Showing 57001 words to 60000 words out of 167047 words
Chapter 20 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt
aiki yake wahala a kasar nan? .”
Ya kankantar da idanunshi tare da yin shiru yana tunanin abinda zai sa wani mutun biladam mai jini ajiki yayi rejecting din aiki a maakatarshi ya hade rai sosai cike da takaici a fuskarsa sannan Ya koma ya zauna sosai akan kujera yana jujjuyawa a hankali yana cigaba da tunanin Ya furzar da iska mai zafi yana tsotsa keyarsa “ina ganin wannnan yarinyar tana da damuwa a brain dinta ,kai kwata kwata ma dakikiya ,for god sake ni me ye damuwata yanzu ? me yasa zaka kawo min wannan banzar maganr ?meye damuwata daita dan taki amsar aiki inda ga mutane can bila adadin suna nema ?ya qarasa mgnr cike da jin haushi yana ja tsaki “ noncess !Ya furta yana dungule hannunsa .
“Am very sorry sir daman dan ka bukaci mai ilimin lissafi ne shiyasa har muka bukaceta amman dai tace zuwa nan gaba zata iya kasancewa damu “I don’t care kawai make sure bata samu aiki a koina ba a duk fadin garin nan, kai har karshen rayuwarta duk inda kuma aka dauketa aiki let me know .”
“an gama sir …ring din wayarsa yasa seun yayi shiru tare da daukar wayar ya mika masa cike da girmamawa Ya amsa ya manna a kunnensa tare da mikewa Ya qarasa jikin window office dinsa yana kallon haraban ma’aikatan yana amsa wayar ransa duk abace “daga can bangaren nana hauwa’u ta gaishesa “ ina kwana yaya ?”lafiya ya kike auta? “lafiya ! daman na kira na fad’a maka zan biya na d’auki maryam muje gaishe da mami “okay ! ya fad’a tare da katse kiran .”ya cigaba tsayuwa yana jin zafi aransa .”
Nana hauwa’u tayi shiru kafin daga baya ta mike tsaye ta kammala shirinta ta fito ta shiga mota kai tsaye hanyar gidansa ta dauka daman sunyi waya da maryam din itace ma tace ta kirasa ta fad’a masa a bakin kofar gidan ta tsaya ta kirata bayan ta fito ta shiga gaban mota suka dauki hanya suna tafiya suna hira maryam tace “sister ya zamanku da yaya hisham kuwa naji kwana biyu bakya magana akanshi “na gaji sister na kawo ido na zuba masu duk wanda yayi da kyau zai gani ina sauke duk abinda ya rataya a wuyansa na zamantakewa aure hakinsa ne ban tauye masa ba idan ya nema zan bashi ,idan bai nema ba huta roro zama haka maryam ta sauke numfashi tace “duk da haka dai ai naki da sauki tunda yana cin abincinki “eh to da sauki gsky Kinsan daman shi ba mai daukar abu da zafi bane kamar yaya bane .
“Ni dai gsky babu wani sauki a zamanmu dashi muddin yana gida bani da kwanciyar hankali sausaucin da nake samu dukkaninmu kuna kokari dani ,kuma na gode sosai da kulawarku ‘yanuwa allah ya bar zumunci amman ina jin tsoron ranar da zai hadu da wacce yake so yace zai qara aure ina rokon allah kafin zuwan ranar allah ya kasheni dan nasan bakincikin da zan qunsa yafi wanda nake qunsa yanzu “ babu wannna ranar for now mami fa tace muddin yana son qara aure sai ya kwantar miki da hankali shi kuma Kinsan halinsa da wahala ya kwantar da kai “kina ganin har yarinyar mafarkinsa in da zasu had’u mami bazata yarda ya aureta ba ?”yadda idan mutun ya mutu baya dawowa haka labarin wannan mafarkin nasa yake.”
