Showing 144001 words to 147000 words out of 167047 words

Chapter 49 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

fad'a ba  ya soma qoqarin ficewa "okay sir ."



A dogon koridoor suka hadu da sultan bai  kallesa ba bare ya tsaya duk da yasan wurinsa yazo ya ra'ba ta gefensa ya wuce ,har yayi taku biyu ya jiyo sautin muryarsa " Adam...! ya kira sunansa a gadarance har yanzu kai muke jira da mahaifinmu domin muna da bukatar wani kaso daga cikin kafanuni  araba abamu namu kowa yaci gashin kansa, cak ATA  ya tsaya daga tafiyar da yake ya zura hannunsa daya cikin ajihun wandonsa "idan naki fa ?yayi mgnr batare daya juyo ba " dole kabi umarnin mahaifinmu dan bazamu cigaba da aiki akarkashinka ba alhalin dukiyar nan gabadaya  tamu ce dan dole kayi wani abu akai .”a fusace ATA ya juyo gabadaya ya fuskancesa "kasani wannan dukiyar gabadayanta ta mahaifina ce kamar yadda na fad'awa mahaifinka yau da rokona kukayi zan iya daukar wani bangare na bawa mahaifinku amman tunda zalinci ne abun bazan bada ba kamar yadda na fad'a kuma  zan iya dakatar da duk wani mai numfashi dake d’akinku wanda yake karkashin ma'aikatar nan idan kace karya ne ka cigaba da shiga track dina "shiru ne ya biyo baya"kafin ahankali ata ya wucesa yana jan tsaki tare da furta "nonsense."


*****

Zaune ata yake akan kujera sanye da suit baki yana jujjuya jikinsa bayan ya watsawa chief adisa tambayoyi cikin 'bacin rai ,cheif adisa yayi shiru yana nazarin abinda zai fad'a masa "answer me !ya furta cikin tsananin bacin rai mara misaltuwa "komai zance yanzu bashi da wani amfani sir tunda  na rigada nayiwa sectary dinka bayani komai "Eh nasani but ina son naji daga bakinka ,yayi maganr yana gyara zama tare da daddana system din gabansa  batare daya dago kanshi ba , dalilin dayasa muka daina amsar produc din  design dinku sunyi matukar tsaida ne,dan alal hakikanin gsky kudin daaka sa sunyi yawa yayinda muke samun exactly irin design din a wasu wurare akan farashi mai sauki atakaice dai wannan shine dalili."
shiru ata yayi byn ya gama sauraronsa ya cigaba da tura sakonni kafin daga baya ya dago kanshi a hankali ya kafe cheif adisa dake  zaune a gabansa da ido yana qare masa kallo ta cikin farin glass dinsa sai daya furzar da iska mai zafi sannan ya bude bakinsa da kyar yace "kasan abinda abu original yake nufi ? cheif adisa yayi shiru ,"wadan da kuke siya a sauran compaing's  copy din namu ne, namu kuma asalin masu kyau  ne ". ba maganr quality  ake yi ba sir maganar contitie akeyi kafa san dan kasuwa duk wani dan kasuwa yana bukatar  farashi mai sauki wanda  shine business,  da dai zaa cigaba da bamu farashin daaka saba ne sir da komai zai tafi normal ".ATA ya sauke numfashi yana jan tsaki " ko ku siya a haka ko kuma ku barshi domin bazan rage naira daya daga farashin dana saka  ba yana gama fadar haka yace "get out .cheif adisa ya mike tsaye tare da cewa "okay sir ya dauki system dinsa  ya qara gaba tsaki yayi ta ja babu kaukautawa ,ya mike tsaye ya shiga zariya acikin office dinsa yana shafa sumar kanshi.”


