Showing 63001 words to 66000 words out of 167047 words
Chapter 22 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
wata taji dadina sai dai a nemo min ita, idan ba haka ba wallahi wallahi kowa bazai ji dadina ba acikin gidan nan , yadda zuciya take quna a kullum haka take son kowa yaji radadin da take ji, kun kasa samo min ita ,kun kasa yi min komai akai ,kun kasa fahimtata kun kasa min uzuri kullum maganar mrym marym !! ku dai burinku yarinyar taji dadin rayuwar aure ni kuma ko oho Inpossible wallahi bazai yuwu ba sai dai mu taru muyi rayuwar qunci gbdy ."
suka zuba masa ido kawai suna kallonsa cike da tausayawa "matuqar kuna son farincikina ku nemomin mafarkina ya qarashe mgnr yana huci sannan ya mike."
" ina kuma zaka "ina bukatar na kasance ni kadai daga haka bai qara cewa komai ba kai tsaye step ya haye mrym ta juya tana kallon bayansa zuciyarta na bugawa da sauri sauri gbdy suka qaraso suka zagayeta "karfa ki yarda ki saka damuwa aranki muna sonki mahaifiyarmu tana tare dake me ye abun damuwa ?kai ta girgiza "yan'uwana bazaku gane yadda nake ji araina ba ,aunty zuciyata kamar ta fashe idan naji yana magana akan mafarkinsa da furta bai sona, idan ya zama dole ne sai ya furta ni ya dinga fad'a min ni kad'ai ciwo bazai dame ni haka ba wai har a gaban aunty abida ,rukkaya ,diyana ."
In fact ya nunawa duniya ni din bakowa bace garesa hatta zumuncin dake tsakaninmu yayi watsi dashi ."
"Kiyi hakuri komai zai zama labari wata rana "babu komai allah ya nuna min wannan ranar bari naje na kai masa wani abu yaci ta barsu tsaye ta nufi kitchen bayanta suka bi da kallo suna jinina girman hakurinta dan ko su bazasu iya daukar wulakancin nmj haka ba ,amman tunda ita haka allah yayita da hakuri sai su tayata da addaur allah ya qara mata hakuri ."tana qoqarin had'a masa abinci wayarta ta soma ringing ta duba taga mahaifiyarta ce dan haka tasa wayar a handsfree muryarta a sanyaye ta gaisheta "umma ina yini ?lafiya kalau maryam ya kike da wannan mugun mijin naki ?yana nan yana halin nasa ko ?"duk lafiya muke dagani har shi amman dan allah ummah kiyi hakuri ki daina kiransa da mugu yaya adam nada kirki fa kawai dan bai sona ne ."
"Wannan shine dalilin da yasa bana son shi yanzu bai son jinina me zanyi dashi "tô ai shi só halitta ne umma amman ina sa rai wata rana zai duba lamarina da izinin allah ki tayani da addua,addua kam muna yi dan tun daakayi auren naku ban zauna ba wajen neman miki taimakon samun 'yanci a gidan miji ,yanzu haka ma ga wani taimakon nasa an amso miki daga zuru zan turo miki ta jirgi kije ki karbo da kanki acikin abinsa zaki zuba masa idan allah ya taimaka yaci wallahi sai dai wani ba wannan adamun ba sai yadda kikayi dashi maryam tayi sauri ta cire wayar a speaker tana waiga bayanta dan datasan mgnr da zai cigaba da fitowa bakin mahaifiyarta kenan bazata saka wayar a speaker ba."
Ta sauke numfashi sannan ta maida wayar kunnenta ta rage murya sosai ta cigaba da magana "gsky ummah bana son nayiwa yaya adam wani abu tukun ya soni nafi son ya soni dan kanshi "tô shikenan zanyi amfani dashi tayi discounting kira tare da soke wayar acikinta ta kawo karshen maganar né da fad'ar haka dan ita bazatayi masa amfani da komai ba , taji ma da tarin zunubin dake kanta ta hada masa abinci akan qarami tray ta fito ta nufi hanyar d'akinsa bynta suka sake bi da kallo cike da tausayawa a hankali ta tura kofar d'akin ta shiga yana zaune a kasan d'akin ya tokare hannunsa yana kallon sama . yana jin motsin shigowa d'akin ya kalli kofar ganinta yasashi jan tsaki yana kwar da idanunshi gefe ta karaso ta tsugunna kusa dashi jikinta da murya na rawa ta d'an saci kallon hannunsa mai ciwo sannan tace "ga ...ga abinci!