Maryam tayi shiru tana tunani nana hauwa’u ta dafata tana cewa “don’t worry siater komai zai daidaita kinji “ naji amman rayuwarta abar tausayi ce baya son ganina baya son ko jin muryata idan ya ganni ko yaji muryata Kmr ya matu mgn kadan nayi yace na cika surutu ni yanzu dan allah ina da magana ?tai mata tmby tana dubanta girgiza mata kai nana hauwa’u tayi “wallahi bancin na bar gidansa mami zata shiga damuwa wallahi dana gudu,” ki gudu kije ina? kar ma ki soma muna tare babu inda zaki maryam ta girgiza kai tana jin zafi aranta sister wallahi baki san abinda nake hadiya bane .”idan kika tafi babu ni babu ke har abada zumunci mayi a lahira maryam tayi saurin goge hawyenn daya soma bin gefen idonta tare da cewa “ nima wasa nake babu inda zani muna tare mutu ka raba tafiyar mintuna ta kawosu bakin get din estate dinsu sukai hon masu tsaron get suka bud’e masu suka shigo sukai parking .”
atare suka nufi gidan mami suka kunna kai ciki tare da sallama a parlour’n suka iske Aunty shahida ,da Aunty khadija ,har ma da Aunty zabiba zaune sai mami da mamaki maryam ta bude baki cikin tsananin farinciki da gudunta ta kwaso bata zube gaban kowa ba sai a gaban aunty shahida ta ruqunqumeta tsam ajikinta tana cewa “wayyo allah babbar yaya naji dadinku daman sister kinsan suna nan ne ?ko daya yadda kika gansu yanzu nima haka nagansu ta zame jikinta ta durkusa gabanta “ina yini babbar yaya aunty shahida ta shafa fuskarta “ya kike maryam “lafiya lau .” ta isa gaban mami ta durkusa ta gaisheta cike da farinciki da girmamawa cike da kulawa mami ta amsa tana kallonta a tsanake “ dan tun washegarin tarewarta sai yau ta sake daura kwayar idanuna akanta “wallahi Allah mami jiya kasa bacci nayi saboda zan zo na ganki sai kuma gashi naga yan’uwana gabad’aya .”allah sarki maryam nima nayi kewarku sosai .”
Tayi murmushi mami ta cigaba da kallonta “tunda sister ta fad’a min zamu zo tare nake murna sai naga gari kaman da gangan yaqi wayewa don kada inxo na ganki” to gaki ga maminki kinganta cikin koshin lafiya “wallahi gashi na ganki kuma naji dadi sosai ai ni ina ganin ma na dawo kenan bazan koma wannan gidan mai kama da makabarta ba sai na kwana biyu “.nana hauwa’u ta zungurinta kan tayi shiru amma ina maryam bata fuskantarta ba mami ta miqe tsam ta basu waje dan tasan dole zasu tautauna a tsakaninsu .” mami na fita nana hauwa’u ta zubawa maryam duka a cinya wallahi ki rufa min asiri baki isa ki kwana a gidan nan ba yadda na dauko ki haka zan maidake gidanki “.
wajen da nana hauwa’u ta daketa take sosawa tana dariya tace “wallahi babu inda zani “kamar zaki iya bayan kina tsananin sonshi ? “kai nana hauwa’u ban da sharri wa ya fad’a miki son 'ya'yan take?inji zabiba ta fad’a tana murmushi nana hauwa’u tace “ai ni tuni na san da wannan ga tanan kuma idan ta isa ta karyata ,sister ban da sharri fa auren daaka samu na amince da kyar zaki zo kice ina son shi nana hauwa’u ta sake qara mata wani dukan maryam tace “babu komai wallahi koda da zafi ni banji zafin ba, dan bakya laifi ko kin kashe dan masu gida wani dan masu gida ?”yayanki ! dariya suka bushe da ita gabad’aya su Aunty zabiba tace "Kefa sabon iskancin mai lasisi kikaje kika koyo a gidan yaya “barta dole tayi iskanci da alamun taga gadon baccinsa shima yaya naga ya canza kwana biyu da alamun ya angwance inji cewar zabiba “.
