Showing 12001 words to 15000 words out of 167047 words
Chapter 5 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
ta bari kukan ya fito da sauti tun baa je koina ba tayi nadamar rashin aurensa."
"Me yasa na biyewa son zuciyata ?me yasa banyi hakuri ba ?kuka take sosai wanda kukan nata yana qara daga hankali da dawainiya da hisham gabadaya ya dawo mata wani iri sai daya dauki second talatin rungume daita sannan ya sautata rungumar da yayi mata".bai ce mata komai ba yaja hannunta ya nufi inda motarsa take "ina zaka dani ?yayi mata banza ya bude gaban mota ya sakata ya maida murfi ya rufe ya zagaya ya bude mazaunin direba yaahiga "dan allah karka kaini gida "me yasa bazaki gida ba ?tayi shiru kawai tana wasa da hannunta dan bata san me zata fad'a masa ba ."
"kin gudu akan bakya sona yanzu kuma wannan ya wuce a tsakaninmu, babu wani batu na soyayya sai na yanuwantaka ne a tsakaninmu, ai gara ki koma gida ki cigaba da rayuwarki ."tayi narai narai da idanuwa tana dubansa kallon dake tsuma zuciya da gangar jikin yaya hisham ya numfasa ya cigaba da mgn "yanzu matsayin kanwa kike agareni ki koma gida ki fara sabuwar rayuwa " daga hk bai kara magana ba yaja motar bai tsaya akoina ba sai acikin haraban estate dinsu tsayuwar motarsa ya sake daga mata hankali yayi parking ya fito yana daidaita nutsuwarsa bai mata magana ba yayi mata alamar ta fito yanayin yadda taga fuskarsa babu annuri ko daya sannan kuma babu wasa yasa ta fito tabi bayansa ."
Duk da dare ne idanun mutane na kansu kasancewar akwai hasken fitilu ahankali ya tsaya bakin kofar gidansu alokacin da shadaya da rabi ta buga hannu ya kai yayi knocking sautin muryar mahaifinta taji yana cewa" waye ?baba hisham ne "hisham kuma adaidai wannan lokacin Allah yasa lafiya? ya fad'a yana bude kofar ya koma gefe hisham ya shigo yana gama shigowa nuzla ta shigo tmkr mai jin sanyi da idanu baba babba ya bita dashi kafin yace "ita kuma wannan fa daga ina ?baba kayi hakuri dan allah."
hajiya salema kam tuni ta zabura ta mike ganin nuzla ta qaraso ta rungumeta ajikinta tana kuka "haba nuzla me yasa zaki min haka kin kuwa san halin damuwar dana shiga "hisham ka dauketa ka maida ita inda ka daukota bazata cigaba da zama dani ba." dan girman allah baba karkayi haka kai din fa mai hakuri ne kayi hakuri ka yafe mata nuzla yarinya ce har yanzu idan kaki amsarta ina kake son taje ."?"ta koma inda tayi kwanakinta amman ba a gidana ba." yana gama fadar haka Ya juya ya shige turakarsa jin haka yasa hajiya Salema ta saki nuzla ta bi bayansa tana kuka ."
Cikin fushi nuzla ta nufi kofar fita yaya hisham bai san lokacin daya fizgo hannuta ba ya sanya cikin nashi ya dan matsota kamar zai shige jikinta ganin kallon da take masa yasa shi janyota gabadaya jikinsa "kina hauka ne ina zaki ?bakaji abinda baba ya fad'a ba? shine saboda baki da hanaki zaki fita to me zanyi ? tayi mgnr a shagwabe "bazaki koina ba kin dawo gida kenan karki sake ganganci sake barin gidan nan ya rad'a mata acikin kunneta wani iri taji agabadaya ilahirin jikinta "ya zareta ajikinsa ya nufi dakin hajiya salema daita yana cewa "matukar kika sake barin gida karki sake marmarin kirana a waya dan haduwarmu bazai mana kyau ba ya zaunar daita akan gado yana já mata kunne."
