Showing 6001 words to 9000 words out of 167047 words

Chapter 3 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

ba, yan'uwansa kuwa gaba
d'ayansu suka sauya masa fuska."


Sosai kwakwaluwarsa ta sake lulawa cikin tunani neman mafuta yana buqatar kawowa rayuwarsa canji da sauki idan kuwa har haka ne dan dole yasan abun yi kafin mahaifiyarsa tayi maganr tsarewarsa da yarinyar, tashi yayi daga zaune da yake ya tura hannuwan sa duka cikin aljihun wondonsa zagaye d'akinsa ya fara kafin ya soma zance shi kad'ai "adam dan dole ka nemowa kanka mafuta to me zanyi ?me zanyi dole dai ina buqatar nayi nisa da rayuwar kowa to ina zan koma ?wata kasa zan tattara na koma ?
"ko kuma wani gida zan koma acikin gidajena na cigaba da rayuwata ?yayiwa kanshi tambayar yana cizan gefen lip's dinsa ."


shiru yayi yayinda ya koma ya zauna akan katifa numfashi yake saukewa kamar wanda yayi gudun tsare kanshi ya shiga ya mutsawa ."muddin kayi haka baka kyautawa sweet heart ba, zaka sake jefa rayuwarta cikin tashin hankali ne,karka duba kowa ka duba halin damuwar da mahaifiyarka zata shiga
a lokaci d'aya ya sauke wani naunayen ajiyar zuciya sakamakon saukar hannun mami da yaji akan sumar kanshi ,wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya kalleta batare da yace komai ba " tunanin ya isa haka ka tashi kayi sallah ". ta fad'a sannan ta ajiye masa flaks din tea ta fito zuwa sallahr magariba ."


Wannan halin da ake ciki ya qara sa hankalin maryam ya tashi matuka ,da gaske dai yaya adam baya sonta dan gabd'aya ta fahimci halin da yake ciki duk akanta ne,uwa uba wulakanci da yayiwa mahaifiyarta dan umma  ta fad'awa faiza ita kuma faizar bata boye mata ba ta fad'a mata komai kafin su bar garin "tana kuka take sheida mata" hakika yaya maryam ni kaina banji dadin abinda yaya adam yayiwa ummammu ba, koma menen wannan ai tsaknin ke dashi ne ita meye laifinta zai koreta acikin mutane ?."


ada can baya ni kaina yaya adam yana matukar burgeni amamn a yanzu qiyayyar da yake nuna miki da abinda yayiwa ummammu ya dasa wani mummunar tsanarsa mai girma acikin  zuciyata a karshe tace "to yaya maryam ni dai sai dai ince miki allah ya qara miki hakuri zama dashi ? shiyasa tunda suka wuce kullum bata da wani aiki sai na kuka a karshe ta killace kanta acikin 'daki ta kule ta dinga kuka kwana biyu kenan da yini amman bata fito ba tana daki tana faman kuka sallah ne kawai ke tashinta."


buga kofar mami take da karfi tana kiran sunanta amman mrym bata bud'e ba ta kira layinta tana ringing amma taki 'dauka daga baya ma ta kashe wayarta gabadaya."wani kuka ta fashe dashi dan ita wallahi da gaske son ATA take so kuma wanda bazata iya rayuwa babu shi ba, dan lokacin da mami ta zatar da hukuncin aurensu dadi taji sosai kawai dai ta boye abun ne acikin ranta saboda sanin halinsa allah ya sani tana matukar qaunarsa bil hakki so wanda bazai misaltu ba, tun kafin tasan kanta take fama da wahalar dakon qaunarshi sai gashi adaidai lokacin da take murnar ya zamo mallakinta ya tsiro da wani sabon salo da nuna kyama ga mahaifiyarta "umma Kiyi hakurin abinda yaya adam yayi miki haka rayuwarsa take karki yi fushi dashi kuka take Sosai tana sambatu ."


