Showing 24001 words to 27000 words out of 167047 words
Chapter 9 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
"kamar ya zaka basu mamaki ?.”
"bazan ta’ba kwana a gidan ba, aure ne nayi ,tariya ce na basu damar sukaita ,rayuwa daita kuma bai zame min dole ba haka zata qare rayuwarta batare dani ba " haba abokina karka yi haka mana ka tausayawa yarinyar nan mana ,”kaga ni ba abinda ya kawoni kenan ba “ mb ya gyara zamansa yana dubansa a tsanake tare da cewa “me ya kawoka?“nazo ne akan hisham ".
”hisham kuma ?mai faru dashi ?yayi masa tambayar a jere cikin tsananin tashin hankali ya sauke numfashi kana ya motsa lips dinsa kadan "hisham yana son mu samu matsala dashi “a natse ya cigaba da magana ya zayyano masa komai mb ya numfasa kana yace "gsky bai kyauta ba zan masa magana amman kai kuma ai bai kamata kaji ciwon abinda yayi ba tunda kaima halinka ne koma nace a wajenka ya koya,kaga yanzu lokaci yayi da zaka canza” ata ya d’an d’ago kanshi ya tsura masa tsumammun idanunshi “
”wallahi ka canza halinka kaga yadda yaruwarka baza taji dadin aure a gidanta ba kana cin zarafin ya’yan wasu da kanen wasu amman kai baka son ayiwa naka ai kai ma kasan hakan ba abu ne mai sauki ba ,kasani duk abinda kayi sai anyi maka “wannan ba gasky bane yayi maganar yana lasar lip’s dinsa “duk dai abinda mutun yayi akanshi zai qare ba akan wani ba mb ya bud’e baki zai sake magana ata yayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa “dan allah na gama da wannan maganar shi kuma hisham ka nemeshi kaja masa kunne, kuma zan kira auta matukar tana facing din matsala a gidansa sai kunji tsoron abinda zai biyo baya dan wallahi sai na kashe auren gabad’aya.”
“idan kuma tana son mijinta fa ? shiru ata yayi batare da ya ce komai ba yana nazarin maganar mb “ka tsaya ka natsu kayi tunani mai kyau domin kashe auren ba shine mafuta ba , ka barta tayi zaman aurenta lafiya , babu ruwanka da matsalar gidanta idan da wata matsala nayi imani nana hauwa’u zata kawo karshensa ,ina baka shawara ka cire hannunka karka zo kayi abinda zaa zo ana kuka da kai “ shiru ata yayi ya kasa cewa komai yana nazarin maganarsa har sanda amira ta sake fitowa ta cika masu table din gabansu da kayan abinci iri iri ta juya zuwa d’akinta ."
"Abokina ..!"rin wannan liyafa haka,gsky ina da rabo acikin abincin gidanka yau shyasa haushina ya kawo ni gidanka kasan bayan mun shigo haraban gidan nan naji kamar bazan shigo ba"yanzu dai kanka ake ji sarkin kwad'ayi,ga abinci nan kayi sarving din kanka ata yace " no bari amira ta fito "ta fito tai maka me ?”yayi masa tmbyr yana hararasa “hankali kwance ata yace “ta zuba min mana “ai kuwa baka isa ba sai dai idan bazaka ci ba ,amman matata ni kad'ai zata sarving ,idan kuma lallai ka matsu da cin abinci kaje ga matarka .”
