Showing 129001 words to 132000 words out of 167047 words

Chapter 44 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

“ ni dai idan kasan zuciyarka ta rabu gida biyu dan allah ka hakura dani ka tsaida zuciyarka wuri daya” tana gama mgnr ta zare hannuwanta zata juya ya riko tsintsiyar hannunta bata juyo ba ya zagayo ya tsaya gabanta yana kallonta tare da kamo d’ayan hannunta ya kai bakinsa yayi kissing sannan ya cigaba da mgn “ina sonta amman nafi sonki maryama akanta ki yarda dani tunda har zan iya hakura daita na aureki ya kamata ki gane sonki yafi nata ,amman wannan ba adalci bane yaya sadam ya kake son tayi da sonka ?ka kuwa san yadda mace take ji acikin zuciyarta idan an kayi breaking heart dinta ?kasan halin damuwar da take ciki a yanzu ?ya zanyi maryam kafin na shigo da maganarta ummah ta zarta da hukunci akaina kin fi kowa sanin komai ya kamata ki fahimceni ki min adalci . magana ta gskiya ni yanzu Ke nake so shiyasa nake bata hakuri ,kiyi hakuri karki yi fushi dashi ahankali ya dinga kwantar mata da hankali . hankalin maryama ya kwanta “kin hakura ? na hakura tana gama fad’ar haka ta zare hannuwanta cikin nashi shige part dinsu shiru yayi kafin a hankali ya juya ya bar wajen ."

***

ATA na zaune a office haka nan zuciyarsa ta kasa samun natsuwa James ya shigo hannusa rike da cup din coffee ,sir ga coffee ATA ya karba ya curbi kadan ya ajiye "dan allah sir ko zan iya cewa wani abu yace “uhm !”me yasa ka damu kanka sosai dan an kira yarinyar nan taki dauka ? sai akayi ya kenan ? ya fad'a yana d’ago kansa” wannan shine abinda ya shigo da kai ?”no sir kawai dai bana son ganinka cikin damuwa ne ya numfasa kana ya cigaba da motsa lip’s finds “ni ba damuwa nayi daita ba yadda aka wulakantata ne ya dameni ,amman sir babu abinda aka mata na wulakanci kawai bayani aka mata akan lokacin da zata samu amsarmu, ni ina ganin damar kamar ranta a bace yake. “enough James ka dameni zaka iya fita please “james ya daga kafafunsa ya bar office din bayan kamar minti goma ya sake neman izinin shigowa cike da girmamawa ya tsaya gabansa “sir akwai wani dayazo yana son ganinka "babu wanda zan gani yanzu sai dai gobe ya fad’a tsawace .”


James ya juya da sauri zai bar office din yajiyo sautin muryarsa cikin fushi   idan ka fita kace wa umar da sauransu suzo ina son ganinsu a conference room “okay sir ya qarasa fita da sauri "ATA ya mike yana zariya a office can kuma ya tsaya cak gaban zanensa yana kallo ya kai hannu yana shafa fuskarsa dake cikin zanen”hakika zuciyata na matuqar qaunar son ganin yarinyar nan zan so ta zana min zanen princess dina a qarshe na ajiyeta a qarqashin ikon AGC domin zatayi mata amfani .ya kai hannunsa ya shafa sumar kanshi yana furzar da iska mai zafi sannan ya d’auki zanen ya nufi wani d’aki dake cikin office dinsa “ kafin kace me manyan ma’aikatansa sun hadu conference hall a natse ya soma magan fuskarsa a hade “abinda zan fad'a maku shine ina bukatar ganin yarinyar data zana zanena acikin kwanaki biyu kacal a nemota a duk inda take acikin garin nan idan ba haka duk zaku rasa aikinku . a lokacin da yakewa maaikatansa magana system ne a hannunsa yana operating yana masu bayani “fatan kun fahimceni .”


“yes sir ."! suka furta gabadayansu ya juya a natse
ya koma office dinsa "ya zamuyi kenan ?suka furta atare cikin tsananin tashin hankali “ya kuwa zamuyi kawai mu dudduba muce masa bamu ganta ba ko kuma mu zakalu d’aya daga cikin wadan da suka kawo nasu muce itace .falalu ya kallesu gbdy yace” wai me yarinyar zata masa ?wata yarinyar mafarkinsa yake nema, ya zanata da kansa yau tsawon shekaru sama da goma sha kenan yana nemanta shine yayi tunanin may be bai zanata yadda ya ka mata bane yasa bai ganta a duniyasa ba shine fa yace a nemo masa kwararrun masu zane zai fad'a masu yadda take su zana masa ya gani tô cikin wad’an da suka kawo gwajin su aka samu mutun d’aya wacce ta zana shi kuma itace zanenta yafi d’aukar hankalisa “falalu yayi masu bayani atakaice “gbdy suka sauke ajiyar zuciya suna jinjina girman lamarin mai gidansu sun dade suna tautaunawa akan yadda zasu bullowa lamarin kafin daga baya duk suka watse ."


