Showing 60001 words to 63000 words out of 167047 words

Chapter 21 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

idanunshi akanta wanda yayi sanadiyyar da suka fad'a kogin tunani hankalinsu ya bar duniyar da suke ciki ya lula dasu can wata duniyar . "friend kayi hakuri ka kwantar da hankalinka hisham bazai ta'ba cutar da auta ba ,sannan hukuncin da d'auka akanshi daidai ne ko yanzu ka taka rawa aciki rayuwar aurensu wannan zai zama kashedi ne mai karfi kayiwa hisham".


"shi kansa bai san yana son matarsa ba sai yau haka zalika itama auta tana son mijinta ka duba ka gani yanayin da suke ciki na damuwa a yanzu "ATA ya sauke hannunsa dake rike da kungunsa ya juyo yana kallon mb a kallon da yake masa ya fahimci ransa ya kai kololuwar tashi da maganar da yayi masa ahankali ya kalli inda hisham yake tsaye yana mikowa nana hauwa'u hannu ranshi ya qara 'baci cikin tsananin fushi yace "wallahi wallahi idan kika kuskura kika isa garesa sai na balballa ki "Jin sautinn muryarsa yasa nana hauwa'u tai saurin dawowa haiyacinta tana mai sunkuyar da kanta kasa ."



A rud'e maryam tace "me yasa yaya adam "! ta matso gabansa ta tsaya tana dubansa hawaye na sauka daga idanunta "me yasa zaka kashe mata aure alhalin tana son mijinta ?ya kamata kayi masa uzuri saboda kai kanka kasan yaya hisham mutumin kirki ne wallahi bazai ta'ba cutar da sister ba duk duniya a halin yanzu sister bata da kamarsa idan ka tsaya domin kwatar mata 'yancinta nifa ?"nida kake min fiyye da abinda yake mata fa"? sai da gaban kowa dake wajen ya bada wani sauti bugu mai karfi
Wani mugun kallo yayi mata da tsumammun idanunshi yana nuna da yatsan hannunsa "wacece ke da ina magana zaki saka min baki ?ya fad'a tare da d'auketa da wani gigitaccen mari yana sake nuna ta how dare you ?".


" duk nan babu wanda ya isa bare ke din banza da ko kwatan matsayi kowa anan baki kai ba ." abinda nake miki ina yi ne dan bana sonki ,suma kuma da kika ga zan rabasu dan nasan basa son juna sukai aure, bana goyon bayan auren da ba'a so, dan bana son a aura min matar da bana só kamar yadda adabaibayeni dake "yayi maganar da karfi jikin maryam yana rawa ta fad'a jikin aunty shahida tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya ."gabad'aya parlour'n yayi shiru tamkar babu wasu halittu acikinsa, babu wanda bai tausayawa maryam ba illa aunty abida wacce taji dadi aranta kuma hankalinta ya kwanta ta qara tabbatarwa kanta sultana ce macen da zatai wining din heart dinsa dan haka ta washe baki cikin jin dadi tace tana ".



"kema maryam da karanbani kike keda kika san matar cushe bata daraja ,me ya kaiki saka masa baki a maganarsa ?."you're very stupid kema nace ki saka min baki a maganata ne ?"ko ina ruwanki ? kai tsayuwar me ma kikewa mutane anan ?da mijinki nake da issue ba dake ba oya leave "ya nuna mata kofar fita cikin kuka tace "ah ah ni ai yar'uwarka ce dole ina da ikon da zanyi magana kuma ma ai anan ka sameni ba daga sama na shigo ba ,magana kuma dole nayi wallahi wannan kam ba irin matarka bace sam baku dace ba ka jira matarka na nan zuwa amman kam sam ba mata bace " abida i saiid out of this hall kuma ko da wasa karki sake shiga hurumina idan ba haka ba zan baki mamaki .yaya ibrahim ya kama hannun matarsa yayi hanyar waje daita amman aunty abida ta turje tana cewa "ka sakar min hannu babu inda zani da kyar ya samu ya fitar daita ya dawo ."



