Showing 135001 words to 138000 words out of 167047 words

Chapter 46 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

mijinta wani yana gurin ATA  ."wani office ya shiga daita kai tsaye  gaban wani farin baod yaja ya tsaya tare da jingina jikinsa da bango segun yayi saurin  janyo kujeru guda biyu daya a gaban baod din dazaayi zane  d'aya kuma a inda ATA zai zauna "sir ka zauna ! ya zauna tare da daura kafarsa d'aya akan d'aya jiki a sanyaye  maryama ta zauna  tana jiransa sai daya gama shan kamshinsa sannna ya sallami segu ya fara mata bayani  tana jin ya fara magana ta d'aura hannunta akan boad ta fara fidda kyakkyawar shep din jikin zanen da yake buqata , yana mata bayani tana zanawa lokacin data zana karan hancinta taji wani mummunar tsoro ya shigeta cak ta tsaya ta kasa cigaba da zanen da take ta tsurawa baod din gabanta ido kwaayr idanunta ta zana da hancinta har ma da yanayin jikinta babu abinda yazo zuciyarta kamar zanenta data gani a office din m . malik “ nan da nan gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta.shi kuwa gyara zamansa yayi sosai yana kallon zanen lallen hannunta da yadda take tafiyar da aikinta bai san ya'akayi ba yaji saukar hannunsa akan hannunta yana shafawa ."


Cikin gigita gangan jikinta ya kama rawa wanda  yasa ATA ya dawo haiyacinsa sai dai ya kasa d'auke hannunsa ajikinta da kwayar idanunshi wani irin tsoro da matsanancin firgici ATA  yaga ya bayyana afuskar maryama ,yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa, cikin sanyin jiki ta sabule hannunta cikin bacin rai  tace "meye haka ?"dan allah aiki nazo yi banason irin
wannan wasan iskanci  mai barazana ga rayuwata wannan ya zamo karo na farko da qarshe karka sake kuskuren sake kai hannunka jikinta "ta fad’a tana jan tsaki" ajiyar zuciya ya sauke tare da kafa mata tsumammun idanunsa cikin sayin murya yace "look at me “ta kallesa Kmr yadda ya buqata  babu wasa acikin kwayar idanunshi   "Kinga nayi miki kama da dan iska ?sosai kuwa dan gashi naga alama daga zuwa aiki sai ka bige da kai hannunka jikina batare da kayi laakari da ni din matar aure bace ko kuwa budurwa bace ".hakan nan yaji ya tsinci kanshi da adduar allah yasa single ce ba matar aure ba  ya sake kai hannunsa tsintsiyar hannunta tayi saurin zare hannunta har agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta ya zame cikin nashi “wai meye haka dan allah nifa matar aure ce kuma tare da mijina nazo aikin nan “ta fad'a hankalinta a matukar tashe shiru yayi yana qare mata kallo qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin  karfi wanda baya jin haka akan kowace mace sai akan mafarkinsa.”



ahankali ya motsa labbansa "ko zan iya ganin fuskarki ?"ya tmbyeta yana qara gyara zamansa
"no !ta bashi amsa a matukar tsorace ya sauke numfashi tare da mikewa tsaye ta sake ja baya tana cewa "karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba  ganin tana nema ta fice daga hayyacinta ya sanyashi kamota  hadi da zaunar da ita "lokacin daya kamota wani irin socking ne ya ziyarci zuciya dama gangar jikinsa nan take bugawar da zuciyarsa take ta qaru fiyye da kaida sai dai ya kasa magana a fili sai a zuci "ki natsu wallahi babu abinda zan miki ni kaina bansan meke damuna ba yau , tun da kika kasance tare dani naji komai nawa ya sauya .”
Yayi shiru tare da tsura mata ido ita kuwa banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi, neman hanyar guduwa take daga garesa ."yayinda wasu irin hawayene masu azabar zafi suka taru a kurmin idanunta "wallahi ka cuceni tun da nake babu wani nmj daya ta'ba kai hannunsa jikina tun ina matsayin budurwa sai yau dana kasance mallakin wani  tana gama fad’ar haka ta   fashe da wani irin kuka "okay ki zauna ki qarasa min aikina na sallameki and ki yafe min bisa kuskurena kafin ya gama mgnrsa har ta soma tattara  kayan aikinta ta zuba cikin jaka ta fice da sauri ."da sauri ya fito ya  biyota yana kiranta "ke!!!


