Showing 48001 words to 51000 words out of 167047 words

Chapter 17 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

me nayi masu arayuwar nan da suka tsane ni."aunty ta zauna kusa daita jikinta na rawa tace "me ya faru maryama ?"na gaji da wannan rayuwar aunty fati so take ta kasheni dan Allah ku barta ta kasheni ni yanzu nafi bukatar mutuwa da rayuwata akan dai ta hadani da muktar .”ta qarasa maganar tana kuka .”


“kwantar da hankalinki kiyi min bayani da kyau ban fahimceki ba ta hadaki da muktar kamar ya ?"
"Wai ya aureni !"numafashi aunty  ta sauke cikin rarrashi tace "haba maryama ki daina daga hankalinki tunda ga maganar yusif nasan baba gali zai yi mata bayanin komai maryama ta fashe da wani sabon kuka dan ta ta’bo mata wani ciwo ne data binne "babu wannna auren bilkisu .”muryar umma suka jiyo daga bakin kofa aunty ta juya da sauri qirjinta na bugawa fiyye da kaida ummah ta gyada mata kai "haka né abinda kikaji na fada shima an canza masa tunani har ma dana iyayensa ahankali ta tako ta dafa kafandan aunty dake kallonta a tsorace cikin tsananin tashin hankali ."


“Ummah ban gane ba me kike qoqarin fad’a min ?“abinda kika ji shi na fad’a miki balkisu yusif ya koma wajen shukura “inna lillahi wa inna ilahi rajiun shi kawai tayita fad’a tana maimatawa nan da nan yanayinta ya sauya ta zauna shiru taji duk wani kuzari na jikinta yayi kasa tsawon mintuna talatin sannan ta bud’e bakinta da kyar tace “shima yusif din ya koma wajensu "Ki kwantar da hankalinki babu abinda allah bazai iya ba kuma in sha allahu allah zai kai maryama matakin da ba'a só allah yasa hakan shine mafi zama alkhairi arayuwarta ummah ta zauna ta dinga tausar aunty da maryama tana bata baki har aunty ta saki ranta sai dai hawaye yaki tsayawa umma ta qara da tabbatar masu duk runtse maryama bazata auri muktar ba “


Maryama ta rungume ummah ajiknta “na gode umma dan allah karki bari a aura min shi wallahi na hakura da auren ma har abada “bazaki hakura da aure ba akan wani dalili domin duk dan sunah baya gudun aure yadda akayi aure aka haifeki in sha allahu kema zakiyi aure har ma da ya’ya da jikoki ummah ta fad’a tana shafa bayanta suna cikin wannan hali habib ya shigo aunty tayi sauri ta goge hawayenta tana daidaita natsuwarta ganinsu haka ya fahimci akwai damuwa dan haka da hanzari ya qaraso ya riko hannun aunty cikin nashi yana tmbyarta “lafiya na ganku haka ?babu komai aunty ta basu amsa “ya babu komai ?ya kalli ummah fuskasa dauke da tambaya .”


“Me yasa zaku boye masa yana da kyau ya sani ko babu komai zai taya yaruwarsa addua nan ummah ta fad’a masa komai “shiyasa nace ta hakura da batun wani aure ,bafa dole sai mutun yayi aure zai shiga aljanna ba “kul kar na sake jin ka fad’a haka zatayi aure musa aranmu dukkaninsu babu mijin aurenta acikinsu mu godewa allah da yasa har tana masu sonta baa barta haka ba babu abinda zai zo da bazai wuce ba wata sai labari ahankali ummah ta shawo kansu suka shiga wata hirar ,”


******


Kwanakin dari   kenan da auren su maryam wanda yayi daidai da kwanakin sabain da tarewar maryam a gidan ata acikin lokacin babu wani abu da yayi sauki acikin zaman auren mai dadi a tsakanin maryam da ata duk abinda maryam zatayi domin ta cire kiyayyarta a zuciyar ata tayi amman ko a jikinsa domin dai yaki sakewa daita ."shiyasa damuwarta ta qaru zamansu babu wani shaawa  dan ata yaki rungumar marym sai ma kyma da nuna ko in kula ."