" bai ce komai ba ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa da karfi "kayi hakuri da abinda ya faru wallahi bani da masaniyar faruwar komai da kuma nasan hkn zata faru wallahi bazan bari ba bazan ma sa bakina ba daman nayi haka né dan "ya waigo a fusace ya kalleta a kaskance hakan yasa ta kasa cigaba da magana zuciyarta na bugawa ganin bai yi magana ba yasa ta sake bude baki zatai mgn ya d'aga mata hannun tare da tsareta da idanunshi wanda hkn ya haddasawa zuciyarta shiga rudani da bugawa da sauri "kin kamu da sona ko ?tai shiru tana duban cikin kwayar idanunshi karo na biyu kenan daya furta mata haka sai dai ta kasa bashi amsa tmbyrsa ."
"kina sona kuma shine dalilin da yasa kika dawo abar tausayi haka ba ? nan ma shiru tai masa dan batasan me zata fad'a masa ba "nonsense girl kawai wallahi kin cuci zuciyarki ke yanzu kinga dacewar mu da zaki kamu da sona ?tai saurin girgiza masa kai "ba.." bana só.."you are very stupid shut up iam talking you talking sai na kasheki da mugun duka taja bakinta tayi shiru tana sauke numfashi."
Ya mike tsaye yana dubanta kamar zai had'eyeta da idanunshi "itama da sauri ta mike jikinta na kyar "ni zaki kalla kice baki so ?ta sake girgiza masa kai ."
"better kin taimaki kanki da kanki ,kingan ni nan har abada bazan ta'ba ganganci barin ki zauna acikin nan ba "ya nuna daidai saitin zuciyarsa da d'an yatsansa ."
" zan baki shawara kiyi gaugauwan cire sona aranki kamar yadda na ta'ba fad'a miki adam mallakin mafarkinsa ne idan ban sameta ba mallakin wata ce dabam amman bake ba "tunda ya soma magana tske jin tashin hankali mara misaltuwa" me yasa zakace haka yaya adam? daga ranar da ka zama miji agareni daga ranar na sanyaka acikin abinda yafi zuciyata da gangar jikina ,zuciyata ta haukace akan sonka ina jin ciwon kiyayyar ka gareni amman na kan kawar dashi domin na samu damar dasa soyayyata acikin zuciyarka ta hanyar maka biyayya "enough...! bana son jin maganar soyayya daga bakinki ai tunda kina iya shiga tsakanina da mahaifiyata kin kad'e a wajena domin wannan son wa ni kadai ya dace ban dake amman gashi an kasashi gida biyu "ya fad'a ya fusace ."
"ban kwace maka soyayyarka ba mami tana sonka fiyye da komai kuma matsayinka na nan acikin zuciyarta ,bazata ta'ba canzaka da wata ba, watan ma ni ai ban isa na taka matsayinka a zuciyarta ba kuma duk wannan kulawar da kake ganin tayi karfi yanzu saboda kai ne saboda ..."please let me be alone ya fad'a yana juya mata baya cike da jarumta ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa "out of this room now ya nuna mata hanyar fita ."shiru tai ta kasa motsa jikinta ."ganin hk yayi tunanin bar mata d'akin ya nufi hanyar fita ta biyosa da sauri tana cewa "d'an allah kayi hakuri kaci wani abu sai daya bari ta fita daga d'akin gbdy ya dawo da baya ya rufe kofar.
