Showing 141001 words to 144000 words out of 167047 words
Chapter 48 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
tayi jajur saboda kuka ahankali ummah ke mata nasiha tana tofa mata addua wani irin yanayi maryama ta shiga alokacin da idanunta da kwakwaluwarta suke sake hasko mata komai daya faru ."
a natse ta dinga bin kowa dake gurin da ido sai dai taga wani irin mugun kallo suke mata zuwa can taji aunty hasana na cewa "ji yadda take bin mutane da kallo wannan yarinyar fa muguwar munafuka ce dan allah tashi ki fad'awa mutane inda kika kai mana d'anmu daga rakiya ai wallahi baki isa ba sai kin fito mana dashi dan shi kadai muke kallo a matsayin mahaifinsa ."mikewa maryama tayi jikinta a sanyaye har ga allah tafisu bukatar yaya sadam arayuwarta sannan yadda suke nuna mata baya mata dadi duk da tasan basa qaunarta amman batayi tunanin zasu zargeta ba kanta ta daura akan cinyar ummah tasa kuka tare da jin wani kullin abu ya tsaya mata yaki gaba yaki baya "ummah ce ta dinga rarrashinta tana yiwa aunty Hasana fad'a "wallahi ummah bansan mutane nan ba bazan iya cutar da mijina kuma danuwana ba wallahi ina son yaya sadam ."
"nasani maryama bazaki ta'ba iya aikata hk ba cikin jin dadin kalaman ummah maryama tasa kuka tana cewa "ku taimakeni ku nemo min yaya sadam domin ban san inda zan saka rayuwata ba tana kuka ummah na share mata hawaye duk da itama hawayen take sosai hankalin mutane ya tashi kowa kuka yake a wajen ".
"ummah Kiyi hakuri ki yafe min nayi nadamar fita wannan aiki ban san me ya jani na aikata haka ba kuma wallahi na daina farinciki da iya wannan aiki da nayi arayuwata ummah kuzo muje inda aka binne yaya sadam da ransa zaa iya samunsa a raye ina ji ajikina bai mutu ba hawaye umma ta share amman maryama kwanaki biyar kenan da faruwar wannan alamarin kina ganin zai rayu "?numfashi ta furza mai zafi "ummah !"sai kuma tayi shiru tana wani irin kuka tana tuna kalamansa na qarshe gareta "abinda nake so dake maryama ki natsu sosai kiyi abinda ya kawoki ina sonki ina kuma alfahari dake na kuma yarda dake a duk inda zaki kasance nasan zaki kame min kanki da kuma mutuncina wani sabon kuka ta fashe dashi "ummah ta riko hannunta gam cikin nata itama kuka ta fashe mata dashi sosai cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunan allah tana cewa "laifin me d'ana yayi masu wannan hukuncin yayi tsauri ga rayuwar sadam babu wanda zuciyarsa batai rauni ba aunty da wasu daga cikin yanuwa hawaye suke dan tausayawa ga umma d'aya bayan suka dinga barin dakin inda dakin ya saura daga aunty sai ummah da maryama "umma muje inda aka binne yaya sadam a fito dashi jikina na bani yana nan a raye ummah ki tausaya min wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba "ki samu natsuwa maryama in sha allahu zamu je gobe"iya abinda ummah ta iya fad'a kenan bata sake cewa komai ba dan bazata iya magana mai tsawo ba ."
washegari aka kai maganar gurin hukuma aka shigar da qara tare da nuna hoton yaya sadam daga nan aka yiwa maryama tambayoyin daya dace sannan aka saka maryama gaba sai hanyar ogun state tafiya suke tana share hawaye tana addua duk kwanar data gani sai ta rikice tace nan ne . sai an tsaya tace a’a ba nan bane ahaka suka kusan kaiwa cikin ogun state dan daga inda suke suna iya hango sambaod din wel come to ogun state tayi sauri tace “ kamar kafin mu kawo wannna sambaod din ne .”cak direba dake tukasu ya tsaya tare da juya Kan motar suka koma dayan hannun sun sha wahala sosai a qarshe dai ta gane daidai inda sojojin suka sha gabansu saka makon warin takalminta data gani yashe a gefen titi .” jikinta na rawa ta soma kuka tana cewa "ku tsaya nan ne !"batare da bata lokaci ba suka firfito “tabbas anan ne suka sha gabanku “ta fad’a tana kuka .daya daga cikin jami’in tsoro yace a ina aka binnesa nan maryama ta hau zazzare ido “tabbas daga nan suka rufe mana ido amman duk da haka jikina na bani wannan kwayar suka shiga damu basu mutsa mata ba suka shiga mota suka bi hanyar tafiya suke amman jikin maryama rawa yake dan bata son tayi kuskure wajen gano wajen .”
