Showing 15001 words to 18000 words out of 167047 words
Chapter 6 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
tsamanin zata amince ba tunda itama bata sonka ai dole ta amince zuciyarsa ta fda masa haka tsaki yaja domin sai ya sake tsintar kanshi da jin haushi "muje ka kwanta ka huta dare nayi bai ce uffan ba ya mike ya nufi kofar d'akinsu itama tabi bayansa ."
Kai tsaye suna shiga d'akin ya fara zare rigar jikinsa bathroom ya shiga ita kuma ta kakkabe inda zata kwanta ta kwanta tana kokuwa da numfashinta duk da bata son yaya hisham amman bazata so wa kanta kishiya acikin kwanakin da ko goma batayi a gidan miji ba ,hassalima bata tare agidanta ba zuciyarta banda rawa da bugawa babu abinda take wasu siraren hawaye suka gangaro mata ta fara sheshekan kuka tana jin motsin fitowarsa tayi saurin danne kukanta tana share hawayenta ."
Numfashi ta dinga saukewa sama sama ya dawo gabanta ya tsaya daga shi sai 3 qauter dake jikinsa duk wani zati dake jikinsa mai daukar hankali ajikinsa ya bayyana wani tsoro ne qarara ya bayyana akan fuskarta dama zuciyarta gbdy wanda yasata saurin runtse idanunta gam ji tayi ya kwanta jikinta har tana jin saukar numfashinsa ya kai hannuwansa ya d'an matsar daita "ki koma wajen baccinki sannan kukan me Kike yi wa mutane ?"
"Ba kuka nake yi ba " ta fad'a muryarta na rawa "uhm shi wannna kuma ya sunansa?ya fad'a yana kwanciya "qoqari tayita ta danne kuka ya fuskanceta sosai "alokacin da numfashinta Ke sama da kasa ya kai hannu daidai qirjinta inda ya suka sauka akan dukiyar fulaninta wani abu yaji alokaci daya yadda numfashinta Ke sauka da kuma tsarga wa wani abu da yaji mai kama da shoucking "
"Kina jina zuciyarki tayi nauyi sosai da alamun akwai abinda Ke damunta "ta lumshe idanunta tana sauke numfashi kuma har lokacin bai dauke hannusa ba "na rashin son hisham ne ?ta girgiza masa kai alamun a'a "to na meye to?bana komai bane "okay yanzu ki bude baki kiyi kuka mai sauti domin ki rage nauyin da zuciyarki tayi aiko kamar jira take ta bude zatayi kuka dan har sautin muryarta ya soma fitowa taga ya zaro ido tare da bude bakinsa ba zato ba tsanani yaji saukar laulausan lip's dinta akan na nashi .."
"Tsura mata ido yayi batare daya sake cewa komai ba illa kwayar idanunshi daya zuba mata yana jin wani irin sauyi ajikinsa tmkr wanda ake jona masa wutar lantarki cikin lokaci kankani komai ya birkice masa bai san yadda akayi ba ya had'eta da jikinsa still bakinsu na manne cikin juna , sai fidda numfashi nana hauwa'u take cikin jin wata irin kunya sam bada wata manufa tayi hakan ba gudun abinda zai fad'a ne dan yanayin yadda ya zaro ido babu sauki zai iya yin komai ."
Da ba dan period din da nana hauwa'u take ba da babu abinda zai hana hisham saninta ya mace a daidai wannan lokacin wannan shine abinda ya hana komai faruwa amman murza kam ta sha gbdy ya manta wata kiyayya jin dadinsa kawai yake da jikinta ita kuwa babu abinda Ke fitowa daga cikin kwayar idanunta sai ruwan hawaye tare da mugun tsoronsa tana son hanashi abinda yake tare da sheida masa bafa ita bace zabinsa amman tsoronsa ya hanata ."