cike da muryar kuka tace" ka yafe min banyi maka laifin komai ba wallahi ban had'aka da mahaifiyarka ba ni kaina bansan hakan zata faru ba wallahi dana san wanda zai fad'a mata alokacin dana hana bai ce uhmm ba bare uhmm ya bar jikin kofar yana jan tsaki tare da furta "nonsense!wani sabon kuka ta rushe dashi"maza masu sanyin halima baka barinsu haka ,bare miji irin naki dole sai kin tashi tsaye wajen mallakesa sannan zaki samu 'yanci agidan aurenki "maganar mahaifiyarta na karshe kenan a wayar da sukai yi d'azu nan take taji ta yarda kuma zuciyarta ta amince zatayi amfani da maganin da mahaifiyarta zata aiko mata domin samarwa kanta kwanciyar hankali a gidan mijinta "ahankali taji an dafata ta waigo idanunta cike da ruwan hawaye "Mami ce !
"Mami dan allah ki fad'a masa cewar bani na hadashi dake ba, dan allah mami ki bari ya fahimce hakan " naunayen ajiyar zuciya ta sauke " na rasa me yasa adamcy yake son caza miki kwakwaluwa mami ta fada hk a fili "ita kuwa mrym kuka kawai take tana rokon mami ta fahimtar dashi "kukan ya isa haka zan fahimtar dashi duk da ba rarrashi ya kawo wajensa ba amman zan kwantar da kai saboda ke "yauwa mami na gode sosai dan allah ki lalla'bashi kar kiyi masa fad'a ta fad'a tare da share hawayenta "mrym ki daina yawon kuka ki dinga dauriya mijinki ba mutun bane mai damuwa da kukan mutun ko sanin mahamancin hk, jajurcewarki ita zatasa kiyi nasara akansa ta runtse idanunta wasu hawaye masu zafi zuka zubo mata ".
"nace kukan ya isa haka "tô mami kice ya bude kofar yaci abincin nasan tunda ya bar gidan bai ci komai ba amman sam sam yaki saurarata"kije for now nasan halin d'ana kema kuma idan da sabo ya kamata ace kin saba da halinsa bazai ce miki komai ba sannan bazai ci komai ba, ki bari zan fada masa komai zan fahimtar dashi baki da laifi kuma zan lalla'ba miki bazan masa fad'a ba ki kwantar da hankalinki naunayen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara janjikinta ta bar wurin mami tai knocking tana kiran sunansa da kyar ya bud'e mata kofa.
Ahankali ta tura kofar ta shiga ta tsaya abayansa bai juyo ba tasan yayi haka saboda fushin da yake daita ."
Numfashi ta sauke tare da d'aura hannunta ta dafa kafad'ansa tana kiran sunansa "adamcy nah !kmr jira yake ya juyo ya zuba mata tsumammun idanunshi yanayinsa kmr zai yi kuka itama mami ganinsa haka ya karyar da zuciyarta domin ya zube ya fita haiyacinsa acikin kwanki hud'u kawai idanunshi duk sun rikid'e sun canza kala alamun shan sigari hannunsa mai ciwo ta kamo tana kallo nan take yanayinta ya sauya idanunta suka fara kawo ruwa .ganin haka ya rungumeta ajikinsa qirjinsa na bugawa da wani irin karfi sai da mami taji tsoron yanayin bugun zuciyarsa . ta zaresa ajikinta tana kallonsa hawaye ta gani a fuskarsa hankalin mami ya qara tashi wannan shine karo na biyu da taga d'anta na kuka a tun tasowarsa lallai adamcy baya son mrym ".
"kiyi hakuri sweetheart ina 'bata miki rai hakika ban rike amanar da dad ya bani ba ki yafe min zuciyata ta kasa son mrym ki bani damar na auro wata please." nasani nasan baka sonta amman ina sa rai zaka sota wata rana ,ni ban hanaka qara aure ba ko kawo zabinka ba amman sai naga irin adalcinka ina son kasan mutunci maryam kasan daraja maryam ka bata kimarta da darajarta ta matarka ,ka bata matsayin mata acikin zuciyarka, ka yarda daita wannan shine burina kafin ka shigo da wata matar gidanka."adamcy maryam na da kirki tana da biyayya da hakuri ban maka zaben tumun dare ba na zaba maka abinda zaka yi alfahari ne ko bayan raina zaka yi alfahari daita fatana ka rike matarka amana na yafe maka na yafe maka na kuma janye fushina akanka allah yayi maka albarka allah ya azurtaku da samu zuria masu albarka ".