"Me ye laifinta adamcy ai gsky maryam ta fad'a maka "wato laifi tudu ka take naka ka hango na wani ya kalli Aunty shahida da kyau yace "ina mata abinda nake mata ne saboda bana sonta kuma da ina da dama zan iya rabuwa daita har abada ,haka zalika shine dalilin da yasa zan kashe auren auta domin zukatan kowa ya huta, yaje ya auri wacce yake so itama ta samu wanda take so yake sonta ya qarasa mgnr gumi na karyo masa sannan ya kalli nana hauwa'u "Ke maza ki koma d'aki "da mugun sauri ta juya tayi hanyar d'akin tana jin wani irin fad'uwar gaba mai tsanani hisham ya kallesa kawai batare da yayi magana ba duk da maganar yake son yi amman idan yace zai yi komai zai qara rikicewa ne shurunsa ne yafi zama alkhairi ."



A rikice mami ta fito alamun tashin hankali aunty khadija na biye daita ."ta tsaida nana hauwa'u aunty khadija ce taje ta fad'a mata abinda yayiwa maryam tana gama qarasowa ta dakawa ata tsawa tace "me maryam tayi maka ka mareta "?yayi shiru yana sake tamke fuska sosai "adamcy kaji tsoron allah, kaji tsoron ranar da hakin maryam zai kamaka idan baka sota ba'ace ka qaunaceta ba amman me yasa zaka dinga tozarta min ita agaban mutane wallahi duk namiji mai wulakanta matarsa agaban mutane yayi asarar rayuwa dan haka ka bata hakuri yanzu yanzu ."

"What !?

ya furta a razane zai sake bud'e bakinsa yaji mami ta d'aukesa da mari "you're very stupid too hakurin ne bazaka bata ba "sweetheart marina kikayi akan wannna yarinyar ?na mareka kai ma baka duba darajata ba bare hisham ya duba darajata har ya ragawa diyar cikina "hisham ya sunkuyar da kanshi kasa yana mai tsananin jin kunyarta "yanzu sweetheart akan na mari wannan duwaf din yasa kika mareni?"eh akanta na mareka idan ka sake ce mata duwaf zan maka double dinsa idan bakaji kunyata ba bazan ji kunyarka ba bare na raga maka maryam ta rike hannu mami dan ta fahimci qara masa wani marin zatayi "dan allah mami ki rufa min asiri kiyi hakuri karki masa komai ."


a fusace yake kallon maryam fuskarsa a tsuke itama din shi take kallo nan da nan jikinta ya dauki rawa ."ido cikin ido suke kallon juna a karo na farko kenan a rayuwarsu duk da suna kallon juna amman ba kamar haka ba kallon nadama take masa yayinda shi kuma yake mata kallon zaki gane kurenki da sauri ta janye kwayar idanunta saboda wani irin mugun kallon da taga yanayi mata yana fesar da iska mai zafi daga bakinsa."hisham !"mami ta kira sunansa ya d'ago a natse yana dubanta cike da girmamawa "ban hanaka qara auren duk wacce kake so ba amman bazan d'auki tozarci da wulakanci ba karka wulakanta min yarinya idan kasan wulakanta min yarinya zakayi na had'aka da allah ka sauwake mata kamar yadda d'anuwanta ya bukata ".



"kiyi hakuri Mami "ba maganar hakuri bane hisham bazan yarda yarinyata tayi zaman rashin yanci a gidan aurenta ba" hisham ya sauke boyayyen ajiyar zuciya domin gani yayi kamar son kai garesu menene ata baya yiwa maryam? irin cin kashin da yake mata shi ko kwatansa ba yayiwa nana hauwa'u amman shine dan son kai irin nasu zasuji haushi har su buqaci raba auresu "idan kasan baka bukatarta arayuwarka kaje ka aiko min da takardarta "muryarsa a sanyaye sannan cike da girmamawa yace "mami Kiyi hakuri ina son aurena ! "to kayi magana da yayanta tana gama fad'ar haka ta juya ta zata koma d'akinta." taji qara fashewar glas tass !



