Showing 27001 words to 30000 words out of 167047 words
Chapter 10 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
bazan janye kudirina ba wannan umarni ne na baka wallahi idan ka kuskura ka sa'bawa umarnina zaka ji abinda yafi haka daga bakina."
Maryam dake tsaye akan step a tun sanda ta bar wajensu jin saukar mari yasa da sauri ta dafe qirjinta saboda tashin hankalin data tsinci kanta ciki ,ta qara taku biyu idanunta ya sauka akan mami da ata dake huci tmkr zakuna ,wani hawaye ne masu zafi suka shiga turereniyar zubo mata ,kuka take sosai tana datasanin kiran mami datai a daren jiya ,dan tasan da bata kirata ba da hankalinta bai tsaidu akanta ba har tayi musu diran makiya da sassafe ba ."
" wayyo allah nah ni maryam na shiga uku nah wannan duk laifina ne”. ta fad'a tana toshe bakinta da hannunwanta duka dan kar sautin kukanta ya bayyana ." cikin tsananin fushi ata yace "okay sweetheart bazan bi umarninki akan wannan banzar yarinyar ba "ya fad'a atakaice yana furza da iska mai zafi daga bakinsa ."
"Naji bazaka bi umarnina ba amman kasani daga yau babu ni babu kai ka cigaba da rayuwarka kai kad'ai har duniya ta nade " tana gama fad'ar haka ta nufi hanyar step tana kwallawa maryam kira da karfi "maryam !!! mrym ta qarasa saukowa da sauri ta tsaya cike da fad'uwar gaba tana duban mami "d'auko mayafinki muje "ina kuma mami ?tayi mata tambayar a matukar firgice ."
"gida mana dan bazan tafi na barki acikin wannan gidan ba "kallon mami take cike da matsanamcin mamaki sannan ta waiga ta kalli ata dake tsaye taga yadda yake fidda numfashi har qirjinsa na sama da kasa wanda yake nuna tsananin tashin hankali".
cike da tashin hankali ta shiga girgiza ma mami kai sannan ta soma magana "mami dan girman allah kiyi hakuri ki barni kiyi tafiyarki ni zan yi hakurin zama dashi haka ta fad'a voice dinta na rawa ".
"dan ubanki zaman me zaki cigaba dayi dashi yana wulakantaki ?maryam tayi narai narai da idanunta tana damke hannuwanta cikin juna ,kin kuwa san babu wulakanci daya kai miji yaki kwana a gidan amaryarsa a daren farkonta zafi da ciwo ?"nasani mami dan ni kad'ai nasan halin damuwar dana kwana ciki jiya , tayi mgnr acikin zuciyarta tana qoqarin daidaita natsuwarta ."
"Ya wulakantanki ya tozartaki ya qunsa miki bakincikin da bazaki iya mantawa dashi ba har abada amman ki tsaya kina 'bata min lokacin" mrym ta girgiza mata kai tana mai share hawayenta "amman bake ya wulakanta ya tozarta ba ni yayiwa kuma na gode masa amman kisani bazan tafi na barki cikin wannan halin ba dan haka ki hau sama yanzu ki d'auko mayafinki muje an gama wannan auren". mami ta fad'a cikin tsanani 'bacin rai.”
"kiyi hakuri mami duk laifina ne dana kiraki na d'aga miki hankali me yasa ma zan kiraki ? sannan me yasa zaki hukuntashi ? da kin barshi ni ki hukuntani mami akan abinda na aikata kina zaman zamanki na d'aga miki hankali " maryam ta fad'a hawaye na zubo mata ."you're very stupid so you're the one caused all this problems ? amman dan munafurci kizo kinawa mutane kukan munafurci ."
" ina zaman lafiya da mahaifiyata aurenki ya shiga tsakanina daita sannan dan kin cika mahaukaciya ballagaza kika kirata kikace ban kwana gida ba ,dan ubanki idan na kwana a gidan uban me zan miki ? "ya fad'a a fusace ".?a matukar rikice tace "please am sorry I never know she wil act like this "ta fad'a hawaye na sake zubo mata, wani irin mugun kallo ya watsa mata sannan yay qoqarin qarasowa inda take mami na ganin haka tayi saurin taresa da hannunta dan ta lura baya cikin haiyacinsa "karka soma ta'ba min lafiyar yarinya mami ta fad'a muryarta na rawa bata ta'ba ganin yanayinsa haka ba ".
