Showing 45001 words to 48000 words out of 167047 words

Chapter 16 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

inda take zaune yana cewa "lafiya umma meke damunki kamar ma kinyi kuka ?."


wani sabon kukan ta fashe masa dashi tana zayyane masa abinda ya faru yace "ikon allah anya kuwa lafiya ?ina fa lafiya sadam kai  ma kasan ba lafiya ba ,"yanzu dai sai a kira abba aji me zai ce ,ai wad'an nan mutanen abun nasu babu imani ai bazasu bar iyayensa ma haka ba duk abinda zasuyi dan su juyar da hankularsu zasuyi ."


jikin yaya sadam yayi sanyi ya kasa cigaba da magana "wallahi da ina da inda zan kai maryama ta cigaba da rayuwarta da nayi dan  ina son taji dadi, maryama tasha wahala a hannun mutanen gidan nan sam sam basa son ganin cigabanta .""Kiyi hakuri umma komai zai wace babu abinda yafi karfin addua maryama malama ce nasan zatayi addua ."ban ta'ba shiga tashin hankali irin na yau ba domin har ga allah naso auren maryama da yusif amman da izinin allah bazasu ci bulus ba duk abinda sukai mata bazai tafi a banza ba  sai allah yayi mana maganinsa ."


bayan fitarsu maryama  yusif ya tattara hankalinsa kacokan akan shukura ita kuma sai faman zuba masa surutu take ,acikin zuciyarsa baya jin dadin hirarta amman kuma zahiri abun ba haka bane murmushi kawai yake sakar mata yana biye mata ."karfe biyu daidai suka  fito tare da shukura sai ga baba gali ya shigo ."yana ganin yusif tare da shukura ya washe hakora yana cewa "a'a  yusif ashe dai kazo?yusif ya gaishesa , baba gali ya amsa yana tmbyrsa "ina ita maryama take dana ganka da shukura ?yusif ya d'an tsotsa keyarsa  yace "yanzu ta wuce tana kuka  wai dan nace shukurace zabina ita zan aura "shukura kuma yusif ?yayi mgnr Kmr bai san komai ba "kwarai kuwa baba ita zan aura dan haka da zarar na koma gida zan sheidawa dady da mumy agaugauta azo a nemar min aurenta ta zama mallakina ".


"Ikon Allah haka kuma abun ya kasance   ?kai kuwa yusif me yasa zakayi haka?" idan wani abu tayi maka sai ka sanar ayi mata magana  bawai ka canzata da shukura ba ya fad'a haka a fili amman a bad'ani murna yayi yace abu yayi kyau aikin salama yayi tasiri  daman yasan zata iya fiyye da hakan muddin akan biyan buqatarta ne "babu laifin da ta min kawai dai bana sonta ne yanzu shukura zan aura  "to to shikenan allah yayi maka albarka Allah yasa ayi damu ."


Yasuf ya amsa da "ameen !ya tura hannunsa cikin aljihu ya  ciro bandir din yan dubu  ya mika wa baba gali "ga wannan baba "kai yusif har da wata hidima ai  da ka barshi  ni murnar auren shukura ma da zakayi ya wadatar dani sukai sallama da baba gali ya wucesu yana murna yasuf ya kira kausar tana dauka yace "Ke kina ina ne ?ina tare da maryama ne " ta bashi amsa da haka "to ni zan wuce idan kin shirya ki fito mu wuce idan kuma na wuce ne na barki to ?ok minti biyu kawai na baki tare da maryama suka fito tana kwantar mata da hankali "



kausar kenan karki wani damu dani fa idan da sabo maryama ta rigada ta saba kawai Kiyi wa dan'uwanki addua in sha allahu nima zan tayaku yi masa addua ki gaishe min da mum kice ina matukar qaunarta "tana gama fad'ar haka ta juya ta soma taku a natse  kausar ta bita da kallo hawaye na zubo mata ."tunda maryama ta juya hawaye ke turereniyar zubo mata qirjinta  banda bugawa babu abinda yake ta kasa shiga bangarensu ta wuce  bayan d'akinsu tana kuka tun daga kasan zuciyarta " ko kallon shukura kausar batayi ba ta fice daga gidan   cike da tausayin maryama suka wuce ."