Tana cikin wannna halin taji ana qoqarin balla kofar d'akin dauke numfashinta tayi ta tsaida kukanta sai dai fa hawaye bai daina gangarowa ba kofar na gama budewa mami ta shigo d'akin gigice ta rungume maryam ajikinta tana tmbyrta "me akayi miki marym da kika dauki matakin cutar da kanki haka ?wasu hawayen masu zafi suka sake zubo mata cikin muryar kuka tace "mami yaya adam ne!"mami ta sausauta rungumar da tayi mata ta zuba mata idanu tana kallonta atsanake "yaya adam kuma ?ta fad'a tare da yin shiru ."


Maryam tayi shiru tana shesheka "Kiyi hakuri diyata ki fad'a min me yayi miki ?"still dai shiru tayi kafin ta fad'a mata duk abinda ya faru ."dafata mami tayi kana ta soma mgn "hakika adamcy bai kyauta ba amamn Kiyi hakuri,sai data numfasa kana ta cigaba da magana "ahalin yanzu adamcy sai kina hada masa da addua "kai kawai mrym ta gyada mata karkice zaki janye jikinki dashi sakamakon abinda yayi saboda yanzu ba kamr lokacin baya bane, a yanzu kusa dashi zaki yi ki fara nunawa mijinki kulawa sannan dole ki koyi juriya akan komai daga garesa har Allah yasa muyi nasara akanshi ."


" nasanki da hakuri maryam zaki iya yin komai Kiyi qoqari ki fara janyo hankalinsa gareki ni kuma zan cigaba da addua in sha Allahu Allah zai sausata masa wannan zafin zuciyar" sannna zan kira ummanki da kaina na bata hakuri .sannan shima adamcy dole ya kirata ya bata hakuri dan haka kar na sake ganin kinyi kuka ko kinsa kanki cikin damuwa idan ba haka ba zamu samu matsala still kai ta gyada mata tana goge hawayenta ,babu laifi ta dan ji sanyi aranta jin zatasa ya kira mahaifiyarta ya bata hakuri ."


Bayan fitar mami daga d'akin tashi maryam tayi tai wanka ta shirya cikin atafa Yellow me flower green ta dauko veil green ta fito zuwa parlour'n tayi breakfast sannan ta shiga neman layin ummanta Allah ya taimaketa bugu daya ta dauka  ta gaisheta  ''maryam me ya samu muryarki haka ?"bana dan jin dadi ne jiya da ciwon kai na kwana gashi banyi bacci ba" "sannu Allah ya sawake, kinsha magani?"eh na sha sukai shiru can maryam ta cigaba da magana "umma dan Allah Kiyi hakuri da abinda ya faru "


"Ai maryam ban san wannna mijin naki dan iskan mara mutunci bane sai daya gwada min cewar shi kwallon tattacce ne,wato giyar kudi na dibarsa shiyasa zai taka duk wanda yaso to wallahi ni bazan taku ba "dan girman allah umma Kiyi hakuri mami ma tace zai kiraki ya baki hakuri "wa ?wannan kwallon shegen ne zai kirani ya bani hakuri ?ai irin tarin qiyayyrki da nagani acikin kwayar idanunshi bazai sa yayi ba "karki ce hka umma tunda mami tace zai kira ki zuba ido kigani zai kira "to wallahi wallahi wallahi nasan adamu bazai kirani ba ko mutuwa zanyi bare ma ya rike hakurinsa bana buqata."


shiru mrym tayi cikin rashin jin dadin saurin rantsuwar da mahaifiyarta tayi ."sai dai hakan bai sa taji tsanarsa a zuciyarta ba ."yaushe ne tariyarki ko a gidan zaki cigaba da zama ?ban san yaushe bane amamn nasan mami zatayi komai akan haka "to walalhi a san abun yi dan bazan sake lamuntar wulakanci ba bayan wanda akayi min "ko da zinari aka kerasa dan ubansa  idan da wulakanci dole a raba auren dan bazai yuwa ba ni uwarki ban sha wahala a gidan miji ba ,ba zai yuwu tun da kuruciyarki ki fara hadiyar bakinciki d'a nmj ba ".

