Showing 84001 words to 87000 words out of 167047 words

Chapter 29 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

yanzu ta fahimci girman tsoronsa da take ji ne yake sawa yake mata  wasu abubuwan ta runtse idanunta  hawayen ciki suka  sake wanke fuskarta tana jin kamar ta kashe kanta ta huta saboda muguwar tsanar da yayi mata ta rasa me ta tsare masa a rayuwa daya tsaneta haka ?."hawaye maryam ta share wasu na sake zubowa ."


Bai barta taji da bakincikin da yayi mata dabaibayi dashi ba  ya sake qara mata wata damuwar cikin wata irin murya yace  "wato ni zaki tsorata da ace banyi saurin d'aukar mataki akanki ba shikenan haka zakiyi wasa da hankalin mutane wai ke mai aljanu yanzu ina aljanun suke ? tayi shiru tana dubansa "ina son ganinsu ido da ido kuma a  yanzu ,idan basu fito a zahiri ba sai naci ubanki ."iya firgita maryam ta firgita jin abinda yake fitowa daga bakinsa kuma yadda yake kallonta sarai ta fahimci ya gane aljanun karya tayi .  Idanunta gbdy sun yi ja har fitsari ta saki batare datasani ba ."ja da baya ta soma tana karkarwa da kyar take fad'in "kayi hakuri nifa bansan me nayi ba "wani kallo ya d'auketa dashi "kenan baki san Kiyi karyar aljanu ba yanzu  sai dana zuba miki maruka kika dawo haiyacinki ?jikinta da bakinta na rawa tace "wallahi allah bansan nayi karyar aljanu ba" wani kallo yayi mata mai had'e da harara "na rantse maka da Allah ban san nayi ba "shiiiii ! ya furta a kasalance."


Nan take tasa hannu ta rufe bakinta idanuta sunyi zuru zuru kamar yace "arr ta zunduma a guje "kafeta yayi da ido yayinda zuciyarsa ke tafasa yace "woww gsky wannan yarinyar kin qaro iskanci mai upgrade ya kai hannu zai damko hannunta tayi saurin zamewa tana ja baya da sauri dan tasan bazai mata da kyau ba muddin ta shiga hannunsa  duk ta rud'e sai hawaye take tana fitar da zufa "tsaki yaketa yi yana kallonta dan dole sai ya gano gaskiyar data boye ,yayinda duk jikin maryam kyar yake tana yarfe masa hannu duk kwaliyar data 'bata tsawon lokacin akanta ruwan hawaye ya wanketa cikin kuka tace "gabad'aya ban fahimci inda maganarta ta dosa ba "ni dai nasan na sauko naga kana cire takalmanka ka tashi ka nufoni bayan haka ni  bansan komai akan maganar aljanu ba ."



juyawa yayi yaje ya kulle kofar shigowa sannan ya dawo ya tsaya yace  "banason jin komai kawai aljanun nake buqatar gani kuma a yanzu maryam ta durkushe qasa "ta ina zan fara yaya dan girman allah kayi hakuri ka bar zuciyata haka karka qara min wani sabon tashin hankali akan wanda nike ciki "you are very stupid I mean ina son ki sake wannan acting din aljanu kuma a yanzu" maryam na kuka tana rokonsa "okay tunda baza kiyi ba kiyi  frog jump kuma zanyi bincike mai karfi idan na gano baki da aljanu na karya kikayi kin mutu "okay naji amman na manta yaake frog jump ." wani mari ya kai mata yace "bismillah start   !maryam ta kama kunne kawai "kina hauka ne frog jump nace  kiyi kuma wannan shine karoki na farko da karshe da zaki sake acting aljanu acikin  gidan nan ko da kuwa da gaske kina dashi ki fad'a masu mijin da'aka masa dole ya aurenki yafi su hauka ."