"uhm !ata ya furta daga kasan makoshinsa sannan yace "banson iskanci fa mb matarka ko matarmu ? mb yayi murmushi yana dubansa adaidai lokacin da amira ta sake fitowa yace "darling zubawa wannan gogaggen dan iskan abinci yaci ba dan halinsa ba “ murmushi tayi ta zuba masu tare ."sai da ya gama shan qamshinsa kafin ya soma cin abinci."mb ya gyara zama yace “gsky abokina karka cuci kanka wallahi kaje
wajen matarka ko babu komai ai ka rage mara “ata najinsa amman yayi masa banza yayi tmkr ba dashi yake mgn ba ya cigaba da kai abinci bakinsa .”
mb ya ajiye spoon din hanunsa ya zuba masa ido yana kallonsa “ wallahi ata ka canza rayuwa “me ya faru da rayuwata da zan canza ?abubuwa daya kuwa sun faru da rayuwarka taya da ranka da lafiyarka ga lafiyayyar mata allah ya baka amman ka tsaya cutar kanka .”kowa da yadda yake rayuwarsa ni yadda nake rayuwata empty yayi min .” ata ya fad’a batare daya jallesa ba shiru mb yayi yana cigaba da kallonsa kafin daga bisani yace “kai ko baka da lafiya ne? ata ya d’ago a natse yana dubansa mgnrsa ta bashi dariya sai dai yaki yi dan ba aladarsa bace yin dariya .”
“Ka tsareni da ido ko kuma maganar mami ce ta tabbata yarinyar mafarkinka aljana ce ?”uhm mb kenan “babu wani mb kenan ka fito ka fad’a min gsky gabanka na tashi ko kuwa zero ne kai ?ata ya dauke kanshi yana cewa “babban tashi ma kuwa dan a halin da nake ciki sannan na samu irin kalar yarinyar da nake so to wallahi sai ahankali dan zataji jiki “mb ya kwashe da wata dariya yana buga hannunwansa “ kasan wani abu abokina ?ata ya kai abinci bakinsa yana dan kallonsa alamun yana jinsa "daman irin ku ne idan suka shiga hannun mace sai allah ,sai yadda akayi daku ba soyayya ba hatta gaban mace sai ku lashe baku sani ba” abincin bakinsa ya tofar da sauri bayan ya dalla masa katuwar harara kamar zai cinye shi ".
”allah ya isa tsakaninmu da kai mb wannan ai cin fuska ne,ko zan so mace sai na kama wani lashe gabanta gabanta fa? ni adamcy ,i think ka fara hauka ,kai allah ma ya isa tsakanina da kai ya sake maimaitawa yana ajiye spoon din hannunsa tare da ture plet din abinci , alokacin da sugura ta fito da mugun gudu daga d’akinsu mansor na biye daita tana ganin ata ta nufo wajensa ta fad'a jikinsa tana kiran "uncle !"kaga yaya mansor ko ."
Ya rungume tsam ajikinsa yana kallon mansor dake haki "
”haba yaya mansor mai baby nah ta maka ?textbook din assignment dina ta yaga” ya fad’a Kmr zai yi kuka ata ya kalleta "baby da gaske kin aikata haka ?tayi shiru tana sake lafewa ajikinsa "ai tunda kaji tayi shiru ta aikata ne dan barna a cikin yarinyar nan baa magana babu abinda zata gani bata 'bata ba “inji cewar mb tare da kai hannu zai zuba mata rankwashi aka ata ya tare hannunsa "yana cewa “haba meye haka kuma ?wannnan hannun naka koni ka zubawa shi ai sai na tashi aiki bare ita ,mb yayi murmushi kawai ata ya kalli mansoor yace “kayi hakuri je ka dauko textbook din na gani ya juya da sauri ya shiga daki ."
ATA ya cigaba da shafa bayan sugura "a duk lokacin dana kalli baby sugura sai naga kamar princess dina tana yarinya "ko itace? Mb ya fad'a yana murmushi ata ya had'e rai sannan yace" banason iskanci yau fa naga wasu abubuwa kake min "babu wasu abubuwa idan itace shikenan sai ka cigaba da jira zan baka aurenta ."ATA bai qara cewa komai ba ya cigaba da shafa bayanta dan ya fahimci yau iskanci abokinsa yake ji ."
