Showing 81001 words to 84000 words out of 167047 words

Chapter 28 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

jikinta har rawa yake wajen fito dashi .


a kitchen ta zauna taci nan da nan zufa ya rufe ta da kyar ta mike ta ajiye plet acikin zink ta sake bud’e frdge ta d’auki vatermilk ta kafa abakinta bata ajiye kwalbar ba sai data shanye tass sannna ta ciro apple da inibi ta daura akan plet ta yayyaka kanana ta dawo d’akinta koda ta shigo wayarta ta kunna kanta ta kulle dakinta ta zauan ta dauki wayarta ta hau what’s app tana duba sakwanin kawayenta suna ta tambayata “ ina ta shige kwana biyu wasu kuma suce wai dadin aure yasa yanzu ta rage hawa online ita dai dariya kawai take musu tana fad’a masu yadda tayi mugu kewarsu bayn ta gama dasu ta kira mahaifiyar ta sun jima suna waya inda take jaddada mata lallai taje airport gobe ta karbo sakonta tun washegarin ranar da sukai magana ta aiko .”


Washegar da ATA zai fita bai bada umarnin cire wutan gidan ba sai dai ya zare key kitchen ya wuce dashi koda ta sauko taga babu key ta fashe da dariya har da tafa hannu ta koma d’akinta ta d’auki waya ta turawa auta sako akan abinda yayanta yayi tana dariya nan take nana hauwa’u ta kira suna masa dariya maryam tace “ga keyn dana sace zanyi amfani dashi wallahi sister wannan yayan naki mugu a duniya babu kamarsa ,ki dai bi ahankali kar ya gane azabtar min dake kunnenta makale da waya ta sauko ta bud’e kitchen lafiyayyen breakfast tayi mai kyau tana ci suna waya da nana hauwa’u bayan gama ta sallami nana hauwa’u ta bar gidan batare da izinin ATA ba zuwa airport ta karbo sakonta a parlour’n gidan ta tsaya tana bud’e bakar jakar dake rike a hannunta wata yar qaramar tukunya ta gani ta sauke numfashi tare da maida tukun yar cikin jakar ta mike ta shige d’akinta tayi masa kyakkyawan ajiya acikin duro dinta har zata rufe durowar idanunta ya sauka akan littafin addu’oin da mami ta bata lokacin da zata tare ,ta dauka tana dubawa ko sau d’aya batayi tunanin ta duba tayi amfani da wasu abubuwa daga ciki ba ta zauna rike da littafin tana qoqarin dubawa wayarta ta fara ringing dan haka ta ajiye ta d’auki wayarta kiran mahaifiyarta ne .”


Har karfe goma shadaya na dare maryam na zaune tana jiran dawowar ATA sai dai shiru bai dawo gida ba, karfe shabiyu daidai ya shigo tana jin motsin shigowar motocinsa ta zabura ta mike tare da adduar neman saa jikin labulenta ta qarasa cikin sauri taga yana tafiya har sanda ya nufi kofar shigowa ta saki labalen tana cewa “ya Allah ka bani sa’a akan maganin nan bakin kofar d’akinta ta dawo ta labe tana kallonsa ya bud’e kofar dakinsa ya shiga batare daya zare key ba wanda ga dukkanin alamu ya manta ne sadaf sadaf ta bud’e kofar d’akinta ta fito ta tura kofar d’akinsa ta leka baya nan sai kayansa ta hango akan katifa alamun ya shiga wanka ta janyo kofar ta rufe ahankali sannan cike da tsoro ta cire key d’aya acikin key’n dakinsa tayi wuf ta fad’a d’akinta ta kulle tana dafe qirjinta da hannuwanta duka tare da furta.”