"Allah yaya adam ka yarda dani ban san nayi maka  haka ba ,zata cigaba da rantse rantse ya dakatar daita yace "karki qara kiran sunana idan ba haka ba zan mugun baki mamaki ,kuma dan allah naji kin sanarwa sweetheart ko wani a gida abinda nake miki kad'an ne wanda zan miki sai yafi shi ,maryam na kuka tana frog jump sai daya balain bata wahala jikinta rawa ko ina na mata ciwo sannan yace "leave this place?aikuwa da mugun sauri ta suri jakarta tayi sama ta shige d'akinta tare da kulle kofar, ta shiga sheshekar kuka  har da rike kai  tana "wayyo allah na shiga ukuna wannan wace irin maseefa ce ? "wallahi na gaji ta jima tana kuka tukun tayi shiru ta zuba tagumi tana tunani  mafuta dan zuwa yanzu ya dace tasan inda Ke mata ciwo tayi shiru tana tunani " kuma fa da fari yaya adam  yaji tsoro acting dinta  wannan marin da yayi mata ne  bai kyauta mata  ba if not da tayi  galaba akansa  yama akayi ya gane ba aljanun gaske bane ?"


"oh my god wallahi yadda ya tsorata da farko abun yayi mata dadi ,ta d'an saki dariya ta nufi gado ta jingina tana shafa kuncinta  daya d'an tashi tana ciza lip's dinta "da'ace allah ya taimaketa da wata killa shikenan ta dan samu sausauci daga garesa, ya allah ka kawo min mafuta duk yadda ta dauko shirinta sai ya wargaza ga tukunyar maganin ma  haka ya gama kwanakisa sai jiya ta shiga ta ciro daga karkashin gadonsa yanzu kuma tayi iskan karya ya gane anya kuwa yaya adam mutun ne kamar sauran mutane ?wai sai yaga aljani ido da ido ko idan yaga aljani zai tsaya  ."?ina ma  tana da aljanun gaske su gyara masa zama, mugu kawai bancin son da take maka wallahi da tuni ta tattara ta gudu ta barsa . tana zaune wayarta ta soma ringing ko baa fad'a mata ba tasan sister ce tana dauka tace "sister kinji shiru ko ?ai babu maganar fita nan ta koro mata komai nan take nana hauwa'u tashiga kyalkyata dariya har da rike ciki "haba sister ina fad'a miki wahalar dana sha amamn zaki bige da min dariya haka ."


bangaren nana hauwa'u tace "wallahi sister na tausaya miki kawai karyar aljanu ne ya bani dariya ai yaya adam sam bashi da tsoro lokacin yana bording school shike zane masu aljanu da kin fad'a min zakiyi karyar aljanu  wallahi bazan goyi bayan Kiyi ba dan bazaki ga duro ba wahala zaki sha kawai a banza .kuma fa wallahi komai ya tafi min daidai gigitaccen marin da yayi min ne ya 'bata komai "karki sake ganganci nan allah ya rabamu da lamarin aljanu ,ameen yace zai yi bincike dan Allah ko ya kiraki kice da gaske ne ina dasu  "kai bazan daura miki wannan lalurar ba .Kiyiwa girman allah ki rufa min asiri idan ba haka ba  na tattara na gudu tun dare bai min ba ."nana hauwa'u ta sake kyalkyalewa da dariya tana cewa "dan girman allah ki rage tsoransa kema fa ya kamata ki kai masa ziyara "ziyara kamar wani irin ziyara kenan kike nufi ?."



"haba maryam yanzu  sai na tsaya na  koya miki "menene amfanin social media din da kike yi ?group's gareki fa  sunfi ashirin da wani abu sannan ina karatun novels din da kike? uhm maryam ta sauke numfashi da ajiyar zuciya tana cewa " nifa wallahi yayanki tsorata yake, ko nayi niyya yi wani abu  sai tsoransa ya shigeni na fasa .da dabara zaki dinga shige masa kawai Kiyi qoqarin kisan weekpoint dinsa bazai ki ba "sister nasan duk wani week point din nmj ,kunnuwansa nipples dinsa sumar kanshi uwa uba jijiyarsu amman yayanki  baya yarda na ra'bi inda yake bai ma son ya bud'e idanu ya gani bare a kusa dashi ai shiyasa nake fad'a miki yaya hisham mutumin kirki ne ,wallahi sister kin samu miji a yadda kuke gudanar da rayuwarku yanzu bana jin zai auri nuzla .ke babu ruwanki da sheidar nmj na fad'a miki duk nmj dake da mata da buduruwa a waje baki biyu garesu idan ma zai aureta suje can su qarata ni dai a kwantar min da hankali abinda zan fad'a miki Kiyi qoqarin ki rage tsoransa kinji sun jima suna waya kafin sukai sallama ."


