Showing 9001 words to 12000 words out of 167047 words

Chapter 4 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

tana d'aga murya ta kwallawa mrym kira ". ATA ya yatsina fuskar sannan ya langwa'bar da kai  yace "sweetheart ki barta kawai  ki zuba min da kanki nafi son naci daga gareki dan ma banson wahalar dake ne da sabon girki zaki min ya karasa fadar maganar yana had'e rai ,mami ta dubesa ta sake yin dariya cike da jin dadi tace "Allah ya shirya min kai adamcy "
"Ameen !ya amsa yana kashe mata idonsa daya " yau kawai ka wanke min zuciya ka sanyani ciki farinciki mara misaltuwa allah yayi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya ."


byn ya gama cin abinci duk da ba wani abin kirki yaci ba "amman hakan ya yiwa sweetheart dadi, ko ba komai ya dan saki ranshi ba kmr kwanaki ba. wayarsa ce ta karade parlour da qara wanda tun soma cin abincinsa yake jin ringing dinta amma ya" share, ahankali yasa hannu ya dauki wayar yana kallon screen din wayar " sunan mb ya gani rubuce yana wayo "tabe baki yyi kana ya manna wayar a kunnenshi ."Mb najin alamun an daga wayar cike da natsuwa muryarsa babu wata alamun damuwa dan daman kuma salim ya sheida masa ya samu sauki yace" yayi angon maryam da girma kujerarka ."
ATA yaja tsaki yace" ya'akayi sarkin matsala.?


bangaren mb kuwa shekewa Yayi da dariya  sannan yace" meye abun tsaki malam ka saki jiki ka morewa angonci"enough mb !"banaso I don't like it please "shiru sukai gbdy kafin ATA ya cigaba da mgn kana ina yanzu ? "okay kazo yanzu , eh zaka iya zuwa ka jirani a waje kuma karka sake kayi min westing time dan nasan halinka da son jikin tsiya fuskar sweetheart dinsa yake kallo har sanda ya gama waya sannan yace mata shi zai fita sai ya dawo tayi masa a dawo lfy " .


mikewa yayi tsam cikin tafiyarsa ta kaisata ya nufi hanyar kofar fita ya daura hannushi kan handle din glass door mami ta kira sunansa "adamcy nah !ya juyo yana dubanta tace "kar kade fa sannan zan turo maka number mahaifiyar mrym idan  ka fita  ka kirata  ka bata hakuri  kaji bai son wani jan mgn dan hk   ya gyada mata kai  tare da cewa " love you sweetheart ya sake juyawa ya  murda kofar ya fice wani irin farinciki ya sake lullube mami tasan ba qoqarinta ba ne karfin addua ne kuma ta lura tunda ya sha tufin limamin nan ya sauya kad'an ba kamar kwanani ba ."yana fitowa masu tsaronsa duk suka mikewa zagaye dashi yana tafiya suna zagaye dashi yana masu bayanin inda zashi har ya qaraso bakin gidan baba babba dan tunda aka samu matsalar nan basu had'u ba shi."


Wasu daga cikin masu tsaronsa suka tsaya a waje wasu suka bishi zuwa ciki a babban parlour'n ya sameshi byn ya gaishesa ya zauna shi kansa baba yaji dadin ganinsa kuma hankalinsa ya kwanta yayi masa nasiha akan zama da iyali da kuma hakuri da rayuwar duniya sun dan jima suna tautaunawa ATA yayi masa mgnr nuzla "ku rabu da yarinyar nan ,na ma fadawa kowa su cireta aransu tunda ta zabi wannan  rayuwar kenan bata da bukatarmu "bazaa yi haka ba hakuri dai zakayi baba in sha allahu zaa san abunyi "karka ta'ba kudinka adamu akan nuzla tunda ita da kanta ta zabarwa kanta haka ni da zaka maida hankali akan hindu ma sai nafi dadi ."