“allah na gode maka da kabani wannan saar gobe da safe yana fice wa daga gidan zan shiga nayi abinda zanyi “kai maryam mai yasa zaki dogara da irin wadan nan abubuwan wannan fa shirka ne qarara zaki aikata domin tukun yar tsaf ce ummah ta aiko miki dashi rayuwar nan fa babu tabbas babu yadda allah bazai yi ikonsa ba qaddara kuma tana fadawa bawa daidai yadda allah ya hukunto masa amman addua itace mafuta cikin ,rayuwar aurenki da Adam qaddara ce ki cigaba da hakuri zama dashi haka sarewa ta kalli mukulli hannunta kafin ahankali ta kira wayar mahaifiyarta ta koma can karshen dakin tana dauka “tace umma abin nan kuwa zan iya sakawa yaya Adam shi ? bana son abinda zanyi na cutar dashi ,sannnan hakan nan wannan aikin yake bani tsoro tun da kika fad’a min zai iya mance har mami tsoro ya shigeni ,rayuwar mami babu Adam akwai damuwa bugu da qari ta damqa min amanarsa idan na cutar mata dashi allah bazai barni ba “.


“ina so mana umma ina son nayi rayuwa mai dadi dashi domin hakan yana da mahimanci ga rayuwata ko sau daya ya soni ya furta ya kuma kula da rayuwata bangaren ummu kuwa cewa tayi “tunda kina son faruwar haka ki manta da wata uwarsa Ke Kinsan irin nata mulkin datayi lokacin mahaifinsa ?tayi mulki kuma har yanzu tana kai haka kawai take juya kowa son ranta ?dan haka kiyiwa kanki adalci ki cire wannan tausayin Kiyi abinda ke gabanki domin raba zuciyarki da nauyi “wallahi ummah ina jin zafi har acikin raina ace sai nayi asiri yaya Adam zai soni “ta qarashe maganar tana zubda kwalla mai zafi bata jin zata iya daukar wannan nauyi “dole kiyi tunda soyayyar da kike masa da biyyya tare da hakurinki bai yi miki amfanin komai ba ,ke bari na fad’a miki wani abu ko Adam nason aurenku dole sai kin tashi tsaye akanshi dan irin masu taurin kansu sai da asiri ake samun kansu Kiyi qoqari kawai ki saka tukun yar nan da zarar ya kwanta aiki ya fara kenan sai dai wani Adam din bashi ba zai fad’a wata duniyar ta dabam lokacin da zai dawo kin tara masa yaya masu yawa “.tana gama fad’ar hk ta katse kiran .”


Yana fitowa daga wanka cikin sauri sauri ya soma shiri dan tafiya ce ta samesa zuwa kasar ingila karfe daya da wasu yan mintuna jirginsa zai tashi bai sheidawa kowa ba har mami ya fito da wata yar qaramar jaka ya kama hanya ya fice ya bar gidan washegari maryam bayan ta gama gyara gida ta bud’e dakinsa ,tana kallon dakin , da mamallakinsa na nan bata isa ta tsaya cikinsa cikin natsuwa ba gaban mirrow dinsa ta qarasa ta tsaya tana duban frame din hotonsa cikin hadadden suit baki idanunshi manne da farin glass ,tana kallonsa tana jin yadda zuciyarta Ke sake narkewa akan son shi wata irin soyayyarsa Ke ratsata bata ta’ba son wani halitta kamar yadda take son shi ba .


ta kai hannunta ta dauki freme din ta rungume ajikinta tana mai lumshe idanunta“akanka na aikata manya manya laifi masu muni da tsayawa arai me yasa bazaka sauko ka karbeni ba ?“wallahi ina sonka da sonka na rayu tun tsawon rayuwata soyayyarka bata misaltuwa yaya adam, a baya nayi babba kuskure a yanzu kuma zan sake tafka wani kuskure akan Kuskuren baya ka sausauta min zuciyata bazata cigaba da bugawa ba idan har babu kai ka soni batare da na aikata wani laifi ga mahaliccina ba “
“Sorry maryam adam fa yayi nisa a qiyayyar ki bazai ta’ba sonki ba karki mata kalamansa na shekaranjiya
“ai tunda kika nacewa aurena ni ne zanyi sanadin mutuwarki dan tun tuni naji rashin alkhairi akan aurenki kinga idan kin mutu ni kuma na tsinci kaina a prison hankalin ke da sweetheart zai kwanta amman tabbas ina ji ajikina idan baki kasheni ba ni zan kasheki .”