Bayan kwana biyu  suna cikin waya da nana hauwa'u taji yana buga kofar d'akin da karfi da sauri tace "sister gashi nan yana buga kofa  ina zuwa ,ta ajiye wayar batare data kashe ba, ta mike tsaye tun kafin ta isa bakin kofar taji yana cewa "gidan ubanki ne da zaki dinga kulle kofa ?maryam najin abinda ya fad'a tayi hanzarin ta bud'e masa kofa tana "cewa duk abinda zakayi yaya adam kayi kuma ya tsaya a iya kaina kawai  amman zagin iyaye bazan sake d'auka ba ATA najin abinda ta fad'a ya gyara tsayuwarsa da kyau abun ya mugun girgizasa  ganin yadda yake kallonta ta juya ta shige cikin d'akin tana cewa "ka zageni kaci zarafina ni naji na gani zan d'auka amman iyaye please kayi qoqarin ka daina sakosu ."ai ko babu komai dady mahaifi ne gareka idan bakayi masa addua ba ai kuma bai cancanci zagi ba  ta fad'a tana rungume hannuwanta duka a qirji ."


A wulakance ya d'auki kallonta daga qasa har sama kafin a hankali  ya shigo har cikin d'akin ya tsaya  yana  kallon yatsun kafafuwansa a hankali ya motsa lip's dinsa "say what you said again ina son tabbatar da najiki da kyau tayi shiru taki cewa komai "gidan nan ba gidan ubanki bane ba kuma da kudin ubanki na gidana shi ba na maimaita abinda na fad'a ina son kema idan kin isa ki maimata abinda kika fad'a yanzu ." ya fad'a mata haka  kai tsaye kamar bashi ba "daman baa sonki   ko digon d'aya baki da matsayi acikin nan ya nuna daidai saitin zuciyarsa da yatsan hannunsa "baa sonki amman kike qoqarin shigo da wani salo rashin kunya to zaki sha wahala akan wahala dan ko ina sonki bazan d'auka  ba bare babu d'igo  sonki acikin nan.ina dai  zaune   dake darajan iyaye ,rayuwar mahaifiyata ke rike da aurenki yau ta fad'i ta mutu kisani aurenki dani ya qare dan rabuwa zanyi dake da huta ."


"yanzu mami na mutuwa zaka rabu dani "?yes of course zaman me zan cigaba da yi dake zan rabu da kwallon mangaro na huta da kuda ,baki san kin  zame min qaya bane  ? ta runtse idanunta she's so much in love with him amman shi kullum tunaninsa  yadda zai rabu  daita , "dan allah meye ribar ka yaya adam da baka son  yiwa mami biyayya   ?ta tambayesa muryarta cike da rauni "ai duk akanki ne na kasa wannan biyayyar kinga kuwa bazan ta'ba sonki ba har na koma ga allah" bazakayi mata biyayya bayan ranta ba "ubanki zanyi ba biyayya bayan rai ba "ya fad'a a zafafe  yana jan tsaki yare da  dafe goshinsa can kuma yace "me keyn d'akina yake ajikin keyn kitchen?tayi shiru tana dubansa a matukar tsorace "me keyn d'akina yake ajikin keyn kitchen?" ya sake maimaitawa  a karo na biyu hankalin maryam ya tashi  sosai ta masa baya da sauri tun kafin ya sauke mata mari ".