wallahi ku daina fad’ar haka kar sautsayi ya shigo dashi mu shiga uku “ku dai shiga uku amman mu ai yayensa ne dole ya daga mana kafa dariya maryam ta saki har da tafa hannu “wannan kanin naku ai mami kawai yake d’agawa kafa hira suke sosai yayinda maakatan gidan suka cika gabansu da kayan marmarin da abinci da abun sha aunty khadija ta dubi auta “da alamun kin samu lafiya “alhamdulillah Aunty khadija rayuwar aure is not easy amman haka zamuyita hakuri har allah ya kawo mana sauki Ameen “ kefa maryam yaya zaman naku da uban shegu ?uhm ta numfashi “to da sauki zance amman ni matsalata mai girma ce kuma ban san ranar da zan fita ciki ba” ta qarasa maganar kamar zatayi kuka .”
Gabad’aya suka zuba mata ido cike da tausayawa “ita fa siater matsalarta mai sauki ce ba kamar ni ba da ko muryata baya son ji baya cin abincina kona girka sai dai masu gadin gida suci bani da kwanciyar hankali matukar yana gida , sister kuwa nuzla ce matsalarta amman ni zanyi maganinta “ki rabu daita huce haushi take akan hisham shi kuma rashin ganewa ne idan ba haka ba ko sauraranta ma yayi “inji cewar aunty khadija “allah ya kyauta daga nan Suka cigaba da hirar matsalolin rayuwa wani suyi dariya wani suyi jimami cikin haka aunty abida ta shigo daman ita tana yawon shigowa ko dan taji halin da ata yake ciki a wajen mami diyana da rukkaya suka shigo su kuma nana hauwa’u ce ta kirasu kusan duk yammatan gidan suka shigo aka sake bud’e habin hira banda nuzla har karfe shida ta buga suna tare ana hira .”
Ahankali motocin ata suka shigo haraban estate dinsu sakamakon kiransa da mami tayi suna gama daidaita tsayuwar motocin ya fito kamar ance ya kalli kofar gidan baba babba hisham ya gani tsaye tare da nuzla ya zuba mata ido kamar zai mata numfashi .”shiru yayi yana mamakin karfin halinsa ko bai ji kunyar kowa ba ai ya duba mami bare tsakaninsa dashi” ahankali nuzla ta kalli inda yake kallo d’aya tayi masa ta d’auke idanunta tana jin farinciki dan yanzu bata jinsa aranta haka ne ma yasa take son dandanawa jininsa wahala kuma har ga allah tana son ta auri hisham yanzu dan hishsm miji ne bancin yana kawo mata uzurinsa akan mahaifiyarsa da yanzu ta dade da kasamcewa a gidansa .”
daya daga cikin masu tsaron bakin get din ya dagawa hannu ya taho da sauri ya tsaya a gabansa cike da girmamawa “daman hisham na zuwa wajen nuzla ne ?Eh !ranka ya dade kusan kullum yana zuwa shiru yayi kafin daga bisani yace “okay zaka iya tafiya “ya juya ya koma bakin aikinsa shi kuma ya nufi kofar gidan mami yana kiran mb ,yayan mami suna shirin mikewa su kama gabansu har nana hauwa’u dan ita maryam mami tace ta zauna ATA zai zo sai su wuce tare suka ga mutun ya shigo kamar wanda aka jehoshi yana huci “gabad’aya suka mike tsaye suna kallonsa .”bai ce masu komai ba ya samu waje ya zauna akan kujera yayinda kannensa suka gaishesa amman yaki magana ya soma waya da yaya Ibrahim .”
