Showing 147001 words to 150000 words out of 167047 words

Chapter 50 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

ba hk ba rayuwata zata qare cikin cakwakiya  "Ameen Ameen in sha allahu zata kasance gsky ta fad'a cike da tausayawa hawaye na kokarin zubo mata .”ya mike ganin halin da mahaifiyar sa ta shiga  sai dai saukowarta akan mafarkinsa ya bashi gwarin gwiwa sosai  da kuma tabbacin zai sameta” na gode sweetheart bari naje na shirya naje office I have some work" bazakaci komai bane ? "No !kawai ya furta ya nufi kofar bathroom yana layi .”tabishi da kallo ina ma tana da halin ciremasa damuwarsa ina ma da yadda zatayi amman babu sai dai tayi imani babu abinda yafi karfin allah zan tayaka da addua adamcy Allah ya sausauta maka ."Idan kuma daga nice ya Allah ka sheida na yafe masa duniya da lahira ka yaye masa wannan danuwar .”


****


bayan ya dawo daga d'aya cikin ma'aikatansa yana sauka idonsa da abida sukaci karo dauke kanshi yayi ya cigaba da taku "AD !!!! ta biyosa tana kiran sunansa sai dai bai tsaya akoina ba sai parlour'n mahaifiyarsa "ka tsaya  kaji me zance mana cak ya tsaya  "uhm ina jinki ya fad'a yana duba file din dake rike ahannunsa "dan allah ka bawa sister dina sultana dama just give her a chance wallahi  zata maka abinda kake so she can’t disappoint you zata maka zane kamar yadda zaka mata discreb din abinda take so wallahi ta kware sosai kalli yanayin zanenta ka gani ."
Yayi shiru yana dubanta tare da dage girasa daya domin dai duk ya fahimcesu so take ta karfi da yaji ta tura masa kanwarta batasan shi din kwararren mai basira bane ta miko masa takadar zanen da take rike dashi "just one chance AD." ke kikasan takware sosai amman ni  babu abinda zanyi da zanenta "ni dai kayi hakuri dan allah to idan bazaka amince ba ka bata aiki akarkaahinka kamar yadda na nemi alfarma a tun farko do it  sake of me please tayi kusa dashi sosai tana magana kamar zata shige jikinsa yayi saurin ja da baya yana mata wani irin mugun kallo "kace ka amince dan allah "nifa bazan kawota kanfani da sunana ba amman duk wanda zai kaita banida matsla da hakan "ya fad'a yana barin wurin gabadaya ya haye sama ta juyo a hankali ta bar parlour'n ."



Umma  zaune a gefen gadonta  cikin tsananin tashin hankali  da alhinin rashin d'anta a lissafinta  Kwanaki 90  kenan wanda yayi daidai da wata uku da rasa sadam dinta   hawaye ne  masu zafi  Ke fitowa  daga idanunta yayinda kwakwaluwarta ke hasko mata fuskar tilon   d'anta "ta yaya zan iya jure rashin sadam arayuwata ?zuciyarta tai mata tambayar "duk runtsi duk wuya zan jure domin na barwa allah komai  zan cigaba dayi masa  addua  kamar yadda na kewa mahaifinsa,shikenan sadam ya tafi ya barni ni kadai a duniya alhalin bani da kowa bani da komai sai shi  kad'ai." ta qarasa mgnr wasu sabbin hawaye masu ciwo da radadi suna sauka akan kuncinta .”ahankali  ta mike tsaye ta qarasa   Inda tangamemen hotonsa yake manne da bangon d'akinta ta tsurawa hoton ido tana kallonsa  "allah na gode maka akan wannan jarabawa da kamin kasan ina tsananin son sadam arayuwata amman ka rabani shi domin ka gwada imanina “allah nayi imani da qaddara da hukuncinka gareni ,na dai  shiga damuwa ne saboda tsananin kewa da sabon da nayi dashi amman zan gargadi zuciyata zan sata tayi hakuri da rashin sadam domin nayi imani rayuwa da mutuwa duk naka ne zan daina kuka ..." a hankali ta dinga furta kalmar zan daina kuka amman still bata daina zubar da hawaye ba ."