Ta tsaya cak tare da juyowa ata ta gani tsaye jini na bin hannunsa ,ya rasa meke masa dadi bakinciki goma da ashirin ga marin da mami tayi masa ga damar da ta bawa hisham yasa zuciya ta dibesa ya bugi show glass din dake gefensa shine nan take jini ya soma bin hannunsa aiko maryam ta rikice "na shiga uku mami yajiwa kanshi ciwo ita kanta mami cikin tashin hankali da kidema take kallonsa ranta ya baci matuka da abinda yayiwa kanshi amman ta danne zuciyarta daga taimaka masa ta maida idanunta ga maryam dake kyarma cikin alamun rashin damuwa tace "meye damuwarki dashi ?cikin yin qasa da murya maryam ta kalleta "jini ne fa mami ."ina ruwanki oya wuce muje d'aki taja hannunta suna tafiya maryam na kallon bayanta ."



Shi kuwa ATA zuciyarsa banda tuttukin bakinciki babu abinda take Mb ,yaya ibrahim yan'uwasa har ma da hisham hakuri suke bashi ganin yadda jinin ke tsiyayya a sakamakon jininsa dake gudu fiyye da kaida amman ko motsi bai yi ba ,da kyar suka kamoshi suka zaunar dashi akan kujerar dinnig d'aya byn d'aya mutanen dake tsaye suka fita a parlour'n ya saura iyasu kawai nana hauwa'u ta yage bakin mayafinta ta durkusa gabansa idanunta cike da kwalla bai d'ago ya kalleta ba ,tana qoqarin kamo hannunsa cikin zarewar ido da maseefa ya janye hannunsa ." cikin tsarkewar murya tace "please yaya karka ce a'a wallahi zan iya had'iyar zuciya na mutu idan wani abu ya sameka bazamu iya jurar rashinka ba muna sonka fiyye da tunaninka ,bazamu so mu rasa d'an'uwa kamarka ba ."


runtse idanu shi yayi kawai jikinta na rawa ta sake riko hannunsa dake tsiyayar jini wannan karon bai dakatar daita ba ta daure tana cewa "bari a kira doctor" still bai ce uhm bare uhm ba sai dai wata irin zufa ke tsatsafo masa akan goshinsa da ilahirin jikinsa ya kamo lip's dinsa na qasa yana cizawa da karfi ya bud'e tsumammun idanunshi da suka gama canza kala tsabar zuciya ,hanunsa dake daure ya tsurawa ido suka dan ja baya kad'an dan ya samu dasataccen iska ." yana zaune yana cikin tsananin damuwa maryam ta fito da sanyi jiki ta kallesa zaune shiru har tsawon minti uku kafin  ahankali ta dinga takowa har ta qaraso garesa ta tsaya taga alamun an daure masa hannu ."


ajiyar zuciya ta sauke kana ta daura tafin hannunta akan goshinsa tare da goge masa zufar dake tsatsafo masa duk da sanyin ac dake ratsa parlour'n idanunshi ya sake runtse wa yana jin qarin ciwo akan wanda yake ji cikin kulawa tace "sannu yaya bai amsa ba sai ji da yayi kamar ya tashi ya rufeta da matseyacin duka, ganin bai ce komai ba ta juya  da sauri ta nufi dining area ta zuba ruwa a glass cup ta nufo inda yake zaune yana huci tamkar zaki da sauri aunty shahida ta rikota tana girgiza mata kai alamun ta barshi hakan sai dai itama kanta ta girgiza mata tana kokarin fixgewa daga rikon datai mata ta qaraso inda yake jikinta na kyarma ta mika masa cup din ruwa cikin tsanani tashin hankali ta furta" ruwa ..! "


ya dago fuskarsa a hade cike da fushi da zafin zuciya ya amshi glass cup din hannunta ya buga akan tayis yana huci tare da cewa "Congratulations maryam kinyi nasarar kinyi nasarar !! sace min zuciyar mahaifiyata ba? Cike da tsoro ta qame a gabansa hawaye na turereniyar zuba daga idanunta tana girgiza masa kai ya mike tsaye yana nuna ta "wannan kad'ai Ya sake ninka wutar kiyayyarki acikin zuciyata , bana sonki kuma bazan ta'ba sonki a matsayin mata acikin gidan nan ,bazaki ta'ba zama suruka acikin gidan ba dan ban amince dake a matsayin matata ba "yana gama fadar haka ya ciro waya daga cikin aljihun wandonsa ya soma kira wata number yana tafiya yana waya "kuna da daki a girls house dinku okay ka duba min ina bukatar d'aki ganin nan zuwa ".