"Yau ne kawai shima nice na jawo ta fadawa zuciyarta hakan, in sha allahu hakan bazai sake kasancewa ba ,ita dai bata jin wanzuwar tsanarsa ko kiyayyarsa acikin zuciyarta idan ya shirya yin rayuwar aure daita zata bashi dukkanin farinciki idan kuma zai cigaba da nuna tsanarta ne zata janye jikinta sosai hisham yazo hannu gashi babu damar aiwatar da komai lumshe idanunshi yayi tare da komawa gefe ya kwanta yana mayar da numfashi bai san meke damunsa adaidai lokacin ba domin kuwa idan yace yasani yayi karya ."
Bayan ta juya masa tana rufe rabin jikinta ya dan waiga ya kalli bayanta wanda hakan yasa shi jin wani irin ajikinsa gabansa ya dinga tashi tsurawa bayanta ido yayi shape dinta mai matukar kyau da d'aukar hankali,duk da yasan jikinsa na da taushi amman sai yaji nata kamar yafi nashi soft kai everything ko dan bambamci halitta ne jikin ,nuzla ya tuno wanda yasa tunaninsa ya koma kanta itama fa masha allah tana da sura mai kyau da taushi uwa uba kuruciya dan nana hauwa ta girmeta da kusan shekaru hudu zuwa biyar ya dauki kusan mintuna talatin a haka bai motsa daga inda yake ba yana kuma jiyo saukar numfashinta ,numfashi ya sauke ya canza hasken d'akin zuwa mara nauyi sannan ya zame ya kwanta ya d'an janyo gefen bargon data rufa dashi ya rufe jikinsa ."
Washegari hisham ya bude ido bai ga nana hauwa'u ba ya kunna wutan dakin tare da kai idanunshi ya sauke akan agogon dake ajiye akan table it was 9:44tsaki yaja tsaki sannan ya mike ya shiga bathroom ,bathtube ya shiga yayi wanka ya fito black boxcer da black singlet ya saka sannan ya daura kaya akai ya fito fuskarsa a hade ya gaishe da abbansa dake zaune rike da jarida sannan ya shiga dakin mumy domin ya gaisheta ko kallonsa batayi ba bare ta amsa sallamarsa, ahankali ya qaraso har inda take zaune juyar da kanta gefe tayi alamun bata son ganinsa "momy Kiyi hakuri nana hauwa'u ma da kike fushi akanta bata damu ba ."
maganarsa ta sake bata haushi "mumy ina magana "a shake ta juyo ta kalleshi "maganarka bata da wani amfani agareni fitar min a daki kar na qara ganin ka shigo min daki sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba korosa tayi daga dakinta ." ya fito sami abban yana masa complain shima da farko abban bude masa wuta yayi amman ganin yana bashi hak'uri da janyo masa ayoyi akan masu hakuri da yafiya ya hakura shima ya daura da yi masa nasihohi yana janyo masa ayoyi da hadisai akan irin tanadin da Allah yayiwa masu hakuri da biyayya ga iyaye ."
bayan ya gama ya riko hannunsa zuwa dakin da mumy take ya mata nasiha sosai akan hakuri da yaya nan mumy tace "naji na hakura amman ka fad'a masa kar na sake ji ko ganin yaje wajen nuzla idan ba haka ba zaka sha mamakina zaka haddasa gabar da baa san ranar qaresa ba akan nana hauwa'u kuwa zan iya tsine maka "hisham ya dan saci kallon mahaifiyarsa Kmr zai mata kuka "wai momy me yasa yanzu kike yin haka ne ?."abinda bakya yi da
"yanzu ka canza shiyasa nima na canza idan ka só abinda nike son zaka cigaba da ganina a yadda kasani sabanin haka kuwa matsaloli zamuyita samu da kai sha sha mara hankali "Ke dai kiyi hakuri ki bar mgnrsa da nuzla raayinsa ne idan yana sonta ya qara daita tunda allah ya halasta masa ajiye mata sama da daya "a ina ?ba dai wannan yarinyar ba sai dai wata dabam kai watan ma ba dai ina raye ba mu iyayensa mu ishesa misali tunda muka haifesa ya taso mu biyu kawai ya gani ya koyi example daga garemu ".
