Showing 126001 words to 129000 words out of 167047 words
Chapter 43 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
taí shiru tsaye tana duban bayansa "yanzu irin wannan mijin zata aura tai rayuwar aure dashi ?anya kuwa idan ta auresa zata ji dadin rayuwar aure kuwa yadda yake da rashin nuna caring ?” yanzu a halin da take ciki kowa Ya ganta yasan tana cikin damuwa dan gbdy komai nata Ya canza amman kalli yadda ya bar gabanta batare da Ya tsaya ya fahimci matsalarta ba bare ya kawo mata mafuta oh allah karkasa nayi Kuskuren aure irin wanda Mahaifiyata tayi ya allah ka taimakeni kasa ya canza duk da banason shi saboda rashin caring dinsa dan kusan matan duniya shine matsalarsu a gidajen mazajensu a yanzu, cike da sanyin jiki har ya bacewa ganinta tana tsaye a wurin rungume da hannunwanta a kirji jiki a sanyaye ta nufi kofar part dinsu ."
*******
motarsa na shigowa haraban ma'aikatan yaji gabansa yayi wani mummunar faduwa da karfin gaske shiru yaki fitowa daga cikin motar yana tunanin abinda yasa yaji hk byn tun a gida bai tsinci kansa cikin wannan yanayi ba sai daya shigo ma'aikatan iskar ya furzar ya daga kafadunsa alamun babu komai a hankali ya zuro kafafunsa dan tuni an bude masa kofar mota ya fito yana gyara zaman suit din jikinsa sannan ya soma taku a hankali qirjinsa na cigaba da luguden bugu yayi qoqarin kawar da yanayin da gangar jikinsa ya shiga ta hanyar tura hannusa daya cikin aljihun wondonsa." duk inda ya wulga maaikata ne Ke kokarin kawo gaisuwa sai dai kai kawai yake gyada wasu ,wasu kuma yayi masu banza har ya hau lift da zai kaisa sama na uku inda anan office dinsa yake yana sauka yaji wani sabon faduwar gaba wanda ya rasa dalili nan ya dan rage tafiyar da yake ya dawo yana daga kafafunsa da kyar saboda sanyin daya ziyarcesu alokacin daya tun daga nesa ya hango bayan wata yarinya suna magana da wasu daga cikin maaikata kamar ya tsaya sai kuma ya karya kwanan da zata kaisa office dinsa cak yaja ya tsaya sakamakon jiyo sautin muryar yarinyar shiru yayi yana cigaba da saurara maganarta tamkar dai mafarkin da daya saba yi “anya kuwa muryar tace ko dai mafarkin daya saba yi daita ne suna hira ?.
hannunsa ya kai yana shafa daidai satin zuciyarsa dake bugawa tmkr zata fasa qirjinsa tayo waje ya dinga jin tamkar yayi reves ya dawo ya shiga inda yake jiyo murayarta ya tabbatar ita din ce ko kuwa muryar ce kawai tazo daya amman sai zuciyarsa ta kwabesa wankakkiyar zuciyarsa ta sake yin magana dashi kaje ka duba ko itace wata zuciyar tace kai ba itace ba ,ba yarinyar mafarkinka bace, dan haka a natse ya daga kafarsa daya bai kai ga ajiyewa ba ya sake jiyo sautin muryarta"."ku ne fa kuka bukaci kwararrun masu irin aikinmu yau tsawon wata guda kenan ina zariya a ma'aikatan ban samu nasarar ma hawowa saman ba sai yau ,yau din tun karfe bakwai na safe nake cikin compaing dinku kafin ma ku yarda na hawo saman nan sai da kuka bata min lokaci na samu da kyar na hawo yanzu kuma kuna kawo min qabli da baadi kunsa irin wahalar dana sha kafin na kammala aikin nan kuwa ?"kunsa lokacin da yake daukar mutun kafin mutun ya kammala ,shikenan shikenan!! tunda bakwa bukata ku bari na wuce na kama gabana daman an fada min wahalar banza kawai zanyi byn hka bakwa girmama masu tallata kasuwancinsu tana gama fadar hk ta juya haka zalika fuskarta a rufe take "no madam bamuce bama bukata ba mutane dayawa sun kawo nasu zanen maganar da nake miki har yanzu mai gida bai duba ba bare ya tantance bazamu iya cewa komai ba a yanzu dole sai an agwadawa boss ".