"ita kuwa da sauri sauri gudu gudu ta shiga lift ta danna grand segun ne ya fito da sauri sakamakon jin sautin muryar mai gidansa , cikin gigita segun yace sir meke faruwa ne ?"karka bari yarinyar nan ta wuce  ka tsayar min daita !ka tsayarda ita segun amman ina cikin kankani lokaci maryama ta sauka kasa tana goge hawayen fuskarta cike da tashin hankali ta nufi inda motar  yaya sadam yake a pake jikinta na wani irin kyarma ta bud'e ta shiga ta zauna kallo d'aya yayi mata ya fahimci tana tattare da damuwa nan da nan ya rud'e ya shiga jera mata tambayoyi "ka taimakeni  yaya sadam ka bar garin nan dani akwai matsala "wacce irin matsala ?zan maka bayanin komai idan mun isa gida daga haka bai sake cewa komai ba yaja motarsa a guje suka fara qoqarin ficewa koda segun ya fito har motarsu ta fice daga ma'aikatan ."


Wani irin gudu yaya sadam ke falfalawa akan titi yana cikin gudu ya hango wasu motoci gudu uku abayansu suna biye dashi idan ya rage gudu suma sai su rage gudu haka idan ya qara gudun motar zasu qara "maryama kamar ana binmu ki fad’a min meke faruwa ? ta kasa magana kawai ta fashe masa da kuka dan bazata iya fad'a masa abinda mai kamfanin creation yayi mata ba ,ya zama abun kunya gareta ace ta fad'a masa wani kato ya ta'ba mata jiki ya zai dauketa ina yarda da yayi mata ?"kuka ta cigaba da yi shi kuma yana falfala gudu akan titi shi kansa kana kallonsa kasan a matukar tsorace yake sun yi tafiya mai dan nesa sannan suka nemi motocin uku dake biye dasu suka rasa sai daf daa zasu fita daga ogun state kawai sai ga  motocin guda uku sun  sha gabansu."cak yaya sadam yaja burki ya tsaya cikin tsananin fargaba wasu tika tikan murd'ad'd'un mutane suka shiga firfitowa daga cikin motar d'aya bayan d'aya har suka fito gaba d'ayansu sanye da kaki wanda ke nuna alamun sojojin nigeria ne wani irin matsanancin tsoro da firgici ne ya kama marayam tayi saurin riko hannun yaya sadam gam cikin nata jikinta na kyarma shima ya riketa gam   bai yi tunanin ko yan fashi da makami bane sakamakon kakin dake sanye ajikinsu zuciyarsa tafi bashi wani abu dabam ,mutun uku daga cikin sojojin suka qaraso da sauri suka bugi kofar motar da karfi batare da 'bata lokaci ba kofar ta bude basu tsaya wata wata ba suka fito da yaya sadam tare da buga masa bakin bindiga nan take ya zube kasa .”