Abba yayi murmushi yana cewa "wannan raayinmu ne ta yuwu shi kuma bashi da wannan raayin "mumy zatayi mgn abba yayi saurin dakatar daita ta hanyar cewa "abar maganar haka yanzu dai ki sanya masa albarka tare da kyakkywar addu'a da kuma fatan alkhairi acikin rayuwarsa " mumy ta numfasa kana tayi Kmr yadda abba ya umarceta ,hisham sam bai ji dadin kalaman mumy ba ya tashi ya fito ransa a bace ya shiga d'akin baccinsa ."
Nana hauwa'u na gyaran daki taji an shigo ta dan juyo ahankali domin ganin wanda ya shigo , yaya hisham ta gani a tsaye fuskarsa babu alamun fara'a ya sha kunu tamkar bai tab'a dariya ba,tana kallonsa ya qarasa inda durowar mirrow yake yana dube dube ta bar abinda take ta qaraso ina yake ta tsaya gabanta na wani irin bugawa da karfin gaske "me kake nema ?shiru yayi har sai data sake maimaitawa, fuskasa a hade yace "ai Kinsan abinda nake nema ki dauko ki bani "babu musu ta nufi inda ta ajiye wayoyinsa guda biyu da wallet dinsa daman da zata goge saman durowar ne ta canza masu wajen ajiya ta dawo ta mika masa tana cewa "fatan ka tashi lfy?bai amsa ba ya fice daga cikin dakin yana jan tsaki tabi bayansa da kallo ."
lumshe idanunta tayi tana jin damuwa cike da sanyin jiki ta gama abinda take ta fito yana zaune a falo ."Kusa dashi taje ta zauna tana wasa da yatsun hannunta "abinci fa yayi ready ? a qalla ya kusa minti goma sannna yace "bana da raayin ci "tayi shiru ta rasa me zata sake cewa" oh allah ban ta'ba tunanin zan yi irin wannan rayuwar ba ,sai yanzu take ganin gskyr maryam akan yayanta aure ba abu ne da zaka iya sadaukar da rayuwarka akanshi ba domin abune da mutuwa ce kawai take rabawa tashi yayi ya nufi wata kujerar yana dane dane a wayarsa ."
daren ranar da kuma wunin safiyar data waye duk a cikin k'unci nana hauwa'u tayisa har izuwa yanzu cin abinci kawai ke fito da'ita shima bisa takurawar mumy ce ."dan kar mumy tazo ta tarar daita a d'aki tana kuka bayi take shiga taci kuka har ta godewa ubangiji, idanuwanta sunyi jajir kamar barkono, da dare ma da mumy tazo zata d'auketa domin kaita gidanta sai da mumy tayita rarrashinta dan ji take gara ta cigaba da zama dasu akan zamanta da yaya hisham mumy ta fito tana bata kwarin gwiwa sai da abba ya sake masu wasu nasihohi masu ratsa zuciya da kuma gangar jiki sannan yaya hisham ya d'aukesu suka wuce direban mumy na biye dasu abaya domin shi zai dawo daita ."
Har suka isa gidan nasiha mumy take masu shi dai yaya hishsm bashi da wani kuzari saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa amsarta dan bai jin zai iya mata irin son da yake wa nuzla yayinda nana hauwa'u itama jin momy kawai take amman har a zuciyarta tasan yaya hisham bazai bari su zauna lafiya ba sai 9 na dare sannan direba ya dawo da momy ta barosu su kad'ai acikin makeken gidansu. d'akin take kallo a tsanake komai yayi mata kyau most especially parlour'n wanda aka qawata shi da kayan zamani masu kyau".