Hankalin mami ya tashi ta qaraso garesa ta dafa shi tana tambayarsa “lafiya adamcy naga ka shigo wani iri ?still shiru yayi yaki magana ganin haka aunty shahida ,aunty khadija da zabiba har da nana hauwa’u sukai ma mami sallama zasu wuce muryarsa a kausashe ya soma magana cikin tsananin fushi “auta kar naga kin fita daga gidan nan kin dawo gida kenan .”gabad’aya suka dawo cikin tsananin tashin hankali suna dubansa “akan wani dalili kenan adamcy ?aunty shahida ta tambayesa “yayi shiru yana huci tamkar zaki “ka barta ta koma gidanta tayi zaman aure tunda suna zaune lafiya da mijinta “inji wa yace miki haka ?ya fad’a a zafafe yana fesar da hucin numfashi “zaku iya wucewa amman ita babu inda zata mami kam shiru tayi ta kasa magana “mami kice wani abu mana kinyi shiru kina kallonsa “aunty khadija ta fad’a tana dubanta “zaku iya wucewa zanyi magana dashi “
Suna shirin fita mb ya shigo dole tasa suka tsaya kallo d’aya yayiwa abokinsa ya fahimci akwai damuwa ya qaraso kusa dashi ya zauna yana cewa “yaakayi friend ! kace nazo yanzu yana qoqarin bud’e bakinsa yaya Ibrahim ya shigo “ya fesar da numfashi sannan ya soma mgn “mb daka shigo yanzu kaga hisham tare da nuzla ko baka gani ba ?“na gansu amman.” dakata mb “an tabbatar min kullum yake zuwa wajenta kuma nasan yana yin hakan ne saboda ne “.juya can ka kalli auta da kyau “haka aka kai masa ita ?yau zaa yita ta qare gidan nan laifin mai tayi masu ?idan laifi ne ,ni ne nan nayi saboda naki amincewa da soyayyar nuzla kuma nasan shine sila da dalilin son a kuntatawa auta tunda ni babu abinda zaa iya min ,dan haka yau zan kashe wannan aure .”mami ta sauke numfashi sannan ta mike ta bar wajen.”dan tasan halin d’anta wani irin murdaden mutun ne mai wuyar shaani ”
Yan’uwansa ma numfasawa sukayi domin wannan karon fad’an gasky yake da son kwatarwa kanwarsa ‘yanci amman sunyi mamaki wannan shine karo na biyu da ya nuna kulawarsa akan nana hauwa’u amman duk da haka bazasu bari ya kashe mata aure ba .”maryam ta kallesa taga yadda hankalinsa ya tashi akan yaruwarsa ya manta irin azabar da yake gana mata ,ya manta cewar itama diyar wani ce yake quntata mata hawaye ya cika idanunta tausayin kanta ya kamata ta kalli nana hauwa’u taga itama hawaye take ta kalli ata cikin sa’a idanunsu ya tsarke cikin juna tayi kamar zata girgiza masa kai amman wata katuwar hararar daya zabga mata mai had’e da kallon banza yasa ta d’auke idanunta akanshi ,tana mai share hawayenta da hannu ta qaraso kusa daita nana hauwa’u ta riko hannunta zuwa gefe “sister kinji hukunci yayanki dan allah karki yarda ya kashe miki aure saboda ya hisham mutumin kirki ne nuzla ce matsalarki .”
“bani da zabi sister bazan iya ce masa a’a ba duk abinda yake son ya zarta akaina na amince ni mai biyayya ce a garesa ,maryam ta rungumeta ajikinta “bakya son yaya hisham ne ?”to bazan ce bana jinsa araina ba , amman idan yayana yace na koma gidansa zanyi idan yace a’a babu inda zani “wallahi sister kina son mijinki “ta fad’a tana zare jikinta a nata ta tsura mata ido tana kallonta hawaye ne kawai yake fita daga cikin idanunta qirjinta har wani sama da kasa yake “ta riko hannunta tana cewa “ shi bai rike nashi auren ba zai kashe auren wasu muje ki fad’awa mami kina son mijinki nana hauwa’u taki binta ta zare hannunta ta rakube gefe tana share hawayenta dole tasa maryam ta dawo ta tsaya kusa daita tana share mata hawaye .”