maryama ta saki qara mai sauti ta fito ta durkushe gabansa cike da matsanancin tsoro yaya sadam ya janyota zuwa jikinsa ai kuwa ta kamkamesa dan gabad'aya a tsorace take hawaye né ya soma bin kuncin maryama cikin sheshekar kuka maryama ta soma magana "bayin Allah laifin me mukayi maku ?dan Allah karku cutar da ni da mijina ,dan allah ku barmu mu wuce tunda nasan bamuyi maku laifin komai ba "ke ce bakiyi mana laifin komai ba amman shi wannan bakin munafikin yasan abinda yayi mana "inji cewar daya daga cikinsu da sauri maryama ta tsurawa yaya sadam idanunta  tana kallonsa "wai kai dan rainin wayo ko ?mu zaka rainawa hankali ?".a d'an rud'e yaya sadam yace "Nifa duk ban fahimceku ba hasalima ban san laifin da nayi maku ba ,su waye ku ?meye hadina daku ?laifin me nayi maku ?ya jera masu tambayoyin yana sake riko maryama jikinsa "kai karka nemi ka rainawa kanka hankali dan ubanka kayi tunani laifin daka aikata acikin satin nan  wanda kai kanka  kasan dole zaa iya bibiyarka?".


yaya sadam yayi shiru yana nazarin maganr  shi dai asaninsa bai aikatawa kowa laifin komai ba baya ga auren maryama da yayi "har kusan minti biyar yaya sadam bai ce uffan ba yasa suka cigaba da magana "me taurin kan tsiya kawai  amman tunda baka tuna ba idan kaje lahira zaa maka bayani dalla dalla akan taurin kan da kayi ,kai jojo ku daukosa mu aikasa lahira yadda yayi taurin kai dan son more duniya bazai zauna a duniyar ba "nan da nan suka rufe masa   ido da bak'in kyalle ,suka d'aure masa hannayensa duka abayansa kafafunsa ma a d'aure ,suka rufe masa baki suka ciccibosa suka watsa shi acikin mota "itama  yarinyar kuyi mata kamar yadda kuka masa ku sata acikin mota ku had'a daita batare da 'bata lokaci ba aka rufe fuskarta aka tasa keyarta cikin mota tunda tashiga motar take rutsa kuka mai ta'ba zuciya tare da kiran sunan Allah yayinda yaya sadam yasa hannuwansa duka ya dafe goshinsa yana zurfafa tunaninsa alokacin da motocin suka karya kwana cikin wani kungurmin  daji mai cike da duhu da ban tsoro suna sharara gudu."


tunanin duniya yaya sadam yayi amamn iya tunaninsa bai ga wanda zai iya masa haka ba  idan safiya ce yasan baa akansa zata huce ba sai dai akan maryama tunda tasha fad'a masa muddin taganta sai ta aikata lahira ."nadiya kuwa yasan kwata kwata bazata masa haka ba shi kuwa wa yayiwa laifi ?"idan ma laifi ne to sai dai akan auren maryama da yayi ne to waye wanda zai masa hk ?bai samu amsar tambayarsa ba yaji motocin sun ja wani irin burki sun  tsaya a daidai karshen dajin tare da bubbud'e kofofin motocinsu a zuciye, na karshen ne ya fito rike da kwalar rigar yaya sadam wanda   babu halin yin kwakwaran motsi ballantana yasamu damar yin ihun ceton ransa da'ake barazanar raba shi dashi, ahankali suka shiga jansa a k'asa suna tafiya dashi  cike da tsansar rashin imani  , wanda kallo daya zaka  masa kasan a rikice yake d'aya daga cikinsu ya rike hannun maryama ."


Basu tsaya akoina ba sai a bakin wani katon rami suna huci "ku binnesa da ransa jin haka yasa maryama ta rikice ta gigice tashiga wage wage tana kiran sunan yaya sadam "dan girman allah karku kashesa karku binnesa da ransa gara ku kasheni wallahi banason na rasashi yana da matukar mahimanci arayuwata na bada rayuwata fansa, gara ku dauki raina ku barshi dan Allah karku kashesa duk wani abu da zaku masa kuyi min ni daman nafi bukatar mutuwa da rayuwata dan bana jin dadin rayuwar nan na rasa komai karku bari na rasa mijina tausayinta ya kamasu "d'aya daga cikinsu ya jawosu gefe yace "me kuka ga zaa yi ?"ya tambayesu "kar mu batawa kanmu lokaci wajen tausayi mu cika aikin daaka ba mu "shikenan a wuce gurin .”


