Showing 72001 words to 75000 words out of 167047 words
Chapter 25 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
abinci uwarsa mai mugun yaji kamar zaa bawa mutun maita bare nasan duk zabga yajinki cikin abinci bazaki taba kai uwarsa ba “.wani irin mugun kallo ATA yayi wa maryama yana qoqarin damko wuyanta .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 14
Da sauri maryam taja baya hankalinta na sake tashi yayinda MB yay sauri ya shiga tsakaninsu yana shafa qirjinsa alamun ya kwantar da hankalinsa inda sautin muryar umma ya cigaba da fitowa cikin munanan kalamai masu zafi “yaji da maggie ne kawai suka yi yawa cikin abinci ka wani d’aga wa mutane hankali , tana sane zata aikata hakan ne ?” babu wanda ya wuce ya samu irin wannan problem din a girki ,zai iya faruwa akaina ,zai iya faruwa akan uwarka hakazalika zai iya faruwa akan kowace mace “.rawar da jikin maryam yake ya qaru taji qafafuwanta suna barazanar kasa d’aukarta lokaci guda taji zuciyarta na barazanar tarwatsewa “shikenan umma ta kasheta da ranta dan tasan yau mai kwatarta a hannun yaya Adam sai allah.”
shawul da salim mikewa sukai suna dubansu cikin tsananin kad’uwa da tashin hankali zasu iya cewa yanayin da suka ga ATA a yanzu basu ta’ba ganinsa cikin irin yanayin ba “enought is enough Adam maryam ba baiwa bace ta fad’a a tsawace sannan ta cigaba da magana “inda ya kamata a d’aukar mata masu aiki bilaadadin suyi mata hidimar gidan amman ita ta hakura ta kwantar da kai tana bauta maka bayan ta gama bauta wa uwarka shine zaka zo ka saka min yarinya a gaba ?”to wallahi kaji na rantse bazan d’auka ba, rashin mutuncinka ya tashin akan maryama ya dawo kaina wallahi adam I can’t take it any more duk kuma abinda ya samu yarinyata bazan duba sanayya dake tsakaninmu ba kotu ce zata rabamu da kai idan kuma kana ganin babu abinda zai faru dan girman allah ka gwada idan kace kai surukin zamani ne to ka had’u da surukar zamani kuma daidai da kai .”
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun “shikenan umma kin sake sakani cikin tsaka mai wuya “me zai miki ?kima kwantar da hánkalinki babu abinda zai miki “umma …!”ta kira sunanta a rud’e tare da wani irin kuka mai karfi dake fitowa daga qarqashin zuciyarta so take ta cigaba da magana amman kukan da take ya hanata ,bata ta’ba tsintar kanta cikin tashin hankali irin na yau ba, wani dogon tsaki ATA yaja sannan yay discounting din kiran alokacin da umma take qoqarin son cigaba da magana ya yiwa MB alamar ya matsa daga gabansa domin ya isa ga maryam “dan girman allah karka mata komai "oh my god MB ka matsa daga gabana nayi ma yarinyar nan abinda uwarta zata kai ni gaba da kotun koli ".
“ ka natsu muyi magana first “no way !” ya fad’a a fusace tare da d’aga hannusa salim da shawul har da mb suka matsosa tare da rikesa suna bashi hakuri wanda dole tasa ya kasa aiwatar da nufinsa yayi shiru kawai sai dai ilahirin jikinsa rawa yake”yayinda maryam ke kallonsa ,banda kuka babu abinda take tana bashi hakuri amman wani sabon tashin hankali take hangowa a tattare dashi a matukar rikice ta kallesu “dan girman allah ku kira mami ita kad’ai ce zata..” wani mugun kallo ya d’auketa dashi da idanunshi wad’an da gbdy sun canza kala “adam ! wai me yasa baka iya control din fushinka ne ?! ATA bai iya cewa komai ba sai ma zuba masa rinannun idanunshi da yayi yana dubansa .layin mami salim ya soma kira domin dai shi kanshi ya tabbatar ita kad’ai ce zata iya sauko dashi daga fushinsa yayinda MB yayiwa maryam alamu da idanunshi cewar ta bar gurin .”
