Showing 93001 words to 96000 words out of 167047 words
Chapter 32 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
tsare dan Allah idan kun shiga jirgi kayi masa hoto ka turo min ta fad’a tana murmushi shawul ya juya ya bi bayan ATA yana jinjina girman hakurin maryam da girman soyayyarta garesa allah ya hada masa komai da komai na duniya amman girman da nuna isa yasa ya kasa gane salihar macen daya samu .”
Tunda ATA yayi tafiyar nan tashiga damuwa madadin tayi farinciki amman sai sabanin haka tunanin rayuwar da take a gidan data rashin isashen abinci agidan da kuma ta kewar mijinta dan yanzu manage rayuwarta kawai take hakan yasa duk tabi ta zabge ta rame abun duniya duk ya isheta gashi babu wanda zata iya tun kara da wannan batun mutun daya ce zata iya fadawa itace nana hauwa’u kuma tasan zata nemammanta mafuta amman dole mami taji idan mami taji kuma dole ATA yaji kuma tasan bazai barta haka ba sai ya gana mata izaya kala kala wata zuciyar tace ta kira mahaifinta ta fad’a masa shima dai dole zai fadawa mami dan abun kaskanci ne ace kamar gidan nan babu abubuwan more rayuwa kusan kullum abu d’aya take ci idan tayi baki duk kunyar duniya ta isheta wani lokacin nana hauwa’u take kira ta tura mata kudi saboda baki to kuma ta dinga tambayarta kenan ?”.
bayan sati biyu mami ta sake kawo mata ziyara alokacin maryam tana wanke wanke a kitchen tana kuka har da shesheka daga bayanta taji sautin muryar mami “Ke me ya sameki hk ?muryar mami yasa maryam ta juya bayanta da sauri tabbas itace tsaye nan da nan tashiga goge hawayenta “ina adamcy?ta tambayesa tana qarasowa gareta tare da kallonta “yayi tafiya zuwa hollond “ kenan bai dawo ba ?maryam ta gyda mata kai alamun eh nan da nan mami ta shiga cikin kitchen din tana bubbude cabinet babu komai na abinci sai shimkafa wacce bata wuce kwatan buhu ba “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun “yanzu haka kike zaune kike rayuwa acikin gidan nan babu kayan abinci ?”mami ta fad’a tana maseefa “daman an fad’a min to wallahi bazan dauki zama da yunwa ba ,duk arzikin da allah yayi maka adamcy a iske gidanka haka wallahi kaji kunya .“mami babu wani problem’s fa ina cin abinci ,karya kike munafukar allah karesa zakiyi kina cin abinci kalli yadda kika dawo duk kin qare kin lalace .”
“to mami Kiyi hakuri amman shi yaya bazai san ko akwai kayan abinci ko babu ba saboda “me bazai sani ba ?ba zamansa kike yi ba .”?shiru tayi tana danne abinda Ke taso mata mami ta dubeta tana mata kallon tsab batare da tayi magana ba kafin Ahankali ta cigaba da magana “maryam kina boye min abubuwa amman kuma ina sane da komai fa hatta kudin cefane adamcy baya baki bare aje kudin kashewa “ to mami wannan ai ba komai bane idan da kwanciyar hankali duk mai sauki .“lallai maryam son adamcy ya gama rufe miki ido .maryam tayi murmushi ta riko hannunta tana cewa “dan allah mami ki kwantar da hankalinki karki masa magana kinsan halinsa yanzu zai dauki maganar da zafi daman ina jiran idan komai ya qare zan fad’a miki ki aiko min dashi ,ai bazan bar kaina da yunwa ba ta zaunar da mami akan kujera .”