Shiru yayi yaki amsawa da ameen "ina son maryam sosai Adamcy kai ma kuma ina son ka koyi sonta .."ya qara tsura mata idanunsa da sukai jazur "zaka min wannan alfarmar?zaka koyi sonta ?shiru yayi ya kasa furta komai "kayi shiru Adamcy ya kamata kace min wani abu ko zuciyata zata samu salama ta fad'a tana d'aura hannunta akan sumar kanshi yayinda hawaye ya cika idanunta ta rasa wani irin baqar zuciya garesa tun yana yaro take fama dashi idan ya tsani abu ya tsana kenan idan yace yana son abu shima haka ne, tasan da wahala ya so maryam kamar yadda take bukata. ta cire hannunta dake Kan sumar kansa ta tsurawa yatsun hannunsa ido hawayenta ne suka dinga diga akan nashi tafin hannun da sauri ya dago kansa ya sanya kwayar idanunshi cikin nata yana furta "why sweetheart me yasa zaki min haka ."?
Hawaye ta cigaba da zuba aiko ya rude "wayyo allah na shiga uku ,mami ki taimakeni karki cigaba da zubar da hawayen nan idan dai ba so kike wani mummunar bala'i ya sameni ba "ya qarasa maganar cikin rawar jiki numfashi ta sauke ta janyo hannunsa mara ciwo ta zaunar dashi sannan ta zauna gefensa tana cewa "babu abinda zai sameka zakayi albarka da izinin allah domin kai ne komai arayuwata babu abinda zai sameka zan daina kuka amman kai ma kayiwa maryam adalci ka duba irin kulawar da take bani irin kulawar da take bawa yanuwanka da kowa naka ni mahaifiyarka ce na fi kowa sanin abinda ya dace da rayuwarka ka sake da maryam zata kula da rayuwarka dan dukkanin alamunta sun nuna tana sonka yanzu ,ganewa bakwa yi amman kun fi samun kwanciyar hankali a wajen matar dake sonku ,matan da kuke so kuma wahala suke baku ."shiru ATA yayi yana nazarin maganarta ."
" kasan me yasa na had'a aurenka da maryam ?ya girgiza mata kai yana daura kansa a saman cinyarta ya natsu sosai ya bata dukkanin natsuwarsa "na had'a aurenku ne saboda ko byn raina maryam zata maye maka gurbina zata baka kulawar da uwa ce kawai zata baka, zata jurewa duk wani shagwa'ba da jin kanka,uwa uba hakuri gareta ,zatayi hakuri da duk wani iskancinka dan haka ina mai umartarka ka dauketa a matsayin mata zakaji dadin rayuwar aure daita". ta qarasa maganar tana shafa sumar kansa ya dago a hankali ya sake zuba mata idanunshi kamar zatai kuka "please sweetheart karki min haka karki bani umarni ,zanyi kokari na koyawa zuciyata sonta ta yadda zata bata matsayin mata amman ki bani lokaci ."
ta numfasa taso ya fadi abinda yafi haka amman a hakan ma ta gode "na gode allah yayi maka albarka ta mike tsaye bari na turo maka maryam ta zuba maka abinci kasa ma cikinka ,kanshi kawai ya gyada mata tana barin d'akin ya sauke wani wahalallen numfashi yana tunanin maganganunta "ta ina zai fara bawa maryam matsayi mata ?"
"matsayin mata da take nufi fa tana nufin wani abu ya shiga tsakaninsu kenan ?ya mike tsaye cike da sanyi jiki "tabbas abinda take nufi kenan idan dai haka ne ta ina zai fara ?a hankali ya shiga zariya acikin dakin yana ciza lip's dinsa at the same time yana hura hancinsa ."
