Showing 51001 words to 54000 words out of 167047 words

Chapter 18 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

biyu aka bashi ta ishesa ya miqa ki ga duk uban dayazo neman aurenki ." aunty  ta sake runtse idanunta tana datasani maganarta data tasan  magangun da zasu gasa mata kenan da babu abinda zai kaita yin magna ."aunty fati ta kalli maryama a wulaqance tace "idan kika kuskura kika kawo matsalar akan auren nan ni da kaina zan kawo wanda zai tura miki ciki kuyi auren dole dashi".


Maryama tayi raurau da idanu "aunty hassana tace "ni kuma  wallahi kinji na rantse muddin kika ki auren muktar  sai dai ku tattara ku bar gidan nan amman aurensa  babu fashi sai anyisa kuma acikin satin nan . "to ni yanzu  idan ma auren ma za'ayi  me muka ajiye da zaayi acikin satin nan ?uwarki zaki yiwa wannan tmbyr bani ba aure ne dai  sai kin auresa kuma ni babu gudumuwar da zan bayar mara kunyar banza zan fad'awa  dangin ubansa  suzo a saka rana aiki banza kawai suna gama fad'ar haka suka juya suka fice daga parlour'n."shiru maryama  tayi cikin tsnanin zullumi da juyayin maganr yayar mahaifinta " wallahi duk aunty ce tajawo masu wannan wulakanci da tozarcin "ta tsani dangin mahaifinta  ta tsanin akidarsu "why aunty me yasa kika cutar damu  haka ?me yasa kika auri mahaifinmu tayi maganr a fili ."



"shiru   aunty tayi ta kasa cewa komai yayinda hawaye suka cika kwarnin idanunta aunty kuka maryama kuka "abinda mahaifiyarsu tafi karfi yau shi yafi karfinta  adalilin biyewa son zuciyarta "
yayar mahaifinta zata  aurar daita ga lalataccen d'anta.",ina ma aunty zata koma zuwa ga dinginta ina ma zatai hakan ko sau  daya né, tasan yan'
uwanta zasu yafe mata su karbeta kuma bazasu ta'ba barin taji kunya ba zasu tsaya mata suyi mata komai hawayen da take kokarin boye né suka samu nasarar zubawa tayi saurin saka hannunta ta goge tana kokarin maida sauran dake kokarin zubowa ."


A tsakar gidan su Aunty fati sukai cikibis da ummah aunty fati tace "yauwa ga aunty nan ma  daman wajenki zan shiga yanzu "ina jinki me  zaki shigo yi? tmbyr ya dan bawa aunty mamaki amman dai ta danne tace "muje daga ciki mu zauna muyi mgnr  ai kamar zaifi ?A'a muyi anan "nan  aunty fati ta zayyane mata komai tana dasa aya umma tace "a'a fati babu mai kamar maryama yayi shaawar bawa muktar aure  "meye illarsa aunty ?tayi mgnr tana zaro mata ido itama ummah cikin zaro ido tace "illoli dayawa, na rasa meke damunku ?ta qarasa mgnr da karfi tare da yarfar da hannu ."


"Aikuwa tunda har muktar yace yana sonta ko sama da kasa zasu hade sai anyi auren sai duk abinda zai faru ya faru "sama da kasa bazasu hade ba haka zalika   babu abinda zai faru aure ne dai bazaa yi shi muddin kika ga anyi wannan auren to maryama ce da kanta taji tana so amman wallahi babu wanda ya isa yayi mata auren dole hayaniyarsu ce ta fito da aunty salma da aunty wani irin asirtaccen murmushi aunty salma tayi tare da karkacewa tana kallonsu .""Bata fada miki akwai wanda suke maganar aure dashi ba ?"ta fad'a amman wannan maganar karya ce babu kowa saboda duk abinda ke faruwa acikin gidan ina sane dashi, dan haka  karya ne babu wanda yake sonta idan kuma har  akwai ya fito mugansa "
tana gama fad'ar haka umma ta juya zuwa bangaren ta, duk suka bi bayanta da kallo".