ATA na tsaye a parlour'n mami  ya zuba hannunwansa duka cikin aljihun wondonsa dawowarsa  kenan daga office ko cikakken minti biyar bai yi da shigowa ba sai ga fahad   ya shigo a matukar fusace kamar an jehoshi  yana cewa "wai kai dame kake takama ne ?yayi mgnr yana nunasa  da d’an yatsantsa .""what  do you mean  ?ATA ya tmbyesa a tsawace yana watsa masa harara  a lokacin da hjy zulai ke qoqarin saukowa daga saman ata   "bani zaka tmby ba kamata yayi ka tmbyi dakikiyar kwakwaluwarka ,  taya ma zaka yanke wannan banza hukunci haka?"lafiya fahad ! ?  " mami ta tambayesa cikin rawar jiki “wannan yaron ne mana yake son  jawowa mutane asara  ,yana yin abu tamkar  shi kadai yafi kowa waye wa da ilimi
yau ko kamfanin ba group bane ai bai cancanta yayi  haka ba bare yasan wannan kafanin ba nasa bane shi kadai .ya qarasa mgnr yana kallon ATA a fusace .


Suna cikin haka sai ga yaya Ibrahim shima cikin tashin hankali ya rufesa da fad'a nan mami ta koma kansa "ki duba ki gani mami  yadda farashin komai  na kaya ya sauko daga sauran kamfanoni amman shi  tashi daya ya qara  farashi nikin baninkin gashi costumers sunki karba kaya  daga hannun kowa "very good ."ata ya furta yana hura hanci “What ?
" I said very good ,"ya sake maimaitawa a natse tmkr maganar ba daga bakinsa ta fito ba “very good ma zaka fad'a saboda baka da hankali da tunani "yes of course it good and to be your last warning da zaka kirani da mara hankali ."yaya Ibrahim bai damu da abinda ya fad’a ba yace “me yasa zakayi haka adamcy ?” me yasa zaka bata kasuwancinmu maganar gsky muddin haka zaa cigaba da tafiyar da kamfanin gara kowa ya watse a rufe kamfani kowa ya kama gabansa "okay wannan shine daman shirina ai a rufe kowa ya kama gabansa "Ibrahim da fahad suka kallesa a rude suna mai mamakin jin abinda ya fad'a " yes haka nake so "okay saboda  kasan kana da wasu compaines masu zaman kanka shiyasa kake son a rufe  wannan ?"yayi kyau yayi kyau gara daka fad'a mana muka sani ."ai daman mugunta ne acikin cikin wannan mugun mai girman kan , kai ne dai ka kasa ganewa kake daukarsa amatsayin mutumin kirki ai ga irinta nan zai janyo kowa ya rasa saboda tsabar bakinciki irin nasa da dai a rufe gara a siyar a bawa kowa hakinsa "inji cewar fahad .


Dan allah  fahad ka samu natsuwa kai ma Ibrahim ka natsu kar wannan abu ya zama damuwa " karki damu mami  ba  wani abu bane ai bazamu biye masa ba  zanyi komai domin naga business din ya tsaya da kafafunsa "ko kuma a siyar ba nifa gara a siyar dashi inji cewar fahad "wannan kuma karya ka fad'a  dan matsawar ina raye babu wanda ya isa ya siyar da AGC "mu zuba mu da kai dan halak ka fasa yadda kake ji da  taurin kai muma muna ji dashi a qarshe zan maka gargadi ka rage wannan  zakewar da jijji da kai idan ba haka ba wallahi zaka rasa rayuwarka a banza kuma babu abinda zaayi "yana gama fad'ar haka ya juya fuuuuu ya fice  har zai bi bayansa mami ta sha gabansa da sauri tare da ware hannuwanta “karka kuskura kabi bayansa ,kana jin mutun yana ikirarin zai kasheka ya kashe banza shine zaka bi bayansa “sweetheart ki barni babu abinda zai iya yi “wallahi bazan barka ba idan kai baka son rayuwarka ni ina da buqatar ka a raye ,oya koma can ka tsaya ko ka wuce d’akinka, tsayawa ya kasa furta komai yana cin ransa .”