ta kallesa shima cikin kwayar idanunta yake kallo yana jin sonta na bin jinin jikinsa yana son nuzla da dukkanin rayuwarsa rausayar da kwayar idanunta tayi a cikin nashi kamr da gaske zai iya aiwatar da wani abu akanta idan ta sake barin gida " sai da safe ki kula da kanki" ta gyada masa kai tana kallon bayansa numfashi ta sauke "wani irin so yaya hisham yake mata haka ?duk shawarwari da nasihar daaka sha mata akanshi basu ta'ba tasiri ajikinta ba sai acikin kwanki bakwai kacal da yayi aurensa ta soma jin wani iri akanshi ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 3
...... A parlour hisham ya iske hajiya salema zaune ta dafe kanta da duka hannuwanta tana risgar kuka, cike da tashin hankali hisham ya qaraso ya durkusa a gabanta yana bata hakuri "dan girman allah hajiya ki daina haka ." "ban san me Alhaji yake so dani ba hisham, taya zamu haife 'ya acikinmu mu watsata duniya?" kuskure ne kowa yasan nuzla tayi kuskuren amman tunda ta dawo ai sai kowa yayi hakuri tunda qaddara tana kan kowa, kuma qaddarar aurenka da nana hauwa'u ce silar fitar nuzla daga gida."
ta d'an tsaida kukanta sannan ta cigaba da magana "hisham ka taimakeni ka shawo min kan alhaj ya barni da yarinyata mu cigaba da rayuwa idan kuma ba haka ba za'a samu matsala domin muddin nuzla bazata cigaba da rayuwa acikin gidan nan ba wallahi nima zamana acikinsa bashi da wani amfani gara na tattara na bita mu bar masa gidansa kamar yadda ya fad'a."
Cike da tashin hankali nuzla ta fito daga cikin d'akin sakamakon jin sautin kukan mahaifiyarta sai dai jin furucinta yasa ta qara shiga tashin hankali mai tsanani cikin rud'ewa ta shiga fad'in "pls umma babu inda zaki sai dai idan nice zan bar gidan nan amman Ke babu inda zaki." ta qaraso ta zube ajikin hjy salema tana wani irin kuka dan duk ita ce silar jefa mahaifiyarta cikin tashin hankali ."dan allah ummah kiyi zamanki bari na tashi na bar gidan nan tun yanzu" ta mike tsaye cikin rawar jiki zata nufi kofar fita."
wani irin razananniyar tsawa hisham ya buga mata wanda ya firgitata tare da yi mata alama da ido ta koma d'aki " kina hauka ne ko kin fara shaye shaye ne ?ya tambayeta a matukar fusace yana tsare gira." Kallonta yake mai had'e da harara "ki shiga hankalinki sannan ki koma d'akin ko kofar parlour'n nan ban yarda ki taka ba bare ki bar gidan nan ."babu musu ta juya tsimi tsimi ta koma tana kuka ."Yaya hisham bai tsaya sake cewa komai ba ya mike tsaye ya nufi d'akin baba babba ."
bakinsa d'auke da sallama ya'isa cikin d'akin baba babba yana zaune yana shan ruwan tea ya amsa masa sallama ." ahankali hishsm ya k'arasa ya durk'usa har k'asa a gaban baba babba ,cikin d'aure fuska baba babba yace "a,a har yanzu baka wuce gidan ba?" cike da fargaban ganin yanayinsa ya d'an sosa bayan keyarsa yace "eh baba wallahi ban wuce ba saboda na kasa samun natsuwa ."
baba ya sauke numfashi kawai saboda yasan kwanan zance shi kansa yana jin alhinin rasashi da diyarsa tayi amatsayin miji domin samun miji kamar hisham wallahi sai an tona ,kaf mazan daginsu yafi su nagarta da hakuri wanda hakan yana d'aya daga cikin dalilin da shi karon kanshi yake ta bin nuzla akanshi amman taki bin umarninsa dan ko adam bazai nuna masa komai ba sai tarin dukiya ".