Ta juyo ta fuskacensu sosai.” har zuwa wani lokaci kenan zaa gwada masa sannan zuwa yaushe zanji feed back ?zai iya daukar wata uku zuwa ..tsaki taja ta sake juyawa tana tafiya tana cewa "gashi nan na bar maku bana da bukata domin ko na koma dashi gida babu amfani da zai min ."snyayen Kamshin turarenta ya bugi hancinsa yayi saurin lumshe idanushi zuciyarsa na cigaba da mugun bugawa ta kusa dashi tazo ta wuce har tayi taku uku ta fahimci ba ta nan hayar fita take ba dan haka ta sake juyo wa ta nufi kofar da lift yake ahankali Ya juyo yabi bayanta da kallo yana kallon every step of her doguwa ce sosai kuma bakar mace ce yayinda tsayinta ya fito da ainin shape dinta na cocacola iya haka kawai ya iya fahimta domin hannunta da kafafunta abayyane suke haka hijab din dake sanye ajikinta qaramin ne hkn ne ya bashi damar dan fahimtar wani abu a tattare daita "
ATA yana tsaye tamkar gunki yana kallon tafiyar yarinyar da bai san ko wacece ba amman jin sautin muryarta da yanayin tafiyarta yasaka zuciyarsa jin wani irin tsoro mai tsanani da shiga tashin hankali shi gani yake ma babu tantama itace ba anya kuwa ba gizo tayi masa ba kamar yadda yake ganinta a mafarkinsa har yanzu kwayar idanunshi yana Kan hanyar databi ya kasa kwakwaran motsi wani irin ajiyar zuciya ya sauke tamkar ya dakatar daita ya daga black nikaf din dake manne da idanunta yaga fuskarta amman gangar jikinsa da komai nasa yayi rauni zuciyarsa kuwa sai bugawa take babu Kaukautawa ba shiri ya dafe daidai saitin zuciyarsa ya a manne jikinsa da bangon wurin dan yanayin da yaji akanta ya wuce misali hakan yasa kafafunsa suka kasa dauakarsa ."ya sake kurawa hanyar data bi ido har lokacin tafiya take mai hade da rasauya tamkar fure hankalinta kwance take taka kasa tana gyara zaman qaramin hijab dinta wanda akewa lakabi da haif sunnah, gyara tsayuwarsa yayi sosai tare da zura hannunwansa duka cikin aljihun wondonsa zuciyarsa na cigaba da bugawa da sauri sauri yayinda gabadaya ma'aikatan dake aiki a office din da maryama ta shiga suka fito domin binta da makeken hotonsa wanda ta zana ."
turus sukai gabadaya suna kallonsa kowannensu ya gyara tsayuwarsa yana kare masa kallon abinda basu ta'ba ganin ya faru ba, basu ta'ba ganin abinda ya dauki hankalin mai gidan nasu ba sai yau ya kusan miniti goma yana tsaye yana fama da zuciyarsa dake karkarwa" Wayyo allah ina ma zai iya da yasa an dakatar daita ko sau daya yaga fuskar ko mafarkinsa ce har ta shige lift bai motsa ba ,sautin gaisuwarsu ce ta dawo dashi hankalinsa a natse .kallo daya yayi masu ya juya batare daya amsa ba yana tafiya yana sauke numfashi a natse ya dinga daga kafafunsa tamkar mara laka a jiki jikinsa baqaramin sanyi yayi ba har ya shiga office dinsa ya wuce sectary dinsa zaune tana ganinsa ta mike da sauri cike da girmamawa ta biyosa office dinsa har sai data ga ya samu wuri ya zauna "good morning sir cewar sectary ya gyada mata kai ta wuce domin komawa bakin aikinta , a can waje kuwa tabe baki ma'aikatan sukai sannan suka koma office bakin aikinsu ."wanda yake rike da katon zanen adam Ya nufi inda aka ajiye sauran zanen da mutane suke kawo ."
, ATA ya zauan tare da kunna system dinsa sai dai zuciyarsa ta kasa samun kwanciyar hankali amman haka ya cigaba da aikinsa amman ya kasa samun natsuwar yin aiki ji yayi duk wani kuzari nasa yayi kasa wata irin soyayya princess dinsa ce ta dinga taso masa daga zuciya yana jin kansa muddin babu ita arayuwarsa tabbas nashi rayuwar bashi da wani amfani ya furzar da iska mai zafi yana ture system zuwa gefe ya dauki waya ya kira number sectary dinsa mgnr daya yayi ya katse ya sake janyo system gabansa ,byn kamar second uku ta bayyana a gabansa rike da wani file cike da girmamawa tace "sir !"yaake ciki game da masu zanen danace?sir ai kwararrun masu zane sun kawo irin zanensu "me yasa baki fad'a min ba ?sir ganin baka da time shiyasa ban maka magana ba "ni nace miki bani da time ?yayi mata tambayar a tsawace nan take jikinta ya kama rawa ta sake kankame file din hannunta "kayi hakuri sir nayi kuskure numfashi ya sauke yana cewa "get out ."