Bangaren maryam kuwa tana can zaune cikin tsananin tashin hankali gefe guda kuma jifa jifa tana duba agogo awani suka dinga zuwa suna wucewa ahankali ta mike ta shiga bathroom din dake manne acikin dakin tayi alwala ta fito tayi sallah magrib ,haka da ishai tayi ta sake mikewa tayi sallah duk abinda take gabanta banda faduwa babu abinda yake .”
"nan da wasu 'yan shekaru zamu fara ajiye surukai ,ya dai kamata kasan ciwon kanka Ata ka rungume aurenka , ko bazaka yi dan kowa ba kayi dan kanka dan rayuwar nan babu tabbas " karka mutu baka ajiye kowa ba “ muryarsa a matukar sanyaye ya motsa labbansa “wallahi ina matukar son haihuwa amman bada wannan yaron ba ,bana sonta mb “kayi hakuri ata ka daina fad’ar haka dan Allah kayi addua kawai “shikenan zan fad'awa sweetheart tayi min addu tunda addaur iyaye babu shamaki idan alkhairi ce arayuwarta allah yasa min sonta ko kad'an ne a zuciyata amman wallahi mb I don't know why ban ta'ba jin son yarinyar nan ba , kullum na ganta kamar na kasheta haka nake ji , suna tautaunawa mansor ya dawo hannunsa rike da textbook ya mikowa ata."
Ya kar’ba yace “mansor ai yagewar ba wani mai yawa bane kayi hakuri kaji yarona” kaiwa mamanku zata gyara maka yaron ya juya zuwa dakin amira sun jima suna tautaunawa har karfe shabiyu sauran sannan ata ya bar gidan zuwa gidansa dake lekki ." Ita kuwa maryam tana nan zaune har karfe goma sha daya ta wuce babu ango babu labarinsa ga tsananin bacci tana ji amman ta kasa ko kifta idanunta saboda tsananin tsoro jiki a sanyaye ta dauki wayarta ta kira mami "maryam ya akayi ya bakunta? adamcy ya shigowa kuwa ?"a matukar razane maryam ta dago ta kallon dakin ,sai kuma ta maida kanta qasa kamar tana gaban mami yayinda idanunta suka qara canza kala sakamakon qwallar data soma dan taruwa mata."
cikin faduwar gaba mami tace "me ya faru maryam ko bai shigo bane ? "mami bai shigo ba gashi tsoro nake ji mai matukar azabar
Idan bai shigo ba bazan iya bacci acikin gidan ni kadai raina ba " ajiyar zuciya mami ta saki"oh my god adamcy ,Allah yasa kar ya kasheni ,kawai dan anyi maka auren da baka so shine zai zama matsala ka dinga wulakanta mutane haka?maryam Kiyi hakuri nasan dole zaki ji babu dadi ko bama dan tsoro ba ki qara hakuri kamar yadda na fad'a miki bazaki taba bakinciki da auren nan ba ki barni dashi nasan yana sane zan sashi yasan aikinsa dan haka ki manta da adamcy kinji kiyi zamanki babu abinda zai sameki ga masu gadi nan bazasu ta'ba yarda wani ya shigo ba ,kinyi haquri ina tabbatar miki adamcy zai shigo komai dare ."
Cike da girmamawa tace "to! mami na gode sosai allah yasa kifi haka allah kuma ya bar min Ke mami ina sonki "nima haka maryam bye take care."yana zaune a parlour’n gidansa dake lekki phase 1 anjus avenue yana zukar sigari wayarsa ta soma ringing ya kai hannu inda ya ajiye wayoyinsa ya lalubo yana dubawa sunan sweetheart ya gani yana yawo a screen din wayar shiru yayi ya cigaba da kallon wayar yana zukar sigari gbdy yaji gabansa ya shiga faduwa dan bai san me zata fad'a masa ba idan ya dauka dan haka kiran na katsewa ya kashe wayoyinsa gabdaya ya kwanta rigingine yana kallon saman parlour'n yana cigaba da zukar sigari sai daya tashi da kwali daya sannan ahankali bacci yayi awon gaba dashi ."