Shiru ya d'an ratsa d'akin can baba ya d'ago ya dubesa sannan yace "hisham ya dace ace ka kama hanyar komawa gida ko akwai abinda kake so ne...?" ya jefa masa tambayar domin yaji meye raayisa akan nuzla ." sake shafa keyarsa yayi sannan ya d'ago cikin yanayin jin kunya ya fara magana "ammm baba .."dama...dama"!! sai kuma ya fara in ina, shiru baba babba yayi yana kallonsa duk ya wani rikice ahankali yace "relaxes hisham kwantar da hankalinka kayi min magana ina sauraronka" .
da kyar ya samu nutsuwa sannan ya fara magana "dama baba na shigo ne na qara baka hak'uri akan abinda nuzla tayi wallahi tayi nadama baba baza ta sake kwatanta abinda tayi ba dan Allah kayi hak'uri ka yafe mata ka kuma bata wani dama zata gyara
Still shiru baba babba yayi yana kallonsa kawai cike da tausayawa duk mai hankalin da ya kallesa yasan yana cikin shaukin só ,koma yace soyayya na tangalili da rayuwarsa ,lumshe idanunshi yayi kawai dan ba hakurinsa yafi buqata daga garesa ba,a halin yanzu babu abinda yake bukatar ji kamar ya furta masa cewar zai aure nuzla ya had'ata da yar'uwarta".
"kayi hak'uri baba nasan kayi fushi sosai daita yanzu idan ka koreta daga gidan nan ina kake tunanin zata ?".mu godewa allah ma data dawo gida da ba'a nemeta gbdy an rasa ba" still dai shiru baba yayi "baba bana son rayuwarta ta lalace dan Allah kayi hak'uri ka barta ta cigaba da rayuwa acikinmu shine kwanciyar hankalina ;;" yai maganar cikin yanayin tausayi yana zubar da hawaye"..
Hmmm....!!! baba babba ya sauke nannauyen numfashi sannan ya fara magana "hak'ik'a hisham nuzla ta aikata min babban laifi wanda kullum na kan zauna nayi tunanin abinda yasa tayi min haka .
"ina tarbiyar dana bata?"wallahi rai na yab'aci sosai akan abinda tayi amma ba komai komai ya wuce ka daina kuka taci darajanka wallahi banci kai da sai dai ta koma inda ta fito ka tashi ka wuce gida dare nayi Allah yayiwa rayuwarka albarka ka gaishe min da matarka tashi kaje"
wani irin sanyin dad'i hisham yaji ya mamayesa bai san sanda ya rungume baba babba ajikinsa kamar wani k'aramin yaro yana fad'ar "thanks my dad i love you so so much am very proud of u my dad" nima ina alfahari da kai hisham Allah yayiwa rayuwarka albarka "ya sakesa ya fita yana murna baba babba kuwa banda murmushi babu abinda yake yana mamakin irin son da yakewa nuzla "....
karfe d'aya daidai hisham ya shigo gidan kuma akan idanun hajiya zulfa'u da nana hauwa'u ya shigo bayan ya shigo ya rufe koina yana qoqarin kwanciya akan kujera mai zaman mutun uku ya ga mumy tsaye akanshi tana masa mazurai da idanunta gabansa né yayi wani irin mummunar fad'uwa muryarta a kausashe ta soma magana "daga ina kake adaidai wannan lokacin?"shiru yayi tare da sunkuyar da kai cikin tsananin tashin hankali dan bai san me zai fad'a mata ba ,gashi shi bai iya karya ba daya girba mata karya ya huta ."
"Ba da kai nake magana ba kana jina kayi min shiru.?"amm daman ..."sai kuma ya sake yin shiru yana shafa sumar kanshi alokacin da nana hauwa'u take taku domin fitowa daga daki "kai nake sauraro ka ji dani bacci nake ji daman me ?".daman mumy nuzla ce ta kirani shine naje na d'aukota na kaita gida ."
"what ?"!