alhamdulillah aunty salma ta furta cike da yalwataccen farinciki wannan magana itace mafi dadi acikin zuciyata "wallahi mama kin gama min komai arayuwata kinga yadda ya rikice yace ma nan kusa zaa daura auren "haba wa ai ni din bata wasa bace ai muddin baku auru ba to wallahi babu mai zuwa ya kwashe wannan banzar yarinyar.""baba gali yace "ai baki ta'ba faranta min rai ba kamar yau na dauka fa abun bazai yuwu ba ashe shi yafi komai sauki a wajenki dan allah kisa ayi aikin da zaayi auren kamar yadda ya fad'a "kai dai ka zuba ido kawai kayi kallo wannan auren kamar anyi an gama ."


"Kinga bari na kira fati na sheida mata ta soma shirinta "ya fad'a yana lalubo wayarsa "wani shiri kuma gareta ?aunty salma ta tambayesa "ai muktar dinta ke mutuwar son maryama tun kwanaki  dana je gidanta take sheida min nace ta d'an jinkirta muga me zai faru kinga yanzu dama ta samu",lallai kam dama ta samu  daman shine daidai da aurenta" aunty salma ta fad'a tana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya zaa qare auren dan giya " kai salama baki da dad'i wallahi bakaji dadin da naji ba ai nan duniya bana qaunar maryama yarinyar kamar aljana ga kyau ga shiga rai suje su karata da muktar, shi din ma bazata auresa ba sai ya'yana sun bar gidan nan ."


     
Cike da murna da farinciki baba gali ya kira aunty fati ya sheida mata komai ai kuwa tayi murna dan muktar din ma ya dameta kullum bashi da magana sai na maryama hatta shaye shayen da yake yace zai daina muddin zaa bashi aurenta" da kyar maryama taja kafafunta ta  shigo parlour'nsu tana  mai danne damuwarta sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci tana d'an cikin damuwa aunty ta dubeta tace "Kuna fita aunty fati ta kira waya wai kizo gobe da safe tana son ganinki "to !kawai maryama ta fad'a ta shige d'akinta dan bata son tayi doguwar hirar da har  zai sã mahaifiyarta ta fahimci wani abu duk da tasan dan dole tasani amman ba da wuri haka ba "safa da marwa ta shiga yi acikin d'akin tare da cure hannuwanta waje d'aya" tsawon shekaru aunty salma na bibiyar rayuwarta ."


"laifin me tayi mata ? me ta tare mata? idan wani laifi tayi mata ta fad'a mata ta nemi yafiyarta ta barta ta huta  "? wasu hawaye masu ciwo suka gangaro mata a yanzu ba kanta kad'ai take tausayawa ba har da  mahaifiyar yusif da yaruwarsa dan ita tsakaninsu dasu aunty salma da baba gali da ya'yanta allah ya isa ne bazata ta'ba yafe masu ba ,domin cirewa kanta damuwa Kan kujerar zanenta ta nufa ta zauna ta zaro farar takarda ta ajiye agabanta ta d'auki pencil ta tura cikin bakinta ta fara tunanin me  zata zana ?".



Babu abinda yazo cikin kwakwaluwarta sai fuskar kausar murmushi mai hade da damuwa ya bayyana akan fuskarta "kausar zan zana domin dai nasan shikenan ni da ita kuma sai wani ikon allah ."ahankali ta soma bada shape din fuskarta tunda ta zauna bata tashi ba sallah laasar né kawa  ya tashita koda ta idar ma Kan aikinta  ta koma ta cigaba ranar a d'akin maryama ta qarasa niyyinta da misalin karfe bakwai   aunty ta shigo d'akin ta isketa tana gabatar da sallar magrib ."