aiko suka dauki yaya sadam suka jefa cikin rami suna shirin jefa maryama mutun daya acikinsu wanda shine yafi jin tausayin maryama yace mu barta tunda daman shi kadai aka bamu aiki "okay! suka amsa. a matukar gigice take batasan ya’akayi ba ta zare kyalen da suka rufe mata ido dashi tana gama bude idanunta yaya sadam dinta ta gani acikin rami suna zuba masa kasa zuciyarta ce ta tsaya cak ta daina aiki a lokaci har suka rufesa da ransa ."
Bayan sun gama suka hau jijigata a gigice ta dawo haiyacinta idanunta na zubar da hawaye wani razananniyar qara ta saki da karfi tana kiran "ina mijina yake ?idan har kun kashesa ku had'a dani ku kashe  dan allah karku barni a raye dan bazan iya rayuwa babu shi ba haka ma mahaifiyarsa ." numfashi suka sauke atare  "aikin gama ya gama yarinya tuni mijinki mai taurin kai yana cikin nan suka nuna mata inda suka binnesa, an gama da  labarinsa sai dai uwarsa ta haifi wani idan an sake haifosa a duniya bazai sake kinjin magana ba "ai tana gama jin maganarsu numfashinta ya soma barazanar d’aukewa "me yasa ?me yasa zaku masa irin wannan hukuncin inna lillahi wa inna ilaihi rajiun me yasa zaku kashesa tayi taku biyu zata isa inda suka binne mata miji kafafuwanta suka gagara daukarta ga wani irin nauyi da kanta yayi idanunta suka fara rufewa jiri take gani nan take ta zube kasa sumammiya ."


Mmn Sudais

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


             Page 26

   Ran ATA a matukar 'bace yake zaune acikin jirginsa yana  tunanin maryama ,wani irin ciwo yake ji a zuciyarsa dan bazai iya misalta  yanayin bugun zuciyarsa ba ,ga wani sara da kanshi ke masa  har baya iya bud'e idanunshi sosai yayinda kowani second 'bacin ransa na sake nunkuwa wanda baya raba d'ayan biyu damuwar  maryama  ce bai san dalilinsa na kai hannunsa jikinta ba ."mai yasa yaji sauyi ajikinsa adalilin sake d'aura kwayar idanunshi akanta ?"mai yasa yaji yana buqatar ganin fuskarta a zahiri ?
yana jin wani irin sauyi akanta lallai yana buqatar ganin halittarta a zahiri zuciyarsa ta amsa masa kuwan haka ." da wannan tunanin ya isa gida alokacin da magariba ta kawo kai .jirginsa mai saukar ungulu na gama tsayawa a haraban gidansu rai a 'bace yake tattaka matattakala yana qoqarin saukowa , kai tsaye ya shiga bangaren mami sosai yake jin damuwa acikin zuciyarsa qoqarin danne damuwarsa yayi dan kar hankalin mami ya tashi sai dai kallo d'aya  tayi masa ta fahimci akwai damuwa atattare dashi ."



         "muryarsa a kasalance ya gaishe da mami ."kamar ko yaushe ta amsa masa tana mai tsura masa kwayar idanunta kamar wacce taga wani  sabon halitta ,cike da kulawa tace "sannu da zuwa adamcy ya hanya ka dawo lafiya ?da sauri ya amsa mata da "lafiya !"yana qoqarin hayewa samansa  hannunsa d'aya soke acikin aljihun wandonsa .bayansa tabi da kallo "shigowarsa cikin wannan yanayin yasa duk mami ta d'an rikice kasa samun kwanciyar hankali tayi ,cike da tashin hankali ta mike tsaye tabi bayansa .
ahankali ta tura kofar parlour'nsa ta shiga duhu falon  dan haka ta kunna wuta nan da nan haske ya haskaka koina a parlour'n sai dai bata gansa ba dan haka ta nufi hanyar bedroom dinsa ta shiga nan ta iskeshi tsaye ya jingina jikinsa da bango d'akin yayi sama da kanshi  hawaye ne kwance acikin  idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa ya rasa meke masa dadi arayuwarsa bai san ta ina zai fara ba ,komai ya rigada ya tsaya masa gabad'aya baya jin dadin rayuwarsa  ,ya kasa fahimtar kansa ko kuma yace yau tazo masa da abubuwa da yawa wanda duk tarin damuwa ne akan wanda yake ciki ya dinga jin kamar ya kashe kansa ya huta da rayuwar da yake ."