Ta rusuna masa sannan ta juya byn Kmr mintuna talatin ya fito yayi hanyar waje yana kiranta ta biyosa da sauri bai tsaya akoina ba sai bakin koridoor ya tsaya yana bata umarni " call ja....kafin ma ya qarasa ta nufi office dinsa ,basu wani jima ba suka dawo tare dashi "good morning sir “amm james muje naga creations din da'akawo "okay sir !
Da sauri yayi gaba ATA na biye dashi wanda da kyar yake iya daga kafafunsa yayinda sectary dinsa ke biye dashi har zuwa babban dakin daaka tanada domin ajiye duk wani creations din da'aka kawo yana gama shiga dakin ya já Ya tsaya batare daya basu umarni ba suka shiga bude masa duk wani creation da'aka kawo yayi shiru yana kallon creation daya bayan daya wasu zanen kaya sukai doguwar , wasu suit da riga wasu kuma zanen mutane haka yayita kallo duk babu wanda ya dauki hankalinsa dan haka yayita jan tsaki yana qarawa har ma ya soma gajiya da kallon creations din har ya juya James yace "sir kalli wannan ka gani juyowa yayi sosai yana kallon zanen da shine aka zana sak
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 24
yadda yake fari tas tmkr balarabe da yadda idanusa suke da d'an girma da dogon hancisa yanayin tsayinsa fuskarsa sai gashin bakinshi dake zagaye da gemunshi komai shine hatta yanayin fuskarsa da take a d'aure ba'a bari ba."muryarsa a kasalance "very nice !ya fad'a yana sauke numfashi had'e da gyara tsayuwarsa yana kallon zanen kansa ."cike da tsinkewar zuciya yace "a kira number wayar wanda yayi zanen nan kasancewar yaga kowani creations dake ajiye ajikinsa akwai farar takarda makale mai dauke da number waya da address sai dai ita maryama iya number wayarta kawai tasa "okay sir cewar James cikin abinda bai wuce one second ba ya juya har ya kai bakin kofa ya tsaya batare daya juyo ba "ka biyoni da creations din "James ya sake cewa "okay sir!"Cikin abun da bai wuce minti goma ba James ya shiga neman layin maryama da number compaing dinsu amman number a kashe ya jaraba kiran yafi sau goma still dai swcth off ake maimaita masa dan haka ya shiga office din ATA cike da girmamawa ya rusuna yana cewa "sir nayita qoqarin neman layin amman swcth off ake cewa "okay keep trying !ya fad'a yana cigaba da operating system." wuni ranar James duk akan kiran layin maryama ya qare amman still the same thing ake fad'a masa ."
Washegari ATA na zaune akan kujera yana kallon screen din system dinsa gefe guda kuma yana jin bayanin James bai ce uhm ba bare uhm umm har sanda ya dasa aya inda a karshen maganarsa ya dan nemi ya rikitashi a natse ya ture system din gabansa ya mike tsaye ya zagayo ya zauna akan table yana dubansa "okay itace girl din jiya kenan ?cike da tashin hankali yayi shiru ya kasa bashi amsa "da kai nake magana fa cike da matsanancin tsoro yace"Yes sir itace !shiru yayi yana sake jin bugun zuciyarsa na qaruwa akan na jiya ya kai idanunshi kan tangamemen zanen dake ajiye a office dinsa yana kallo yana jin wani irin sanyi ajikinsa tunda yake bai ta'ba jin abinda ya tsaya masa arai ba Kmr princess dinsa sai yarinyar jiya da kuma wannan zanen "wanna duk kuskuren ku ne mutun yazo da irin abu haka mai matukar mahimanci ai ko dan darajan kokarin da mai shi yayi wurin zanani ya kamata ku bashi kulawa ta musaman sannan kafin ku aiwatar da komai ku nemeni but wannan laifi stupid sectary ce bani da time dinta yanzu zanji daita later gabdaya zanenta yafi na kowa kyau ina son ganinta eyes to eyes ina son nasan yadda akayi ta zanani haka
bansan me yasa kuke wa masu zuwa ma'aikatan da wata bukata haka ba ?yayi maganar a matuqar fusace “we are sorry sir “ shiru ATA yayi yana ciza lip’s dinsa da karfi ."
Maryama suna zaune a parlour’nsu tare da yaya sadam suna hira kira ya shigo wayarsa kamar koda yaushe shiru yayi gabansa na faduwa ya rasa dalili yasa bata kiransa sai lokacin da yake tare da maryama daga maryama har yaya sadam shiru sukai suna kallon juna muryarta a matukar sanyaye tace “yaya sadam ko akwai damuwa ne ? ya girgiza mata kai alamun babu komai “no yaya sadam karka boye min idan akwai damuwa ka fad'a min zan fahimceka “nace babu wata damuwa still kira ne ya sake shigowa wannan shine karo na biyar ana kiranka baka dauka kuma kace babu komai kuma duk sanda zamu kasance tare zayita kiranka bazaka d’auka ba amman shikenan tunda ni ban kai matsayin da zaka sharing problem’s dinka dani ba gara kawai a fasa auren nan dan ina ganin Kmr akwai damuwar da kake boyewa “ta fad'a tana mikewa tsaye zata shiga da sauri ya rike hannuta yana cewa " haba sauraniyata Kiyi hakuri babu wani damuwa kema kinsan idan akwai zan fada miki idan kika fasa auren nan ai sai dai kisan yadda zakiyi dani da ummah nah dan mutuwa zamuyi ya qarasa mgnr a marairaice.”