tana cikin wannan halin maryama ta shigo d'akin  cikin yanayi na sanyi jiki dan zaune take a falo kananan maganganun su aunty salma ne yasa ta baro falon dan bazata juri jinsu ba .kowa ya ganta yasan ta zube sosai akan yadda take daman kuma ba wata mai kiba kirki bace  sosai ta d'ashe tamkar mara jini dan haka ramarta ta sake  bayyana .”ahankali ahankali take d’aga qafafuwanta har ta qaraso ta durkusa a daidai kafafun umma "umma ki daina kuka ."ta furta mata idanunta na kawo ruwan hawaye "umma ta d'ago idanuwanta  ta kalleta da tarin damuwa  sannan ta d'auke idanuwanta "umma nasan da wuya ki iya mantawa sadam  koni bazan iya mantawa da yaya sadam a rayuwata ba bare ke da kikayi silar zuwansa duniya amman dan girman allah umma kuka nan ya isa haka kar wani mummunar ciwo ya kamaki na shiga uku ,".


“ wallahi ummah ban san ina matukar son yaya sadam zuciyata ba  sai dana rasa shi zuciyata na cike da matsanancin soyayyarsa "nasani maryama allah ya jikan sadam ke kuma Allah ya baki hakurin rashinsa  "ki daina furta hakan umma jikina na bani yaya sadam bai mutu ba tunda na ji ajikina bai mutu ba tabbas bai mutu ba zai dawo garemu ."umma tayi shiru tana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya a duk lokacin da taji maryam ta furta hakan ta Kan samu saukin zugin da zuciyarta keyi cike da matsanancin soyayya ta kamo kafad'an maryama ta d'agata tsaye bisa kafafunta ta rungumeta tsam ajikinta"maryama maganarki tana kwanatar min da hankali duk da nasan da wahala ace sadam dina yana raye ."kusan minti goma suna rungume da juna kafin daga baya maryama ta zare jikinta ta tsurawa hoton yaya sadam  ido ."


A hankali ta kai hannu ta d'auki hoton ta koma kan gadon umma ta zauna tana cigaba da kallon hoton tana shafa fuskarshi yayi matukar kyau sosai fuskarsa kwance da murmushi "umman kin tuna ranar daya d'auki hoton nan ?cewar maryama" na tuna ranar daurin auren mashkur abokinsa  ne ta fad'a tana zama kusa da maryama"yaya sadam ka dawo garemu karka  barmu zuciyar ni da umma na matukar qaunarka bazamu iya jurar rashinka ba dan allah ka dawo garemu ." shiru sukai gabadaya zuciyarsu cike da  tunani umma ta janyo akwatin kayansa ta fito da kayan sawarsa tana nikewa tana maidawa cikin akwatin ,maryama ta d'auki jeans dinsa ta rike tana kallo kafin ahankali ta motsa bakinta "karki damu umma zai dawo fa ".umma ta kalleta kawai dan ita tasan bazai dawo ba har abada mutumin da'aka binne da ransa ta yaya zaayi tunanin zai rayu har ya dawo ?"cike da sheshekar kuka tace "ya allah kabamu hakuri rashin sadam domin zuciyoyinmu  sun gaza hakuri akansa maryama ta matso sosai ta kwanta ajikin umma cike da tsananin qauna "d'ana sadam mutumin kirki ne, d'ana sadam mai kyakkyawan zuciya ne ,d'ana sadam mai hakuri ne gashi ya tafi ya barni batare da kowa nasa da zan kalla naji sanyi araina ba."
“shikenan na rasa mai sakani dariya na rasa mai kawar min da damuwa na rasa mai dibe min kewa."
ta qarasa maganar tana zubar da hawaye."maryam ta kai hannunta ta shiga gogewa umma hawaye tana cewa “ karki damu umma zanyi miki duk abinda yaya sadam yake miki sannan kuma kisa aranki zai dawo garemu mu cigaba da yi miki komai tare "