Sosai motocin  jami'an tsaro guda hud'u dake gaba da bayan motar da ata  ke zaune aciki ke falfala gudu akan titi kamar suna gasar tsare baka jin komai sai jiniya mai tsanani domin a kauce abasu hanya sosai motocin dake Kan titi suka dinga komawa gefe suna basu hanya wanda adaidai wannan lokacin maryam na can tsaye   acikin kitchen tana kwashe abinci tana zubawa a kuloli ."



Bayan ta gama ta jerasu akan table duk abinda take cikin hanzari take yi kar oga ata ya shigo bata gama ba  duk da ba abincinta yake ci ba sai maakatan gidan ke ciki kuma idan tayi lattin ganawa yaci ubanta ,qarar jiniya taji alamar dawowarsa dan zaro ido tayi tare da daga kai ta kalli agogon dake manne a parlour'n karfe takwas da minti ashirin cikin sauri ta haye sama ta shiga dakinta  wanda ya sha gyara gwanin burgewa.  ta cire kayan jikinta ta daura towel sannan ta nufi bayi ."


Cikin  jin isa  ya turo kofar parlour'n tare da shigowa babu kowa a parlour'n jakar dake hannunsa ya ajiye akan kujera da wayoyinsa sannan ya nufi sama yayinda zuwa wannan lokacin maryam ta fito tana tsaye a gaban madubi tana shafa lip's dinta byn ta gama ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka can zuciyarta ta bata umarnin ta saka marasa nauyi tun sanda ta tare a gidan tsawon sati tara kenan atamfa da dogayen riguna take sakawa ta sanya kaya marasa nauyi masu yanayi dana bacci yana tsaye a dakin yaji an turo kofa bai juyo ba ."


cike da faraa ta tsaya a gabansa tana cewa "oyoyo baby sannu da zuwa "wani kallo yayi mata a dage yana sake tamke fuska tmkr yaga wani mugun abu cike da sanyin jiki ta kallesa ganin yadda yayi mata kallon kaskanci "leave my side “ya fad'a yana nuna mata kofar fita yayi maganr cikin bacin rai bata wani damu ba tunda idan da sabo ta saba da halinsa "ga abinci "bana ci kina tunanin zanci abinncikin ne ko me ?”kayi hakuri please kaci ko kadan ne na sha wahala sosai kafin na gama bai ce mata komai ba ya juya ya bar parlour'n.”


Wani bakinciki ta dinga ji acikin ranta "oh ni maryam me zan yiwa wannan bawa naka na canzashi?gani bata da abinda zatayi yasa taja kafafunta ta koma dakinta ."ta fad'a kan katifa wasu hawayen bakinciki na zuraro mata nasihar sister ce ta fado mata "maryam kinsan yadda akayi auren nan hakuri zakiyi da Adam idan kina son kici riba ,auren da kayi dan soyayya ma hakuri kake yi bare wanda iyaye suka had'a zaman aure dan hakuri ,gidan aure makaranta ce mai girma ba zaka gane hakan ba sai ka shiga, akwai darussa kala dabam dabam sai kin zauna acikinsa zaki fahimta."wasu hawaye suka qara tsiyayo mata yanzu haka zata qare rayuwarta cikin hakuri "tunda kina son shi dole zakiyi hakuri dashi ."zuciyarta ta bata amsa da hakan .”




Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


             Page 10


Ahankali ta yunkura ta mike tsaye kamar wata mahaukaciya ta soma zariya acikin d'akin  tana sambatu "yanzu me  zan masa na  kawowa kaina  kwanciya hankalin acikin gidan nan ?tayiwa kanta tambayar tana mai qara shiga tashin hankali "babu abinda zaki iyawa wannan mai shegen taurin kan da zaki burgesa ,komai zaki  masa a banza ne a wajensa "tayi shiru na minti biyar tana tunani kafin ahankali ta qarasa inda wayarta take ajiye, ta kai hannu ta d'auka tana  tunanin kiran d'aya daga cikin yan'uwansa wani tunani tayi sai kuma  ta fasa kiran  domin dai tasan kowa a cikinsu abu d'aya yake fad'a mata shine hakuri hakuri !! kuma yanzu da zata kirasu  hakurin dai zasu bata ."