mb ya kira layin hisham cikin kankanin lokaci sai gashi ya shigo yayi mamakin ganin mutane cike ya tsaya yana kallonsu d’aya bayan d’aya sai dai bai ga matarsa acikinsu ba , wani mugun kallo ata yayi masa sannan ya qaraso gabansa ya tsaya tare da jin kai ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa “baka son auta shiyasa ka zabi ka dinga quntata mata ta wannan hanyar ko ?hisham yayi shiru yana mai sunkuyar da kanshi kasa dan jin kunya “kasani nasani kowa yasani ban bada goyon bayan auren nan ba dan har yanzu bana son aurenku daita “cool down ata mb ya fad’a yana dafashi ya buge masa hannu yana qoqarin cukumar wuyan hisham yaya ibrahim ya shiga tsakaninsu “dan girman allah ka matsa “ babu inda zani ka samu waje ka zauna ayi magana ta natsuwa “idan har kaga na zauna to ya miko min takardar sakinta dan bazata qara zaman aure daahi ba har abada ya saketa yaje ya auri wacce yake so .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 12
Jin abinda ATA ya fad'a yasa maryam duk ta rud'e sai zufa take fitarwa hankalinta yayi matukar tashi gbdy ta nemi natsuwarta ta rasa domin tasan halinsa tunda ya furta zai raba auren lallai zai aikata hakan "ta fashe da wani irin kuka mai karfi , haka ma nana hauwa'u kuka take sosai , yadda maryam ta rud'e haka matan dake tsaye a wajen suka rud'e gashi babu damar yin magana .mazan kuwa sai faman bashi hakuri suke yana fixgewa mb ya fuskancesa sosai yana cewa "haba ATA ka kwantar da hankalinka abi komai ahankali "kasan allah muddin ina raye sai na kashe wannnan banzar auren ."
qanqame maryam nana hauwa'u tayi ajikinta suna mai fashewa da wani kuka cike da tashin hankali maryam ta soma magana muryarta na rawa "sister ke kad'ai ce zaki kawo karshen wannan matsalar "nana hauwa'u ta zare jikinta ta tsura mata ido ,idanunta na sake cika da ruwan hawaye . saboda babu mai fad'a ma yaya adam yaji sai ke a yanzu idan kika nuna masa kina matukar son mijinki shikenan magana ta qare dan dole zai hakura ya barku "nana hauwa'u ta girgiza mata kai "dan allah sister karki bari ya rabaku yaya hisham mutumin kirki ne ki tashi kiyi wani abu ta karashe mgnr tana kuka numfashi nana hauwa'u ta sauke tana share hawaye "bazan iya ba sister duk abinda yayana ya zaba min shine daidai ."haba sister haba sister !! karkice haka mana kiyi hakuri kiyi wani abu mana ta qarashe maganar tare da qoqarin mikar daita tsaye "
da kyar nana hauwa'u ta mike tsaye bisa kafafunta ta soma tafiya jikinta na rawa rawa taku biyar tayi ta tsaya cak ta kasa cigaba da tafiya hawaye na sake wanke fuskarta yayinda ata da hisham suka tsurawa juna ido kowannensu zuciyarsa na zafi cike da tashin ahankali ." hisham ya janye kwayar idanunshi cikin nashi ya tsurawa nana hauwa'u yana mai shafa kanshi abu d'aya zuwa biyu ne suka tsarga masa a tsayen da yake a gabansa ,abu na farko farinciki yadda Adam yaji zafi da ciwo acikin zuciyarsa ,abu na biyu kuma mahaukaciyar soyayyar nana hauwa'u da yaji yana bin jinin jikinsa tare da huda duk wani tsoka dake sansar jikinsa ,cikin wani irin sauri zuciyarsa ta dinga tsalle tana bugawa da matsanancin karfi kamar zata fito daga cikin qirjinsa hannuwansa duka ya miko mata alamun tazo garesa dan bazai iya rabuwa daita ba ."
ta kalli yayanta dake tsaye rike da kugunsa, ta waiga ta kalli yan'uwanta sannan ta kalli hisham da har lokacin yake miko mata hannunwansa gabad'aya nana hauwa'u ta nemi natsuwarta ta rasa ji take kamar zuciyarta zata buga sakamakon fad'uwar gaban data risketa ,haka ne ma yasa jikinta ya cigaba da rawa gashi yaya hisham yaki d'auke kwayar