"Zo zo!! ku  ga  wani abun mamaki Aunty salma ta jawo hannun baba gali da aunty hasanaa  zuwa bakin kofar d'akin umma, kalli ku gansu "wannan matar anyi shasha an kashe mata d'a amman dan shashanci ku kalli shirmen da take "ke yanzu wannan ne ya dameki ? baba gali  ya fad'a tare da juyawa ya samu waje ya tsaya suka biyosa suka tsya  kusa dashi suna  dubansa bakinsu  na son furta wani abu "salma ki  rabu dasu kawai  mu dai muyi yadda zata  dawo daidai kafin wannan yarinyar ta gama takaba araba gado ,aunty salma ta saki murmushin jin dadi burinta zai cika "kai wallahi ina cikin farinciki saboda kaso  mai yawa zaka samu “sosai kuwa dan kaso biyu zanci tunda ni nmj ne "ya qarasa maganar cikin tsananin farinciki wannan kuma haka ne bari kama gabanmu su kuma suje su qarata da kukansu hawaye ne yayi masu yawa" wallahi nima allah allah nake lokaci yayi araba abani kasona inji cewar aunty hasana baba gali ya saki murmushi "ni Allah yasa a mallaka min kamfanin burodi gbdy aunty salma tasa dariya murna kmr su rungume juna a wajen ."baba gali da aunty salma suka fice suna dariya aunty Hasana ta shiga kitchen domin daurawa umma abinci dan tun daaka nemi sadam aka rasa  kusan rabin yininta anan take yi ."



Umma ta kai hannu ta shafa sumar kan maryama  "allah yayiwa rayuwarki albarka ,allah ya qara mana hakuri, muyita hakuri da sannu allah zai mana sakayy.. “qarar wayar umma ce ta katseta maryama ta mike da sauri ta shiga duba inda wayar take "gashi can a karkashin pillow ta fad'a tare da d'auko wayar  ta mika mata cike da ladabi ta d'auka "assalamu alaikum, wallahi alhamdulillah mun godewa allah ya kunfan jiki Aa da kanki ai da kinyi zamanki hjy ba sai kin wahalar da kanki ba to shikenan allah ya kawoki lafiya sukai sallama " umma waye zai zo ?granny ce "shiru tayi tana tunani , tashi muje parlour'n tare suka fito zuwa parlour umma na kiran sunan   "hassana "kanwar hajiyata na nan zuwa in sha allahu gobe ,hasana ta fito daga kitchen tana goge hannunta tana cewa  "kai allah ya kawo mana ita lfy  ta kalli maryama ta galla mata katuwar harara "maza ki d'auke wad'an mugayen idanunki akaina  aí mu dai wannan yarinyar ki  zame mana balai a danginmu wai aunty yaushe zata bar bangaren  nan ne ta koma can gurin uwarta kar muma ta lashe mana kurwa ?wallah duk san dana daura idanuna akanta  ina jin kamar na kasheta ta mutu kamar yadda ta zama silar  kashe min dan danuwana dan girman allah ki sallema ta bar bangaren  nan mu huta da jaraba "ke dan Allah ya isa haka ina zata alhalin tana cikin takaba? wallahi hassana banason  abinda kike wa yarinyar nan yana matukar kona min rai dame kike son yarinyar nan taji ?Ko ance miki ita ta kashesa né ?Kiyi hakuri aunty in sha allahu na daina umma ta juya mata baya tana danne hawayenta ".amman Aunty  ya kamata ki  fito da kayan sadam  tunda yanzu ya zama na magada sai bawa yara su yi amfani dashi tunda ya mutu kafin wannan mayar ta gama takaba araba gadonsa .."