"hisham kana da hankali kuwa?"ka tsallake matarka kaje ga wata nuzla din banza " numfashi ya sauke sannan ya motsa lip's dinsa yana mai d'ago kanshi daga sunkuyar wa da yayi "mumy nuzla fa ba banza bace, bai kamata dan tayi d'an wannan Kuskuren ba ki d'auki zafi dayawa akanta ,sannan ko babu komai nuzla diyarki kuma kinga dai irin halin da kowa ya shiga akan rashinta ,"kiyi hakuri dan allah nasan nayi ba daidai ba dana fita adaidai wannan lokacin amman nuzla tana da matukar mahimanci arayuwata domin zuciyata ce bazan.."
saukar mari akan kuncinsa ya katse masa maganarsa ,hatta nana hauwa sai da jiyo saukar marin ajikinta dan tana daf da fitowa parlour'n mumy tayi masa marin ."cak ya tsaya yana kallon fuskar mumy dafe da kuncinsa yayinda nana hauwa'u ta fito jiki a matukar sanyaye ta tsaya abakin kofa tana dubansu cike da tashin hankali idanunta suka cicciko da ruwan hawayen abu biyu rashin son da hisham yake nuna mata da kuma na dawowar nuzla gida." "hakika tayi farinciki da jin wannan labari dan daman kullum zuciyarta cike take da tunanin inda take ."
"wallahi wallahi !! sau nawa kaji na rantse idan ka sake min magana akan nuzla zuciyarka ce sai nayi mummunar sa'ba maka ,idan ban iya tsine maka akanta ba allah yayi min yadda yake so, kai shashan ina ne ?da zata gudu tayi shawara da kai sai da zata dawo gida ne tasan da kai ? kai kuma ga shasha tantabara sarkin alqawari ka girba wa matarka karya an kiraka an contract ka kwashi jiki kaje wajenta ,in da da wani abu ya sameka fa ?"tayi masa Kmr zata zubar da hawaye ."
"yarinyar nan tace bata sonka bata sonka !! dole ne hisham ?ko dole ne soyayya da bazaka hakura daita ba "? hisham ya sauke numfashi yana shafa kuncinsa yace "wallahi mumy sai kin ganta ,tayi nadama sosai "babu ruwana da wata nadamarta tunda bata min alkunya akanka ba nima bazan mata ba ,kai kad'ai fa na mallaka arayuwata ni duk yadda muke da mutun yace bai sonka ai sai inda karfi ya qare akan kiyayyarsa ,kasani nuzla diyar dan'uwana ce amman bana sonta da kai tayi rayuwarta kayi naka allah ya bata wani mijin ."
"Haba mumy take it easy now duk fa abun bai kai haka ba "ka kamin baki anan karka sake min magana akanta bana són ji ta fad'a à hargitse, tsayawa yayi kawai yana duban mahaifiyarsa gbdy ta hargitse ta canza masa Kmr wata mai ciwon iska " wallahi ka sake zuwa inda take sai na ...."saukar hannun abba taji a bakinta yana cewa "haba my dear wai meye haka ne ?hucin numfashi ta fesar na 'bacin rai tana dubansa cike da takaici, bai sake barin tace komai ba yaja hannunata zuwa d'akin baccin su yana rarrashinta."
Ahankali nana hauwa'u ta tako ta tsaya gaban hisham tana kallonsa rasa abun yi tayi saboda ganin yadda fuskar hisham tayi tana cikin yanayi na tsnanin damuwa dan haka ta zuba masa idanunta tana canza fuskarta zuwa yanayi na murmushin farinciki shi kuwa sunkuyar da kanshi kasa yayi zuciyarsa na tafasa"yaya hisham !" ta kira sunansa ahankali bai amsa ba yaji ta cigaba da mgn "ina tayaka murnar ganin nuzla hakika naji dadi sosai."
d'ago kanshi yayi ya zuba mata kwayar idanunshi yana kallonta kamar yadda take kallonsa sai dai nashi kallon mai cike da tsananin mamakin jin abinda ta fad'a ne sai daya d'auki wasu mintuna sannan ya motsa bakinsa ya fara magana "idan har da gaske kinji ddin dawowarta na gode "yaya hisham me kake nufi ?". abinda kike nufi nima shi nake nufi ya fad'a a d'an tsawa ce ."