     "bana son wannan hakurin  gashi kuma hakurin dole zanyi  tausayin kanta ya kamata tana mai jin kamar duk ita ta jefa rayuwarta cikin matsala a dalilin zunzuruntun qaunar da take masa da taki auren tun farko data zauna da rayuwarta lafiya ."yanzu me zanyi ?ta sake tambayar kanta tana cure hannuwanta waje d'aya "idan da hali ki sake zuwa wajensa ki kwantar da kai tunda kece a kasansa "da sauri ta girgiza kai alamun shawarar bata yi mata ba  "wallahi da zan  cire kulafucinsa nayi hakuri na  bar rayuwarshi da komai zai zo min  da sauki "ta sake bawa kanta wannan shawara  "amman ina bazata iya ba dan tana da kulafucinsa tana mutuwar son shi kamar yadda yake mugun kinta murmushin takaici  maryam tayi tana cewa "Allah kasani ina wa  adam wani irin so mai girma, allah ka nuna min ranar da zai soni kamar yadda nake sonshi dan zan só faruwar haka."


"burina a koda yaushe mu kasance a matsayin miji da mata kamar sauran ma'aurata dan haka maryam karki gaji da halin mijinki kije ga mijinki baki san abinda allah zai yi ba  wata rana sai labari ga kuma alqawarin da kika d'aukarwa mahaifiyarsa kuma mami ta yarda dake shiyasa ma ta baki amanarsa
da wannan shawar ta fito daga cikin d'akin cike da sanyi jiki ."bayansa ta hango yana taka step ahankali yayinda hannuwansa duka ke cikin aljihun wandonsa kunnensa manne iPod ."kai tsaye bayansa tabi yo tana kallon yadda yake taka step yana wani rangaji." alamun taku yaji abayansa ya  waiwaya ya kalleta sannan ya juya ya  cigaba da taku ,yana gama sauka  ya samu waje ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun parlour'n ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya yana cigaba da wayarsa "karka qara min damuwa ammar akan wanda nake ciki, ina ruwa da wata yarinya ta gama bautar qasanta mana ina ruwana ."


"idan zanyi aure dole sai ita zan aura ?" kaga dan allah malam mu bar maganar nan ta isheni haka
yes of course ni na furta zan qara aure amman ba lallai sai wannan yarinyar ba .""Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryam ta furta a kasan zuciyarta qirjinta na dukan uku uku  sakamakon jin maganarsa ,ta tsaya nesa kad'an dashi tana kallon yadda yake motsa bakinsa  tare da sauraron maganarsa .shiru ATA yayi can yace "ammar ba lallai tayi min ba ka dai san halina  ba duk abinda yayiwa mutane yake min ba ina da test "maryam ta runtse idanunta qirjinta ya cigaba da beating very fast amman kuma ta d'an ji sausauci jin abinda ya fad'a dan haka ta taka ta shige kitchen tana mamakin yaya ammar ."


"In da wani ne ya fad'a mata zai kasance cikin masu bawa mijinta  goyon bayan ya qara aure zata musa sai gashi taji da kunnenta sosai taji ciwon abun aranta   ta had'o masa shayi irin wanda tasan yana so ta qaraso inda yake zaune jikinta a sanyaye ta mika "ga shayi !".ya d'ago tsumammun idanunshi ya zuba mata batare daya kar'ba ba ya cigaba da wayarsa "kasan Allah da nayi niyyar naga yarinyar nan ko sau d'aya ne  amman jin yadda kake wani  zuzutata naji bazan iya ganinta ba ." wani naunayen ajiyar zuciya maryam ta sauke najin dadin abinda ya fad'a dadinta dashi akwai ra'ayi kuma ra'ayinsa nayi mata dan ba duk abinda mutane ke so yake masa ba "ga shayi ka sha " ta sake furtawa a raunane kwayar idanunsa ya sake d'agowa ya zuba mata wanda yasa ta sake shiga tashin hankali  "nasan kana da d'abiar shan shayi a duk lokacin da ka dawo daga aiki ".