"sadam bai mutu ba"maryama  ta fada da iyakacin karfinta tana juyowa ta fuskanceta  tare da dafe qirjinta "tabbas sadam bai mutu ba  ta qarasa mgnr tana kuka "yanzu ke hasana har kina tunanin abinda ya mutu ya bari sun zama na magada ku kenan ?dan kune magadansa sai ni da matarsa maryama nan  da  nan idanun umma  suka cika da kwalla ta shiga girgiza kai "wallahi  hasana ki bani mamaki sam banyi tunanin haka daga gareki ba "idan ma kiyi hakuri ni da kaina zan nemi araba duk abinda ya bari domin allah ne yace araba gado ni ban isa nayi jayayya da hukuncinsa ba amman at least kunyi hakuri   ku daina  daga hankalinku ,baku barni na huta ba baku  bar yarinyar mutane ta huta ba wai me yasa haka né ?karki manta maryama jininki ce domin kinfini kusanci daita dan diyar yayankice uwa daya uba daya wallahi naso sadam ya rayu kodan ya kula min daita ya gatanta min ita ya bata kulawar da duk wani miji yake bawa matarsa ."ta qarashe mgnr tana kuka ".


maryam ma ta fashe da  kuka ."Umma ko zaa raba abinda sadam ya bari dan Allah a d'an jirkinta tukun har zuwa wani lokaci saboda har yanzu police suna Kan invesgetion idan ya zamo yana raye fa bai mutu ba kuma an rigada an raba komai nashi ni dai a nawa shawarar kar a ta'ba komai nashi hatta suturarsa abarshi tukun nan." da wani irin mugun kallo ta d'auketa dashi " yanzu ke maryama kina tunanin  yana raye ? " bai raye yana raye ya kamata  abari hukuma ta gama bincikenta alabashi komai zaa yi sai ayi amman for now abar komai gsky
Tunda tasoma magna Aunty hasana tayi shiru tsaye tana mka maka  mugun kallo, da ashariya daga cikin zuciyarta "kaji min tsinanniyar shegiyar yarinya suka jiyo muryar aunty salma gabadaya suka juya bayansu suna kallonta ahankali ta dinga taku har ta qaraso inda suke "lafiyarki ma kuwa maryama ?gsky akwai  alamun kin zauce ayi hanzari akaiki asibitin mahaukata a duba lafiyar kwakwa kuwarki,"kece fa da kanki kika tabbatar mana  yaro nan ya mutu tunda a gabanki kika ce an binnesa  da ransa amman ki kekashe kasa akan bai mutu ba " wallahi aunty bai mutu ba dan ina ..."ke jaira kiyi mana shiru anan kafin na zuciya na soma yar yar fa miki mari sadam  ya mutu kuma bazai dawo ba har abada idan ma zaki cire hkn aranki ki cire ki fara tunanin wata rayuwa."
ta fad'a tana huci “wallahi bai mutu ,kuma babu mai raba gadonsa hasalima babu takabarsa akaina ina nan ma tsayin matarsa har tsawon shekaru hudu “lallai hasashena ya tabbata yarinyar nan ta samu tabin hankali “to tsaya kiji da kyau duk macen da mijinta ya bata ne zatayi dakon aurensa na tsawon shekaru hudu sannan bayan haka tayi idda idan kin haukace ne gara tun wuri musani amman rabon gado tabbas zaayisa acikin gidan nan inji cewar aunty salma .”




Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


             Page 28


Kwanciya maryama tayi a kasa tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya da ban tausayi  sai dai duk wannan kukan da take sautin muryarta bata fita sosai ,tana jin ina ma sautin kukanta ya fito fili da hakan zai fiye mata sauki fiyye da rashin fitowarsa bugu da qari ko yasa yan'uwan mahaifinta sun sauko daga tsatsauran raayinsu  su tausayawa rayuwarta ta jurewa kowance  irin jarabawar da Allah yayi mata amman ta kasa jurewa wannan  jarabawar, ta kasa jurewa jarabawar rashin miji da kuma d'anuwa gareta."meye tarin zunubina?tayiwa kanta tambayar hawaye na sake gangarowa akan kuncinta "ya Allah ka sausautawa rayuwata domin idan abubuwan dake faruwa akaina  suka cigaba da faruwa  zuciyata zata buga ."idanun umma dake cike da ruwan hawaye ta zubawa aunty salma tana kallonta  cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da bakincikin mummunan kalamanta ga maryama ."cike da tsananin tausayawa  maryama umma ta qaraso gareta ta durkusa ta riko tafin hannunta cikin nata cikin yanayin tashin hankali tace "kukan ya isa haka maryama  kada kanki yayi ciwo ."