“Tabbas zai iya komai dan kawar dake a duniya saboda tsananin kiyayarsa gareki kiyayyarsa tun fil azal ce wato tun ran gini tun ran zane karki cutar da kanki gara Kiyi amfani da komai ya zama mallakinki na har abada ,amman kuma duk daren dadewa asiri zai karye maryam ga laifin asiri ga hakin mami akanki ko ba dade hakinta zai bibiyi rayuwarki ranar nadamarki na zuwa kuma alokacin nadamar bazata yi miki amfani ba jikinta yayi sanyi tana zubar da hawaye tana makale da hotonsa “maryam ki bar wannan tunani a yanzu yadda yaya adam zai soki shine mafuta agareki ,ki dauko tukun yar ki saka ki kama gabanki jiki a sanyaye ta ajiye freme din hannuta taje ta d’auko tukun yar ta daga katifa tasa sannan ta gyara masa d’aki tsaf ta fito ta kulle ta zare key ta koma dakinta ta shiga yanat gizo .”


Maryam batasan da tafiyarsa ba ta dai zuba ido taga dawowarsa mami kam tun a daren jiya taji batun tafiyarsa ,ranta yayi matukar baci sakamakon rashin fad’a mata da bai yi ba amman kuma hakan bai hanata yi masa addua da fatan alkhairi arayuwarsa ba , bangaren maryam kuwa hankalinta yayi matukar tashi ganin bai dawo ba har washegari batayi tunanin tafiya yayi ba ta d’auka yaji yayi mata kamar yadda ya saba ,hankalinta a tashe ta kira mahaifiyarta ta sheida mata halin da’ake ciki “ki kwantar da hankalinki tabbas kaidarsa kwanaki uku ne zai tashi aiki amman akwai mafuta dan zaa iya yin wani sabon aiki “ irinsa umma? Eh mana irinsa zaayi “ wannan maganar ya kwantar da hankalin maryam ta cigaba da tsabgoginta tunda tana da wuta kuma tana da keyn kitchen a hannunta burinta ya dawo ya bud’e d’akinsa ya kwana akan gadon .”



Washegarin ranar da ya cika kwanaki bakwai nana hauwa’u ta kirata ta fad’a mata qawarsu safiya ta haihu har jibi suna dan haka jibi su hadu a gidan safiy daga suka hira inda nana hauwa’u Ke tmbyata ko yayanta ya dawo ?bai dawo ba har yanzu ,sister kina ganin bancin na sace keyn kitchen ba niyyar kasheni yaya adam yayi ba kamar yadda ya fad’a “? nana hauwa’u tayi murmushi “bazai ta’ba kashe common sauro ba bare mutun wannan duk fad’a yake kuma tunda akwai waya a hannunki kuma akwai wuta a gidan duk zai zo da sauki ba kamar kwanaki ba koni da kaina zan dinga zuwa ina kawo miki abinci sun jima suna hira a tsakaninsu .”


Ranar da ya cika kwanaki goma cif sai gashi ya duro gidan tmkr mashi alokacin maryam na tsaye gaban madubi tana ta shek'a kwalliyar zuwa suna kamar wacce zata canja fuska, ta shafa wannan ta goga wancen ta dangwala wancen, ta d'auki lokaci me tsawo kafin ta gama,dan kwallinta ta d'auka ta d'aura, ta dauko takalmi hil tasa saida ta k'are ma kanta kallo ita kanta tasan tayi kyau dan ita bata ganin illar rashin tsawonta tunda akwai hil kuma duk tsadarsu tana siya sai dai idan bai mata ba
tana murmushi ta d'auko mayafinta da jaka ta fito da zumar zuwa gidan suna a hanakali take taku kwas kwas saitin takalminta kenan tana gama saukowa qasa kawai taga mutun zaune a parlour’n yana cire takalma ,a natse ya dago yana duban step sakamakon qarar takaliminta mai mugun tsini kallo d’aya yayi mata gabad’aya yaga ta canza shi da yake jiran ya ganta ta qanjame tsabar yunwa amman yaga tayi fresh .”