Ta qarasa gaban table din kayan zanenta nan idanunta yaci karo da hoton kausar har da kalar kayan  data zo dashi  yau din nan aunty ta saki murmushin jin dadi  tare da cewa "lallai princess an fad'a soyayya ko da yake yarinyar tana qaunarki ta qarasa mgnr adaidai lokacin da maryama ta sallame ta  mike jiki a sanyaye take kallon aunty dan wallahi sai take jin kamar bata kyauta mata ba tunda ta tabbatar kota fada mata kuka kawai zatayi tayi hakuri sannan ta kwantar mata da hankali "


"kinyi shiru kina kallo meke damunki ?girgiza mata kai tayi alamun babu komai "amman tun bayan tafiyarsu  kausar na lura kike cikin damuwa idan wani abu ne ki sheida min mana ?ajiyar zuciya ta sauke da karfi tace "babu komai "to muje kici abinci ta kamo hannunta suka fito tana cewa "gsky zanen kausar yayi kyau idan tagani zataji dadi sosai tare da aunty suka ci abinci bata wani ci abincin kirki ba tace ta koshi ta sha ruwa ta mike ta shiga bayi ta dauro alwala ta koma d'akinta  sallar ishai ta gabatar byn ta idar ta mike tana nade daddumar sallah ."


Ta ajiye a inda yake ta tsaya shiru  acikin d'akinta tana jin wani irin faduwar gaba ta qarasa ta kakkabe wajen kwanciyarta sannan ta kwanta rigingine ta hade hannuwanta duka a qirji tana tunanin rayuwa ganin zata damu zuciyarta ne kawai a banza ta sauke ajiyar zuciya ta soma karanta suratul mulk ahankali bayan ta gama karantawa  ta shafe jikinta da addua ta kwanta, ahankali bacci ya dauketa cikin baccinta tayi mafarkin umma tace a daura aurenta da yaya sadam har ma ya amince da auren kiran sallah asuba ne ya tasheta daga mafarkinta ta mike ahankali ta zauna ta zuro kafafunta kasa   tare da dafe goshinsa ."



Tayi shiru tana tunanin mafarkinta addua tayi Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi arayuwarta da kyar ta yunkura ta mike tsaye ta fito ta shiga bayi  ta dauro alwala ta dawo daki tayi sallar asuba duk ta rasa meke mata dadi duk da tasan mafarki ne amman sai taji abun ya tsaya mata arai cike da raunin zuciyata  ta koma ta kwanta ahankali bacci ya kwasheta aunty ce ta shigo ta tasheta tana cewa "bazaki gidan aunty fati bane kinfa san halinta  babu hakuri sai ta d'auki abun wani iri azo ana damun rayuwarki “ numfashi ta sauke kawai tare da mikewa zaune tana dafe goshinta "ko baki jin dadi ne  dan tunda kika koma kika kwanta bacci bayan sallahr asuba to baki da lafiya tayi mika tace "kaina ke d'an min ciwo sai dai kuma .."sai tayi shiru ta kasa mgn "sai dai kuma me ?"


"Wallahi umma mafarki nayi wai umma tace a daura aurena da yaya sadam kuma har ya amince ?aunty tayi dariya tana cewa "kai princess wani irin aure kuma bayan ga maganar yusif ? ta kalli aunty tana jin fad’uwar gaba mai tsanani tace “aunty ki bar maganar yusif muyi maganar mafarkina gsky banji dadin mafarkin nan ba " to ai mafarki ne mafi yawon lokuta mafarki baya zama gasky tashi ki sha magani kije tun karfe tara aunty fati take kiran waya "to ni me zan mata ne ?tayi magana Kmr zatayi kuka "ni wallahi bana son zuwa koina idan kaga sun nemeka to aikin wahala ne ga wannan d’an nata mai shegen maseefar kallon tsiya kamar zai cinye mutun ".


"To ko na fad'a mata bakijin dadi bazaki samu damar zuwa ba  ta kira kaulat ko Islam suje idan wani aiki zaa mata sai suyi mata ?maryama tayi shiru can  tace  "yanzu rashin zuwan nawa  zai zama tashin hankali azo ayita kananan magana "shiyasa nake son kije idan ma aiki ne kika ga zai miki yawa Kiyi iya wanda zaki iya ki dawo ,nifa ba aikin bane damuwata kamar matsefaffen kallon da yaya muktar yakewa mutane ".