cike da natsuwa mami ta cigaba da kallonta yayinda maryam ta kwantar da kanta saman cinyar mami tayi kwanciyarta lamo tare kamkame jikinta hawaye na gangaro mata “son adamcy ya zame mata masefa ita kanta tana son raba kanta dashi amman ta rasa ta ina zata fara kullum sonshi da kishinsa na makale da zuciyarta most especially data d’and’ashi taji dadinsa duk da baya cikin haiyacinsa amman wallahi ko a yanzu wani irin kewar mijinta ke damunta , kuka take sosai akan cinyar mami ina ma yadda mami ke sonta shine yake sonta haka da damuwarta bata kai haka ba a yanzu tasan damuwarta na shafar mami kuma a dalilinta mami zata iya muzgunawa yaya adam ita km abinda bazata so ba Kenan ba batasan abinda zai sake
hassalashi akanta dan bayan izayar da zai mata tana masa wani irin matsanancin so wanda batasan tun lokacin data fara masa ba."
Mami ta numfasa tare da daura hannunta a saman kanta “duk itace silar komai ,itace silar jefa rayuwar yar mutane cikin ukuba yanzu ita yaya zatayi da wannan auren ?”mayye rudeta da sha,awa cikin hada wannan auren ? take zuciyarta ta bata amsa da
rashin hakuri da maida lamarinki ga Allah ne yasa kika aikata wannan kuskure kin hada aure dan kawo kwanciyar hankali a zuriarki gashi hakan bata kasance ba sai zallar damuwa a boye mami take goge hawayen dake bin kuncinta ‚ domin tana matukar tausayawa maryam da bata hada wannan auren ba maryam da bata kamu da son danta ba Ahankali maryam ta shanye kukanta sakamakon tunowa datayi akan cinyar mami take da goge
hawayen idanunta ta mike zaune ta riko hannunta cikin nata “dan girman allah mami karki masa magana zan miki list din komai ki aiko min dashi “kina ganin rayuwarki haka shine mafuta ?to ya zanyi mami bani da zabin da wuce zamana acikin gidan nan “kina son na kashe auren nan maryam ?”
Mmn sudai
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Dan allah Ina son masu karatu su san wani abu ,bana son yanke wani abu daya danganci abinda yake cikin labarin nan domin duk abinda aka rubuta akanshi yana da matukar amfani ga makaramci kuma kowani bangaren yana buqatar a ta'ba shi domin idan an zo hukunci ,só ina son masu karatu su bani hadin kai domin samun damar cigaba da rubutu kamar yadda aka bani a kasin haka kuwa babu abinda zai haifar sai zuwa hutun rubutu ko kuma abun ya koma sai randa naji nishadi nayi typing kuma kad'an domin ina iyakar qoqarina na ganin na kawo maku komai daki daki kamar yadda yake aciki amman kamar ku bakwa gani ko kuma nace kamr kunfini hanzarin son ya had'u da mafarkinsa ko kuma son a gama rubuta labarin nan to wallahi na fiku son naga na kammala na huta shiyasa tun farko nace arewabooks zan kai wasu daga cikinku suka nemi alfarma na kawo what'sapp sannnan sunji kuma sun amince ko sau d'aya ne na dinga basu a wata amman adalci nawa yasa nake baku kullum dan abini a sannu dan nesa tazo kusa 😉😉."
Page 18
Kan maryam yayi wani irin mugun sarawa da karfin gaske sakamakon jin abinda ya fito daga bakin mami ,yayinda qirjinta ya dinga bugawa fiye da kaida “kina son na kashe auren nan maryam ?” kwakwaluwarta ta sake maimaita mata kalmar da take daf da tarwatsa rayuwarta ahankali ta zame ta zauna a qasa cikin tsananin tahain hankali mara misaltuwa tayi shiru tana jin yadda magnr mami ke yawo acikin kwakwaluwarta da zuciyarta, haka ne ma yasa jikinta ya kama rawa gashi mami taki d'auke kwayar idanunta akanta tana jiran taji abinda zata ce akan hukuncinta . gano yanayin cewar maryam ta shiga cikin tsananin damuwa yasa mami kiran sunanta .."
“maryam..”!