"don't let me rept my self wallahi idan baki fad'a min abinda yasa yazo hannunki ba zan baki mamaki yanzu .maryam ta sake tsorata dan tasan zai iya aikata komai tunda ya rantse muryarta na rawa "tace daman saboda na dinga gyara maka d'akin ne "na buqaci haka daga gareki ?"a'a kawai dai ni naga dacewar haka ne shiyasa "tunda nayi tafiya kina sharewa ?tace "eh ina sharewa "kina sharewa amman kuma naji d'akin yana warin mushe ya d'ago yana kallonta tsab  yana nazarinta  "dan allah dan annabi dan darajan iyayenka karka min komai  ta fad'a haka ne saboda kusancin da suka samu komai zai iya faruwa.tunda ya tsura mata tsumammun idanunshi bai sake cewa uhm bare uhm uhm  ba sai dai kana kallonsa zaka fahimci ya gaji da damuwarta
"Dan girma allah Ke wace irin halitta ce ?duk abinda mutun bai so shi kike yi ni wallahi na gaji dake dan hannuna ya gaji da ta'ba jikinki."


"Kayi hakuri nima jikina ya gaji da duka da mari
"To zaman me kike yi ?"ai  sai kin bar gidan  kuma bari na har abada  ba sai kin qara dawowa cikinsa nonsense kawai "yana gama fadar haka ya juya fuuuuuuu naunayen ajiyaar zuciya ta sauke kuma sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta  safa da marwa ta soma kafin ahankali ta tsaya a tsakiyar dakin ta hade hannuwanta duka guri daya bata ta'ba shiga tashin hankali da nadama irin wannan ba, domin har ga allah ta gaji da zama dashi amman kuma zuciyarta na kanshi  sonshi bai ragu acikin zuciyarta ba wayarta ta d'auka nan taga ashe  har lokacin nana hauwa'u na kan layi ta sauke ajiyar zuciya tare da furzar da zazzafar iskan daga bakinta muryarta a sanyaye  tace "sister Kiyi hakuri ashe ban kashe wayar ba kema kuma baki kashe ba "tausayinta ya kamata nana hauwa'u "har zuwa yaushe ne  zaki fita daga cikin wannan matsalar."


" wannann tsana tayi yawa zuciyata karon kanta ta gaji da ganin halin da kike ciki na fahimci qiyayyar yaya mai karfi ce akanki ya kamata mami ta dauki mataki mai karfi a kansa" yanzu sister me kika ga  zanyi domin kawowa kaina sauki "maryam ta tambayeta "son da kikewa yaya yayi yawa gashi kuma baya samar min da kwanyar hankali  ?"bari dai yau na  kira yaya da kaina nayi masa magana ya sausauta miki maryam wacce idanunta suka cika da ruwan hawaye tayi saurin cewa "a'a sister  karki masa magana "dan me yasa zaki ce aa?"kinsan halinsa  yanzu zai dauka kararsa na kawo tsaki taja tayi discounting din kiran  da kukan nana hauwa'u ta kirasa "a zaune  yake yana kallon labarai amman bai sanda ya mike tsaye ba "a'a auta lafiya kike wannan uban kukan ?"me hisham yayi miki auta?"


Cikin kuka  tace "haba yaya me yasa kake wa maryam haka ?au qarata ta kawo miki ko me ?sam sam bata kawo qararka ba, nan dai tayi masa bayani yadda akayi taji "dogon tsaki yaja " ke bazaki gane wannan yarinyar muguwa bace sannan makarya ce gata da siffar munafukai gabad'aya alamunta na rashin gsky ne, nifa ban ta'ba ganin makirar yarinyar kamarta ba ga taka min dokoki da take  "Allah yaya sister nada kirki kuma tana sonka "kinga auta ajiye maganar so wannan yarinya muguwa ce na fad'a miki "wallahi yaya zuciyar maryam a wanke take akanka ,haduwar aurenku daita baku kuka tsara ba allah ne  dan yaya adam kayi hakuri da yadda qaddararka tazo ,sannan sister bazata taka  duk wasu dokokinka ba tana da gudun zuciya gashi ita din mai biyayya ce . Kayi mata sausauci dani ina son naganta cikin farinciki kamar yadda na kasance a yanzu , bata ragewa ATA komai ba akan canjin rayuwar daya kawo a gidan aurenta a sanadiyar matakin da yayi qoqarin dauka akan hisham "