yaya Ibrahim yace" idan har baka bari an sauko da komai ba ina tabbatar maka gobe goben nan zan bar aiki a kamfanin ."so what idan ka bar aiki ? ya kallosa a fusace yana huci ,ka sani ni  kasuwancina ba kamar na kowa bane kuma nasan kan business dina kuma babu wanda ya isa acikinku ya janye daga hukuncina "enough adam  ya fad'a a tsawa ce shima tmkr zai maresa shima AD yayi kusa dashi sosai yana zaro masa idanuwanshi da suka gama canza kala tsabar bacin rai "ka sausauta muryarka akaina Ibrahim " idan ba haka ba me zakayi ? "Zan... zan canza maka kamani  yanzu ya fad'a yana huci kamar zaki .shima sai da mami ta shiga tsakaninsu "wallahi  adam ka raina ne  kana magana dani kamr bakasan tazzrar dake tsakaninmu ba, kai duk abinda yazo bakinka kake fad'awa  mutane da wadan da suka girme maka da saaninka "adam ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa yana hura masa hancin "dan allah ku daina fad'a akan dan wannan matsalar duk ku kwantar da hankalinku komai zai daidaita kai adamcy wuce d'aki .


naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana furzar da iska acikinsa sannan yayi wani juyi ya hau step da sauri sauri yake taka step yana cewa "babu wanda ya isa ya canza tsarina shi kuma wancan d'an iskan zai gane kurensa har ni zai yiwa barazana da mutuwa ? bayansa suka bi da kallo har da suka daina hangosa sannan yaya Ibrahim ya kalli mami "dan allah mami kiyi masa magana nasan ke kadai zaki fad'a masa yaji mutane bila adadin ne suka dogara da wannan kamfanin me yasa zai yi qari ? ban san me yasa  zuciyar adam bata da tausayi ba wallahi idan bai sauke  raayinsa ba akan wannan matsalar am sorry to say mami zamu samu babbar matsala dashi ."
Mami  ta riko hannusa ta qarasa dashi kan kujera ta zaunar dashi taje ta dibo ruwa mai sanyi a glas cup ta dawo ta mika masa " sha ruwa Ibrahim ka samu natsuwa  " bai yi mata mutsu ba dan yana bukatar ruwan ya karba ya sha kadan ya mika mata cup  yana sauke numfashi "kayi hakuri  kaji ibrahim ka bar komai a hannuna kamar yadda kace maganata  kawai yake ji ,zai ji da izinin allah duk yadda kuke so zaayi ya sauke  numfashi yana cewa "na gode sosai   mami  allah saka miki da alkhairi dan allah kiyi kokari ki sauko da adam nasan yayi  haka ne da wata manufa amman ya duba mutane dake amfana da ma'aikatan ba wadan da suka bata masa rai ba in sha allahu zai ji kuma zaka ga canji " allah yasa ya fad'a tare da mikewa  ya  rusunawa yayi   mata sallama ."


tsaye  yake a d'akinsa yana faman zariya yana cika yana batsewa "har ni fahad zai wa barazana da mutuwa ?daga yanzu bazan cigaba da daukar wulakancinsu ba a hankali yake magana yana balbale botiran gaban rigarsa ya cilla rigar a saman gado ya saki numfashi da karfi tare da kwance agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yayi taku biyu ya ajiye a inda ya saba ajiyewa.jkinsa na tsuma  ya tsura wa mirrow idanunshi yana kallon kansa gabadaya sai yake jin rashin dadin abinda yayi sam sam bai kyauta ba kuma ya tabbatar da maganar Ibrahim gaskiya ne mutanen da zasu shiga damuwa idan mummunar abu ya samu  da kanfani suna dayawa amman bazai ta'ba daga wa kowa kafa ba ya furta a fili yana jan tsaki ya juyo ya fad'a kan katifa "
Mami ta hada abinci a qaramin tire kamar yadda ta saba dan abinci idan ba daga hannunta bane baya ci saboda tsoro abinda zai cutar da rayuwarsa a natse  ta nufi  kofar parlour'nsa ta wuce bedroom dinsa  ta shiga yana kwance flat akan gado ya daura hannuwansa duka à faffadan qirjinsa ."