"Yau sai na kashe yarinyar nan da uban daya haifeta ya fad'a cikin cigaba da takowa cikin isa da 'bacin rai jin abinda ya fad'a yasa maryam rungume mami ta baya tana wani irin kuka tmkr qaramar yarinya "mami ki taimakeni dan girman allah "weetheart ki bani hanya naci ubanta na ganar daita kuskurenta wanda har abada bazata sake aikawata wani ba bare ni "ka shiga hankalinka “ita dai tashiga hankalinta “
“ adamcy banason abinda kake min dan babu laifinta ko d'aya idan hukunci ne ni dana mareka zaka hukunta."
"please sweetheart ki matsa dan babu abinda zai hanani ban hukunta wannan yarinyar ba akanta fa sweetheart kika mareni “yana qoqarin kamo hannun maryam mami ta sake sauke masa wasu marukan ji kake tas tass !! har biyu ajere ."wannan karon kam ata daskarewa yayi awaje d'aya yana kallon mami cike da tsananin mamaki abun yayi mugun girgiza shi "yau sweetheart dinsa ce tay masa mari har uku kuma duk akan wannan banzar yarinyar ".?
maryam kam fashewa tayi da wani sabon kuka ganin abinda mami ta sake aikatawa " matsawar ka ta'ba maryam ban yafe maka ba tana gama fad'ar haka ta juya rike da hannun maryam sai dai abun mamaki mrym din taki biyota ta turje jikinta na kyamarrr , dole tasa mami ta tsaya ta juyo tare da zuba mata ido tana neman qarin bayani, amman mrym tayi shiru sai hawaye dake sauka akan kuncinta"kina ganin irin wulakanci da yayi min amman da yake ke baki da zuciya zaki ki biyoni wato ke gaki mai ..."
kafin mami ta qarasa maganrta mrym ta zube kasa gabanta tana kuka tana bata hakuri .""Kiyi hakuri mami wallahi ba haka bane, ba kuma abinda kike nufi bane ,nayi nadama dan allah mami kiyi hakuri ki yafe masa ki daina fad'a masa kalamai haka marasa dadi ,kuma ni babu inda zan biki zan zauna a gidan mijina,da dad'i da babu zanyi hakuri dashi "tana gama fad'ar haka ta sunkuyar da kanta kasa ganin irin kallon da mami take mata mami tayi shiru kawai tana kallonta gbdy taji kwarin gwaiwarta yayi kasa ."
Jin mami tayi shiru hankalin mrym yayi mugun tashi rawar da jikinta yake ya qaru ta d'ago kanta ahankali taga ita din mami take kallo har lokacin muryarta a sanyaye tace "kiyi hakuri mami kece fa kike bani hakuri da kwarin gwiwar da har muka kawo matakin maaurata ,to me yasa akwana d'aya kawai da nayi a gidansa zaki d'auki zafi akansa alhalin kin fi kowa sanin waye shi ."?
nan kuma jikin mami yayi sanyi ta tsaya kawai tana cigaba kallon mrym , shi kuwa ata zuba masu ido kawai yayi yana jin zallar 'bacin rai na ratsashi yaji tsanar mrym ya sake qaruwa da mamaye duk wani sansar jikinsa "wallahi bancin mami dake tsakaninsu da shi kad'ai yasan irin azabar da zai gana mata amman duk da haka bata tsira ba zai ganar daita Kuskurenta ,runtse idanushi yayi yana cizan lip's dinsa na kasa da karfi yayinda hawaye ke bin kuncin maryam , tsaki yaja sannan ya juya a fusace ya haye sama cikin tsananin fushi yake taka step ."