gabad’aya babu inda baa duba ba ko zaa ga alamar tudun kasa amman babu ,jami'an tsoro suka tsaya suna kallonta "kin tabbatar nan ne?tayi shiru tana share hawaye dan gbdy ta rikice ummah Ummah duk ta rude sai zufa take fitarwa ta matso kusa daita tace “maryama ki natsu da kyau a samu a gano inda suka binnesa” tayi mgnr cikin rawar murya maryama ta fashe da kuka tare da zubewa kasa sakamakon ta rasa mafuta.”dan kwakwaluwarta ta cunkushe waje d’aya yadda maryama take kuka haka umma take kuka tana janyota jikinta gabdaya jikknta ya d’auki zafi kamar garwashin wuta yayind jami’an tsaro suka cigaba da dudduba wajen ko zasu ci karo da tudun kasa amman still dai babu wata alama inda aka binnesa ganin suna bata alokacin su ne yasa suka ce su wuce zaa zaa sanar a gidan radio da tv maryama kam duk ta gama rikice masu sai sunan yaya sadam dina kawai take kira “ku nemo min shi dan Allah karku barni haka da kyar aka samu aka saka acikin mota suka kama hanyar gida .”
******
Shabiyu ne na rana yana tsaye acikin office dinsa sanye da t shirt long sleeve light puppy da wondo baki sai tie baki zagaye da wuyansa ya tura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa wani irin kamshi jikinsa ke fitarwa mai sanya natsuwa da kwantar da hankali fuskar nan tashi a murtuke zariya ya soma yi acikin office din yana tunanin maryama wanda bai san dalili ba tunaninta yaki barinsa babu abinda zuciyarsa yake kwadayin sake gani kamarta kafin ahankali yayi burki a daidai mazauninsa turo kofar office din akayi batare da an nemi izinin shigowa ba ya kalli kofar ammar ya gani yanayin yadda yaga fuskarsa ya dan fahimci akwai wani abu yana gama shigowa ya soma magana cikin tsananin fushi "burinka ya cika maryama tayi aure “
“so what idan tayi aure what’s my business with her ?wai menene matsalarka adam ?"da nayi me kenan ?wallahi ban san baka da sa'a arayuwarka ba sai da maryama tayi aure "tô ni menene damuwa ta da aurenta ?kaga dan Allah karka sake min maganar ta karka qara min damuwa akan wanda nake ciki "kai ne kuwa kake da damuwa daita ."hade rai ata yayi sosai yana yiwa amar wani irin mugun kallo mai bugar da zuciya "kasani inada dalilina na son ku hadu daita tun kafin tayi aure.ata yayi taku daya biyu yana mai juya masa baya wallahi da ka daure kaga maryama da zaka fahimci abinda na gani har yasa nake son ku hadu daita."
juyowa ata yayi ya fuskancesa yana hura masa hanci tare da kai hannu yana sunce tie din wuyansa "kai ma tunda kaga na na nace ai ya kamata kayi amfani da sense dinka ,bazaka ta'ba jin dadin wata mace a duniya ba sama daita" look ammar bana son damuwa ,"my friend you have to use your common sense and think akwai dalili mai karfi dayasa naso ku hadu "ata ya sauke hanunsa daga wuyansa ya maida cikin ajihunsa yana nazarin maganar ammar "ba dai ka rasa maryama ba kasani zuciyarka zatayi nadama fiyye da kowani nadama da d'an adam keyi a rayuwarsa "ya d'ago ya tsurawa ammar idanunshi tare da cire hannunsa d'aya cikin aljihunsa ya rike kugunsa," wasu ma suna janyota jikinsu domin su amfana daita bare kai da ..."wai meye haka ammar ?ka dameni ka cika min kunne da surutun banza da wofi dole ne sai na aureta ko dole sai na janyota jikinta ?"kaga enough please ka rabani da maganar wata maryama din banza bana son jin ko sunanta bare na aureta "yayi maganar a tsawace yana furzar da iska mai zafi "ai kuwa ka shiryawa shiga tashin hankali da damuwa domin duk ranar da zaka ganta kuma amatsayin matar aure sai kayi nadamar rashin haduwarku akan lokaci ,kuma lallai bazan daina fad'a maka rashin haduwa daita damuwa ne akan damuwa kuma har qarshen rayuwarka bazaka daina da kasani ba kai in takaice maka zaka iya rasa ranka ". ata ya dafe goshinsa da hannunsa daya "ammar kana rikita min kwakwaluwa zuciyata tana tsinkewa magangunka gabad'aya suna nema tarwatsa min zuciya gabad'aya na kasa fahimtar abinda kake nufi yayi maganar kamar zai yi kuka tare da zama akan kujera yana kallonsu "you are mad adam yanzu abinda ya rage maka ka zauna kayi tunani akan maganganuna " yana gama fad'ar haka ya buga masa table din gabansa ya juya ya fita a fusace ."