"Babu ruwanki da kallonsa kiyi abinda ya kaiki maza tashi ki tafi dan ki samu ki  dawo da wuri “numfashi ta sauke” gsky aunty bazanje yanzu ba “ya fad’a tana wasa da yatsun hannunta “sai yaushe zaki?maryama tayi shiru ta kasa mgn “da dai kin daure tunda kinga baki da lokaci sai asabar da ladidi tsaki maryama taja kana tace “wallahi ban san dalili ba hakan nan najin fad’uwar gaba kuma dai yau bana son zuwa koina “aunty ta numfasa tace “to shikenan Kiyi zamanki muje kiyi wanka ki karya ki sha maganin ciwon kai ta mike ta fito wanka tayi ta shirya ta karya aunty ta bata magani ta sha tayi kwanciyarta akan kujera .”


Ahankali ta rufe idanunta lokaci d’aya kwakwalu warta ta bud’e tunani ya kusantota yaki barinta ta huta duk da bata son tayi tunani akan matsalarta amman haka tunani ya mamayeta , ahankali ta dinga tunanin maganganun yusif ,me yasa zaki damu kanki maryama already kin rigada kin yarda kin rasa yusif har abada kamata yayi kin haka rami ki binne komai ya zama tahiri arayuwarki” zanyi haka zan cire komai araina kuma zan dage da addua har na samu nasara arayuwata ahankali tabi shawarar zuciyarta ta haka rami mai zurfi aciki zuciyarta ta binne duk wata matsalarta .”


tun daga wannan ranar maryama ta cire tunani da damuwar komai acikin ranta ta toshe kunnenta duk abinda ke faruwa aciki gidan tana ji kuma tana gani amman ta share sannna taki bari mahaifiyarta tasan halin da’ake ciki yayinda kullum sai aunty ta sheida mata sakon kiran aunty fati har sanda sati ta cika aunty ta matsa mata lallai taje taji dalilin kiran da take mata “Allah aunty bana son zuwa duk sanda kika fad’a min sakonta gabana faduwa yake “kiyi hakuri ki daure kije bana son tazo gidan nan “ta fad’a muryarta a raunane ganin yanayin aunty yasa ta riko hannunta “shikenan aunty zani bari na sauya kaya naje yanzu na dawo .”


“Yauwa princess maza tashi kije Allah ya tsare min Ke “Ameen !ta furta a tsanake ta fito ahankali take taku har fito  titin unguwarsu ta mike zuwa captor road tana gama garasawa bakin titi ta samu adaidai mai zuwa unguwarsu  aunty fati tafiya kad'an suka yi ta sauka pencilima ta mikawa mai adaidaita kudi ta ta tsallako hannunta na hagu inda zai shigar daita amawo ."a natse ta shiga gidan kai tsaye bangaren aunty fati  ta nufa bakinta dauke da sallama ta shiga parlour'n inda ta iske muktar da aunty fati zaune ."
Rike da remut tana qoqarin canza tasha a tare suka kallo kofar tare da amsa sallama .”


tun daga kasa muktar  ya dauki kallon maryama ransa nayi masa dadi wani irin yanayi ya tsinci kanshi  ciki mai wuyar misaltuwa yana jin yadda soyayyarta ke fixgarsa yayinda maryama ta had'e fuska sosai tmkr taga wani mugun abu  ta qarasa ta tsugunna har kasa ta gaishe da aunty fati ,aunty fati ta amsa mata fuskarta a d'an sake wanda hakan ya dan bawa maryama mamaki domin tunda suke daita  kyara da hantara tattare da zagi né a tsakaninsu ."