Yana shiga d'akin daya zamo nashi ne ya soma zariya aciki he's thinking of if someone else did what his mother did to him today da wallahi allah ne kadai zai rabasu amman sweetheart rayuwarsa ce yana matuqar qaunarta, yana son duk wani abinda take so wajen had’in aurensa da wannan bazar yarinyar ne kawai raayinsu ya sha bam bam tsaki yayita ja tare dafe goshinsa dan wani irin sara kanshi ya cigaba da yi ."
"Maryam ta kamo hannun mami ta zaunar daita akan kujera sannan ta durkusa kasa gabanta "kiyi hakuri mami kema fa kinsan halinsa Kmr yadda kike cewa zai canza nima haka nasa araina wata rana idan allah ya taimakemu sai kiga ya canza, nayi miki alkwarin zan zauna dashi har tsawon rayuwata sannan kiyi min alkwarin bazaki sake kai hannunki fuskarsa ba sannan ki daina fad'ar kalamai marasa dadi akanshi nima kona kiraki karki saurareni akan kowacce matsala ki bani hakuri kamar yadda kike bawa sauran ya’yanki."
Mami ta qirgiza mata kai alamun bazata iya ba “please mami do the same thing to me “bafa zan zuba ido ba maryam ,dole nayi mgn idan ma baki fad’a min ba dole zan san komai “please!..”bafa zan zuba idanu yayi miki wulakanci daya ga dama ba domin Ke din amana ce a wajena kuma duk abinda yayi miki dole ne ya dameni ko bakya adamcy ya aura ba dole ne nasa ido a gidansa idan naga zai cutar da ‘yar mutane bare ke da kika kasance jinina "duk da haka dai mami Kiyi min alkawarin bazaki sake damun rayuwarsa akaina ba mrym ta fad'a tana sakar mata murmushin dole wanda kana kallo had'e yake da tarin damuwa.”
"Shikenan bazan sake ba “mami ta fad'a tana kukan tausayinta dana tilon d’anta data san haka auren zai kasance wallahi data hakura tun farko daya nuna baya so ."ahankali maryam ta kai hannunta tana goge mata hawaye tana cewa "mami ki bar kuka .
zubar da hawayenki akanshi maseefa ne a gareshi "ta d'aga mata kai kawai dan batasan me zata ce ba dan kukan ne ya fiyye mata sauki akan mgnr da zatai " daga nan mrym ta cigaba da kwantar wa mami da hankali ."zuciyar mami tayi sanyi ta sake amanna maryam itace mace d'aya da zata kular mata da rayuwar tilon d'anta."
murya a sanyaye mami tace "tashi kije ki kirashi yazo ya bani hakuri "maryam ta zaro ido tana kallon mami a matukar firgice "wallahi mami bazan iya ba he wil beat me to the exetended sai kin koka min kina kallo fa if bancin kina nan da yanzu ba wannan labarin ake fad'a ba ."allah bazan ta'ba iya tunkarar sa ba kawai Kiyi hakuri ki yafe masa "mami am so much in love with your lovely son amman bani da wannan kwarin gwiwa ." ta fad'a aranta hawaye na gangaro mata ."
hankali ta dora kanta akan cinyar mami tana zubar da hawaye ."tana matuqar sonshi and she don't want to loose him at all, she don't know what's happening to her brain, dan tana jin idan ya saketa ko idan mami ta raba auren zata iya mutuwa for real mami tace "kiyi hakuri mrym ki daina kuka nasan adamcy baya sonki shiyasa kikaga bana tuna duk wani halin da zai shiga nake yanke hukunci akanshi ta fad'a tana shafa kanta ."
"Ni kuma kinga bana son abinda kike masa " mrym ta fad'a a fili tana sheshekan kuka "baki so ?"mami ta tmbyeta ahankali tace "eh mami bana só ina jin ciwo a zuciyata sosai kinga sakamakon abinda kika yi yau ya qara d'aukar zafi dani tsanata ya sake qaruwa a zuciyarsa , mami ta sauke numfashi ,gbdy ta gama karantar maryam tana mugu mugun son adamcy ,ta kuma san muddin ya gano hk zaa qara samun matsala ne ."