wani dogon tsaki yaja yana  d'auke kwayar idanunshi akanta "abinda ya kamata tayi tun a farko shine dan shirme irin nata ya dawo karshe" ya sake jan tsaki ."
Daga can bangaren ammar  kuwa cewa yayi  "haba ATA kaji da madam mana ,dan allah kayi qoqarin kabi mahaifiyarka shine kawai zai samar maka kwanciyar hankali da natsuwa "na sani ammar ina iyakacin qoqarina the girl  always doing nonsense wai abinda ya kamata ayi da farko dan hauka irin nata shine ya dawo karshe "haka zaka d'aure kayi hakuri kuma da zaka d'aure ka .."enough ammar ! ya fad'a tare da amsar qaramin cup din hanunta ya  ajiye akan table  ya mike ya  nufi kofar fita ya barta a wajen tsaye  bayanshi tabi da kallo tana furta "oh ni maryam naga takaina."


Haka taja kafafunta ta koma d'aki duk yadda taso kin kiran kowa acikin yan'wansa amman zuciyarta ta gaza hakurin haka sai data kira nana hauwa'u "tana dauka ta fashe mata da kuka tana cewa "sister me  na tsarewa yaya ammar da yake son yaya Adam ya qara aure?" "aure kuma ?wallahi da kunnena naji suna hirar inda allah ya taimakeni yayanki yana da raayi yaki yarda da maganarsa "to ki godewa allah da bai yi raayin qarawa ba dan koni bazan so akawo miki wata matar gidanki a halin da'ake ciki  ba ciwo zaa qara miki  akan ciwo "."Sister wai taya zaayi na shawo Kan yayanki ne ?ina ji ajikina hakurina ya kusan qarewa acikin gidan nan "na sani sister kina hakuri sosai da yaya Adam amman ki qara akan wanda kike yi sannan karki gaji dashi ki cigaba da bashi duk wata kulawa da mata ke bawa mijinta  idan babu mutuwa akwai rabuwa  wata rana zai ga amfaniniki sai abu na gaba " ki dage da addua abinda na fahimci kina sakaci dashi kenan sister wallahi idan kika rike allah zai isar miki ,dogaro da allah shi ke yaye wa mutun damuwa sosai nana hauwa'u ta ajiye damuwarta ta dinga kwantar mata da hankali ."


******


Maryama na  zaune a d'akinta tana nike kayanta yayinda kunneta Ke makale da hearpis tana waya da ammar "tayi murmushi ai kam da zamu samu zamu ji dadi sosai dan ance samun aiki a Z&A akwai matukar wahala amman tunda  kana nan nasan bani da wata damuwa ,Allah kuwa zuwa lokacin ma  mun qare nysc dinmu allah dai yasa muna da rabo , daga can bangaren ammar yace "wai waye wanda yayi muku  hanyar samun nysc dinku a Z&A  ?"ta sake fad'ad'a fuskarta da murmushi sannan tace "wani tsohon saurayina "kai dan allah?wallahi kuwa malamin islamiyyarmu ne mutumin kirki ai ina ganin da allah ya qaddaro aure a tsakaninmu da yanzu ana daf da bikinmu  amman yanzu babu wannan maganar ".me ya faru da babu maganar "long story ne sir "tana rufe bakinta  tajiyo  muryar aunty fati  tana cewa "ina maryama !"