Bayn kamar minti biyu ummah ta fito hannuta rike dana sadam a d'an rikice aunty salma ta maida kallonta sosai  garesu  "ba kowa bane illa sadam  shine wanda suke soyayya da maryama."aunty ta tsura ma ummah  ido idanunta na kawo ruwan hawaye."aunty salma zaro idanu tayi tana girgiza kanta bata so saka bakinta cikin maganarsu  ba amman ya zama dole tace wani abu dan haka tace "umma yaushe suka fara  so.."bata bari ta qarasa ba tace " bakiyi tsammanin faruwar hakan ba ko ? to haka rayuwa take salma sadam shine wanda zai auri maryama  da izinin allah "ba aunty da Aunty salma da sauran mutanen dake tsaye ba shi kanshi sadam ya shiga rudani da tashin hankalin jin abinda mahaifiyarsa ta fad'a "taya ummansa zata masa haka ?"  yaushe suka yi haka daita  ."?yayi wa kanshi tambayar ajere yana had'a zufa .


"Gsky wannan had'in  yanzu ne  ,wallahi a yanzu aka shiryasa ta kalli sadam "da gaske kuna soyayya da maryama ?kasa amsawa yayi dan gbdy ya gama daburcewa kwakwaluwarsa ta toshe kansa ya cunkusheya rasa me zai fad'a mata yayi dan duk abinda aunty salma ta fad'a haka ne  a yanzu aka shirya komai kai shi sai da suka fito yasan dalilin da yasa mahaifiyarsa ta fito dashi "kun gani ba ai bazai iya cewa komai ba dan wannan had'in shirin yanzu ne sam sam babu maganar a kasa  "Ke salma bana son makirci  da shashanci banza d'anki ko d'ana ?"
"d'anki ne  amman wannan had'in yan.." babu ruwanki  had'in yanzu ko akwai maganar a kasa naki ido ne idan kuma kikace zaki bi dare kibi dubu akan maganar nan zaki mutu ."



"Kai sadam kalleni nan  ya d'ago kwayar idanunshi da kyar ya kalli Aunty fati  "karka boye min komai sadam kasan matsayinka a wajena ina sonka fiyye da ya'yan cikina  nan kuma jikin ummah ya fara yin sanyi ,"nan ji  duk abinda mahaifiyarka ta fad'a amman ina son naji gskyar magana daga  bakinka ,da gaske ne sadam kana son auren maryama"?  ya runtse idanunshi gam yana jin wani sabon tashin hankali  na ta'ba zuciyarsa da kwalkwaluwarsa sai data sake tmbyrsa sannan ya bude idanunshi ya kalli mahaifiyarsa dake tsaye cikin tashin hankali tana dubansa ,a yanayin yadda take kallonsa bazai iya kunyatata a bayyanan nasi ba".



"kai nake sauraro sadam wallahi da gaske zan iya bar maka maryama na nema muktar wata matukar kana sonta " jikin ummah ya sake yin dan tasan akwai soyayya a tsakaninsu ,"kace wani abu "da gaske ne aunty ?ya fad'a cikin wata irin murya mai cike da tsananin tashin hankali "aunty salma ta zaro ido tana cewa "kai wallahi aunty fati karya ne , babu wata soyayya a tsananinsu "kinga salma magana ta qare sadam nawa ne koda karya ne tunda ya amsa da bakinsa bani da ja domin soyayyar sa dabam ce acikin zuciyata "shiru aunty salma tayi dan ta dade dasanin son da take wa mahaifinsa ne ya juye kanshi  .dariyar mugunta aunty salma tayi ta   juya ta koma bangarenta abun bai mata dadi ba dan bata son maryama ta riga ya'yanta aure  amman zata yi iya yinta taga ya'yanta sun rigata aure ita da take da suruki kamar yusuf me zai dameta da wani  sadam gashi  ga dukkanin alamun dole akayi wa sadam din zai aureta."


aunty fati tace" sadam d'ana ina maka fatan alkhairi suna gama fadar haka suka bar wajen zuwa bangaren aunty hassana suna shiga aunty hassana tace "yanzu ke kin yarda da wannan tsarin"?nasan karya ne dole akayi masa amman tunda ta zabi haka ki zuba ido Kiyi kallon abinda zai biyo baya da wannan maganar suka kawo karshen zance suka shiga wata ."maryama na  zaune cikin  halin tashin hankali umma ta shigo parlour'n tana ganin ummah ta mike ta  rungumeta tana kuka "ummah me nayiwa su aunty fati ?"me  zanyi  su soni  ?wallahi banason muktar ki taimakeni ummah kar a d'aura auren nan   laifin me nayi masu ummah ?ina ta  bawa zuciyata hakurin  rayuwa dasu, amman kullum burinsu suga bayana ."ta karashe mgnr tana kuka."