Tsaye James yake a gaban ATA a office dinsa cike da girmamawa yana masa bayani “sir yarinyar nan dana baka labari kwanakin baya akan tana da kwarewa sosai akan ilimin lissafi duk wani calculations na Z&A itace take yi wanda yasa ta samu gurbi aiki a karkashin Z&A amman taki, itace the same yarinyar da tayi zanenka ,kaf a garin nan itace ta iya zane mai matuqar daukar hankali ,intakaice maka sir yarinyar ta had’a komai na samu nayi waya daita amman tace bata bukatar yi mana zane “da mugun sauri ATA ya d’ago yana dubansa cikin tsananin fad’uwar gaba yace “ what ? She rejected our job again duk yadda masu zane suke shan wahala a kasar nan kafin a karbi zanensu .”wallahi sir nima nayi matuqar mamakinta babu yadda banyi daita ba amman ta kafe bata son aiki damu .”ATA yayi murmushin ciki sannan ya koma ya zauna sosai akan kujera yana jan numfashi da kyar “wannan shine karo na biyu da aka fad’a masa baa son yin aiki a masikatarsa, yaji abun ya damesa matuqar . “



a hankali ya cigaba da murmushin gefen baki wanda da gani kasan na bakinciki ne “ina ganin wannan yarinyar tana da damuwa a rayuwarta amman me yasa ka kawo min wannan dogon bayanin akanta tun kasan bazatayi aiki damu ba ?”kawai dai wai dan ..” dogon tsakin daya ja tare da furta “noncess.”yasa james yayi saurin cewa“Am very sorry sir ,amman tace zuwa nan gaba zata iya kasancewa damu tunda ATA yayi shiru bai sake yin mgn ba kawai bakinciki ne ke cin zuciyarsa sai faman tsaki yake ja yayinda kwakwaluwarsa na shirya masa yadda zai yi tazo hannu cikin sauki “lallai tunda zuciyarta ta zabeta dan dole sai ta kasance a qarqashin ikonsa kuma kome zaiyi zaiyi kuma yasan shi né da nasara “leave !ya furta wanda tuni james ya isa bakin kofar fita nan da nan ya kira layin wani yaronsa segun dake ogun tsate bayan ya d’aga kiran ya shiga fad’a masa abinda yake son yayi masa tare da number fad’a masa number wayar maryama kai tsaye batare da ‘bata lokaci ba ya soma aiwatar da aikin mai gidansa ta hanyar tura mata sako .”


***

“Heartbeat! firgigib maryama ta farka daga baccinta tana cewa “after dad ta kirasa tana hamma hade da mika tana dubansa” a ina ka kwana habib anan na kwana ina jiran shigowar ka ? “yanzu ka shigo ? shiru yayi yana dubanta “ kasan bana son kana kwana a waje habib mai yasa baka jin magana na kiraka yafi sau babu adadi wayarka akashe ,mai yasa baka jin magana “kiyi hakuri heartbeat wani abokina bello ne bashi da lafiya shine gabday nida sauran abokanmu mukaje dubasa to kuma babu wanda zai kwana awurinsa shine nida atiku muka tsaya” okay ! ta fad’a tana sakin fuska “gsky wannan abu ne mai kyau nasan dole zaka rama bacci da ganin idanunka bacci bai isheka ba, dan allah ka dinga kiyayewa karka daukowa mahaifiyarmu magana ka dai ga yanayinmu dan Allah ka rufa mana asiri karka bari abokai su koya maka shaye shaye ,domin shaye shaye shine abinda mutun zai yi ya gurbata rayuwarsa dan shi da samun kwanciyar hankali har abada “in sha allahu zan dinga kiyayewa amman fa yau ma acan zan kwana babu damuwa ai taimako ne amman ka kiyaye dan Allah ,ya shiga dakin mahaifiyarsu ta sake yin mika ta shiga dakinta .