Karfe tara da minti shabiyar daidai wayarsa ta soma ringing ya d'auka ya duba, ita kuwa tunda wayar ta fara ringing ta tattara gabad'aya hankalinta kacokan akanshi , bata san dalili ba taji wata irin muguwar faduwar gaba ,ta dan saci kallon inda yake a zaune a tun sanda suka shigo ,bata dauke kwayar idanunta akanshi ba har sanda ya dauka yana cewa "wallahi nuzla rigimarki tayi yawa dare fa yayi okay shikenan ganin nan zuwa yana gama wayar ya fice batare da yace mata komai ba ."
wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sauke tana dafe qirjinta tare da fashewa da kuka ,ahankali ta durkusa kasa ta cusa kanta cikin qafafunta tana kuka tare da kankame jikinta ,sai da tayi kuka mai isarta sannan ta mike ta shiga bayi wanka tai ta fito ta bude wordrobe dinta shiru tayi tana kallo babu abinda babu hatta kayayyakinta na gida an kawo mata ta
saka kayan bacci wondo dogo da riga mai long sleeve butter colour touch of brown ta saka hijab sannan tayi sallar shaf'i da witiri tayi addua akan Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi a tsakaninta da yaya hisham ."
sai data rufe kofarta da key ta kashe fitilun dak'in tayi shirin kwanciya bacci , koda ya dawo ya tarar har tai bacci yana murda kofar d'akin yajita gam nan da nan yaji ranshi ya 'baci meye abun kulle kofa tsaki yaja ya juya ya shige d'akinsa ."
Washe gari tana farkawa daga bacci tai sallah sannan ta fito ta wuce kitchen, had'adden breakfast ta had'a masu naji da gani bayan ta kammala sannan ta d'auka ta kai dining, d'akinta ta koma tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar abaya bak'a mai ratsin ja tai rolling kanta da mayafin abaya sannan ta saka takalmi silifas ja , ta feshe ilahirin jikinta da turare tayi kyau sosai abunka ga farar mace ta d'auki phone d'inta ta fito zuwa falo ."
tana fitowa shi kuma yana fitowa daga d'akinsa sanye da jallabiyya brown , cikin sakin fuska ta masa barka da kwana ,wani kallo yayi mata mai hade da harara sannan yaki amsa tsabar bakinciki "meye jiya zaki wani rufe daki ?tayi shiru "me kike tunani akaina ?"still dai shiru tayi masa tare da sunkuyar da kanta kasa "ko gidan nan naki ko kuma da kudin wani naki aka gina shi ?shiru tayi tana nazarin maganarsa ,a wannan shirun datayi ta fahimci inda maganarsa ta dosa yana son ta'bo yayanta ne abinda bazata d'aukar masa ba kenan muddin baya son zaman tashin hankali daita ya tsaya iya kanta kar ya ta'bo mata wani nata ita dai zata jure komai akanta amman akansu bazata iya ba ."
Numfashi ta sauke tace "ga breakfast can akan dining idan ka tashi ci ".ta fada haka né dan kawo qarshen maganar sai dai bata kai ga k'arasa rufe bakinta ba yayi saurin cewa "to baa ci ina miki magana kina min maganar wani abinci d'an yunwa kika dauki ne ko me ?" yadda yayi maganar sai da ya gigitata "na fahimci haushin nuzla kike ji a zuciyarki "idan har fahimtata gsky ne wallahi kiyi maza ki cire a zuciyarki daman munafurci ne yasa kikace kin amince idan zan aureta na aureta well idan na tashi aurenta ba amincewarki nake nema ba ."
A natse ta durkushe a gabansa tana kuka "karka min mummunar fahimta bazan iya bacci ba matsawar na bar kofar a bude tunda kofar shigowa falo a bude take amman kayi hakuri bazan sake ba maganar nuzla kuma wallahi babu ruwana ko mata goma zaka aura byn ita kana dama "saboda ga dan iska ba ?"ka rufa min asiri ba abinda nake nufi ba kenan yaja tsaki ya juya a fusace shifa ba lalla'ba yake son tayi ba so yake ta biye masa daga nan komai yazo qarshe ."
nana hauwa'u ta mike da sauri ta rungumeshi ta baya tana rera masa kuka mai cike da jan hankali "yaya hisham dan Allah ka bari na samu natsuwa a gidan nan idan kuma har baza ka bani wannan kwanciyar hankalin ba kana iya sakina Kmr yadda nace ,sosai ta shige jikinsa tana goga masa dukiyar fulaninta sannan ta cigaba da magana "nasan baka sona amman ni ban ta'ba jin tsanarka ba zan iya mutuwa akanka yaya hisham dan allah me nayi maka da ka tsaneni haka ?"dan allah kayi hakuri ka daina tsana haka bana bukatar komai bana son kuma daga gareka ni dai mu zauna lafiya cikin sheshekar kuka ta qarasa mgnr."