"ta d'ago kanta da kyar ta zubawa mami idanunta da suka sauya kala tsabar tashin hankalin data tsinci kanta "kinji abinda na fad'a kuwa ? maryam ta lumshe mata ido kawai dan bazata iya magana ba a halin da take ciki wanda take jin yafi duk wani tashin hankali har ma da qiyayyar yaya Adam gareta ."ki bud'e baki kiyi min magana domin kawo qarshen wannan matsalar ,nice da kaina na had'a auren nan naku ,idan kina ganin bazaki iya cigaba da zama dashi ba wallahi a bud’e take bazan cigaba da takura miki ba ko kuma na ji haushinki dan kinyi min qoqari fiyye da tunanina ,dan zama da adamcy sai mai katoton hakuri zai iya, dashi kuma daman yana cikin dalilin da yasa zuciyata ta tsallake kowa acikin yan’uwansa da yan’uwana ta za'beki amatsayin matarsa ,amman yanzu ni kaina na gaji kuma nasan kema kin gaji maryam hakuri kawai kikeyi .
Ruwan hawaye ya cika idanun maryam “me yasa mami zatayi wannan tunanin ?ita dake cikin taskon wahala ba tace ta gaji ba me yasa ita zata gaji har da yunkurin rabata da muradin zuciyarta ?ta yiwa kanta tambayar tana qoqarin danne kukanta “idan dai har kina ganin babu damuwa maryam zan rabaku kuma a yau domin bazan juri ganinki cikin wannan tashin hankali ba. kije ki auri wanda zai soki ya kula da rayuwarki shi kuma ya cigaba da zama haka tunda rayuwar daya za’ba wa kansa kenan ."zuciyarta maryam kamar zata tarwatse tsabar tashin hankalin data sake tsinci kanta ciki tayi shiru tana kallon mami tana assessing maganarta fuskarta d'auke da tarin damuwa tana lissafa idan ace wani ne ya fad'a mata haka da ita kad'ai tasan irin matakin da zata d'auka akanshi ,amman mami ce babu abinda zata iya "zazzafan numfashi kawai ta sauke tare da dukar da kanta qasa jikinta na wani irin karkarwa tana son boyewa mami damuwarta ."
mami ta kai hannu ta d’ago ha'barta tasanya kwayar idanunta cikin nata ido cikin ido suke kallon juna ruwan hawaye ne taf acikin idanunta "kinyi shiru maryam banason shirin nan naki ,banason kiji aranki kamar nice silar shiga damuwarki domin ni karon kaina ina jin haka araina cewar duk nice silar shigarki cikin wannan tashin hankalin ,kina zaman zamanki lafiya tare da masoyanki masu sonki da qaunarki na shigo miki da abinda ya zame miki damuwa ,banason ganin tashin hankali shiyasa nake neman izininki ."wannan buqata ta mami ba abu bane mai sauki ko yuwuwa agareta "idan zaki d'auki sharawata maryam ki rabu da adamcy ki huta nima zuciyata ta huta "anya zan iya kuwa mami ?na rabu dashi wanda rabuwa dashi din yana nufin har abada bayan a yanzu ne ma nake jin bazan iya daidai da kwana d'aya batare dana yi masa magana ko sanya shi acikin kwayar idanuna .
“Maryam mami tafiki gaskiya rabuwa da yaya Adam shine mafuta agareki amman kuma tashin hankali ne mai tsanani ga rayuwarki wanda baki san ranar fita acikinsa ba .ta sake d'agowa taga har lokacin ita mami take kallo tana nazarinta "ki rabu dashi maryam !mami ta sake bata umarni a karo na biyu "amman mami kina ganin rabuwar mu itace qarshen komai "?tayi maganar muryarta da jikinta na rawa
"zaman da kuke a tskaninku maryam bashi da wani amfani a yanzu ni kaina ina nadama had'a wannan auren, na d'auka komai zai samu sauyi a samu cigaba ashe damuwa akan damuwa kawai za'a haifar. murmushin 'bacin rai ya bayyana akan fuskar maryam kana ta girgiza kanta "please maryam Kiyi tunani mai kyau kamar yadda nayi bana son ki bata shekaru cikin wannan halin, still dai shiru maryam tayi wanda hakan yake nuna alamun shawarar mami bata mata dadi ba “maryam ba kya tausayawa kanki ?ki tausayawa kanki maryam nasan kina yin komai saboda ni ne na kuma gode da biyayyarki gareni allah yayi miki albarka ."