Bai samu aunty a daki ba dan haka ya fito ya nufi kitchen adaidai bakin kofa suka hadu ya gaisheta male ki dafa min indomi amman a soya” kai kuma daga ina haka amman ba gidan nan ka kwana ba ?ta fad’a tare da bin gefensa ta wuce tana rike da kular shiru yayi “a ina ka kwana ? uhmm aunty laifina ne da ban fad’a miki ba dan ya fad’a min bazai samu damar kwana a gida ba “wai a wurin abokinsa bello zai kwana a hospital maryama ta bawa mahaifiyarsu amsa tana karba kular hannunta “wai mai yasa aunty bakya bari na miki aikin komai ne byn na iya ?ai sai na sangarce naje gidan mijin na kasa yiwa mijina komai “ ai kina aiki kuma ma girki ai na safe kawai nake “babu wata matsala da zaki samu dan kin kware in dai wurin girki ne maryama tayi murmushi farinciki samu nasarar kare danuwanta da tayi “kai aunty banda yabo fa kar azo aji kunya ta fad’a tana ware idanunta “.



babu wani yabon kai ai gsky na fad’a bazanji kunya ba matukar akan girki ne kai dama komai ma “wannan gsky ne male muna alfahari dake ,nima ina alfahari daku yarana shiru sukai gbdy har habib suna tunani maryama ta dubesu yau fa a lissafina sauran sati day’a a daura min aure gashi har yanzu aunty bakiyi maganar zuwa wajen yanuwanki damu ba “kai heartbeat kina son damun kanki akan wad’an nan mutanen idan mu bamuje ba su me yasa bazasu zo nememu ba ?”kawai ki sharesu mu cigaba da rayuwarmu cikin qaddarar rayuwar iyayenmu tare da yiwa mahaifinmu addua ,muje muyi breakfast suka zauna kusan atare suka saka aunty a tsakiya sannan suka fara breakfast maryama na cin abinci taji shigowar sako wayarta ta dauka ta duba tare da yin shiru ta dafe goshinta da hannu daya ta shiga dogon tunani “ya’akayi naga kinyi shiru ina tunanin yadda zan bar gida ne na rigada na saba da danuwana ,muyi hira tare muci abinci tare muyi kuka tare muyi dariya tare in fact komai ma “gara dai kiyi aurenki shine kwanciyar hankalinmu gbdy inji cewar habib maryam ta dungure masa kai” tana cewa “kenan bazakayi missing dina ba ?” zanyi mana ni ne ma zan fi kowa kewarki amman ya zanyi tunda aure zakiyi kuma zamu dinga ganin juna a duk lokacin da muka so kinga ai banga abun damuwa ba zamuyi komai Kmr yadda muka saba ya fad’a yana kallonta komai dai menene zan fi jin kewarka sosai .”


“ karki damu heartbeat idan ma kikace mu tattara kayanmu mu dawo gidanki mu zauna tare zamuyi tunda nasan yaya sadam ba mai damuwa bane inji cewar habib wani sako ne ya sake shigowa wayarta ta duba tana gama dubawa taja tsaki” yakayi princess ya kikayi tsaki “ wani kafanin ke son nayi aiki dasu na tura masu yanayin zane na tun da dadewa to basu tashi bukatata ba sai yanzu , at the same time ga wani sako daga ogun state wai suna son naje har kamfaninsu dake ogun state nayi masu zane , ni bama zanen bane damuwata ba yadda kmr yadda date din da zaa masu zanen ya zamo date din daurin aurena bari kawai na tura masu bazan samu dama ba su kuma wad’an can zan tura masu sako nan da qarshen wata zan zo na fara aiki dasu .“ fine daidai kenan amman zuwa ogun state din ma ai ba damuwa bane ta dubi habib taya zakace ba damuwa bane ?Ko nace zanyi hankalina bazai kwanta ba ,”zaki iya zuwa Kiyi bayan an daura aure idan kin dawo sai ki cigaba da hidimar bikinki tunda abun kwana daya ne “ ni dai gsky ban yarda kije har ogun state ba aunty ta fad’a gara ki hakura idan ba haka ba bazaki samu natsuwar hidamar yin biki ba daga yau hankalinki zai rabu gida biyu shiru sukai gbdy can maryama tace “ gsky kika fad’a “ni dai ina son kike ki fad’awa yaya sadam sai ya rakaki kuje tare “okay bari zan yi masa mgn muji meye raayinsa Kiyi masa mgn idan ya amince sai kuje tare .”