Sosai ta rud'a yaya hisham jikinsa sai rawa yake ya juyo ahankali tana jikinsa ta sake narkewa a qirjinsa "kada ka canza yaya hisham kowa yabonka yake yi akan nayi saar samun mijin da babu kamarsa gurin kyakkwar halayya kana da kirki bazaka ta'ba barin nayi bakinciki ko kuka ba , samunka amatsayin miji ba qaramin nasara nayi ba amman why kake son canza halinka?runtse idanunshi yayi tabbas haka né shi kanshi yasan ya canza amman duk ita ce silar komai da bata amince da aurensa ba dole iyayensu su hakura ."
kuka take sosai har da shesheka tausayinta ya kamashi ya soma jin kamar ya bata hakuri ta daina kuka amman ya kasa magana, dago kanta tayi taga ita yake kallo ta matso da fuskarta kusa da nashi ido cikin ido suke kallon juna suna shakar numfashin juna, gbdy wani iri suka dinga ji ajikinsu ya bude baki zai fara magana ta matso da lip's dinta kan nashi tana kallonsa tana motsa lip's dinta akan nashi "am sorry yaya hisham I don't mean to hurt you bansan rufe kofar zai 'bata maka rai ba da ban rufe ba "ta fad'a tana kamo lip's dinsa ta shiga tsosa cikin salo kamar ta samu sweet ,cikin son qara rusa shi ta kamo harshensa tana mai wani irin sha tana goga masa qirjinta ."
wani nishi yaya hisham ya saki cikin fitar hankali da mamaki ya zare bakinsa yana já baya tare da cewa "meye haka ?ya fad'a Kmr bai ji dadin abinda tayi ba sunkuyar da kanta kasa tayi tana mai jin wata irin kunya "kayi hakuri" lumshe idanunshi yayi yana jin wani sanyi na bin jikinsa "muje kaci abinci dan allah ba dan ni ba" bai ce uffan ba suka wuce dining a tare itace tai saving nasa sannan ta zauna ta d'auki spoon ta kai bakinsa "bude bakinka na baka da kaina mamakin abubuwanta yake wani lokacin ta nuna masa Kmr tana son shi wani lokacin kuma sa'banin hk most especially idan tace ya auri nuzla ita kuma ya saketa ko ya qara wasu matan ma a bayan nuzla yasan ba so bane kawai biyayya takewa mahaifiyarsa "
Tana bashi abinci shi kuma sai kallonta yake
wani irin bak'inciki yake jin yana taso masa da takaicin bai wani ci sosai ba ya tashi ya wuce, tabi bayansa da kallo har sai da ya bace mata sannan ta daina kallonsa tana jin fad'a uwar gaba ta d'auki wayarta ta soma chart din maryam ."tana zaune ya fito cikin shirin fita aiki tayi masa adawo lafiya ya amsa ta hanyar taga mata hannu ,yana fita ta sauke numfashi ta kira maryam domin taji muryarta dan chart dinta ya nuna mata tana cikin damuwa ".
"kiyi hakuri dai sister har sanda ubangiji zai kawo mana mafuta ta alheri ,In sha Allah zaku daidaita da yayana, ni dai fatana kullun kenan ubangiji ya daidai taku damu gabadaya ."wallahi babu wani gara ni sister nima hakuri nike yaya hisham ya canza sosai fiyye da tunaninki ,duk babu wannan fara'ar da wasan daya saba mana Ke wallahi tsoro ma yake bani ga damuwa ta qaru daman ba wani samun kanshi nike ba bare yanzu ga farincikinsa ta dawo jiya fa na tare a gidan nan amman ina ji kuma ina gani nuzla ta kirasa kuma ya tashi yaje ,tô ya zanyi sister bai dameni ba dan na auresa ne