"ai na dauka abun nashi na mutunci ne na yarda da zabin yaya ashe tantiri ne ,da shegen kansa Kmr ball hankalin maryam duk ya tashi sai hakuri take bata"ke wai hakurin me kika bani ai murna zakiyi tunda  daman bakya son aure gara araba auren tun baa je koina ba kar azo ana cewa Kiyi hakuri saboda ya'ya ."mrym ta sauke wani wahallen numfashi ."aranta tace umma bazaki gane yadda karfin soyayyarsa yake kwance acikin zuciyata ba "dan dakatawa umma tayi taji me zata ce sai dai shiru tayi batare da tace komai ba ,a tunanin umma ko maryam bataji abinda ta fad'a bane yasa taja bakinta tayi shiru dan haka ta soma fadin hello hello kina kina jina kuwa .?"

dan numfashi taja ta sauke tana jin yadda soyayyar ATA Ke kwarara ajinin jikinta "maryam !Na'am umma!" kinyi shiru ko kina son zama dashi ne da wannna mugun halin nashi ?"wani numfashi ta sake saukewa "umma Ke ba wacce zan boyewa bace tunda ke mahaifiya ce ko babu komai zaki tausaya min tayi shiru tana faman sauke numfashi cike da zaku wa ummah tace "uhm ina jinki !
"allah ya sani umma na dai nuna maku bana son aurensa ne a zahiri amman a bad'ani  ina matukar qaunar yaya adam so wanda zan iya rasa raina akanshi "inna lillahi wa ina ilahi rajiun shikenan yayi galaba akainmu na shiga uku ni habiba madadin mu juya shi shine zai juyamu sai ta fashe da wani irin kuka tana kiran ta shiga uku ."


rarrashinta mrym tayita yi a kashe tayi mata sallama ta kashe wayar ."tunda ta kashe wayar take rike da wayr a hannunta cike da damuwa ta rafka uban tagumi diyana ta shigo assalamu alaikum shiru mrym bata amsa ba kasancewar ta lula duniyar tunani dan girgiza ta tayi ,a sanyaye ta dubi diyana "maryam lafiya kuwa "?murmushin yake tayi tace "lafiya diyana "Aa mrym karki min karya tunani fa na samu kina yi ki fad'a min gsky me Ke damunki amarya?."murmushi ta sake yi duk yadda diyana taso taji damuwarta taki sai ma shigo da wata hirar tayi byn tafiyar diyana ta kira nana hauwa'u hira suke kowannensu na fad'awa danuwansa yadda yayi kewarsa  ."


***


ATA na tsaye a gaban mirrow yana kallon sansar jikinsa ya rame sosai ,kallo daya zaka masa ka fahimci irin ramar da yayi wanda Ke tattare da tsananin damuwa tsawon lokacin ya d'auka tsaye yana kallon kansa ta mirrow kafin daga baya ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya janyo wata qaramar  stood dake gefe ya zauna hannushi ya d'aura a saman faffaad'en qirjinsa yana shafa kwantaccen gashin qirjinsa hade da lumshe tsumammun idanunsa ,shi kansa yasan duk matar data mallakesa matsayin mijinta bak'aramin lucky tayi ba ".

cike da sanyi jiki ya soma  shafe jikinsa da body lotion yana qoqarin binne dukkanin wata damuwa da tunanin ,a yanzu yasan bashi da wata damuwa ko tunani sai na rashin princess amman yana jin  lokaci yayi da zai raba kanshin da tunaninta wani dogon tsaki yaja yana furta "muguwa daga yau babu ni babu tunaninki ,mikewa tsaye yayi cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufi wordrobe dinshi dan saka kayan shiryawa yayi cikin wasu had'add'un kananan kaya blue jeans with white t shirt " wani irin kyau kayan yayi masa na d'aukar hankali, ya sake komawa gaban dress mirrow ya d'auki turare ya feshe ilahirin jikinsa sannan ya kwashi wayoyinsa da sukayi kwanaki hud'u akashe ya kuna."


nan da nan sakonni sukai ta shigowa ya zuba hannunsa daya cikin aljihun wandonsa "ya sanya silifas fari sol ya fito yana taku kamar baya son taka kasa a natse yake saukowa daga step koda ya gama saukowa da maryam idanunshi ya soma cin  karo tana zaune sanye da atamfa ja kayan sun yi mugun haskata abuka ga farar mace sai dai kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa daga kanta yayi tamkar bai ga wata halitta a wajen ba ya maida hankalinsa inda mami Ke zaune rike da jarida ita kuwa mrym idanunta kyam akanshi har bata son kifta idanunta idan tana kallonsa wani abu take ji yana fexgarta mai kama da shoking."