babu musu maryam tabi umarnin MB da sauri ta haye sama jikinta na rawa ta shiga d’akinta ta d’auki wayarta ta soma kiran layin mahaifiyarta tana d’auka tasa mata kuka .”haba umma haba ummah!! “mai yasa zakiyi min haka ?wallahi idan kinyi haka ne dan ki kwatar min ‘yanci to kisani kin sake jefa rayuwata cikin mummunar bala’i ne “daga can bangaren umma ta fusata “kenan tashin hankalin mijinki kike jin tsoro akan abinda yayi min ?maryam tayi shiru tana goge hawaye “gif haka ATA ya zauna saman kujera yana qoqarin runtse idanunshi cikin murya mai cike da tashin hankali yake furta “muddin ban canzawa yarinyar nan kamani ba to shege ne cikin uwata da ubana “kayi hakuri dan allah itama fa kamar mahaifiyarka ce karka manta danganta dake tsakaninku ko babu maryam atsakaninku ita din matar kanin mahaifiyarkace “.
“amman ai kunji irin maganganun ta gareni da kuma mahaifiyata ?munji amman kai ma ai abinda kayi bai dace ba ,bai kamata ka kirata kana fad’a mata son ranka ba “ya d’ago kwayar idanunshi yana duban MB wanda shima tashin hankali ya nuna a fuskarsa lokaci guda ATA ya cigaba da fad’in “but MB how dare her talk to me like that “?mahaifiyata fa ?yanzu sweetheart ta cancanci haka “?ya mike tsaye yana girgiza kai yana duban MB da salim dake rike da waya da karfi ya shiga jijiga MB “MB Mahaifiyata fa ?! “zagin ma ya wuce kaina har mahaifiyata she could have kill me akan cin mutuncin uwata da tayi.” yadda yake maganar zaka fahimci yana cikin tsananin damuwa .”
kamo kafad’unsa MB yayi ya zaunar dashi a saman kujera yana qoqarin calming dinsa “plse ATA try to calm down d’ago idanunshi yayi wad’an da gabad’aya a rikice suke, kau da kai gefe ATA yayi yana sake tariyo abubuwa da ummah ta fad’a masa lokacin guda ya dunkule hannuwansa yana murzasu waje d’aya .”shawul ya qaraso ya kamo hannun ATA yana dubansa cike da tausayawa dan gsky shima bai yi sa’ar samun suruka ba ,sam sam bai yi exepeting haka daga mahaifiyar maryam ba ,yadda yake kallon maryam ya d’auka mahaifiyarta zata fita saukin kai a she abun ba haka bane . ATA huci mai zafi ya furzar sannan ya mike ya isa jikin window ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa cikin rashin sanin abinda zai yi.”
suna tsaye cirko cirko mami ta shigo cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunansa “where’s adamcy ?
”Kasa juyowa yayi sai dai jin muryarta ya soma qoqarin saisaita kanshi ,MB ya numfasa wanda har lokacin yana tsaye ya tsurawa waje d’aya rinannun idanunshi, dafashi yayi yana fad’in “try to calm down ga mami tazo karkayi abinda zai ‘bata mata rai “duk kuna nan zaune aka dinga ciwa mahaifiyata mutunci babu wanda ya taka mata burki ,kodan dan ba mahaifiyarka aka zaga ba ?” MB yayi shiru yana dubansa daman kuma haka yake duk sanda ransa ya ‘baci he can talk nonsense. ya sake dafashi yana qoqarin cigaba da magana “ don’t ever ask me to calm down again .” yayi maganar jijiyoyin goshinsa na sake fitowa sosai gumi na kuma tsatsafo masa kafin ATA ya sake cewa wani abu mami tace “wai meke faruwa ne ?!.