ATA bai boye baba babba komai ba akan hindu abubuwan da suka rincabe ne yasa ban nemi naji yadda ake ciki ba kuma duk kwanaki nan wayoyina a kashe suke nasan da zasu nemeni  amman dai idan abubuwa sukai sauki zan kira naji yaake ciki dan dole nasan hindu taje prison domin zargi sun tattaru akanta " Allah ya kyauta ya shige mana gaba yaran yanzu ne ka haifesu baka haifi halinsu ba allah ya shirya mana gbdy kiran mb ne yasa yayiwa baba babba sallama ya mike ya fito tsaye ya iske Mb shi kadai jingine da jikin motarsa hannuwansa rungume da kirjinsa  ya mikawa ata hannu suka gaisa ."

daya daga cikin motocin ATA yansanda masu farin kaya suka bud'e masu suka shiga yansanda dss suka soma yin gaba sannna motar da ata yake ciki wasu motoci guda uku abayansu suka fice daga cikin gidan sai da suka hau titi sosai sannan mb ya waigo ya tmbyesa "wai ina muka nufa ne ? gidana dake ikoyi "me zakayi a ikoyi by this time kai da baka da lafiya ?"me ya sameni?ya fad'a yana jiransa da wani irin kallo kai ma kasan baka da lfy amman dai yanzu naga alamun ka samu sauki "tsaki yaja yana qarawa ."

"fad'a min abinda zakayi a ikoyi dan yamma tayi kasan wannan hanyar babu sauki sai na kira madam na sheida mata karta ga na dade ban dawo ba ta dauka ko wani abu ne wani tsaki ata yaja "ku dinga jin tsoron mata kamar su suka kawoku duniya ni yanzu akwai macen da zan tsaya fadawa inda zani da dalilin jimawata a waje ?"never babu ita wannan macen a duniya ."Mb yayi murmushi kawai "bazan ce komai akan wannan ba saboda baka zauna da mace kasan dadinta ba sannan baka da wani experience na zaman aure zamuyi wannan maganar amman sai anan gaba idan ka zama cikakken mai gida ."


wani tsaki ya sake ja tare da kiran "nonsense sau kuyita yi tunda kun zama bayin mata kai ma zaka zama bawan mace ne muje dai zuwa ."a natse ya cigaba da motsa lip's dinsa "wani sako na gani daga m malik to nayita kiran wayarsa baa dauka ba shine naji hankalina bai kwanta ba nake son naje naji me sakon yake nufi, hakan naji sakon ya tsaya min arai ,sakon ma yayi three day's da turowa ."Allah yasa lafiya shiru kowannensu kafin daga baya suka cigaba tautaunawa wanda kusan duk akan rayuwar da ATA ya jefa kanshi ciki ne ."


suna cikin tafiya daya daga cikin wayoyin ata ta fara Ringim ya dauka ya duba sunan aunty khadija ya gani kamar ba zai dauka ba sai kuma ya dauka tare da cewa"kanwa yaaakayi fatan ba da wata matsala kika zo ba ?gsky adam kayi mugun rainani kema Kinsan shishigi kawai kikayi kika rigani zuwa duniya amman duk da haka dai kece akasana "tunda kasan da haka ai shikenan ya karfin jikin naka "daman bani da lafiya ne "baka dashi mana amman yanzu na fahimci ka samu lafiya yanzu daman na kira ne akan abinda kayiwa ummu habiba wacece haka kuma "bangane wacece haka ba ?ummu habiba din ce bakasani ba?"

"kiyi maganarki kai tsaye dan bangane ko wacece ba shi yasa nace haka "to mahaifiyar maryam "tsaki yaja yana sauke numfashi sai lokacin ya tuna mami tace ya  kira "Adamcy ya dace ka kira mahaifiyar maryam ka bata hakuri ."akan wani dalili kenan ?" akan abinda kayi mata mana "ni bansan nayi komai ba" idan kayi haka baka kyauta ba dan gsky abinda kayi yayi tsauri dayawa amman zan ari bakinka naci maka Albasa" ni dai ban sakaki ba idan zakiyi Kiyi da sunanki karki yi da sunana yana gama fadar haka ya katse kiran ."mb ya dan waiga ya kallesa "kai mai yasa baka son gsky?" ka bada hakuri shine zai zama wani aiki "amman kai zaka bawa wani labarin halina bazan ta'ba bada hakuri ba ."