"ki qara  hakuri da kowa da komai  akan wanda kikeyi maryama rayuwarki  qaddara ce zuwa yanzu ya kamata ace kin saba da qaddararki karta dinga baki tsoro "wallahi ummah  jarabawa bata bani tsoro saboda na maida alamarina zuwa ga allah "yauwa abinda nake son ji kenan kowa ce  rayuwata cike take da  lullubali  da qaddara kuma sai allah yana sonka yake jarabaka domin yaga karfin imaninka idan kuma akace haka dole sai ka shirya, jarabawa ko ta class ce yaya kike jinta bare jarabawa daga allah? fatana allah ya bamu ikon cinye jarabawa ."ta fad'a tana shafa bayanta tana jin fad'uwar gaba ."tana Tunanin yadda zata shigo mata da zance sadam  taji sautin muryar maryama tana cewa "ni dai ummah kisa abar maganar muktar ke kad'ai ce nake da yakinin zata min wannan gatan ."


ummah  ta zareta ajikinta ta kamo fuskar maryama da hannuwanta duka tana  kallon fuskarta  tace "babu wani muktar da zaki aura na yanke shawarar zaki auri yayanki sadam, maryama ta zaro idanu  tana duban umma cike da matsanamcin mamaki "yaya sadam kuma  ummah ?"a matukar rikice  ummah tace "Eh ko baki sonshi."ahankali ta shiga girgiza mata kai domin dai tasan  ko giya ta sha bazata iya furta hakan gareta ba ,bare kuma tasan
tayi hakan ne dan yantota daga hannunsu aunty fati ."ai ko bata son yaya sadam ta karba kuma ta amince sai dai fargaban yadda yaya sadam din zai karbeta muryarta a raunane tace "ummah kina tunanin yaya sadam din zai  amince   ?


"ya ma amince  maryama "kuka ta fashe dashi  mai karfi "shikenan mafarkinta ya tabbata"ya allah kabani kwarin gwiwar cinye jarabawar da duk zaka min "alhamdulillah alhamdulillah shine kawai abinda umma taji yana fitowa daga bakinta "allah ne abun godiya maryama babu abinda zai biyo bayan wannan auren sai alkhari, karshen wahalarki yazo ta fad'a tana sake  rungumeta ajikinta " aunty ta qaraso ta zauna kasa kusa da kafafuwan ummah "ban san da wace irin kalmar godiya zanyi amfani dashi wajen gode miki ba amman zan zabi wannan kalmar allah yay miki sakamakon da gidan aljana "na gode na gode !!sai kuka ya kufce mata daga maryama har Aunty  suka saka ummah tsakiya suna mata kuka ."


koda habib ya dawo yaji hukuncin ummah abun yayi masa dadi sosai  dan gara sadam sau million akan wani muktar fatan alkhairi yayi yana tmbyr aunty maryama .""Tana d'aki  !" ta fad'a atakaice tana sauke numfashi a daki ya iske maryama kwance  akan katifa tayi kuka har idanunta sun kunbura tana tunanin  yadda qaddarori suka yita zuwa mata daki daki akan aurenta a she tana tare da mijinta bata sani ba "ya zauna kusa daita  yana kiran sunanta "heartbeat ".ta sauke numfashi tana dubansa da kunburarrun idanunta "bakiji dadin hukuncinsu umma ba ko ?ta langwabar da kanta kawai  batare da tace komai ba "heartbeat idan da wani aka baki zance Aa amman yaya sadam dabam ne karki ce aa bazaki samu kamarsa ba "