“salim tunda ka kirani jikina ke rawa haka ma zuciyata bugawa take fiyye da kaida ina maryam take tukun ?shiru sukai gabad’ayasu “kunyi min shiru ,ku fad’a min abinda Ke faruwa “mami ki zauna first zan miki bayanin komai “inji cewar salim “ina maryam take ina son nasan halin da take ciki kafin komai ?“maryam tana lafiya babu abinda ya sameta tana sama ya fad’a yana kamota ya zaunar daita akan kujera yayinda MB ya janyo hannun ATA ya zaunar dashi bai d’ago kanshi ba sakamakon zafin da zuciyarsa keyi masa tunda yake babu wanda ya taba ciwa mahaifiyarsa mutunci sai yau .”
“Ku sanar dani abinda Ke faruwa tun kafin zuciyata ta tsaya ta daina aiki gabad’aya “MB ya bud’e baki zai yi magana kenan ATA ya d’ago tare d’aga masa hannu ya janyo wayarsa ya shiga recond dan tunda ya fahimci rashin mutunci ummah zatai ya danna record ya kunna ya tura wayar gaban mami nan take sai ga muryarta ta bayyana ,mami tai shiru tana sauraro tare da runtse idanunta abun ya girgizata matuqa ,kuma yayi mata zafi duk da tasan halin d’anta he can talk rubbish and nonsense idan rashin ya’baci amman ai ita bata cancaci haka a wajen madina ba” mami ta numfasa irin nasu na manya tana dubansu, sannan ta soma magana a natse “duk me ya kawo wannan tashin hankali haka ?”duk sukai shiru “ lallai akwai abinda ya faru bancin haka ina da yakin madina bazata aikata haka ba ?gabad’ayansu suka tsaya suna duban mami suna duban ATA “magana nake daku kuna jina kun yi min shiru kuna dubansa ?MB ne yayi karfin halin fad’a mata komai daya faru “tabbas mami abinci yayi yaji da maggie amman ban so yadda adam yayi react ba.”
“Naso ko zai mata magana ba a gabanmu ba bare har ta kai ga kiran mahaifiyarta ,sannan itama ummah bai dace abinda tayi ba babba dasanin ya kamata akasanshi amman duk ataru ayi hakuri .”
mami tayi murmushin takaici tana tsarke hannunta cikin juna lokaci guda ta maida hankalinta ga ATA tana dubansa a tsanake “ I hope you learned lesson now?” you should know there’s no right way to do wrong things, next time sai ka kiyaye bakinka tunda baka son a ta’ba maka mahaifiya .”ATA ya tsura mata idanunshi yana kallonta zuciyarsa na tafasa “dan me zaka kirata ka fad’a mata haka? “yanzu sweetheart tsakani da allah yaushe kika ta’ba girki mai yaji ko maggie yayi yawa?zaginta fa kayi ka kuma had’a da yar cikinta dan ma kayi sa’a maryam diyar kirki ce bata iya rashin kunya ba ?”ai wallahi data gane bata da wayo “ya fad’a a zafafe “kai dai kayi qoqarin ka canza halinka sannan ka dinga control din zuciyarka da fushinka ba kowa zakawa ya kyaleka ba.”