lumshe tsumammun idanunshi yayi sai ga hawaye sharrr na bin kuncinsa "adamcy nah ! ".mami ta kira sunansa cikin tsananin tashin hankali har jikinta na rawa . amatukar firgice ya tsaida kwayar idanunshi dake cike da ruwan hawaye  akanta qirjinsa na wani irin dokawa da  sauri dan bai ji motsin shigowarta ba sai sautin muryarta wani irin zazzafan numfashi ya sauke yana sake maida kanshi sama tare da ciro hanky ya shiga d'auke hawayensa"lafiyarka kake zubar da hawaye adamcy ?ta tambayesa cikin tsananin tashin hankali dan duk abinda zai sashi zubar da hawaye baqaramin abu bane  da muninsa ya wuce misali. shiru yayi ya kasa magana dan bai san me zai fad'a mata ba "kayi min magana mana  adamcy dan kasa har zuciyata ta fara tsinkewa."
da yatsan  hannunsa  ya nuna mata daidai saitin zuciyarsa dake bugawa fiyye da kaida ."sake matsoshi tayi sosai tana cewa "meke damunka "?"zuciyata sweet.."   yana kai wa nan yayi shiru ya kasa cigaba da maganar idanunshi na sake cikowa da ruwan hawaye"me ya samu zuciyarka ?" ta sake tambayarsa hankalinta na qara tashi "I don't know what's wrong with me sweetheart amman dai nasan  zuciyata kullum ciwo take min"."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun " allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta "abinda mami ta shiga furtawa kenan tana sake maimaitawa " i know something is wrong with my heart wallahi sweetheart akwai ciwo  mai zafi acikin zuciyata wanda zai iya kasheni nan kusa .."



nan da nan fuskar mami ta qara sauyawa  hankalinta a matukar tashe tace "ka dinga sausautawa kanka adamcy da yawon tunani ,ka dinga addua akan duk abinda ya dameka  addua tana canzawa bawa qaddararsa kuma tana saka natsuwa acikin zuciyar bawa "numfashi ya sauke da karfi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ,magana yake son yi amman zafin da zuciyarsa keyi ya hana shi cewa uffan "kasamu natsuwa adamcy ka dinga furta wannan adduar zaka samu natsuwa da sausauci a wajen Allah zai yaye maka dukkanin damuwarka "allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta ahankali ya sauke idanuwanshi ya tsura ma mami  kawai yana kallonta cikin yanayi na tsanani  damuwa "ka sani idan wani abu ya sameka nice farkon wacce zata fara shiga damuwa ga kuma d'an  cikin jikin maryam wanda bamu san abinda zata haifa ba karka bari muyi maraicinka. adamcy  kasan yadda nake sonka  idan na rasaka zan shiga damuwa a kullum adduata na mutu na barka  a duniya ba ka mutu ka barni ba tunda ta fara magana bai ce mata  uffan ba sai ma ciro wayarsa da yayi ya soma neman layin likitansa  muryarsa ce ta katse mami daga maganar da take masa ahankali yake magana tamkar mara lafiya "doctor kazo ka dubani please ".daga haka bai sake cewa komai ba ya katse kiran d'akin yayi tsit tamkar babu mutane acikinsa ."



Ahankali ya soma d'aga kafafunsa zuwa Kan gado ya fad'a ya kwanta flat ransa duk babu dadi yayinda idanunshi na kallon saman d'akin babu abinda yake gani sai kwayar idanun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login