"Nima baa son raina bane dan burina bai wuce na ganku tare cikin koshin lafiya da farinciki ba amman shi adamcy din ne zuma ne sai ancisa da wuta "haka zamuyi hakuri dashi muyita masa addua allah ya sausauta zuciyarsa ta fad'a tana sake kwantar da kanta a cinyar mami shiru parlour'n yayi baa jin motsin komai sai na saukar numfashinsu dana ac dake aiki sai kusan shabiyu mami ta mike tana jaddada mata tayi qoqarin ta shawo kansa yazo anjima bata hakuri ."ta qarasa mgnr tana dariyar tsokana ."
"Dan allah mami ki rufa min asiri ina ni ina tarar aradu wannan ai sai ke "mami tayi murmushi tare da yi mata sallama ta shiga mota suka baro gidan, mami kam da direbanta ya d'aukota bai wuce koina daita ba sai hanyar gida tana zaune abayan mota tana tunani abubuwa dayawa abinda yafi komai daga mata hankali soyayyar adamcy din data ga ya samu kyakkyawan mazauni a zuciyar maryam da kuma qiyayyar adamcy gareta tasan baqaramin wahala da qalubali zata sha a hannunsa ba dole tana bukatar taimakonta ,dan dole kuma tasa ido arayuwar gidansu idan ba haka ba maryam bazataji dadin rayuwar aurenta ba ."
Tana cikin wannan tunanin wayarta ya fara ringing it was nana hauwa'u sai data sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta dauka tana cewa "auta ya kike ya gida da fatan kuna lafiya ? to ya zaman naku yake ? "To shikenan ayita hakuri wata rana sai labari okay zan kirata in sha allahu ,yanzu ma ina Kan hanyar komawa gida ne daga wajen marym nike "eh to lafiya dai ba lafiya ba "mami ta fad'i haka cike da raunin murya baangaren nana hauwa'u tace "lafiya mami me ya faru daga tarewa jiya jiya km ?.”
"Kinsan halin yayanki ai "me yayi mami? "wai akai masa amarya yaki kwana a gidan wallahi jiya kwana nayi cikin damuwa da tashin hankali amman nima yau nayi masa hauka dan na nuna masa ba tsoronsa nike ji ba mari uku nayi masa masu kyau ,wallahi kuwa nasan da zarar ya sauko zai shiga hankalinsa ya dawo ban hakuri ,ku barni dashi duk zan sauke masa abinda Ke damunsa in sha allahu bazan bar duniya ba sai ya canza rayuwa ai ko da mutane suke ganin Kmr yafi karfina, ba karfina yafi ba zan haifi d’a ne nazo ina jin tsoronsa? kawai dai ina lallabashi ne sbd bana son takurawa rayuwarsa mota na tafiya suna hira da auta har ta kawo gida."
Wayarsa ce ta fara ringing sai data katse bayan ya gama shan kamshinta ya ciro yana dubawa Hannunsa daya yasa ya rike qugunsa dashi yana takawa zuwa bakin window din dakin ya bude yana kallon haraban gidan inda masu tsaronsa ke safa da marwa magana yayi wanda bai wuce ta minti uku ba ya katse ya soma cire kayan jikinsa ya fad'a bayi dan wani irin zafi jikinsa ya d'auka ga sarar da kanshi yake masa zama yayi acikin bathtub ruwa na sauka a sansar jikinsa "
ita kuwa maryam ta shiga d'akinta cike da faduwar gaba ta zauna abakin gadonta tana tunani ta dauki lokaci zaune tana tunani hali irin na mijinta har sai data duba taga lokacin sallar azahar tayi ta mike ahankali ta shig bathroom ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah bayan ta kammala ta koma ta zauna a inda ta tashi ta tsurawa tv dakin ido sai dai sam batayi shaawar kunnawa ba bare ta debe mata kewa tayi shiru tana tunanin ya kama taci wani abu dan tun abinci jiya ne acikinta dan haka ta fara tunanin fitowa ta samawar cikin wani abu ."