Zuciyar maryam wani irin zafi take mata da tuttukin bakinciki tana jin wata irin tsantsar soyayyarsa na sake ratsata baza ta'ba kuskuren rabuwa da yaya Adam tayiwa kanta wanan alqawarin suna tare mutuwa ce kawai zata rabusu ,koma yayi qoqarin rabuwa daita baza barshi ba tagumi ta zuba cikin zullumi da rashin sanin madafa dan bazata iya aikata abinda mami take buqata ba ,duk magiyar da mami take mata amman maryam taki bud'e baki tace zata rabu da ATA." sosai mami ta fahimci soyayyar adamcy din ce mai tsanani ta hana maryam bin umarninta jikin maryam a matuqar sanyaye ta mike batare data kalli fuskar mami ba tace "mami dan allah ki bar maganar rabuwar nan haka ,ni abinda nafi buqata daga gareki shine addua ko kad'an yaya Adam ya soni acikin zuciyarsa tana gama fad'ar tace "bari naje na kawo miki abun sha har tayi taku biyu ta taya "dan allah mami karki masa magana akaina tana gama fad'ar haka ta cigaba da d'aga qafafuwanta ."
Mami tabi bayanta da kallo duk ta zube ,duwawukan nan nata duk sun kusan qarewa, ramar da tayi tasa ta qara kankacewa ,ta fito daga kitchen rike da cup da jug ,kawai taga mutun tsaye kikam tamkar wani jami'in tsaro cikin wani had'ad'den suit ash colour haka ma takalman dake sanye a qafafuwansa ash ne sai sheki suke ,tsintsiyar hannunsa makale da agogon rolex ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ga sihirtaccen kamshin turarensa mai tsananin kamshi ,nan da nan kamshi parlour'n ya canza zuwa na kamshinsa ."suka tsurawa juna ido shi yana kallonta cike da tsantsar tsana yayinda ita Ke kallonsa cike da tsantsar qauna satinta uku kenan bata sanya shi acikin kwayar idanunta ba
bata san tayi kewar ganin kyakkyawar fuskarsa ba sai a yanzu da take kallonsa tsaye agabanta ,kullum kamar qara masa kyau ake sam bazaka ce 40 garesa ba ,ga kamshin daddan turarensa duk inda ya shiga sai anji wannan mayataccen kamshin nashi mai tsayawa arai da dagula lissafi,taji kamar tayi wulli da cup din hannunta taje ta rungume shi ajikinta taji d'umin jikinsa ."
Qaramin tsaki yaja ganin yadda take kallonsa kamar bata ta’ba ganinsa ba arayuwarsa baya son yawon kallo ya d'auke kwayar idanunshi ya qarasa shigowa sosai ya zauna kusa da mami ya baje akan kujera yana furta "wash allah nah na gaji “yayinda maryam ta qaraso tayi masa sannu da zuwa aciki ya amsa mata shima ganin mami zaune ne ,a natse maryam ta fara hidima da mami "sweetheart a she dana biya ta gida bazan sameki ba ?"tace uhm bazaka sameni ba amman nasan ko kwanaki nawa kayi zaka zo ka sameni zaman jiranka kallonta kawai yayi ya d'an ciza lip's dinsa yana d'aure fuskasa dan ya fahimci kamar akwai wata a qasa . mami ta kalli maryam dake zaune kusa daita taga ta girgiza mata kai alamun karta masa maganarta take ta fahimci abinda take nufi numfashi ta sauke inda ATA ya fara jan mami da hira maryam ta tashi ta dawo gabansa ta tsugunna yayi saurin janye qafafuwansa tmkr yaga mugun abu numfashi ta sauke ta sake matsowa ta kai hannuwanta ta janyo qafafunsa saurin runtse idanu yayi yana jin kamar da wuta ta ta’ba shi .”