Ta girgiza masa kai jikknta na rawa tace "walalhi har cikin zuciyata naji dadi sosai kuma allah yafi kowa sani meye acikin zuciyata ,meye riba ta idan naji dadin rashin dawowarta?rashin dawowarta ba zai ta'ba canza zani daga halin da nake ciki ba ta fad'a tare da juyawa ta shiga kitchen bata jima ba ta fito hannunta rike da qaramin cup ta durkusa gabansa ta mika masa tana kallon cikin kwayar idanunshi cike da tashin hankali sakamakon rashin sonta da take hangowa acikinsu ."
Yaki amsa ta kai hannunta ta kamo laulusan tafin hannunsa ta saka cup din ciki ,yaki amsa ya cigaba da kallonta "kayi hakuri kasha zaka ji sauki zugin da zuciyarka take maka "na sani akwai zafi akwai radadi da ciwo sosai abaka wanda baka so ,ka sani ni nana hauwa'u bazan takura maka ba bazan hanaka abinda kake so ba ,idan ma ta kama ka auro nuzla ka had'amu kana da damar yin haka bazan damu ba ."
Idan kuma bazaka iya had'amu ba zaka iya sakina ka zauna daita kad'ai na yarda na amince idan kuma zaka iya cigaba da zama dani shima na yarda na amince koda baza kayi komai na aure dani ba, abu daya kawai nake so daga gareka shine ka bani kwanciyar hankali." tsareta yayi da oly eye's dinsa masu firgitartata a yanzu , hakan yasa tayi saurin kawar da kanta gefe tana danne kukanta."
Bin jikinta da kallo yayi yana mamakin jin abinda ta fad'a ,hakan nan yaji tausayinta ya mamaye jinin jikinsa tana da matukar saukin kai sannan bata da yawon damuwa da fari ta tayi qoqarin tsaida mutuncinsa dana iyayensa har ma dana dangi gabdaya domin auresa, sannnan tayi qoqarin karesa a wajen mahaifiyarsa daya fita yanzu kuma tana tayasa murnar dawowar masoyiyarsa har ma da albishir din ya aurota "kai sakarai ka dawo cikin haiyacinka bata son kaga dole zata fad'a haka ,kai ba haka bane to me yasa taki fad'awa mumy komai bayan taji wayarka da zaka fita .?"
Wani zazzafan numfashi ya sauke yana cewa" idan ni kuma bana raayin aurenta fa? ya fad'a tare da amsar cup din hannunta yana sauke numfashi "bazai ma yuwu kace baka son aurenta ba wannan ma ba abinda hankali zai dauka bane nuzla fa zuciyarka ce ta fad'a tana qoqarin mikewa tsaye zata juya taji ya hard'e mata kafafu nan da nan gbdy ta juyo ta zubo jikinsa a gigice take kallonsa duk da tasan shine ya hard'eta amman hakan nan ta tsinci kanta da bashi hakuri ."
"Ka..Ka... kayi haku... "shiiiii! ya fad'a yana kai cup din hannunsa ya ajiye akan table din dake gefensa ya tsura mata ido suna shakar numfashi juna yayinda ita kam tuni ta runtse idanunta dan bazata iya jurar kallon ba dan duk yadda take jin numfashinsa na saukar a fuska da wuyanta hakan bai sa ta bude idanunta ba ."
laulausan tafin hannunsa ya kai saitin wuyanta sakamakon zafin da yaji ajikinta yayi wani abu yaji ya tsarga masa da sauri itama ta bude idanunta suka tsurawa juna ido muryarsa a rauni yace baki da lafiya ne ."?numfashi ta sauke da karfi sannan ta mike daga jikinsa ta zauan a gefensa tana cewa "lafiyata lau nima haka naji yanayin jikinkina ya sauya."
"Okay yanzu mu ajiye maganar wasa da gaske kin amince na auro nuza ?ta gyada masa kai alamun eh ! ya gyara zamansa yana kai cup din madara bakinsa "nima zan miki abinda kike so amman sai kin shawo min kan mumy ta amince na auri nuzla idan kika min haka zan baki duk wani kwanciyar hankalin da kike bukata daga gareni ".
shiru tayi tana tunanin kafin daga baya tace "dan wannna mai sauki ne zan mata magana kuma in sha allahu nasan mumy zata amince ."shiru Kawa yyi "gsky nana hauwa'u tana da kirki da hakuri dan kwata kwata bai ta'ba