Bangaren maryam kam karfe uku na dare bata runtsa ba har garin allah ya waye bata ko kifta idanunta ba balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare tausayin kanta ya kamata shi kuwa ata ko tunaninta bai yi ba dan babu digon tausayinta acikin zuciyarsa karfe shida daidai ya tashi ya shige bedroom dinsa ya shiga bathroom yayi wanka yayi alwala yazo ya gabatar da sallah bayan ya idar ya koma saman gado ya kwanta idanunshi na kallon saman d’akinsa cikin kankanin lokaci bacci ya daukesa ."
Karfe takwas daidai a gidan maryam tayiwa mami direba bai gama daidaita parking ba ta fito tana addua" Allah na rokeka ka kawo min sauki acikin rayuwata ka kawo min karshen wannnan damuwar "ta qarasa fada tana dafe goshinta ta tsaya a bakin kofar parlour’n tana kiran sunan maryam "maryam !! mami ta shiga kwalla mata kira da sauri ta miqe a rude ta sauko ta bude mata kofar parlour'n mami ta tura qofar ta shiga,yanayin fuskarta kawai ta kalla ta tabbatar mata ta sha kuka har gaji "ina adamcy yake ?cikin mutuwar jiki ta bud'e baki "ammm uhm baa gida ya kwana ba yanzu Ke kadai kika kwana a gidan nan ?ta gyada mata kai idanunta na kawo ruwan hawaye "ina masu gadi ?"suma tun jiya da misalin karfe goma ban sake jin motsinsu ba.”
mami bata san sanda ta fashe da kuka mai tattare da tausayinta ba ,da sauri cikin rawar murya mrym tace"dan allah mami kiyi haquri ki daina masa kuka sai wani mummunar abu ya samesa maganarta ta katse mata kukanta saboda yadda taga tashiga tashin hankali ta zubawa fuskarta ido, kawar da kanta tayi gefe tana qoqarin boye damuwarta dan hankalin mami ya kwanta kusan minti biyar kafin mami ta soma neman layin ata
Karfe goma daidai ya tashi wanka ya sake yi ya shirya cikin kananan kaya ya kunna wayoyinsa yana gama kunnawa kiran mami ya shigo.”
jiki a sanyaye ya dauka yaji tace "ni kuwa uwar data kawoka duniya ce ?wani irin tsinanne yaro ne kai ? cike da tantamar ba mahaifiyarsa bace ta kira numbersa,amman dan ta tabbatarwa kanshi sai ya cire wayar a kunnensa ya duba yaga tabbas sunanta ne sannan ya kuma karawa a lokacin da muryarta Ke cigaba da fadin"wai ni kam sa'arka ce adamcy ? ‚lallai na sakar maka da yawa kaga gadon barcina,wallahi sai na dauki tsatstsauran mataki a kanka kamar yadda yayana suka bani shawara "jin sunan yayanta kawai data ambata yasa shi dauke wayar daga kunnensa yana kiran sunan Allah “yau shi sweetheart ta kira da kalmar tsinuwa wani irin tsinanen yaro ne kai ?”ya sake maimaitawa kanshi cikin tsananin tashin hankali."
” tabbas akwai wani mummunar bala'i na daban dake son kunno kai cikin rayuwarsa ."
Yana tsaye cikin wannan tashin hankali kiran mami ya sake shigowa jiki a sanyaye ya dauka "kazo ka same yanzu yanzu ina gidan ina jiranka, sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba ,iska kawai iya fesarwa daga bakinsa ya kwashi wayoyinsa ya fito masu tsaronsa na ganin fitowarsa duk suka mike ya shiga mota suka fice a guje tare da jiniya cike da mutuwar jiki ya shigo parlour'n batare daya kalli inda maryam take ba dan gaba daya idanunshi na Kan mami né wacce kallo daya yayi mata yasan tana cikin tsananin damuwa amman km zuciyarsa babu digon nadamar abinda ya aikata bare tausayin maryam sai ma tarin qiyayyarta data ninku acikin zuciyarsa ."