"amman ita wannan ai tmkr mahaifiyace adam yadda zaka girmama mami hk zaka girmamata "wannan  raayinka kenan .
"dole fa ka sauya yanzu bazai yuwu ka dinga bin raayin zuciyarka ba kana aikata ba daidai ba " dan allah malam  karka damu rayuwata raayinka dabam nawa dabam hakuri ne bazan bayar ba idan dole sai na bayar  wallahi sai  na saki yarta inga ta tsiya  " a fusace yake maganar yana kaiwa nan yaja tsaki sake girgiza kawai kai  mb yayi tare da yin shiru tafiya mai dan nisa sukayi suka qaraso bakin get din gidan  securities na ganin motocin ATA sukai saurin bude masa tafkeken get din ."


Ahankali suka shiga sukai parking a haraban gidan kusan atare suka fito cike da girmamawa suka shiga gaishesa inda yake tmbyrsu m malik nan suka sheida masa abinda ya faru babu bata lokaci ya tmbyi hospital din da yake suka fad'a masa suka koma cikin mota suka fice ."ATA ya shiga tashin hankali matuka lokacin da yake iso cikin dakin da m malik Ke kwance  yana kallonsa rai hannun Allah.abakin matarsa yake jin qarin bayanin yadda abun ya kasance hawaye na zuba daga idanunta ".

shiru kawai ata yayi zuciyarsa cike da tashin hankali" yanzu mai likitoci suka ce ?"wai sai dai a fita dashi waje ya gyada kai tare da cewa "ku shirya at any time zaku iya wuce yana gama fadar haka ya fito daga cikin dakin zuciyarsa cike da tausayawa ,matarsa ta biyosa tana masa godiya. da tunanin me m malik yake son fad'a masa ya baro hospital  sai tunaninsa ya kai ga mafarkinsa sai kuma yaji ba haka bane menene abinda zai fad'a min haka yayita aikawa kwakwaluwarsa tmby karfe takwas suka dawo gida mb ya shiga motarsa ya wuce gida shi kuma sai da yayi magariba da ishai sannan ya nufo gidan mami  ."

da kyar ata yake daga kafafunsa a  natse ya sanya hannu shi ya turo kofar falon tare da sallama akan lip's dinsa ,mrym na ganinsa ta  lumshe  idanunta  sakamakon kamshin turarensa da ya bugi hancinta dan ta gefensa yabi ya zauna a kusa da mami yana kiran "washiii Allah !" sannu ka gaji ko  "wallahi  sweetheart ya gida ?daga hk bai sake cewa komai ba yayi shiru "lafiya dai ko naganka wani iri ? "ba lafiya ba sweetheart ya fad'a sanda yake gyara zama .


gbdy mami ta tattara hankalinta garesa "
"wallahi sweetheart wani tsautsayi ne ya samu wani babban yarona maganar da nike miki ma sai an fitar da dashi waje anyi masa aiki a kwakwaluwarsa "suballah mami ta furta nan yayi mata bayani komai "ai kuwa mun gani a labarai lallai dole matarsa ta shiga damuwa shi km direbasa Allah ya jikansa ta qarasa mgnr  mami tayi wa mrym alamar tayi masa sannu da zuwa "yaya adam !ta kira sunansa ya bude idanunshi dake runtse ya zuba mata" barka da dawowa ta ambata tana kallonsa bai amsa ba kamar yadda bai dauke idanunshi akanta ba "Allah ya qara kiyayewa shi kuma allah ya bashi lafiya "still dai bai amsa ba illa karfin halinta da ya gani ."


" mrym kawo masa ruwa ya sha ta tashi taje ta kawo masa "ga ruwa yayi mata banza dole ta ajiye a kusa dashi tana jin fad'uwar gaba  bayani ya cigaba yiwa mami tana jimami bai sha ruwan ba ya sake lumshe tsumammun idanunshi byn Kmr second biyar  ya bude idanunshi yaga idanun maryam kyam akanshi tana kallonsa kwayar idanunta cike da qaunarsa wani abu yaji ya tokare masa makoshi mikewa yayi tsaye dan baya son ya sake yin wani abu da zai ta'ba zuciyar sweetheart dinsa "sweetheart sai dai safe "allah ya tashemu Lfy ya nufi step bayansa tabi da kallo har ya bacewa ganinta gbdy ya tafi da rayuwarta  bata son abinda zai sa tayi nesa dashi ."