"kai ma ka amince dashi  ?sosai kuwa dan mutumin kirki ne kuma yana duk wasu quality's da zaa so shi ta sakar masa murmushi  wanda ya bayyana wushiriyarta sama da kasa tana gyara kwanciyarta
ta jingina bayanta da abun gado ta janyo pillow ta rungume tana jin wani nauyi a qirjinta"bana jin son yaya sadam  ko kad'an acikin raina amman bani option zan rayu dashi muddin rai "yayi shiru kawai yana kallonta cike da tausayawa dan bai san me zai sake cewa ba ,domin farincikinta farincikinsa ne haka zalika damuwarta damuwarsa ne zai sake magana ta katsesa ta hanyar cewa "karka ce komai after dad tunda har ka amince  daman kai kawai nake jira naji raayinka tana gama fadar haka ta sauko "muje parlour'n muci abinci ta riko hannunsa binta kawai yake jikinsa a sanyaye ."


*******

Tun bayan da ummah ta furta   maganar aureta da yaya sadam habib  bai zauna ba ya shiga buga bugan neman aiki karfi daga wannan kamfani zuwa wannan duk kuma saboda ita da mahaifiyarsu ne daman da karatu da kwallon kafa ya dogara dan yana d'an  samu a buga kwallon kafa amman ba wani samu sosai ba dan kudin ba wani kudin azo agani bane amman babu laifi yana toshe  masu wata kafar dan  hatta mashin din da yake dashi yanzu  da dan kudin da yake samu ya siya ."matslar dai   ba koda yaushe ake samu  ba sai a dauki alokaci baa daukesa ba shiyasa yaga gara ya had'a da aikin kamfani ranar da'akayi dashi za'a d'aukesa  a ranar ya samu damar  buga kwallon kafa  zuwa ogun state kenan  ya samu promotion daga  jahar lagos zuwa wata jahar  ."


Adaidai wannan lokacin maryama ta kammala bautar kasa tare da kawarta subai'a babu inda take zuwa tana zaune a gida abinda tafi tsana kenan zaman gida sam a yanzu bata son zaman gidansu  gashi dai tana samun kulawa gata sangarta só qauna soyayya tarairaya daga  mahaifiyarta  haka ma habib sai ummah wacce sanadiyyar sadam yasa yanzu motsin kad'an tana bibiyar me take ciki komai ta samu ita zata  bawa amman zaman gidan baya mata dadi saboda zuciyarta ta rasa abu d'aya wato mai d'ebewa zuciyarta kewa dan gabad'aya tunda akayi maganar aurensu da yaya sadam ta rasa gane kanta dashi karon kashi sadam din sai ma taga ya rage bata kulawar daya saba bata ada can baya ."

****
A hankali ATA ya shiga office dinsa babban ma'akacinsa  mai tantance ma'aikata na  kamfaninsa Z&A na biye dashi  abaya ,ya zauna a mazauninsa yana kallonsa  batare da yace komai ba "good morning sir ? ya gaishesa cike da girmamawa "uhm ! yayi gyara murya kawai alamun yana jinsa  yana maida hankalinsa Kan system "uhm amm  sir ko zan iya magana yanzu "uhm ! ya fad'a a takaice "adadin mutane kimanin dubu dari uku ne suke bukatar aiki a karkahainmu ,sir wannan shekara ko zaa hada da  masu degree ? Ko kuma daga master zuwa sama ne zaa dauka ."?" ka ma da kake maganar daga wani mataki ka  fara aiki ?"sorry sir ya fad'a a tsorace "duk mutumin da aka tabbatar takurdunsa sunyi kyau ayi  masa interview idan ya cancata a d'aukesa ."
"sai  abu na gaba kada a Kuskure akarba'  kwabo duk wani mutun domin samar masa aiki a duba cancanta yana gama magana ya dauke idanunshi akan system zuwa wani bangare dabam  yana cewa fatan" ka fahimta "yes sir sai kuma game da compaing dake kasar  togo sun kira suna bukatar almustapha "me zance masu?" kai komai bazakayi da tunanin kanka ba sai ka tmby ? "am sorry sir"ya juya da sauri ya bar office din ."