ata ya kai hannu goshinsa kafin daga baya ya soma jujjuya jikinsa akan kujera wani irin ihu yayi yana kai hannusa ya ture tarin file din dake Kan table sannan ya mike tsaye zambur Kmr zaki ya dafe kanshi gabad'aya ya rasa meke masa dadi dan wani irin abu yaji yana yawo acikin ilahirin jikinsa mai kama da abinda yake ji akan mafarkinsa yau shine karo na biyu da yaji wani abu wanda ya shafi mafarkinsa akan wata mace "wacece mai zanen creation wacece maryama datai aure coz the same abu yake ji akansu wanda yake da kusanci da abinda yake ji akan mafarkinsa “karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba itama matar aure ce “ya rabbi what’s wrong with me ?yana cikin wannan halin james yayi knocking yana neman izinin shiga sai da ata ya dauki lokaci sannan yace "coming !" ya shiga cikin taka tsantsa "mai gida ina son nayi magana da kai ko zan iya magana ?" leave!" mai gida magana ce mai mahimanci "I said leave bana bukatar jin komai yanzu."da sauri ya juya ya fice .cikin company ranar kam kowa ya kama kanshi dan dukkanin alamun sun nuna an tabosa, duk kuma wanda yayi kuskuren shiga track dinsa zai sha bala'i idan ma bai ce ya kori mutun ba har ya dawo gida maganar ammar na damunsa cikin rai sai yayi kamar ya kirasa ya sake masa karin bayani sai muguwar zuciyarsa ta gargadesa "
Bayan sati d’aya wanda yayi daidai da kwanaki shabiyu da daura auren maryama da yaya sadam sultana ta dirá a kasar kuma kai tsaye abdullahi estate aka nufo daita murna wajen aunty abida abun baa magana ,tun daga lokacin da sultana ta shigo estate din aunty abida ta fara aiwatar da shirinta kullum suna bangaren mami sai dai basa samun ganin ata suna samun sa’banin shiyasa yau sukai sakamakon yau .ahankali yake ssukowa daga Kan step cikin shigarsa na kullum sai kamshi yake idanunsa bai sauka akan kowa ba sai akan aunty abida da sultana kallo daya yayi masu ya dauke idanunshi ya cigaba da taku har ya wucesu ta mike ta sha gabansa tana kiran sunansa “adamcy barka da saukowa.” ya tsaya kawai yana kallonta batare da yace mata komai ba “ga sister ta kawo mana ziyara Ya ganta ta hadu ko ?still dai bai tanka mata ba tayi murmushin yake tana cewa “daman nace bari na kawota ku gaisa sultana ga cup din tea dinsa can dauko ki bashi .” jikinta na rawa ta juya ta dauko Orenge cup din dake ajiye wanda daman dan shi aka tanada ta mika masa ,sai dai bai kar’ba ba yace "am okay coz am oready late” zai wuce ta sake tsaidashi Ya tsaya cak yana duba agogon dake daure da tsintsi yar hannunsa kamr yadda kasani sultana kanwarmu ce kuma ta kware a harkar zane dan naji ance kana bukatar kwararun masu zane shiyasa nace tazo dan tasan Kan aikinta sosai idan bazaka damu ba ko zaka bata dama kaga irin nata kwarewar ?shiru yayi bai ce uffan ba “.
“nasan bazaka ta'ba zuba ma yaruwarka kasa a ido ba zaka gwada yaruwarka kaga irin nata baiwar bayan shi ma ina son ka taimaka ka bata aiki a maakatarku Z&A idan ma da hali ka barta a kusa kusa da kai wato P.A dinka dan na yi imani zaka ji dadin aiki daita dan ....”duk naji bayaninki.” ya katseta ta hanyar fad’ar haka kafin ya cigaba tayi saurin cewa “ zata joining compaing kenan ? kai amman na gode sosai sultana bana fada miki ba bashi da matsala gashi da sauki kai ga kirki da son yanuwa gyaran murya yayi yace " ammm karki yi Godiya tukun dan bani zan bata aikin ba kiyiwa mijinki magana I know he can do more that for her “mijina kuma ?tai masa tmbyr tana kallonsa tare da nazarin maganarsa tana kallonsa ya zagayesu ya kama gabansa “nifa Aunty duk ba wannan bane matsalata ni dai kawai kisan yadda zakiyi na kasance a kusa dashi nasan komai zai zo da sauki “amman yanzu a gabanki kikaji ina masa magana zaki ce bakiji abinda yace ba, wai nayiwa Ibrahim mgn Ibrahim din da ba wuri daya suke ba .”