Yana tafiya suna biye dashi babu irin kiran da Aunty shahida batayi masa da yaya Ibrhim mb har da hisham ba amman ina ATA bai waigo ba ya ma dade da yin nisa dan tuni ya shiga motarsa atare gbdynsu suka sauke ajiyar zuciya suna sauke numfashi su aunty shahida suka riko hannun maryam suka shigo parlour'n suka bar su yaya ibrahim tsaye a waje suna tautaunawa ."suka zaunar da maryam wacce ta gama rikicewa tare da zuba masa ido "dan girman allah waye ya fadawa mami ya mareni ?sukai shiru "wallahi ko waye bai kyauta min ba saboda kunga abinda aka jawo min, kunga bala'i da aka had'a min allah ne kadai zai kwace a hannunsa ta qarashe mgnr tana zubar da hawaye."


"kiyi hakuri maryam na d'auka hakan da mami tayi zai kawo miki mafuta né arayuwarki " maryam ta matso ruwan hawaye tace "dan allah karku bari mami tasan ya tafi guest house dan damuwar zata sake mata yawa mu bar shi a tsakanin mu ta qarasa mgnr tana sheshekar kuka dan tasan yau allah ne kawai zai kiyayesa daga koma wa shan giya sigari kam ma baa magana tasan dole sai ya sha aiyar zuciya suka sauke gabad'ayasu babu wanda zai fad'a basu sani ba bayan shigar mami ta dawo parlour'n kuma taji duk abinda ya faru sam batayi nadamar abinda abinda ta aika masa ba duk da tasan a yanzu  adamcy yayi girma da ya kama ta ace ya wuce ta kai hannunta jikinsa amman bazata iya d'aga masa kafa akan maryam ba "su aunty shahida suka qasa komawa gidajensu kuma basa jin zasu koma din har sai sun san halin da danuwansu yake ciki suna zaune jugun jugun ."



bayan awa d'aya suka soma neman layinsa sai dai babu abinda computer Ke fad'a masu sai swichoff .maryam ta zamo daga Kan kujerar kushin din da take zaune zuwa kasa ta dafe kanta tana ganin itace silar faruwar komai da bata tsoma bakinta ba da duk hakan bata faru ba "me yasa na saka bakina ta furta a fili tana fashewa da wani sabon kuka cike da kulawa aunty khadija tace "lahaula wala kuwata illa billa babu tsumi babu dabara maryam dole hakan zata faru "ahankali ta kalleta da idanunta da suka yi jazir alamun tarin tashin hankalin tace "bazaku tafi gida ba ?"bazamu iya tafiya ba dole mami tana bukatar mu "."zaku iya wucewa suka tsinkayi muryar mami cikin rashin nuna damuwarta ."


ahankali ta cigaba da motsa lip's dinta "kuci abinci ku wuce gbdy na sallameku suka girgiza mata kai "ni ba uwar banza bace yadda bazan dauki haka daga matar dana ba haka bazan barku ku kwana batare da kun sanarwa mazajenku ba da kwarin gwaiwar mami suka wuce gida ya saura daga maryam sai nana hauwa'u da mami .mami tasa aka kawo masu abinci ita kuma ta maida hankalinta ga tv kamar abun bai dameta ba , kasa ci sukayi ta waigo ta kallesu a natse "ku ci abinci mana!" suka girgiza mata kai alamun basa ci' ko akawo maku abinci mara nauyi ?da kyar nana hauwa'u ta fixgo magana "ni dai bazan iya ci komai ba amman ban san ko sister ba mami kam tasan maryam bazata ci ba dan haka ta mike ahankali tana cewa "sai da safenku "yanzu mami bacci zakiyi ?to me zanyi maryam ?Zan kashe kaina akan adamcy ne ."kuma kuje ku kwanta ku hutar da ranku dan shi bai ma san kun damu da halin da yake ci ba ta juya ta fara tafiya ."