murmushi tayi wanda ya bayyana wushiyarta sama da kasa sannan ta koma ta zauna tana cewa “haba yaya sadam wasa nake maka amman bani wayar naga su wa ke kiranka haka “ ta kai hannunta zata d’auki wayar ya dauke wayar da sauri yana cewa “no no!!” oh am sorry shikenan kayi hakuri na shiga rayuwarka ,no karki damu kace kana sona yanzu ?
”sosai kuwa dan zan iya rasa raina idan kika barni amman me yasa baka son fad'a min damuwarka matsalarka sannan ni ina son ka dinga tmbyta wasu abubuwa da suka shafi rayuwata sirrikana me nayi da sauransu "yanzu duk abinda nake miki bakya gani ? Ta gyada masa kai alamun a’a “zan fashe miki da kuka fa maryama yana rufe bakinsa kira ya sake shigowa wannan karon yace “ excuse me tare da mikewa tsaye “ am very sorry yaya sadam saboda ni ka kasa daukar kiran daake maka ,babu komai kaje daga waje ka amsa kiran ya gyad’a mata kai ya fito waje yana amsa kiran muryarsa can qasa qasa.”
Mikewa tayi cike da sanyin jiki ta fito haraban gidan tana tafiya a hankali tana tunanin yanayin yaya sadam wayarta ce ta dauki qara ta duba taga number compaing din da taje neman aiki ne suka mata wulakanci "taja dogon tsaki ta katse kiran wani kiran ya shigo still tayi discounting kira na uku ya sake shigowa " ta sake jan tsaki "ina ganin sai na kashe wayata gabad’aya zasu daina kirana ta kashe wayar tana cewa “marasa mutunci bayan kun gama wulakantani sannan ku dawo kuna kirana kiran me kuke min? .dan girman Allah nadia ki daina damun kanki da yawon kuka ,nima ina sonki amman maganar da nake miki yanzu aurena ma ya kusa ana daf da daura min aure da yaruwata , ki manta dani kawai komai ya rigada yazo karshe a tsakaninmu Allah ya baki wanda ya fini , look nadiya dan allah karki sake kirana ..” yana juyowa yaga maryama tsaye a bayansa “kai dawa kuke waya har kake cewa karta kara kiranka aurenka ya kusa ?”shiru yayi ya rasa amsar da zai bata dan haka ta juya zata bar masa wurin ya riko tsintsiyar hannunta "please maryama! ta juyo tare da tsura masa narkakkun idanunta wad’an da ‘bacin rai ya qara narkar dasu “ka tsaya kana kallona tambaya ce mai sauki nayi maka.”
“ shikenan wata yarinya ce dake sona tare mukai karatu daita amman na rigada na fad'a mata bazai yuwu muyi aure daita ba dan na kusa aure nan bada jima ba ,amman gbdy ta kasa fahimtata numfashi ta sauke tare da cewa “ maza Kenan " allah ki yarda dani Kiyi hakuri idan kinji babu dadi aranki yaya sadam mai yasa zaka wani damu kanka haka ai babu komai? “ tayi shiru tare da kamo lip’s dinta tana jin zafi a zuciyarta , yanzu taji da kunnenta yana furta mata yana sonta amman kuma wai ita Ke sonshi tô su maza zuciya nawa garesu ?”numfashi ta sauke tace “amman duk lokacin da zamu kasance tare tana kiranka amman idan na tmbyarka sai ka boye min why yaya sadam alhalin zuciyarka na sonta ?” shiru yayi ya kasa furta komai yana kallonta gabad’aya yanayinta ya canza har kwayar idanunta ? ni kinji na fad’a miki ina sonta ?da mamaki take kallonsa lallai halin maza sai su idan suna da mata biyu soyayyarsu biyu ce fa byn ta gama kallonsa tace “yaya sadam ban san me yasa ba zuciyata ta kasa yarda da baka son yarinyar nan domin gbdy yanayinka ya nuna akwai soyayyarta mai karfi a zuciyarka ,do you know something yaya sadam ?cigaba da kallonta yayi ya kasa cewa komai “idan kasan tsakani da Allah kana sonta ka aureta dan ni bana son boye boye arayuwata komai nafi son gsky da gsky amman kai gbdy baka son mu gina soyayyar mu akan hakan“.
“no karki yi wannan tunani