"to yaya ya kake tunani idan maryam tana da yaya ?shima zai dauki mataki kwatankwacin irin wanda ka dauka akaina amman sai ya kasance sister bata dashi  bata da kowa sai allah da kai ,nayi imani yaya a yadda kake son yanuwanka ko wani kaga yayi mata haka sai inda karfinta ya qare dan allah ka sausata mata sister na sonka fiyye da soyayyar kowa da zaka bata dama zakaji dadin rayuwa daita" ata ya kalli tv yana jin haushin maganarta amman dan ya kawo karshen zance yace "naji sai anjima kafin tace wani abu ya katse wayar  yana jan tsaki ko ana soyayya dole tunda nace bana yi a rabu dani mana bata ga wahala bane da qafafuwanta zata arce na huta da jaraba   idan taki  km zan san yadda zan batar daita a nemita a rasa haba wannan naci da maseefa ya isheni kowa maryam idan aunty sajida ta kira maganar kenan maryam duk yan'uwansa  maryam dai maryam shi ko Oho babu wanda ya damu da damuwarsa ."



Bayan kwana biyu maryam ta d'an samu natsuwa sakamakon baya shiga lamarinta sabgar gabansa kawai yake sai dai ita tana iyakar qoqarin na bashi duk wata kulawa idan yana gida kullum kafin ya fita aiki zata kula dashi idan ya dawo ma haka wasu ayyukan yace bai so wasu kuma miskilanci ya hanashi magana sai dai yayita cika yana batsewa.
Yadda take kula dashi  ita bata isa ya nuna mata kulawa ko tausayawa ba idan kaga annuri a fuskarsa to baki yayi  amman ita ko oho kuma rashin mutuncinsa agaban kowa yake yi  wannnan yanayi yana sakata cikin tsananin damuwa sai ta zauna tayita kuka saboda tausayawa rayuwarta idan babu mami a raye tayi imani ko bai rabu daita  kamar yadda ya furta ba allah babu mai kwatarta a hannunsa ."



Ranar lahadi tana  parlour'n kasa tana wanke bocxer dinsa da singles tana tunanin  karshe ma yazo yace me yasa tayi dan bai san ta cire acikin kayan wankinsa ba  mami ta shigo bakinta dauke da sallama ,maryam bata san ta shigo ba har sai data maimaita sallamar sannan tayi firgigib ta dawo haiyacinta tana cewa "waalaikumussalam ta cire hannunta daga cikin boket ta dauraye ta fito tana cewa "a'a mami sannu da zuwa "mami tayi murmushi tana cewa yauwa maryam ,maryam ta durkusa har kasa ta gaisheta  ina yini  mami ?lafiya maryam ya gida ta fad'a tare da zama tana qare mata kallo tsab "sannu da zuwa ta sake maimaita fad'ar haka tana murmushi mami ta kalli parlour'n komai tsaf sai kamshi ke tashi kamar yadda parlour'nta yake "ji yadda parlour'n Ke kamshi kamar yau aka kawoki "maryam tayi murmushi kawai " ina fatan dai kina lafiya komai lafiya ko ?lafiya kalau  mami ta fad'a hk dan bata son ta sake yin abinda zai sake kawo masu damuwa "karki boye min komai maryam idan akwai damuwa  ko wani abu dake faruwa tsakaninki da mijinki ki fad'a min domin nafi kowa kusanci dashi da sanin halinsa."


"Wallahi babu komai mami shikenan tunda kika ce haka daman daga gidan auta nake nace na biyo na duba ki nasan halin da kuke ciki tunda kince lafiya Allah yasa haka "Allah sarki mami ya kika baro sister ?duk da dai koda yaushe muna tare , idan bama waya waya to zaki samemu muna chart, bata gama rufe bakinta ba suka jiyo sautin muryar ATA a  can kasan makoshi yana sallama fuskarsa a hade tmkr zaki ganin mami yasa ya dan saki fuska kad'ai "sweetheart kice a gidan ?."eh nice ta bashi amsa tana kallon fuskarsa  tsam maryam ta tashi daga zaunen da take ta shiga kitchen domin samawar mami abinda zata ci ."a natse ya zauna  yana cewa "sannu da zuwa sweetheart ina yini ?"lafiya ya aiki ?"alhamdulillah yay shiru yana d'an ciza lip's dinsa na kasa batare da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login