     "mai yasa abubuwa suke zuwa min haka umma ?"ya zanyi da wannan rayuwar ? ya Allah ka d'auki rayuwata na mutu na huta da wannan duniyar da babu komai acikinta sai tarin bakinciki ya Allah ka d'auki rayuwata tunda haka rayuwar duniya take "daga wannan tashin hankali sai wannan tashin hankali meye laifina ?nan take tausayin maryama ya sake ninkuwa acikin zuciyar umma tare da jin wani irin tarin qaunarta mara misaltuwa "kiyi hakuri maryama ki daina furta wad'an nan kalaman haka rayuwa take cike  da kudirorin ubangiji ,sannan dukkan rayuwa d'an adam rubutaccen al'amarin ne daga Allah,na shafa fad'a miki duk mutumin da Allah yake so shi yake yiwa jarabawa." wani sabon kuka ta fashe dashi tana jin kamar ranta zai fita ya bar gangar jikinta aunty salma ta kwa'be baki tana duban umma da maryama a kaskance kafin ahankali ta cigaba da cewa "da dai kin daina wannan kukan  munafurci da kike yi da bazai ta'ba miki maganin halin da kike ciki ba, mutuwa ce da bakinki kika ce agabanki aka binne sadam da ransa to me kuma yayi saura ?Jin haka ya qara sa  ran umma yayi  matukar 'baci  ta d'ago  idanunta cikin zafin rai ta  kira sunan aunty salma "salma !"


Yanayin yadda ta kira sunan cikin tsawa ya d'aga masu hankali gabad'aya sukai tsuru suna kallonta domin wannan shine karo na farko da suka ga tarin damuwa da 'bacin rai acikin kwayar idanunta,"salma  karki bari 'bacin raina ya sake ninkuwa akan wanda nake ciki ,nayi ta qoqarin na danne zuciyata akanku  amman naga alamun so kuke  sai na nuna muku  fushina da 'bacin raina"me maryama ta tsare maku ?wani irin numfashi mai zafi umma ta fesar kamar an tsikareta haka umma ta tashi daga gaban maryama "wallahi wallahi !!kunji na rantse akan maryama zan iya 'batawa da kowa dan haka ku  shiga hankalinku ku san irin magangun da zasu dinga fitowa daga bakinku  saboda kuma kuna da naku ya'ya,allah yasa mata kuka haifa dayawa kusani duk mugun nufinku ga maryama kanku  ko kan ya'yanku  zai dawo domin allah baya zalinci kuma baya son mai zalinci amman nasan rashin ilimi ke damun rayuwarku domin da kusan dukkan rayuwar rubutaccen
lamari ne daga rabbi, kilan da baku tsaya ' batawa kanku  lokaci ba gurin matsawa kanku da hassada da hankoron neman duniyar da wani ba ."



aunty salma ta kalli umma wacce  har lokacin kwayar idanunta  na kanta cike da tarin 'bacin rai sannan ta waiga inda baba gali da aunty hasana suke tsaye suma cike da mamakin umma .aunty salma ta daure zuciyarta da maganar umma tace "irin fatan da zaki mana kenan ?"irin fatan dai da  kukewa  kanku kenan." da sauri umma ta bata amsa da haka sannan tana cigaba da cewa  " maza ku fice min daga parlour bana son ganinku  kuma wannan ya zamo karo na farko dana qarshe da zaku  shigo inda nike kuyi lamarinku nayi nawa bana son ganin gaba d'ayanku a inda nake kowa ya zauna inda allah ya ajiyesa ."saboda an ta'ba miki yar so zaki fad'a mana haka ? Inji cewar aunty hasana "kwarai kuwa zan ma iya yin abinda yafi haka matuqar akan maryama ne aunty hasana ta numfasa kana tace "idan bake ba aunty ai murna zakiyi da abinda ake wa yarinyar nan yarinyar da ta zama silar rasa tilon d'anki  "sadam dai d'ana ne dana   haifa da cikina  duk kuma  wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login