Yana tsaye a dakinsa yana kokarin cire kayansa yaji anyi knocking cike da mamaki  ya qarasa yana balle maballin gaban rigarsa ya bude kofar , daya daga cikin masu aikin gidan ne hannunta rike da wani qaramin tire dake dauke da glass cup an rufe sbd sanin halinsa ta rusuna cike da girmamawa sannan ta mika masa yayi shiru yana dubanta tare da mamaki, ganin yadda yake kallonta tai saurin cewa "hajiya ce tace na kawo maka jin tace mahaifiyarsa ce ya kar'ba ya maida kofar ya rufe ,  madara  ne mai sanyi ya kai bakinsa ya fara shan  kad'an  wani dadi ya ji dan  har sai da kunnensa ya motsa dan hk ya sake kai bakinsa ya shanye ya ajiye  cup ya soma cire kayansa ."

tabawa mai aiki ta nufi inda maryam take tsaye tana jiranta tana ganinta tasan adduarta ta karbu tai murmushin jin dadi tana dafata tana cewa  "bai miki tambayoyi ba "yana shirin yi nace hjy ce ta aiko ni" da kyau na gode  sosai tabawa mai aiki ta kama gabanta "ya kwashe kayansa ya zuba a basket ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito ya sanya kayan bacci mai budaden gaba  ya qara karfin ac dakin  kwanta ya lullube rabin jikinsa ya canza wutar dakin sai dai  ya kasa runtsawa  m malik ne ya fado masa ya tashi ya zauna ganin tunanin nason hanshi bacci ya yaye bargon daya lulluba dashi ya sauko ya dawo falo ya kunna sigari yana  zuga Ahankali  tunani sosai yake yana bukatar sanin abinda m malik yaso fad'a masa sakonsa kuwa ya karanta yafi sau goma amman ya kasa fahimtar akan me ye ?dole dai ya jira har zuwa lokacin da zai dawo norma.


******
Yau asabar wanda yayi daidai da  kwanaki  shida kenan da aurensu ata Wanda ya kama a lissafin hjy zulfa'u Gobe ne nana hauwa'u zata tare a gidanta hisham yana kwance akan kujera mai zaman mutun uku sai ga hjy zulfa'u ta fito daga dakinta ta kai idanunta kan agogon dake manne a parlour'n karfe goma har ta wuce gashi tun da nana hauwa'u take gidan a parlour'n yake kwana baya shiga dakin da take sai dai idan zai dauki wani abunsa mai mahimanci ranta a bace tace " ka tashi ka shiga daki ka kwanta ka wani zo ka kwanta anan ka bar nana hauwa'u ita kad'ai" ." babu mutsu ya mike tsaye dan bai son damuwa har yayi taku uku ta tsaida shi ta soma magana "hisham ka kular min da yarinya kada ka wulakantar min da 'ya idan na lamunce komai banda wulakanci bai tsaya jin kalamanta ba dan idan ya tsaya ya cigaba da ji zuciyarsa zata tarwatse

A natse ya tura kofar d'akin ya shiga tana zaune aka katifa ta jingina bayanta da abun gado ya zagaya dayan bangaren ya samu waje ya kwanta bai jima da kwanciya ba wayarsa ta dauki sautin qara ya d'auka ya duba ganin sunan dake wayo akan screen din wayr ne yasa shi ya zabura ya miki zaune yana daukar wayar tare da kiran sunan da dan karfi "nuzla !" Kina ina ? tun da ya fara wayar ta zuba masa idanunta kawai tana kallonsa yayinda idanunta ya ciko da ruwan hawaye "karki damu nace miki ganin nan zuwa ki tsaya a wajen ya qarasa wayar yana bude kofa ya fito zuwa haraban gidan yana qoqarin shiga motarsa qarar tada motar ya janyo hankalin hjy zulfa'u dake tsaye tana shirin kwanciya ta yaye labulen window taga hisham ne kallon yadda yaja murfin da karfi ya rufe da yadda figi motar zai nuna maka da baya cikin haiyacinsa."