Ranar  monday   tun asuba da maryama ta tashi tayi sallah bata koma ta kwanta ba ta soma shirin zuwa wajen interview duk abinda tasan zaa buqata ta had'asu waje d'aya  acikin jakarta hatta kayan da zata saka ta fito dashi sannan ta shiga wanka karfe bakwa  daidai ta gama shirinta ta fito parlour'n ta hango aunty tsaye a kitchen ta qarasa ta rungumeta ta baya "good morning mumy "ta kai hannunta ta shafa gefen fuskarta morning my princess har kin fito ?yes !ta fad'a tana duba agogon dake daure da tsintsiyar hannunta "muje ki karya kafin ki fita "aunty da kin bar breakfast din nan Kiyi min addua kawai" bakince akwai wanda zai tsaya maku  ba ?aunty ta fad'a tana fitowa daga kitchen maryama ta biyo bayanta tana cewa "akwai but bashi zai mana interview ba amman dai ina ji ajikina zamu samu nida subai'a "to Allah yasa a dace "Ameen !ta fad'a a lokacin da wayarta ta d'auki qara ta ciro ta duba tana cewa "aunty subai'a ce ."


Tayi sauri ta d'auka tana "cewa hello suby okay gani nan fitowa mgnr second biyu sukai  ta katse kiran tana cewa "aunty ni zan wuce subai'a har ta fito "kema yanzu zaki wuce ta kai cup din tea bakinta ta kurbi kad'an ta kai bread bakinta a haka ta shanye cup din tea tace "na gode sosai Allah bar min Ke mamana ina sonki ta kai mata kiss a kumatunta ta nufi kofar fita da sauri tana cewa aunty "bye ye sai na dawo "bye ta d'aga mata hannu tana kallon bayanta kai tsaye bangaren ummah ta shiga da sallamarta yaya sadam ta gani zaune  Jiki a sanyaye ta gaishesa "yaya sadam ina kwana?"ya dago idanunshi ya kalleta sannan ya amsa da" lafiya !"

ta nufi hanyar dakin ummah  sai ga umma ta fito"maryama har kin fito ?na fito umma to Allah yasa a dace  tace Ameen " ina zata ?ya tambaya batare daya kallesu ba "interview ! ummah ta bashi amsa da haka "aiki zatayi kenan ?" to meye amfanin karatunta idan batayi aiki ba ya dan yi shiru can yace "nifa gsky bana da wannan raayin yana gama fad'ar haka ya mike yana cewa " ni na wuce tsaya ka sauke  min ita "bai ce komai ba ya fita maryama tabishi da kallon mamaki dan bata ta'ba tunanin zata samu matsala dashi akan aiki ba ganin shima dan boko ne ita kam akan aikinta zata iya hakura da auren dan
sam aure baya ranta a yanzu mutuntakan umma ne ta duba  da tausayin mahaifiyarta bawai son aure take ba ,ganin yadda yanayinta  ya canza  yasa ummah tace "karki wani damu zakiyi aikinki "amman  ummah alamunsa ya nuna baya so "gsky ne sadam bai  son  amman zai yarda kinji  wahalar karatunki bazai tafi a banza ba ,yana ma daga cikin abinda yasa ban bari an daura maku aure ba nafi son  ki  shiga da aikinki". kanta kawai ta gyada mata "maza bishi ya saukeki ."


Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 11


Jiki a sanyaye maryama take taku gabad’aya kuzarin jikinta yayi kasa ,”aiki zatayi kenan nifa bana ra’ayi ? maganarsa ta shiga yawo acikin kwakwaluwa da zuciyarta , tana tafiya tana tunanin maganarsa , a qalla yaya sadam ya kusan minti shabiyar zaune acikin motarsa yana jiranta , ya dubi agogo a karo kusan na shabiyar yaja qaramin tsaki a lokacin da wayarsa ta soma ringing ya kai hannu ya d’auka ya duba yaga sunan ummanshi ke yawo akan screen din wayar. numfashi ya sauke sannan ya d’auka cike da girmamawa “sadam !”ta kira sunansa ya amsa da “na’am “ina son kaso maryama tun daga qasan zuciyarka ,sannan zaka iya zama madadi ko ka cike gurbin abubuwan da maryama ta rasa a rayuwarta na shekaru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login