jikinsa ya basa idanunta na kanshi dan haka ta kasan idanunshi ya kalli inda take tare da jifanta da wani irin kallo wanda yasa tayi saurin dauke kwayar idanunta akanshi ta sunkuyar  zuciyarta na wani irin luguden bugu ,tana son ta gaishesa amman tsoro da firgici sun taru sun hana , ya cigaba da taku cike da izza da jin kai da jin shi wani ne ya qaraso ya ajiye wayoyinsa a kan qaramin tablet dake ajiye a gaban mami ya zauna a kujerar da sweetheart dinsa take zaune ya daura kansa kan cinyarta batare da yace uffan ba ".


Mami ta'ajiye jaridar dake hannuta wanda tun soma jin kamshin turarensa da takunsa ta daina karatu da take muryarsa a kasalance yace "gud afternoon  my sweetheart"ta daura hannuta akan kwantaccen sumar kansa tare da fadin" afternoon  my adamcy fatan ka tashi lfy ? ya dan tabe baki "nut bad !"
maryam dake zaune a wajen tamkar mutun mutumin zuciyarta banda bugawa babu abinda take tsabar firgici ita kanta tana tunanin yadda zaman aure zai kasance a tsakaninsu ta koina ta duba matsala ne tattare dashi idan aka barta da matseefaffen tsoron da take masa ma kawai ya isa ya kasheta a gidansa mutun sam babu saukin kai hatta mahaifiyarsa shan kamshi yake mata  ."



ATA bai sake cewa komai ba ya dauki daya daga cikin wayoyinsa daga kwance da yake yana duba sakwanin mutane da akayi ta turo masa a cikin kwanaki hud'u data gabata sakon m.Malik ne na farko farko ya tsurawa sakon ido yana karantawa a hankali yana jin wani iri a gbdy ilahirin jikinsa lumshe tsumammun idanunshi yayi kana ya soma qoqarin nema layinsa wayar tana ringing baa dauka kusan sau biyar ya kira wanda a dabiarsa baya kiran mutun sama da sau daya yayi shiru yana cigaba da kallon sakonsa "adamcy nah!"mami ta kirasa cike da kulawa."


"Hakika mahaifiyarka tayi .."stop sweetheart !" ya fad'a yana kai idanushi inda maryam take zaune tana kallonsa Kmr zata cinyesa wani mugun kallo mai hade da harara yayi mata wanda yasa ta mike tsaye da sauri ta nufi hanyar dakin ,mami ta sauke numfashi tana cewa "me yasa zaka korar min yarinya ?"idan ba rashin kunya irin nata ba da munafurci zaman me take ?"kuma ma ni bana son kina min fad'a a gabanta ai sai ta qara raina ni ."wa ya fad'a maka fad'a zan maka "?ni babu fad'an da zan maka hasalima  rokon gafararka zanyi adamcy nasan na cutar da kai akan auren nan ."


"Adamcy bani da wani zabi ne yasa na yanke wannan hukuncin akanka wanda bansa cikin maseefa zan jefa rayuwar d'ana ba." ka yafe min "haba sweetheart ki daina bani hakuri da neman yafiyata  wallahi baki min laifin komai ba "wallahi nayi maka laifi tunda gashi a fushin da kayi dani yasa ka min hukunci mai zafi da radadi na sha wahala sosai acikin kwanakin nan da ka jefa rayuwarka cikin maseefa "wannan bashi yake nufin nayi fushi dake ba " yayi maganar Kmr zai yi kuka ".