Bayan kwanaki uku

Tsaye yaya sadam yake a d’akinsa muryarsa can qasa qasa yana waya da nadiya “haba nadiya nasani nasan ban miki adalci ba amman kema Kinsan yadda nake mutuwar sonki ,soyayyar shekaru biyar fa ni kad’ai nasan me nake ji ajikina tabbas nasan laifina ne da ban shigo da maganarki da wuri ba har aka zartar da wannan hukunci ,No bazan iya cewa mahaifiyata haka ba . zan dai san abun yi ki kwantar min da hankalinki ki saurareni at anytime .a natse ya fito cikin jallabiya ruwan qasa kawai yaga maryama zaune ita kad’ai a falon .”sai daya zauna sannan suka kalli juna shi da maryam gano yanayin maryama kamar tana cikin damuwa ya matsota sosai har suna iya shakar numfashi juna dan a tunaninsa ko taji wayarsa ne ahankali ya kamo yatsun hannunta wanda yasa taji wani irin zirrr a sansar jikinta nan da nan tayi qoqarin zare hannunta bai damu ba yace “lafiya na ganki haka ?daman magana nake son muyi “ina jikin me zaki fad’a min ?”amm amm daman akan wani aiki ne daaka kirani nace na fad’a maka nan dai tayi masa bayanin komai ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta “kinji abinda naji kuwa ?wani irin aiki ne har ogun state kuma a ranar daurin aurenmu ?nan da nan jikin maryama ya kama rawa “kayi hakuri bansan mgr zata bata maka rai ba na hakura ba sai naje ba na cigaba da aikina anan daman ba wai zasu d’auke bane aiki ne na lokaci zuwa lokaci kuma ba aikin kwana bane amman kayi hakuri karkayi fushi dani ta qarasa mgnr muryarta cike da rauni .”


ya kalleta cike da tausayinta sakamakon yadda take magana cikin sanyin murya da tsoro ,ita kanta a yadda take maganar tana jin babu dadi har cikin ranta “shikenan ki kwantar da hankalinki yanzu me kike ganin zamuyi ?”ya tambayeta cikin sanyin rai “tô wai idan ka amince sai muje tare da kai ,idan kuma baka amince ba wallahi babu komai na hakura allah ya zaba min abinda yafi zama alkhairi murmushi ya sakar mata yace “shikenan karki damu amaryata zamuje tare ai ni yanzu duk abinda kike so ina so ko bangon duniya kika ce zamuje tare allah ya nuna mana ranar nan da nan murmushi ya bayyana a fuskarta “amman naji dadin amincewarka wallahi baka ta’ba sakani farinciki irin na yau ba na gode sosai allah ya jikan iyayenmu Allah yasa suna aljanna Allah ya saka maka da alkhairi Allah yaja da kwanan ummah ,Allah ya bamu zaman lafiya a arayuwar aurenmu “Ameen Ameen ya Allah Allah ya nuna min kin haifa min yara masu yawa tasa hannu tana rufe fuskarta nan suka cigaba hirarsu.”


Ranar lahadi 14 ga watan October shekara ta dubu biyu da bakwai aka daura auren maryama da yayanta sadam .ana gama daurin aure suka fara shirin tafiya ogun state wanda kusan yaya sadam ne yayita matsa mata ta d’auko kayan aikinta tare suka shiga wajen ummah lokacin tana tare da yan’uwanta dana mijinta tayi masu fatan alkhairi fuskarta dauke da farinciki maryama ta zama mallakinta gabdaya lokacin da zasu wuce aunty hassna tace “yanzu dan lalacewa aunty har da murna kike tun baaje koina ba an mallake miki d’a “cak maryama ta tsaya cike da sanyin jiki “me zanyi hassana matarsa ce kuma ya amince tunda ya amince meye nawa aciki ?kunga kuyi maza ku kama hanya Allah ya tsare min ku suka sa kai zasu fice har sun kai bakin kofa umma tace “sadam ya juyo daga inda yake “ka kular min da maryama da kyau ,Allah ya tsare hanya “to ni ummah bazakice ta kular miki dani ba ?tayi murmushi shikenan “maryama ki kular min dashi Allah yayi maku albarka suka ce “ameen suka fito suka shiga mota suka d’auki hanyar ogun .”


Cikin sauri sauri ATA ya fito daga dayan bedroom dinsa cikin wasu had’ad’den kanana kaya bakake ajikinsa ,ya  shiga dayan dakinsa wanda kusan abubuwansa masu mahimanci anan suke, yadda jikinsa ke fitar da kashin turarensa reed akoda yaushe haka dakin Ke dauke da kamshin turensa, cikin sauri ya dauki farin glass dinsa   ya manna a kwayar idanunshi sannan ya qaraso ya dauki agogo baki ya daura a tsintsiyar hannunsa ya bude bedside  ya dauki  wallet dinsa ya tura cikin ajihunsa ya daura facing cup yayi mugun kyua ya fito sanyayyen kamshin turarensa na binsa cikin sauri yake taka step cikin . a zaune ya iske mami tana waya ya d’an tsaya yana kallonta dan ga dukkanin alamun da wannan yarinyar take waya gyaran murya yayi yana sham kamshi ta waigo tana dubansa “ina zuwa kuma ? wani aiki !ya bata amsa atakaice yana had’e gira sama data kasa dan kar ma tayi masa mgnr mrym “naga yau weekend ce ?eh ogun state zani zan iya dawowa a yau watakilla kuma sai gobe dan aikin nada matukar mahimanci .”yana gama fad’ar haka ya nufi kofar fita .”


To adamcy mami fatan nasara




Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login