baki ya saki yake kallonta kafin ahankali ya kai dubansa ga kofar kitchen nan ya hango key kwaya d’aya,wani irin tsoro ne ya shigeta nan take jikinta ya kama rawa wani irin numfashi ya sauke ya dawo da kallonsa gareta tun daga qasa ya sake daukar kallonta kafin ahankali muryarsa a can qasan makoshi yace "ke ina zaki?”yau ne sunan wata k'awarmu da ta haihu shine zamuje tare da sister yana qarasa cire takalminsa ,ya mike tamkar zaki ya fara nufota yana cewa “a ina kika samo extra key na kitchen?ganin yana nufota cikin wata irin tafiya mai daga hankali qirjinsa har wani dagawa yake duk wani taku da yayi sai zuciyarta ta buga da karfi .”
bai fi sauran taku daya ya qaraso gareta ba kawai ATA yaga tayi wuli da jakar hannunta ta saka wata razananniyar qara ta zube qasa tare da dafe kanta tana jujjuya shi cikin rashin jin tsoro ATA ya qaraso gabanta ya kai hannu da niyyar sauke mata mari yaji ta daka masa tsawa cikin wata irin kaukausar murya tana fadin “kar ka kuskura ka taba mana godiyarmu.”cak ya tsaya yana kallonta cike da mamaki


“hahhhh tashiga babbaka dariya cikin wata irin murya mai cike da ban tsoro tashiga fad’in “wannan ba maryam bace daka saba duka kana wulakantawa nine aljanu gagare wato kai kullum tunaninka dukanta da wulakanta mana godiyarmu ,ka dauka bata da gata ne, ita din fa matarka ce ba baiwarka bace ,tana magana tana nufosa, ATA ya dan ja baya kadan yana qare mata kallo tsab “ daga yanzu idan ka sake kai hannunka jikinta ko wulakantata hukuncinka agareni shine kisa.” ATA ya kankance idanunshi yana qare ma fuskarta kallo da abinda Ke fitowa bakinta da kuma yadda idanunta suka juye kamar gaske kamar kuma wasa tana matsoshi yana ja da baya.” bakasan karfin aljanin gagare bane shiyasa kake abinda kake yi wallahi duk ranar da ka sake bata mata rai na rantse bazan duba cewar matarka bace sai datse maka numfashi kafin ka kashe mana godiyarmu mune zamuyi ajalinka.”





Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


             Page 16



Daga inda yake tsaye yake qare mata kallon tsab yayinda gaba d'aya yanayin jikinta ya sauya exactly kamar yadda masu aljanu suke react, maryam  tana fidda ido ta sake kallon ATA  that's lookin  at her wani iri, gashi nan dai  kamar ya tsorata  da yanayin ta  kamar kuma bai tsorata ba ,amman zatayi komai dan ta tsorata shi ,shi kuwa he's thinking of  gaskiya ne ko karyar aljanu zata masa.  tana kallonsa ya sake d'an ja baya kad'an adaidai lokacin da wayarsa ta soma ringing iPod dinsa dake manne da kunnensa ya ta'ba taji ya soma  magana can kasan makoshi ta yadda bazata iya jin me yake fad'a ba ,shirun da taji yayi ya cigaba da kallonta ya bata damar sake nufosa bai fi sauran  taku d'aya ta isa garesa ba ,sai ji tayi ya buga mata wata razananniyar tsawa wacce tasa gabad'aya gidan ya amsa sautinsa ."