Ta ajiye tiren abincin akan wani qaramin table wanda daman dan cin abinci aka tanadeshi ya mike a hankali daga kwanciyar da yayi ya zauna ya hade hannunwansa wuri daya bata tace   masa komai ba kamar yadda shima bai ce mata komai ba ta dauki plet da spoon din abinci data shigo dashi ta kai bakinsa ahankali ya dinga amsa yana ci har sai data fahimci ya koshi ta ajiye sauran ta sakar masa murmushin farinciki tare da kamo hannunsa cikin nata kafin tayi magana ya motsa labbansa ahankali "na gode sosai sweetheart allah ya bar min ke "ameen adamcy nah kai ma allah ya bar min kai bata nemi tayi  masa mgn  akan lamarinsa dasu Ibrahim ba ta barshi har ya dan sauko hira ta soma janshi ."Ahankali ahankali ya dinga biye mata suka shiga hira ta tsakanin uwa da d'a a qarshe ta shigo masa da maganar .”ka zama mai hakuri da yanuwanka adamcy dan baka da kamarsu sannan ka zama mai tausayi domin kai ma kana buqatar tausayawar ubangijinka , akwai mutanen da kamfaninku suke ci suke sha suke komai na rayuwarsu ka duba allah da ire iren su ka sauko da komai sai kayi tawassali da aikin alkhairin da kayi ka roki Allah wata buqata kaga yadda Allah bazai maka ba “babu abinda nake buqata sweetheart kamar mafarkina ina tsananin son kasancewa daita “ya fad’a acikin ransa.”mami ta dade tare dashi har sai data ga bacci na qoqarin daukarsa sannan ta barshi ta shafa sumar kansa.”


tana tsananin son danta bata qaunar abinda zai kawo masa damuwa arayuwarsa yanzu shiyasa ma tayi qoqarin danne damuwarta akan matsalarsa da   maryam tunda yace bai so ta hakura har abada Allah ya raya abinda zasu samu  blanket ta janyo ta lullube masa rabin jikinsa ta fito daga dakin ." bacci mai dadi ata  yake yana rungume da hannunwansa cikin baccinsa ya fara mafarkinsa wanda a qalla ya kusan wata uku  bai yi ba koma yace fiyye da haka ,yarinyar daya saba gani ita ya gani sai dai wannan karon cikin mawuyacin hali ya ganta  acikin wani kungurmin daji  gashin kanta duk ya hargitse ya zubo gadon bayanta tana gudu tana ihun kiran sunansa da iyakacin karfinta cikin haka wasu mutune guda uku maza suka biyota  tana gudu suna binta har sai dai ta bace masu amman ita bata daina gudu acikin dajin  ba juya ne ya soma dibanta kanta ya soma juyawa tana kokarin zubewa kasa  sai gashi ya qaraso gareta ya tarota  da hannuwansa duka sukai zube kasa tare ." lumtsatsun idanunshi ya tsura mata yana kallonta yana kiranta da sunan da yake kiranta dashi dan tuni numfashinta ya dauke ganin halin da take ciki yasa hankalinsa yayi mugun tashi ya kamo hannunta yana murza tafin hannunta cikin sauri amman still bata tashi ba hakan yasa ya hade bakinsu waje d’aya ya fara tsotsa yana sake hade hannuwansu  ya cigaba da murzawa ."


Yana shan  bakinta hankalinsa na tashi dan jijiyarsa  tuni ya tashi, ahankali numfashi ta ya dawo ta soma bude idanunta har ta budesu akanshi still bakinsu na hade ya kasa cire bakinsa cikin nata ,hannuta ta kai ta shafa gashin dake kwance a fuskarsa wanda hakan yasa ya zare bakinsa a nata yana dubanta .ahankali idanunshi suka sauka akan  tudun brest dinta nan take yaji shaawarta ta kamashi ya rungumeta ajikinsa tsam ajikinsa yana shafa bayanta naunayen ajiyar zuciya ya sauke Jin yadda jikinta ya dauki zafi gbdy jikinta yayi sanyi ya sake "su waye wadan nan  mutanen dake binki ?shiru tayi babu amsa "me kika yi masu suke binki ?shima shiru tayi masa  ya zareta ajikinsa ya tsura mata ido ina ne gidanku ?sai lokacin ta motsa jikinta ta nuna masa wani doguwar  hanya ya mike daita rungume ajikinsa da hannunta ta dinga nuna masa hanya har suka qaraso wani gida mai get kai tsaye suka  shiga da gudu yaga wata mata tayo kansu tana kuka , tasa hannu ta karbeta a hannunsa ta kwantar daita ajikinta yana qoqarin bude bakinsa yaji "allahu akbar !! Kiran sallahr daaka kwalla daga masalacin gidansu ne ya farkar dashi  agigice ya mike ya zauna a tsakiyar gadonsa gbdy zufa ne ke tsiyaya ajikinsa gabansa sai faman bugawa yake ,jijiyarsa yaji ya harba da sauri yabi jikinsa da kallo yadda gabansa ya tashi sosai gbdy ruwan shaawa ya jika masa qaramin wondonsa  nan take ya dauke idanushi dan ba wannan bane damuwarsa halin daya ga princess dinsa ne ya damesa ko a wani hali take ciki "oh my god a ina zangaki princess ?ya jima zaune yana tunani har lokacin sallah yyi ya sauko ya shiga bayi ."