byn kmr minti biyar mami ta dawo d'akin hannunta rike da mrym tana bata umarni "maryam zuba masa abinci" ta fad'a tare da samun wuri ta zauna kusa dashi tana dubansu adamcy nah bari mrym ta zuba maka abinci kaci ka d'an kwanta ka huta kafin zuwa anjima ka d'auki matarka ku wuce gida kaji masoyina ."kallonta kawai yayi yana mai tausaya mata " maryam ta zuba masa abinci ta janyo qaramin table gabansa ta ajiye masa tana satar kallonsa aranta tace "rigimamme kawai da baya son zaman lafiya ."
yayi shiru kawai yana kallon abincin kafin ahankali ya fara tsakura babu laifi ya d'an ci kad'an ya ajiye spoon alamun ya koshi mami ta tsiyaya masa ruwa a glass cup ta bashi ya sha sannan ta mike idan ka tashi ka d'auki matarka ku wuce gida kanshi ya gyada mata batare da yace uffan ba , ta juya har tayi taku biyu taja ta tsaya "batun hisham kayi hakuri kabar auta ta koma d'akinta zai yi magana tace "alfamar na nemar masa a bashi dama ta biyu stil bai yi magana ba ta fito ta bar maryam tana tattara wajen ."da yamma mami ta kira hisham yazo ya d'auki matarsa bayan tayi masu nasiha mai ratsa jiki ." haka ma maryam tabi mijinta suka wuce. gidan ya saura daga mami sai yayanta wad'an da suke shirin tafiya ."
Akan hanyar su nana hauwa'u ta koma gida tafiya ce sukai tamkar kurame hassalima bata kalli inda yaya hisham yake ba ta juyar da kanta gefe tana kallon tsirarrun motoci dake wucewa akan titi saukar hannunsa taji akan nata wani irin yarrrr taji a gbdy ilahirin jikinta, sai dai bata juyo ta kallesa ba ta cigaba da kallon titi "auta !" ya kira sunanta yaushe rabon da ya kirata da wannan sunan ?sai daya sake kiranta sannan ta juyo da kyar ta zuba masa idanunta ya kwantar da murya sosai "kiyi hakuri da abubuwan da suka faru a tsakaninmu shiru tayi Kmr bazata yi magana ba sannan ta motsa labbanta tace "babu komai ,komai ya wuce ,"Kinsan ko wanene ba haka halina yake ba ."
"Nasani shiyasa nayita mamaki wai yaya hisham mai tausayi da kulawa ne nake rayuwa dashi cikin fargaba da nadamar da tsoron kasancewata dashi yadda baka son auren nan haka nana hauwa'u bata só ,alfarma tayi ta sadaukar da farincikinta, na dauka yadda nayi zai sa na kasance masoyiyarka tare da tunanin zaka fi kowa jin dadi da sona amman sai naga sa'banin haka wallahi nayi mamaki yaya hisham ban ta'ba tunanin haka daga gareka ba". ta qarasa mgnr cikin rawar murya ya kamo hannunta ya tsarke cikin nashi" yana murzawa ahankali yana jin canjin yanayi a sansar jikinsa ,yayinda soyayyarta ke sake huda zuciyarsa "kiyi hakuri hisham zai dawo miki fiyye da yadda kika san shi a baya ,bazan sake yunkurin cutar dake ba ."wani sanyi dadi taji yana bin jinin jikinta ahankali ta dinga jin gurbin daya fara samu a zuciyarta yana qaruwa ."
Washegari ATA na barin gida aka kira maryam sakonta ya iso take ta shirya ta fita batare da neman izininsa ba ta karbo magani cike da farinciki ta dawo gida ta kira mahaifiyarta ta sheida mata ta kar'bi sakon ,yini ranar cikin farinciki da murna maryam tayisa da yamma ATA ya dawo gida cike da kulawa ta tarbesa da abinci ,bai kalli inda ita da abincinta yake ba ya haye samansa wanka yayi ya sauya kaya ya bar gidan gbdy .hankalinta a tashe ta kira mahaifiyarta tayi mata bayani "umma ki tambaya ko zan iya zuba masa cikin abun shansa dan baya cin abinci sai coffe da ruwan gidan kawai yake sha?to shikenan sai najiki ."
*****
Bangaren maryama kuwa zaman gida ya soma damunta yayinda subai'a tuni ta fara aiki da kamfanin Z&A dan haka ta fara