"Shine mana idan ba fushi kayi ba me yasa zaka min hukunci da shaye shaye bayan kasan shine abu mafi muni da zai kassara min rayuwa ?shiru yayi kawai yayinda maryam ta lallabo ta fito daga cikin dakinsu ta rabe tana son taji tautaunawarsu "dan allah karka sake kai giya bakinka "shiru ne dai ya sake biyowa baya yayinda mrym ta sake kasa kunne sosai ko zataji mami ta cigaba da mgn "ka min alkwari adamcy bazaka sake kai giya da duk wani kayan shaye shaye bakinka ba "

"Naji !"
"Ba maganar kaji ba ka bud'e baki kayi min magana "nayi miki alkwarin bazan sake shan giya ba daman ni ba mashayinta bane damuwar da zuciyata take ciki ne silar fara shanta na bar giya har abada amman zan sha sigari."mami tayi shiru tana duban fuskasa "wato dai shi fad'i ka hutu ne kome zai faru sai dai ya faru amman sai ya fad'a abinda ke ranshi ahankali taji ya kamo hannunta cikin nashi tare da tsaida kwayar idanunshi akanta "sweetheart ki yafe min domin na kasa miki biyayya akan abinda kike so nima ba laifina bane ,wallahi da zan iya tursasa zuciyata da zan so yarinyar nan ko dan saboda darajarki ."


Ta zare hannunta cikin nashi ta daura a sumar kanshi tana cewa "na yafe maka duniya da lahira" "daman kuma mami ba me iya dogon fushi da tilon d'anta bace dan tun yana yaro idan yayi mata laifi tayi fushi dashi tofa dare nayi zata tashi tayi alwala tai nafilfili da masa addua tare da nemammansa sauki da afuwa a wajen Allah shiyasa rayuwarsa ta cigaba, dan tasan a yadda Allah yayi sa da baud'ad'dan hali irin wannan tace zata yi fushi dashi to rayuwarsa zata lalace rayuwar bazata masa kyau ba kuma akarshe dai itace acikin matsala cike da kulawa tace "adamcy  me kake son kaci akwai dish iri iri akan dinner wanda matarka mrym ta shirya maka."


turo baki yayi cike da izza har zai yi magana " kome ya tuna sai Kuma ya fasa cewa komai sai dai yaji zafin mgnrta matarsa a ina shi baya son ana had'ashi da yarinyar aure dai an daura bashi da yadda zai yi amman sai ta gwamaci mutuwa da rayuwa dashi da kanta zata zo tace araba auren idan taji wahala
mami ta tsurawa fuskarshi idanu kana tace"adamcy nah kayi shr "ya lumshe idanunsa kawai " muje kaci wani abu , ahankali ya ware idanunshi akan mami yana dubanta sannan ya motsa labbansa da kyar yace "sweetheart  na koshi fita ma zanyi yanzu ....."



"fita zakayi byn baka sakawa cikinka komai ba ina fa hankalce da kai  duk kwanakin nan bakason cin abinci, ina zaka ma tukuna da naji kace fita zakayi byn kana cikin hutun angonci ?ta fad'a tana hade fuska tamau hade da zuba masa idanunta."ya d'an ytsina face dinsa har dimple dinsa ya lotsa" kyawunsa ya sake bayyana" ya mike daga kan cinyarta ya zauna sosai shima yana kallon yanayin Sweetheart dinsa yana jin soyayyarta  fiyye da komai  "yana sonta baya son damuwarta, itace duniyarsa sannan itace ke tattare da duk wani farincikinsa tana tsantsar sonshi da nuna masa duk wata kulawar da uwa kad'ai zata iya yin haka kawai inda tayi masa ba daidai ba hadashi aure datayi da mrym shima kuma ya yafe mata yasan batayi hakan dan kuntatawa rayuwarsa  bane ."


Hannuta ya kamo duka cikin nasa ganin yadda ta damu muryasa a sanyaye kmr koda yaushe  "am so sorry my sweetheart zan dan fita ne amman muje zanci tayi murmushin jin dadi "alhamdulillah! ta furta acikin ranta da alamun adamcynta ya fara dawowa daidai tace" kai ko hade da dan dungure masa kai " kai komai zakayi sai kayiwa mutun kwalisa ai naso ace mafarkinka gsky ce ta canza min kai byn ta canza min kai ta juya ka son ranta "haba sweetheart kina ganin akwai wannan matar da zata iya canza miki ni daga yadda nike ko juya ni ?akwai mana idan nmj na son mace babu abinda bazai iya yi akanta ba "banda wannan d'an naki dan bazai jiyu ba duk son da zan yiwa mace bazan ta'ba bata wannan chance din ba ."


"Allah ya shirya min kai" ta fad'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login