Da misalin karfe goma na safiya yana zaune ya dan jingina jikinsa akan wani karamin table a dakinsa yana tunani mafarkinsa na  jiya bai ta'ba mafarki mara dadi akanta ba sai jiya "ina jin sonki sosai princess ko a wani hali kike "wacece wannan? yaji sautin muryar mahaifiyarsa da sauri ya dawo haiyacinsa yace "ba kowa ! ya bata amsa Kmr zaiyi kuka  "karka ce haka adamcy na shigo dakin nan kayi zurfi cikin tunani ta qarasa mgnr tare nufar inda wordrobe dinsa yake ta ajiye masa kayansa ta dawo kusa dashi" kana damun rayuwarka dayawa adam numfashi ya sauke yace " sweetheart bazaki fahimci halin da nake ciki ba  ta sauke numfashi tare da dafa kafafansa" fad'a min naji zan fahimceka shiru yayi yana tunanin abinda zaice mata , ganinsa  ko ya fad'a mata shirme zata dauki maganarsa kamar yadda ta saba kawai gara yace mata babu komai ya hutar da rayuwarsa muryarsa a sanyaye yace babu abinda ke damuna numfashi ta sauke "bazaka iya boyewa mahaifiyar komai dake damunka ba fad'a min me kake tunani ?shiru yayi yayinda abinda ya gani a mafarkinsa yana sake dawo masa kamar a zahiri ."



"sweetheart !
Sai kuma yayi shiru yana girgiza kai kana kallonsa kasan yana cikin damuwa "ya kayi shiru ina jinka ka fad'a min abinda ke damunka adamcy fuskar yarinyar ya soma gani acikin kwayar idanunshi cikin muwuyacin hali " tell me what's the matter ".dan allah sweetheart ki fahimceni akan abinda zan fad'a miki "uhm ina jinka gskiya  akwai abinda yake damuna amman akan mafarkina daman har yanzu kana mafarkinta ne “?ya d’aga idanunshi sama alamun tunani sannan ya saukesu akanta “na dan jima ban ganta ba sai jiya na ganta cikin mawuyacin hali wanda yasani shiga damuwa sosai nan ya shiga fada mata irin abinda ya gani duk sanda nayi mafarkinta tana min murmushi tana min magana cikin sanyin murya sweetheart intakaice miki tana min komai amman jiya duk babu sai tarin tashin hankali.”


shiru sukai gbdy byn second biyar ya motsa labbansa " sweetheart zan dage da yi mata addua allah yasa ba wani abu ne ya faru daita ba "Ameen !"ya tsinci muryar mami  ta amsa da sauri ya kalleta "ina ma wannan yarinyar gasky ce adamcy  ?amman na sha fad'a maka mafarki ba gaskiya bane ."walalhi yarinyar nan da gsky ce da ina tabbatar maka ko ina take zan nemo maka ita ka aurenta saboda na fahimci kana tsananin  sonta "."so much sweetheart ya furta yana dafe daidai saitin zuciyarsa shiru hjy zulai tayi tana dubansa Kmr zatai masa kuka  "ya allah kasa wannan yarinyar gsky ce a duniya idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login