"Ya allah ka shirya min hisham ina kuma zashi adaidai wannna lokacin ta tambayi kanta tana jin faduwar gaba hankalin hajiya zulfa'u yayi matukar tashi dan haka ta kasa kwanciya  ta fito daga dakinta ta shiga dakin da nana hauwa'u take ."take taji zuciyarta ta karye dan koda tashiga dakin kuka take sosai tamkar ranta zai fita duk yadda taso daurewa ta kasa ta fad'a jikin mumy da kyar ta iya daure abinda take ji .mumy ta shiga rarrashinta da kyar ta samu nana hauwa'u tayi shiru ."


"Har abada bazaki yi danasanin auren hisham ba muddin ina raye sai kin zama tauraruwa a gidansa ki qara hakuri ,amamn idan har kika ji bazaki iya zama dashi ba ki fad'a min aurenku bazai qara koda second daya ba wannan kalmar dake fita daga bakin mumy yana mata dadi da sanyaya ranta a duk sanda ta furta hakan ma yana sa ta danne duk wani abu da take ji dan tasan ba cuta tasa ta hada  auren da danta ba ."wani tausashen murmushi ya subuce mata sosai take jin dadin kalaman mumy tana ganin yadda abun zai zo masu da sauki ta hanyar mumy yanzu ya kike jin zamanki kina ganin zaki cigaba da rayuwa da hisham ?ta gyda mata kai .

"Yauwa diyar albarka allah yayi miki albarka Ameen ta fad'a tana jin qaunar mumy acikin ranta "yanzu fad'a min ina hisham ya tafi ?shiru tayi tana neman abind zata fad'a mata domin ta kareshi a wajen mumy byn Kmr second biyu tace "na dai ji yana magana akan wani contract "contract? mumy ta tambaya nana hauwa'u ta sake gyada mata kai tana sunkuyar da kanta kasa mumy tayi mata sai da safe ta juya idanunta ta zubawa mumy har ta fita daga dakinta ta lumshe idanunta "bata ga abinda nuzla ta fita ba da yaya hisham ya kasa karbata acikin zuciyrsa yanzu dai tasan sai dai tayi zaman aure dashi darajan mumy ."

Yana tuki yana jin wani irin bugun zuciya kuka zuci yake wanda yafi na fili ciwo idan har ya tuna nuzla bata son shi sai yaji radadi sautinta yanzu ma yawo sautinta yake masa acikin kunnensa yana jin kamr ya juya ya koma gida amman sai yaji bazai iya ba ko babu komai zataci darajan baba babba salim da yaya Ibrhim yasan muddin ya maidata gida zasu ji dadi kuma hankalinsu zai kwanta ."yana gama isa inda nuzla ta kwanta masa yayi parking ya fito cikin tsnanin tashin hankali ya rufe murfin motar da karfi nan da nan zuciyar nuzla ta karye ta qara sautin kukanta da take akaro na biyu" allah sarki yaya hisham hakika sai yanzu ta soma jin nadama abinda tayi masa ."


daga inda take ta fito ganin yana waige waige da qoqarin neman layinta "yaya hisham ta kira sunansa da sauri ya juyo ya ganta tsaye abayansa tsayawa yayi yana kallonta tun daga kasa har sama cikin wata atamfa dinki riga da siket kayan sun mata cif cif ajiki ta rame sosai sai dai baqaramin kyau tayi masa ba wani abu yaji ya tsarga masa tun daga tsakiyar kanshi har zuwa yatsun kafafunsa ,bai san sanda ya fixgota jikinsa ya rungumeta tsam kamar zaa kwace masa ita." ahankali ta saki wani kuka mara sauti ya sake kamkameta ajikinsa yana shafa bayanta "tun tana kuka slow slow har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login