daren ranar daga maryam har nana hauwa'u babu wanda runtsa damuwar nana hauwa'u ta hade mata biyu na halin da danuwanta yake ciki da kuma kewar mijinta dan tasan da yanzu suna can makale da junansu duk yadda yake nuna mata bai sonta amman basu ta'ba raba wajen bacci ba kuma kwana yake yana wasa da jikinta ganin baccin yaki zuwan mata sai juyi take ta juya gefenta inda maryam take kwance yadda ta barta haka take ta mike ta shiga bayi ta dauro alwala ta soma gabatar da sallam ganin haka yasa maryam ma ta yunkura da kyar ta tashi itama taje ta fara jera nafilfili ."



washegari tun karfe takwas yayan mami suka wa gidan diran makiya dan kwana suka yi kiran layukansa amman baya shiga ita dai mami bata ce masu komai ba ta cigaba da tsabgar gabata ."kwana biyu ATA bai dawo gidan ba kuma gbdy sun sa an bincika gidajensa bai je can ba hatta office bai zuwa gashi babu wanda yasan girls house din da yaje gbdy yanuwana sun shiga damuwa maryam kam kallo daya zaka mata ka fahimci yadda ta fita haiyacinta Har mamakinta suka dinga yi gabad'ayasu sun gane tana mutuwar sondanuwansu "zabiba ta matso kusa daita "ki rage son nan maryam zai miki illa ta kalleta kawai tana sauke numfashi "ki yawaita addua sai komai yazo miki da sauki babu wanda bai kira layinsa ba amman yaki daga wayar har da wasu layuka da dabam sun kirasa da zarar yaji muryarsu zai katse kira tun suna boyewa har dai sai da mutanen gidan  fahimtar sun nemesa an rasa ne  dan duk sunfita haiyacinsu ."


Ganin da mami tayi ya'yanta sun fita haiyacinsu yasa ta dauki wayarta ta soma neman layinsa kira daya tai masa ya dauka alokacin ana bude masa bayan mota zai shiga "barka da... "bana bukatar gaisuwarka
"Kana ina? ta katseshi da fad'arhaka ?ina wani wuri !"tô ka dawo gida yanzu yanzu muddin baka son ka hadu da mummunar tashin hankali arayuwarka ".tana gama fadar hk ta katse kiran dole ya bada umarni a dauki hanyar zuwa gida dashi yana shigowa gbdy yan'uwansa sukayo kansa banda mrym dake rakube cikin farinciki dawowarsa "big sister aunty shahida ta zauna kusa dashi tana shafa gefen fuskasa tana kamo hannunsa me ciwo "hope kana Lfy ?yayi mata banza hannun suka tsurawa ido nad'e da bandages "dan allah adamcy ka dinga hakuri wannan maganar bai kai ace ka bar gida ka tare a guest house ba,  "dan rani wayo kawai wallahi wannan ba mutuncinka bane tô ita mrym meye nata laifin "?



"Oh My god ! taya yarinya na had'ani da mahaifiyata zakice meye laifinta wallahi tana damun rayuwata sweetheart kuma na damuna akanta, kuma kullum mgn d'aya ya zanyi ne? dame zanji ne? bana sonta amman kun matsa sai dana aureta dole , kuna son na mutu ne ?duk yayi masu tmbyr a matukar rud'e gbdy suka girgiza masa kai alamun a'a ita kam mrym hawaye ne ke zuba a idanunta tana jin ciwon yadda yake iya furta kalmar bai sonta a gaban kowa "ka dubi allah ka duba lamarin maryam " what ! ni kun duba lamarina da zan duba nata ?ihu nake kamar mahaukaci amman bani da mai fahimtata acikinku bare ku taimaka min ."



"Samu natsuwa adamcy ,yanzu me kake so?" mafarkina nake so !"muddin ana son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login