a zafafe yace "ke maryam meye haka ?wani irin hauka ne haka ? hahahaha ta cigaba da babbaka dariya cikin wata irin murya tace "sau nawa zamu  fad'a maka wannan ba maryam bace god'i..." wani gigitaccen mari ya zuba mata wanda yasa nan take ta durkushe qasa dafe da kuncinta dan sai da taji ganinta da jinta  tare da numfashinta ya d'auke na wani lokaci ,kafin ahankali numfashinta ya dawo  ta saki wani marayan kuka mai cike da ban tausayi tana cewa "me nayi maka ? "ke ni zaki yiwa wannan iskancin da rashin hankali? ?ni zakiyiwa karyar  aljanu  ?gaban maryam ya bada rasss ya shiga bugawa da sauri sauri "kin manta ko waye tsaye a gabanki ?ko kinga alamun zuciyar tawa tana cike da tsoro ? ko nayi miki kama da matsoraci ?yayi mata tambayar a here tare da  kai hannu ya damki  wuyan rigarta ya kifa mata wani gigitaccen mari ."



ta saki qara mai sauti tana qoqarin kwatar wuyanta daga hannunsa amman ta kasa dan baqaramin damka yayi ma wuyanta ba  yana huci  tamkar zaki "wallahi idan hauka kike ji  na fiki hauka "ya fad'a yana zaro mata idanu kamar zasu fad'o qasa kuka ta fashe dashi har da majina "ki sani ba aljanu ba ko haukacewa zakiyi babu ruwana kuma hakan bazai  ta'ba girgiza zuciyata ba ."wani kuka ta sake saki tana rokonsa" dan  allah kayi hakuri ka sakar min wuya  numfashina. wai ma me nayi  maka ne  "?wata tsawa ya buga mata tare da sakinta da karfi sauran kad'an bayanta ya bugi center table din dake parlour'n tayi taga taga ta tsaya bisa qafafuwanta tana shafa wuyanta yayinda  jikinta ke wani irin kyarma. ta tsura masa ido tana kallonsa hawaye na turereniyar zubowa "wannan fa zalinci ne daga shigowarka ka hau marina da shake min wuta tayi maganar cike da matsanancin tsoro sai dai jarumtar data aro ta sanyawa jikinta bai sa ya gane tsoronta ba  ."


"Laifin me nayi maka ?ta sake tambayarsa yayi shiru yana kallonta a wulakance maryam ta share hawayenta ta cigaba da magana "ban maka laifin komai ba  ,idan kuma key daka gani ne ,nice na cire domin bazan zauna yunwa ta kasheni ba , yau kwanaki goma kenan rabonka da gidan nan  ,da kai a tunaninka haka zan zauna nayi rayuwa tattare da yunwa ? "me kake so dani yaya adam?  gaskiya wallahi na gaji na gaji!!  da  wannan zalinci,  ka tozartani ni daga ni sai kai ,ka tozartani agaban kowa   ga azabtarwa ga horon yunwa "Enough is enough yaya adam da wannan tozarci da wulakanci biyayya fa ba hauka bane ..."ai bakin maryam tsayawa yayi cak sakamakon ganin "ATA ya nufota gadan gadan cikin tsananin fushi kamar mayunwanci zaki idanunshi sun kad'a sunyi jajur a matukar zuciye ya cigaba da magana yana hararta "shut dare kuma ki natsu ki saurare ni da kyau karki kuskura ki sake magana batare da izinina ba ".



Idan akwai abinda yafi shiru maryam tayi agurin rawar da jikinta yake kuwa sai ya baka mamaki "wato Ke gaki yar iska wuyanki ya isa yanka ni zaki dinga fad'awa magana son ranki ?"ba wai na fad'a maka maga..."I said shut up ki shiga hankalinki har yau baa haifi d'a ko 'yar da ina magana yana magana ba,  ba'a min haka sai dai ni nayi  kuma kinsan da zaman haka ni senior man ne you understand ba'a min haka koda kuwa ana min ke baki isa kiyi min  ba saboda baki da wannan darajar da wannan matsayin a wajena .dan haka to be your first and last da zaki fad'a irin wad'an  nan maganganun saboda bazan barki ba idan kin sake" shiru  maryam tayi cike da tsoronsa wanda a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login