“ yanzu sweetheart baki ji zafin abinda tayi ba ?to ko naji zafi adamcy ya zanyi ?wa yaja min cin mutunci da akayi min ? da bakayi ma madina rashin kunya ba bazatayi min haka ba dan bata isa ba ,nafi karfin ta fad’a min haka .”ta karshen maganar cike da jin zafi dan da zaa bud’e zuciyarta bakinkirin zaa gani tsabar ciwon da taji amman babu yadda zatayi dan kuka shi ke jawowa uwarsa jifa “ATA bai ce uffan ba har ta gama maganganunta sai dubanta da rinannun idanunsa yake “yanzu nasan zakace zaka huce akan maryam “?ta tambayesa tana tsaresa da ido wanda ko motsi mai kyau ya kasa sai ma damke hannunwan sa da yayi ,mami ta gyara zamanta tana karantar d’anta tasan halinsa tasan abinda zai yi da wanda bazai yi ba “tunaninka a yanzu yadda zaka huce akan maryam kakeyi ko?still shiru yayi ya kasa cewa komai dan ya ma rasa mai zai ce amman tabbas tunaninsa kenan ,mami ta dubi MB ta kuma dubi salim da shawul “ku sheida muddin adamcy ya ta’ba lafiyar maryam ban yafe masa ba “ta fad’a tana dubansu d’aya bayan d’aya nan taga yanayin ATA ya sauya tamkar wanda aka cirewa laka ajiki sai dai zuciyarsa tayi bakinkirin jin abinda mami ta fad’a.”
ahankali mami ta yunkura ta mike ta nufi hanyar step bata tsaya akoina ba sai abakin kofar d’akin maryam ta tsaya sai dai hakan nan zuciyarta ta dinga rawa rawa har ta kai hannu zatai knocking sai kuma ta sauke hannunta tana nazarin zuciyarta .”ahankali ta tura kofar d’akin ta shiga maryam na tsaye ta juyawa kofar d’akin baya tana sheshekan kuka “inda acan bangaren ummah take cewa “wallahi maryam wannan miji naki ya zame miki damuwa arayuwarki amman bamu da yadda zamuyi tunda allah ya jarabeki da mutuwar sonshi amman idan muna son muyi nasara akanshi dole sai munyi abinda zamu rabashi da tunaninsa dole ya zama abokin rayuwarki ya shiga jikinki ki shiga nashi ku zama abu d’aya “mai zanyi ummah da zan samu wannan matsayi a zuciyarsa ?”ya kusanceki shine cikar burina a yanzu bayan ya kusanceki ina fatan kuma ya zama “d’a “zan so faruwar hakan “amman ummah ta yaya hakan zai faru a tsananimu ?Kai nifa gsky ummah na gaji na
gaji !! da yin amfani da magungunan da kike aiko min dashi dan baya ci komai daga gareni “wallahi kuwa duk wannan bala’i da yayi bana tunani ya had’iye abin…“.
“Maryam !” mami ta kira sunanta a matukar firgice ta juyo ganin mami tsaye tayi saurin sauke wayar a kunnenta tare da kashewa tana dubanta jikinta na kyarma kafin ahankali tace “a’a mami har kin zo ?sannu da zuwa mami ga waje ki zauna ,tayi mgnr a rud’e cikin rawar jiki ,mami tai mata duban natsuwa sannan tace “ban jima da zuwa ba daman kin san zan zo ne ?ta gyad’a mata kai alamun eh !“ai nice ma nace yaya salim ya kiraki ta fad’a tana duban mami mami tayi shiru itama maryam tayi shiru cikin rasa abinda zatace dan hankalinta yayi matukar tashi adduarta d’aya allah yasa bataji maganarta ba.
cikin zafin nama mami tace “ya kikayi shiru haka ?ta girgiza mata kai tana cewa “babu komai “dawa kike waya “? muryarta cike da tashin hankali tace “ummah!”okay !”amman ya’akayi maryam kika bari yaji da maggie yayi yawa acikin abinci?naunauyen ajiyar zuciya ta sauke dan ba abinda tayi tsamanin zai fito daga bakinta kenan ba duk tunaninta mami taji maganarta cikin rawar murya tace”wallahi mami bada niyya bane sautsayi ne kawai sai gani nayi ya kira umma yana fad’ar maganganu marasa dadi .”