Maryama ta dauke kanta tare da mikewa tsaye ta zauna tana jiran taji dalilin nemanta da aunty fati take "ke maryama baki ga muktar bane da bazaki iya bud'e ki gaishesa ba ko shi kike jira ya gaisheki ?
"murmushi ya saki yana cewa"Kinsan ‘yan boko ba dai girman kai ba " wani kallon takaici maryama tayi masa daga sama har kasa wanda yasa ma kasa cigaba da magana illa ya zuba mata kwala kwalan idanusnhi masu firgitarwa ."sama da awa daya tana zaune tana wasa da yatsun hannunta sannan aunty fati ta gyara zama ta kira sunanta .”


"maryama !

muryarta a raunane ta amsa da “na’am !"na kiraki né domin na samu labari wannan yaron yusif ya canzaki da shukura yanzu ita zai aura shine muktar yace abashi ke tunda kowa gudnki yake kinga kenan shi zai taimaka ya aureki sai yanzu na na gane dashi kika  dace ba da sauran mazan da suke zuwa neman aurenki suna guduwa , d'ago idanunta tayi ta zubawa aunty fati tana kallonta gabanta na dukan tara tara sannan ta waiga ta kalli inda muktar din yake yana kallonta kamar tsohon maye ."


"Karki dauka ya rasa wacce zai aura ne yasa zai aureki aa tausayi kika bashi domin yaji babu dadi aransa , yanzu me kika gani zaki auresa ko kuwa zaki tsaya jiran masu kudin da basamu zakiyi ba ?ta tambayeta tana gyara zamanta tare da tsareta da idanunta "parlour'n ya dauki shiru na kusan mintuna goma batare da maryama tace uhm ba bare uhmm illa nazari maganar aunty fati da take da kuma tunani amsar da zata bata domin dai a halin yanzu wannan shine labari mafi muni daya kusanto rayuwarta muktar fa ? "ke nake sauraro !?"


Murayarta can kasa ta soma magana a tsanake "a zahirin gasky ni ina da wanda nake só kuma wanda a shirye yake da aurena idan da hali zaa iya bashi kaulat ko Islam ,ko kuma sakina amman ni dai gsky ayi min hakuri akwai wanda muka tsaida magana dashi ."ta tsinci kanta da fad’ar haka ba dan akwai din ba sai dan tsiratar da rayuwata daga shiga maseefa”waye shi kuma a ina yake ?"maryama tayi shiru ta kasa magana hankalinta idan yayi dubu tô a tashe yake tayi datasani zuwa gidan amman tasan ko bata zo wannna maseefar sai ta biyota har gida "


“ke banson iskanci banza bayan nasan babu kowa a kasa shine zaki ce kina da wanda zaki aura tô ke nake son ya aura ,oh a zuwan kinfi karfin aurensa shine kika lissafo min daidai shi ko ?"ko d'aya aunty a dai bashi cikinsu shine zai samar da kwanciyar hankali "bata son wata fitina ta kuma lura kamar fitinar ce take bibiyarta arayuwarta, ran a aunty fati a matukar bace tace "d'an ma Kinsamu zai taimaka miki maza tashi ki bani waje na sallameki sannan ki fara shirin aurensa dan dolenki ki auresa"

Jiki a sanyaye maryama ta mike hankalinta a matukar tashe  bazata ki dan shaye shaye ba dan mahaifinta ma har ya bar duniya yana sha babu komai acikin rayuwarsu sai matsala ita me kai ta saka rayuwarta cikin ha'ula'i ?kuma tasan idan ba tsanarta da aunty fati tayi ba babu yadda zaa yi tace ta auri d’anta domin ko ita take da diya kamarta tayi imani bazata dauketa ta bawa muktar aure ba mutumin da idan yayi shaye shayensa har kwata yake fadawa haka maryama ta koma gida tana cika tana batsewa duk ranta a dagule ."


Aunty ce ta fito daga kitchen tace "lafiya kuwa naga har kin dawo yanzu ?hawaye maryama ta share tace" aunty laifin me nayi da allah ya qaddaroni cikin wannan dangin ?basa sona basa qaunar cigabanna idan akwai wacce suka tsana a duniya tô nice suna jin kamr su kasheni wallahi suzo su kasheni su huta da muguwar tsanar da suka min na rasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login