"sweetheart ta kasa ganewa tursasa zuciyarsa da take akan yarinyar Ke sake hura wutar qiyayyarta acikin zuciyarsa ,ahankali ya samu waje ya zauan kusa da mami yana cewa "ina kwana sweetheart!dakata adamcy bana bukatar wata gaisuwarka" shiru yayi kawai yana kallonta yayinda yaji kanshi yana masa wani irin sara ,"ni zaka wa haka ko "? bai ce mata komai ba illa ya kalli inda maryam take zaune ya daka mata tsawa " ke tashi ki bar nan". ta mike da tsaye da sauri jikinta na rawa zata juya mami tace "Ke koma ki zauna " maryam ta girgiza wa mami kai hankalinta a tashe ."
"ni nace ki koma ki zauan babu inda zaki , ai ya raina ne shiyasa tunda ina masa fad'a dole ya huce akanki "no sweetheart ni ba haka nake nufi ba but at least ai.. "na rantse da girman allah idan ka sake kwana a wani gida ba gidan nan inda matarka take ba babu ni babu kai har abada kuma ko mutuwa nayi karkazo Kan gawata zan sheidawa ya'yana kowa ya sani "haba sweetheart Kiyi hakuri mana "nace kayi min laifi ne bare ka bani wani hakurin banza ?
"Ina baki hakuri ne dan kin janye maganrki "to bazan janye ,ba dai ka raina ni ba to wallahi bazaka qara jin dadina ba haka kawai ka dinga gana min azaba kana ganawa yarinyar mutane azaba, laifi ne dan ta rufa maka asiri ta aureka? "wace azaba kuma sweetheart yarinyar da babu abinda ya taba hadani daita ya qarasa maganar yana kallon maryam"ke nace ki bar nan ko ?"ta tsaya tana kallon fuska mami ya sake mata alamar ta bar gun akaro na biyu a matukar fusace ya mike tsaye "Ke kina hauka ne ina mgn kina zaune ? ya buga mata tsawa "
"babu fa inda zata karki sake ki bar wajena matsawar bani nace ba "wai sweetheart me nene haka né ?ya fad'a yana sake kallon maryam dake qoqarin komawa ta zauna yace "wallahi kika cigaba da zama a wajen nan sai na canza miki kamani"maryam ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali tace "mami dan girman allah kiyi hakuri ki barni na bar wajena" ai kafin mami ta sake cewa wani abu tuni maryam ta bace .”mami tayi shiru ta zuba tagumi tana dubansa kawai domin ta rasa me za tayi har kusan mintuna goma sannan yace "sweetheart kinyi shiru kina kallona "me zance tunda kafi karfina ka rainani ka nuna min ban isa da kai ba ,duk lokacin da nace ga abinda zakayi bazakayi ba ,”amman wallahi bazanyi kaffara ba muddin baka cigaba da kwana a cikin gidan nan ba na rantse da girman allah babu ni babu kai har abada kuma zan cireka acikin ya'yana sai dai ka nemi wata uwar amman bani zulai ba ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 6
"Wai meye haka ne sweetheart ?"dan Allah ki daina fad'ar wannan maganar, karki manta nine fa d'anki wannan yarinyar kuma diyar wasu ce " me yasa zaki dinga fad'ar wad'an kalaman akaina?me yasa zaki min wannan hukunci ?ya fad'a cikin tsananin 'bacin rai tunda wannan hukunci kika zartar akaina ai gara ki kasheni kawai ki huta nasan bani da gata da galihu just kill me sweetheart ko kuma ki janye wannan hukuncin naki ." yayi maganar Kmr zai yi kuka ."
"Okay haka ma zaka fad'a ko ?ta daka masa tsawa yana qoqarin sake bude baki mami ta zuba masa lafiyayyen mari tana cewa "kaji magana kawai sannan kayi abinda nace kuma