Mami ta numfasa kana tace “kiyi hakuri maryam nasan adamcy baya kyautawa kuma bai kyautawa ummanki ba kuma naji dadin abinda tayi masa allah yasa ya zame masa darasi kuma nayi masa gargadi mai karfi akanki dan haka ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru kinji diyata mami ta riko hannunta ta zaunar daita a saman kujera tana cewa “kema ki dinga kula most especially akan girki .
“ba tun yau nake fad’a miki ba ,ba’a són maggie da yaji na zarcewa abinci ,a wannnan rayuwar da muke ciki idan nmj na tsananin son mace ko bata iya girki ba ya Kan yi hakuri yayi rayuwa daita a yadda take amman Idan tana da matsalar girki ko tsaftacce muhalli da jikinta kuma akayi sa’ar babu so tsakaninsu to shi yafi komai rashin kwanciyar hankali dan kuskure kad’an zatayi zai zame masu damuwa .“ina sonki da adamcy shiyasa nake yawon jan hankalinki ,ki dinga kula daidai girkin da zakiyi daidai maggie da yajin da zakiyi amfani dashi ,karki lura da yanayin girkin da’ake nunawa a social media kice zakiyi amfani dashi a’a suma suna duba yanayin yawon girki ne ,dan haka ki dinga duba yanayin yawon miyarki ko qanqantarsa , ki dinga kula kinji allah ya baku zaman lafiya .”
Zuciyar maryam tayi fari qal farinciki biyu suka hade mata fahimtar mami bataji komai ba da kuma tabbatar mata dole ATA yayi hakuri ya barta batare da yayi mata komai ba ,ta mike tsaye tare da riko hannu maryam suka fito zuwa parlour’n kasa “nayi closing case din nan kuma har abada banason naji an sake ta dashi ATA ya gyara zama yana mai shan mur sosai ,kafin ya soma girgiza kafarsa d’aya cikin tsananin bacin rai yana duban mami “zanyi maka gargadi na karshe adamcy for the last time karka sake kiran madina da magana irin makamanciyar wannan dan ba abokiyar wasanka bace, uwarka ce duk abinda zai faru a tsakaninka da maryam ka barshi a tsakaninku .”tana gama fadar haka tace “ni zan koma gida allah yayi maku albarka gaba d’ayansu har maryam suka fito yiwa mami rakiya amman banda ATA dake zaune cikin tsananin ‘bacin ran bai samu damar cin uban maryam ba “.
Maryam taja mami kusa da motar data kawota tana cewa “mami na gode sosai bancin inada ke da bansan ya rayuwata zata kasance acikin gidan nan ba na gode na gode !! allah ya shirya miki zuriarki Allah kuma ya jikan iyaye “nima na gode maryam allah yayi maku albarka mami ta d’an yi shiru can kuma ta numfasa sannan ta fuskanceta da kyau “maryam kamar koda yaushe ga d’ana adam ,a kullum shi masa albarka nake, duk da abinda nake masa akanki ba wai banason shi bane a’a kema kinsani adamcy raina ne ,ina matukar sonshi fiyye da komai ban had’a shi da komai ba ,duk abinda ya shiga raina ya kan shiga ransa ya zauna daram ,sai dai a waje d’aya muka samu sa’banin ra’ayi shine aurenki dashi wanda yaki ya kar’ba uzurin da nazo masa dashi nasan yadda yake jin radadi zama dake amman nasan da sannu zaki zama jinin jikinsa “ki cigaba da hakuri da adamcy kinji ,ta gyada mata kai tana wasa da yatsun hannunta “ki kular min dashi karki manta adamcy amana ne agareki sai kinyi hakuri dashi kafin kiyi nasara akanshi “cikin rawar murya tace “in sha allahu mami zan kular miki dashi ta qarasa maganar cike da tausayawa mami .”
“Anya kuwa tayiwa mami adalci da take son biyewa mahaifiyarta ?”tayiwa zuciyarta tambaya nan take gur’bataccen zuciyarta tace “adalcin kenan kina tsananin sonshi ita kanta mami tana son faruwar haka kuma zata fi