace “lallai yarinyar nan wuyanki yayi kauri har kin soma shigar masa ?.”
“ba dole ba miji ai ba wasa ba” zaro idanu sukai duk hirar da suke ATA yana jinsu amman bai ce uhm ba bare uhm uhm sai ma wani kololon bakinciki daya tokare qirjinsa yadda ta wani saki baki “yaya bello bari naje na shirya maku dining na dawo “ta yunkura ta mike ta soma taku su kuma suka cigaba da kallon ATA mb yace “dan allah dan annabi abokina ka sausautawa yarinyar nan haka “me nayi mata ?ya tamnayesa batare daya kallesa ba ,bansani ba !kai ka iya wulakanta ya’yan wasu amman baka son ayiwa taka ai wallahi hisham yayi min daidai da yake cin kaniyar auta “au kaniyarta yake ci har yanzu kenan ?ya fad’a tare da kallonsa a fusace “shiru mb yayi “tmbyrka nake kayi shiru kabani amsa kafin naje na samesa yanzu “to sarkin zuciya kwantar da hankalinka maganar da né numfashi ya sauke “ko ma nene tunda ka furta akwai kamshin gsky dole na ziyarci gidan “.
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun “dan girman allah kayi hakuri kayi zamanka tare da matarka ba sai kaje ka d’aga masu hankali ba ,yayi maganar kamar zai fashe masa da kuka ganin yadda ya koma kamar ba soja ba yasa ATA yace “nonsense !kai wallahi ko kasuwanci bai kamaceka ba bare aikin soja ni ban san yaakayi aka daukeka aikin soja ba ,mutun kamar mace.” gbdy suka sa dariya shi kuwa ATA bai dara ba “ya zanyi ai dole na kwatar da kai nasan halinka ne , haukanka bashi da magani yanzu sai ka tashi hankalin kowa “suna nan zaune maryam ta dawo tana cewa “kona kawo abincin nan ne ?yaya salim yace kawo kawai uwargida sarautan mata the only first lady Adam tariq” nan da nan annurin fuskarta ya sake bayyana yayinda annurin fuskar ATA ya d’auke qaramin tsaki yaja yana maida hankalinsa kan wayarsa ya cigaba da danne danne.”
Cikin kankanin lokaci ta cika masu gabansu da abinci da kayan fruit kala dabam dabam haka lemuka yadda take zuba kamshi haka girkinta ke zuba gamshi ta dan suguna ta fara zuba masu mb yace “had’a min da abokina mun kwana biyu bamuci abinci tare ba aiko murna ya kamata dan tasan da wahala bai ci ba,dole mb zai tursasa yaci ko babu yawa ,ta godewa allah data barbade abincin kafin ta kawo gabansu abinda ake so wanda daakayi aikin dominsa yaci ko yaya ne shikenan bukata ta biya .”maryam ta goge gun da abincin ya taba zuciyarta fess sai sannu suke mata amman shi ATA sam bai kula da ita ba ,ta juya domin dauko hadin salad shawul ya kalli abinci ya hadiye miyo yana cewa "kai mutumina,irin wannan liyafa haka,gsky kana cin dadi allah yayi da rabona ne shi yasa muka zo"kanka ake ji sarkin kwadayi,yi inji cewar salim.”
Ta dawo a natse ta zuba masu hadin salad fuakarta dauke da mayalwacin murmushi sai dai ta qagu ta kammala ta bar gun, tun dagowar farko ta lura da yadda ATA yake faman zabga mata harara da sauri ta bar gurin ta samu waje ta zauna akan d’aya daga cikin kujerun dining .da kyar da rarrashi mb yasa ATA ya fara qoqarin cin abinci tana zaune rike da wayarta amman hankalinta kacokan yana wajensu tana Allah Allah yaci ko loma daya ne tana kallo ya kai spoon bakinsa wani boyayayyen ajiyar zuciya take qoqarin saukewa sai dai kafin ta sauke taga ya furzar da abinci yana kallon inda take zaune .”
a fusace ya soma zuba mata ruwan bala’i “zaki kashe mutane ? ai daman nasan babu komai acikin girkinki sai hauka haka ake girki .”?cool down ATA me ya samu abincin nan ?bana son rainin hankali kai yanzu zakace bakaji abinda ya samu abincin nan ba ?”uhm dan yaji ne kad’an amman wannan ai norma ne bazai sa kar aci ba. tsaki yaja ya fara danne danne wayarsa text ya turawa auta cikin kankani tayi masa reply dinsa dan hk batare da bata lokaci ba ya soma neman layin mahaifiyar maryam tare da saka wayar a speaker dan wannna karon uwarta zai kira ba mahaifiyarsa ba, yadda mahaifiyarsa ke biye mata tana d’and’anan bakinciki haka uwarta zataji yau .”
"hello Adam ya kake ? " muryar mahaifiyar maryam ya bayyana” inna ilaihi wa inna ilahi rajiun maryam ta furta ba ita ba hatta su mb sun shiga tashin hankali mai tsanani nan take mb ya girgiza masa kai alamun kar yace komai dan ya fahimci rashin mutunci yake son yi amman ina ATA yayi kamar bai gansa ba " ammm yarinyar nan taki aure aka kawo ta gidan nan ko kisan kai ?"a matukar razane maryam take kallonshi tare da d’aura hannuwanta bisa kai cike da tashin hankali ta juya sai kuma ta dawo ta tsaya ta maida kanta qasa yayinda tunin idonta suka canza kala sakamakon qwallar data soma dan taruwa mata.” rashin mutuncinsa ya tashi daga kanta ya koma Kan mahaifiyarta kenan ?”fatanta allah yasa kar mahaifiyarta ta biye masa .”
cikin faduwar gaba umma tace”Adam ina da baki yanzu amman me ya faru me maryam din tayi haka ? ta tambayesa tana hadeye damuwarta " wannan shashar yar taki ce zata kasheni da yan’uwana da yaji mai mugun azabar zafi ga maggie daman can baki koya mata yadda ake girki bane kuka turota gidanmu tayi mana babakere har aka samu damar makala min ita gashi zata kasheni ?ajiyar zuciya ummah ta saki "kasan yadda ka bani tsoro kuwa ?yayi mata banza yana hura hanci “wallahi na d’auka wani gagarumin laifi tayi da yayi kamanceceniya da kisan kai a she just akan yaji yayi yawa ne kake wannan hauka?”
“what !?
eh !hauka mana menene aciki dan yaji yayi yawa cikin abinci ?nan da nan jikin maryam ya kama rawa bata san sanda ta qaraso kusa dashi ba tana cewa “umma dan Allah! ke rufe min baki anan idan Ke zaki dauki iskancinsa dan kina son zama dashi ni ba son shi nake ba kuma ba qaunar zamanku dashi nake ba bare na lallabashi ,tunda aka haifesa ya girma yake cin yaci a gidan uwarsa bai yi complain ba sai yanzu ?ko sau nawa muke cin