mikewa aunty tayi da sauri tare da kallonta ganin ta shigo mata babu ko sallama kamar wata zararriya  " ina maryama take ?" jiki  a sanyaye maryama ta kai dubanta ga kofar d'akin ,sannan a tsanake cigaba da waya da oga ammar har  ta qarasa ninke  riga kwaya d'ayan  dake hannunta ta had'a da sauran  kayayyakin da take nikewa muryarta a sanyaye tayi masa sallama ta mike ta  ajiye kayan  a ma'ajiyarsu sannan ta fito parlour'n  tana jin mummunar fad'uwar gaba wanda adaidai wannan lokacin sautin muryar aunty ya  shiga kunnenta "maryama ta .."tana d'akinta  "yauwa hakan ma yayi kyau dana sameta a gida ,ta sheida miki yadda mukayi daita ?".
numfashi Aunty ta sauke tace "akan me kenan?Karya kike mara mutunci kice baki san komai ba dan nayi imani babu abinda take boye miki idan kuma baki sani ba bari  ni na fad'a miki da kaina akan aurenta da muktar ne  nasan kina sane  da zamansa karki ce min a'a kiga tashin hankali yanzu ."


nan da nan zuciyar maryama ta jagule taji kamar ta d'ora hannu aka tasa ihu ko taji saukin zafin da zuciyarta take mata ."aunty tayi shiru tana kallon Aunty fati a tsanake kafin ahankali tace " idan wannnan maganr ne ta fad'a min "amman  .."ya isa !tunda ta fad'a miki ya kuke ciki ?akan me kenan aunty fati ? wani kallon raini aunty fati tayiwa Aunty sannan tace "kan batun saka ranar aurensu  mana dan na matsu  na matsu naga maryama  a gidan muktar".aunty muktar yaron kirki ne ,sannan  bashi da wata makusa amamn  maryama ta nuna min bata da ra'ayinsa mafi alkhairi abar maganar allah ya had'a kowa da rabonsa na alkhairin ".Karya kike mara mutunci  ga dukkanin alamun  na fahimci
daga gareki zaa samu matsala " ta fad'a tana zare mata  ido "ai wannan  matar  bata da kai bata san mai sonta ba yaro ya had'u yana da aikinsa mai kyau ,ita  yartaki ba yar  kowan kowa ba dilalin kashi zaki ce bata da ra'ayinshi "inji cewar aunty hasana data shigo ."



aunty ta kalleta wani iri ,cikin jin haushi tace "idan dai haka ne me yasa ke bazaki bashi d'aya daga cikin ya'yanki ba ?"ki bashi Islam ko kaulat mana ."
"Oh haka ma zaki ce ?kwarai kuwa na fad'a tunda auren zumunci kuke só had'awa kunga zumunci zai fi maku dad'i ,ina dalili zaku saka min yarinya gaba dame zata ji duk mutanen kirki kun kuresu zaku wani had'ata da muktar ".amman yanzu kika gama cewa muktar yaron kirki ne ?ai bazan ta'ba aibanta d'an wani ba  tunda inda nawa " oh kice dai kina gudun yarki ta auri dan shashaye?aunty hassana tayi mata tmbyr tana murmushin mugunta "aunty tayi shiru kawai tana kallonta zuciyarta na tafarfasa."



"ke yanzu har kin guji  mai hali irin nashi ?"kinga ni bana son kananan magana aure ne dai maryama bazata auri muktar ba tun da bata son shi  "wallahi baki isa ba karewa ubanta ma menene ."?inji cewar aunty fati hankalin maryama yayi matukar tashi jikinta rawa tace "aunty fati please mana dan allah duk abun bai kai haka ba bana son ana tashin mahaifina ta wannan han.."bata qarasa ba ta qara bud'e murya "wai  dan giya ne  da shaye shaye bakya son ana fad'a kome ?"maryama ta sunkuyar da kanta kasa tarasa meke mata dadi "wannan wani irin dangi ne gareta?" hakika aunty bata masu adalci ba data zabar masu uba acikin wannan zuri'ar ."


Cikin wani zare ido da maseefa aunty fati tace "kaf dangin ubansa babu mai shaye shaye bare giya sai acikin dagina kinga kuwa ubanki ya gada, aunty ta runtse idanunta tana jin wani irin zafi acikin ranta "wallahi aunty fati wannan yarinyar muguwar yar bakinciki ce kuma ba kowa take wa bakinciki ba sai wannan tsinanniyar uwaratata takewa domin ubanki kwalbar giya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login