Ahankali ata yake saukowa sanye da wasu kaya , jikinsa na fidda kamshi mai sanyi dadi ya ajiye wayarsa akan center table ya samu waje ya zauna ya d'auki remut ya kunna tv ya qara karfin ac ya daura kafafunsa akan table yana duban tv ,ahankali maryam ta fito daga dakinta cikin sanda kamshin turarensa ya bugi hancinta sam batayi tunanin yana parlour'n ba tafi tunanin ko yana dakin yana shirin fita ya bar gidan ne, dan haka ta cigaba da saukowa tana saukowa tana sake jin kusancinta da kamshin turarensa mai sanyi da bugar da zuciya ta lumshe idanunta tana cigaba da daura kafafunta akan step ai tana gama saukowa kawai taga mutun zaune tmkr wanda aka dasa ."
Tsananin tsoron data tsinci kanta ciki sauran kad'an ta saki fitsari a inda take tsaye ,nunayen ajiyar zuciya da numfashi ta sauke alokacin daya ta sanyawa jikinta jarumta kana ta soma tafiya cikin sanyin jiki zata shiga kitchen, a natse ya d'ago idanunshi ya zuba mata oly eye's dinsa masu firgitar da mutun dole taja ta tsaya sakamakon idanunshi da taji suna yawo a gbdy ilahirin jikinta ta hade yatsun hannunta waje daya ta dago kanta zuwa Kan kujerar da yake zaune taga yayi mugun hade fuska tmkr zaki yana kallonta a kaskance ."
" zata iya cewa tunda tasanshi arayuwarta bata ta'ba ganin yanayinsa haka ba alama yayi mata da ido ta koma amman ta dauke kanta tayi kmr bata fahimcesa ba har tayi taku biyu taji Kmr ya mike ai da mugun gudu tayi Kan step, bata tsaya akoina ba sai a dakinta har da rufe kofar ta tsaya tana haki da maida numfashi "bayan ta samu natsuwa kwalla ta zubo mata "bata san tana tsananin tsoronsa ba sai yanzu yaya adam baya sona gashi ni kuma ina sonshi ta fad'a a fili cike da sanyin jiki ta zauna jugun tare da dafe kuncinta ."
kusan awa daya taji motsin fitar motocinsa ta sauko da sauri sai dai hawaye ne ya zubo daga idanunta
Sakamakon ganin ya rufe kitchen din duk inda ta kalla acikin parlour'n babu wani abu da zata iya sakawa cikinta dole taja jikinta ta dawo daki bayi ta shiga ta dauro alwala ta gabatar da sallar laasar ta kwanta lamo a saman abun sallah yunwa na nukur kusanta sai tayi kamar ta kira mami akawo mata abinci sai tayiwa kanta fad'a ta maida wayar ta ajiye ."
wasa wasa awanni suka dinga wucewa duhu ya fara sako kai lokacin magariba yayi a daddafe ta tashi tayi sallahr magariba ta dawo ta kwanta a haka ishai tayi wanda zuwa wannan lokacin ta fara raina kanta tuni hawaye ya fara fareti akan kuncinta tasan mugunta da kuma hukuntata yasa yayi haka tana daga kwance amman jiri take gani saboda tsananin yunwa tuni idanunta suka canza kala saboda kukan yunwa da take bata san yunwa bata da hakuri ba sai yau hatta test din miyon bakinta ya canza ."
Ata kuwa tunda ya fita yana wajen wani abokin kasuwancinsa daya sauka a kasar yau din nan sun jima suna tautaunawa akan kasuwanci shi kanshi banda coffee babu abinda yasanyawa cikinsa karfe bakwai daidai a haraban family house dinsu tayi masa, yana qoqarin fitowa daga mota yaga direban mami na fitowa daga gidanta hannuwansa duka rike da wasu hadaddun kuloli “ aransa yace “shegiyar yarinya sarkin rashi hakuri har ta kira akawo mata abincin ,ai da baki kira ba yau haka zaki kwana da yunwa nonsense girl kawai .”
massalaci dake cikin esate din ya shiga yayi sallah bai fito ba har sai daaka idar da sallah ishai ya zauna yana