Dan allah ayi min afuwa posting zai koma a sati sau daya sakamakon bana samu lokaci ga hidima da mai gidana ga business ga typing sannan ina bukatar hutu Kunga abun yayi min yawa ina maku fatan alkhairi sai Saturday ko sunday in sha allahu.”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 27
Jiki a sanyaye ATA ya fito cikin 'bacin rai daga d'ayan bedroom dinsa wanda ya rasa dalilin 'bacin ransa , a yanzu kusan kullum ransa a 'bace yake azaba yake ji sosai a cikin zuciyarsa so yake ya rabu da damuwar dake damunsa amman ya rasa yadda zai yi ,cike da natsuwa yake taku acikin d'akin yadda jikinsa ke fitar da kamshi mai sanyaya zuciya haka d'akinsa ke d'auke da kamshin dad'ad'an turarukan sa .a natse ya d'auki farin glass dinsa ya manna a kwayar idanunshi sannan ya qaraso ya d'auki agogon fata mai tsada ya d'aura a tsintsiyar hannunsa, ya bud'e bedside domin ya d'auki wallet dinsa." ya kai hannu ya d'auka ya tura a bayan aljihun wondonsa yana qoqarin rufe bedside din ne idanuwanshi suka sauka akan agogon sarka hannun maryama daya zamo cikin hannunsa a wancan ranar ,yayi shiru yana kallon agogon yana jin wani iri a gaba d'aya ilahirin jikinsa, ya kusan minti goma tsaye yana cigaba da kallon agogon gabansa na wani irin bugawa da sauri sauri tunowa da yayi matar aure ce yarinyar yasashi jan dogon tsaki yana ciza lip's dinsa."
a natse ya maida agogon ya ajiye ya qarasa inda wayoyinsa suke business phone dinsa ya fara kunnawa nan take kira James ya shigo lumshe tsumammun idanunshi yayi batare da ya d'aga kiran ba, kiran na qoqarin tsinkewa ne ya d'aga "hello sir! good morning sir ya fad'a a tare ?"morning !ya fad'a atakaice yana hura hanci "akwai wasu mutane da suka zo da buqatar ganin sabon creation shine nake neman izini a wajenka ko zamu nemi d'aya daga cikin kwararrun da suka kawo zanensu ko zaa dace ?"lumshe idanunsa yayi yana jin wani irin d'acin maganarsa dan a yanzu bai buqatar ganin zanen kowa sai na wannan yarinyar amman kuma sai ya tsinci kanshi da cewa "okay ! yayi maganar a can kasan makoshi kamar mara lafiya sannan katse kiran ya fito daga d'akin zuwa kasa ya nufi hanyar da zata kai shi bangaren mami bai wani jima ba ya fito kai tsaye AGC aka nufa dashi "
Bayan kamar awa uku da zuwansa office james ya shigo tare da some cike da girmamawa James yace "sir bayan munyi waya da kai d’azu da safe sai kuma muka canza shawarar mu sake neman wannan yarinyar data zanaka dan gsky gabad'aya zanenta yafi kyau amman anyi rashin sa'a layinta baya zuwa " take ya fahimci kowace yarinya yake magana akai, bai ce masa komai ba ya cigaba da mgn "kayi hakuri sir nasan zakaji babu dadi aranka amman ni ina ji ajikina zata zo mana da sabon design masu ... "enough james you can leave ."sorry sir ! tamkar wanda akayi wa duka ko wanka da ruwan sanyi ya simi simi nufi hanyar fita ."some ta sauke numfashi tana mai gyara tsayuwarta tare da fara magana "sir masu supply din kaya daga kafaninmu wasunsu sunki kar'bar kayanmu in group wanda ban san dalilin faruwar hakan ba "one second! ya furta yana cigaba da operating system din gabansa shiru tayi cike da girmamawa ,yayinda office din ya d'auki shiru baka jin motsin komai sai na qarar ac da system din gabansa sai kuma saukar numfashinsu "kuma kun tabbatar babu wata matsala a kayayyakin mu ?"no sir babu wata matsala ectually ma wasu sun kar'ba wasu ne dai basu kar'ba ba" amman ai gashi ina ganin sakoninsu cewar basa bukatar design din da akayi masu ne yanzu ke wannan ba wata matsalar bace a ganinki ? eh nayi magana da oga Ibrahim sir amman har yanzu bai ce komai ba ina tunanin yana son sai kuyi magana dashi ne "shikenan zan san yadda zaa gyara komai ya mike ya zagayo daga wurin zamansa yana kokarin fita yayi taku d'aya biyu ya tsaya batare daya juyo ba "kisa a binciko min inda yarinyar nan take da zama sannan kice james ya kira chef adisa ina son ganinsa gobe goben nan bai tsaya jin abinda some zata