Ahankali yaji ta soma kwance igiyan takalminsa d’aya kamar ya zare qafarsa ya buga mata takalmin a fuska amman ya share sakamakon darajan mami dake gurin ,tana gama cire masa takalman ya janye qafafuwansa ta kwashe takalman ta nufi hanyar step ."ya bud’e idanunshi ya cigaba da jan mami da magana acikin hirarsu da mami take fad'a masa kwanakin nan zuciyarta na mata nauyi "wallahi adamcy bana jin dadin zuciyata jiya fa da kyar na samu na runtsa numfashina kamar zai bar gangar jikina "haba sweetheart ya zaki min haka?ya kina jin ciwo ajikinki amman ki kasa fad'a min ko fad'awa aunty shahida "yaushe rabona da kai adamcy ?” duk ya’yana suna zuwa su duba lafiyar jikina ,amman kai yaushe rabon kazo wajena ?idan dai mai rabawa ta rabamu ai shikenan kowa ya huta ko da yake kai ne zaka huta idan na mutu amman sauran zasuji babu dadi "allah ba zai sa naga wannan ranar ba "kema kinsani sweetheart kina cikin raina da bamu raba gida ba ,babu abinda zai sa kiyi rashin ganina a duk lokacin da kika só ,dole duk tsananin aikin daya sakani gaba dole zan dawo gida na kwanta .”
“ wallahi yanayin aiki ne yanzu da kuma d’a nisan da mukayi amman da zaki min alfarmar rabuwa da auren nan da na huta domin zan dawo gidanki gbdy ta yadda zan dinga kula da duk wani motsinki "kaji dashi idan zaka kare kanka kayi amman babu ruwan aure da rashin zuwanka akai akai "to ma meye amfanin auren?me zanyi dashi tunda bana sauke nauyinsa dake kaina shiru mami tayi tana nazarin maganarsa "to ma meye amfanin auren?me zanyi dashi tunda bana sauke nauyinsa dake kaina ta sake maimaita abinda ya fad'a tayi wa maganar falla falla domin fad'a dashi dan ta fahimci abinda yake nufi idan dai ta fahimta bayan rashin kwanciyar hankalin da baya bawa maryam har da hakin aurenta baya saukewa kamar tace ya sauwake wa maryam din kowa ya huta amman maryam din take ji a halin yanzu ,domin dukkanin alamun sun gama nuna soyayyar adamcy tayi mata kamun kazar kuka "sweetheart Kiyi hakuri ki yafe min na kasa miki biyayya na kasa son abinda kike mutuwar so "wannan son ranka ne kake fad'a da nuna baa isa da kai ba "bai sake cewa uffan ba akan maganar da take sai ma canza magana da yayi zuwa ta lafiyarta "sweetheart ki shirya next week zamuje India a duba min lafiyarki "a'a ni bana buqatar zuwa koina anan ma ina samu kulawar shahida tana iyakar qaoqarinta akaina "dan sweetheart ki amince please ".
“na yafe adamcy abarni anan idan ma mutuwarce na mutu acikin ahlina allah dai ya bamu saar tafiya tunda yaji inda mami ta dosa ya lalubo wayarsa ya kira musa yana bashi umarnin yayi order abincin mutun biyu "mami ta kallesa a tsanake tare da katse masa hanzari ta hanyar cewa "mai yasa za'ayi order abinci bayan ga matarka a gida ?"shiru yayi yana karkad'a qafa "me ye amfanin haka adamcy ?"allah ya rufa maka asiri ka nemi ka tonawa kanka "sweetheart ya kike magana haka kamar baki san shirmen yarinyar nan ba ?"ai cin abincin wannan sakar yarinyar daidai yake da cin guba ai sai ta kashe mutun da