Showing 96001 words to 99000 words out of 167047 words

Chapter 33 - Mar’adam’s Book 2 Hausa Novel Complete.txt

yaji da maggie "yayi mgnr  a matuqar fusace yana jan tsaki kana ya cigaba da bawa musa umarni yana gama wayar ya mike da kyar ya hau sama ,a bakin kofar d'akinsa yaga ta ajiye masa takalmansa ,ya bud'e dakin sannan yasa hannu ya kwashe  takalman ya shige dakin,wanka ya shiga bai wani d'auki lokaci ba ya fito bayan ya shirya kansa cikin  kananan kaya ya sauko ya zauna alokacin maryam tana tare da mami tana tmbayarta abinda zata girka mata "ki girka min duk abinda kike dashi  maryam zanci “ata ya zauna adaidai lokacin da maryam ta mike zata nufi kitchen muryarsa can qasan makoshi yace "ke.."!


Ta tsaya cak a natse tare da juyowa ta fuskancesa "karki dafa mata wannna banzan abincin naki “
mami na qoqarin bud'e baki musa  yayi knocking ya bashi izinin shigowa musa ya turo kofar parlour'n ya shigo cike da girmama ya gaishe da mami sannan ya rusuna ya gaishe da ATA ya ajiye ledodin hannunsa ya juya da sauri ya fice ."ATA ya janyo ledar farko dake gabansa  ya bud'e kamshi kifi tilafia ya doki hancin maryam wanda yaji kayan hadi da arish had'in  kabej  da sauri ta had'eyi miyo , ya tura takeaway gaban mami yana cewa  "sweetheart bismillah shiru mami tayi taki ci "tana son yi masa maganar abincin da ya hana maryam girka mata da kuma abincin da babu a gidan amman tana  jiwa maryam tsoron bala'insa dan haka dole itace zata kawo mata komai na bukata ta ajiye mata batare da saninsa ba "sweetheart eat !ni babu abinda zanci gida ma zan wuce mami ta fad'a tana haramar  mikewa nan take   ATA yace"a'a sweetheart  kiyi zamanki babu inda zaki "bangane babu inda zani ba ?"haba sweetheart ya kike magana hk kamar kina jin haushina ?saboda ke nasa akayi order abincin nan amman duk kinki ci komai ,nifa ban gane miki ba “idanu ta zuba masa tana kallonsa ta rasa wani irin mutun ne shi ,babu yadda zatayi magana bai canza mata magana ba dan haushinsa tana ji amman meye na fitowa ya fad'a mata ?"dan Allah sweetheart kici komai da nayi miki order "tunda kake dani ka ta'ba ganin naci abinci order ?"yayi shiru yana furzar iska “da kayi order dan ni nace mka zanci ne ?"kai kafi kowa sani bana cin abinci waje kuma kai ma akan haka na raineka ina da tabbacin ko kana cin abincin order sai dai idan baka qasar nan kai ya langwabar yana dubanta dan gskiya ta fad’a.”


“dan haka kafi kowa sanin bana cin abinci waje kuma kaima haka duk abinda nake so ina yi da kaina ko nasa kuku su dafa min amman dan ka wulakanta matarka kake wani aikawa a siyo maka abinci daga waje idan ma nata ne baka buqata ai zaka iya daukar mata kuku ko wane su girka maka acikin gidanka
Mami na fadar haka gaban maryam ya bada rasss "kuku a gidanta a'a ?ina bazai yuwu ba bata son kowa atsakaninta da mijinta tafi bukata ganin gidanta daga ita sai mijinta gabanta na fad'a uwa ta zubawa ATA idanunta taji abinda zai fad'a."ba d'aukar kuka bane matslata sweetheart" meye matsalarka adamcy fad'a min meye matsalarka?"ko kuku nawa zan d'auka basu ta'ba  min abinda sweetheart dina zata min ba"wani boyayyen ajiyar zuciya maryam ta sauke "haka mami yadda yayi maganar sai kuma taji tausayinsa ya lullubeta “duk abinci nan da nake order nake ci wallahi ina dai turawa cikina ne kawai amman maganr gsky ni abincinki nafi bukata fiye da kowani abinci a duniya, idan kina son na daina order  abinci sai dai idan zaki dinga mana kina aiko mana amman sai ta qara hade rai tana zabga masa harara ".



“Ai ba sakar uwa bace ni ,kayi aure yanzu dole ka canza adamcy ka koma kamar tsarin kowani ma gidanci “kai sweetheart ki ajiye wannan batun magidanci ko menene ni har yanzu empty nake jina “kai fa sam bakasan mutunci ba bakasan rarrashi ba bakasan meye hakin aure akanka ba allah ya gani nida mahaifinka muyi Iya qoqarin mu akanka mahaifinka mutumin kirki daya san darajan iyali kafi kowa sanin kirkinsa akan iyalinsa kai ne dai bamu san a inda kaje ka kwaso wannan halin ba tana kaiwa nan a zafafe ta mike saurin riko hannunta yayi cikin nashi "haba sweetheart wai laifin me nayi miki haka ?Kallonsa tayi ta tabe baninta "bazata lamunce wannan iskancin ba ko ya bari matarsa ta dinga girka masa ko kuma ya dauko mata masu aiki cikin biyu yayi d’aya “kiyi hakuri sweetheart idan wani laifi nayi miki  am very sorry ma zan d'auki masu aiki shikenan ki zauan kici wani abu sannan Kiyi zamanki kiyi  mana kwana  biyu ya zaunar daita kusa dashi mami yana shagwabe mata kamar wani qaramin yaro   tace "aa banzo da niyyar kwana ba koma zan kwana ban zo da  magungunan ba "wannan ai mai sauki ne ai sai naje na dauko miki ."


Yadda ya kwantar da kai yau yasa zuciyar mami ta sauko ta sausauta masa daman kuma tsakanin da d’a uwa d’an ma gilashi,ta sauke numfashi tace "karka damu zan dawo nayi maku kwana biyu in sha allahu amman yanzu gida zani "No sweetheart babu inda zaki kin ma dawo nan kenan ko kuma mu tattara kawai mu koma gidanki gabad'aya "dan murmushi tayi kamar ba ita tagama daukar zafi ba "kai adamcy ba dai rigima ba shikenan naji  zan kwana dan tunda ka nace sai dai a sallama maka amman gobe goben nan zan kama gabana maryam tayi murmushi har ta qasa boye farincikinta dan jin mami zata kwana suka cigaba da hira mami ta jawo  ledar gaban maryam ta bud'e mata "maza só ma ci duk an ramar dake abanza ATA ya saci kallon mami da alamun akwai magana abakinta “ aiko maryam kamar jira take ta soma cin abincinta hankali kwance tana cewa "kai gsky mami kici ko kad’an ne abincin yayi dadi sosai " ATA yaja tsaki "nonsense kawai kin iya cin na wasu kice yayi dadi amman idan cewa akayi Kiyi bazaki iya kamarsa ba sai dai ki kashe mutane da .."ya isa ya isa !! dan allah maryam tashi muje dakin ki kar a kashemu da gori suka mike suka soma qoqarin barin parlour’n.”


D’akin qasa suka shige suka barshi zaune ."basu jima da barin parlour’n ba ya fita ya bar gidan gabad’aya sosai maryam ta kasance cikin farinciki tare da mami basu bar farincikin iyasu kadai ba sai da suka rabashi dasu aunty shahida yayinda jifa jifa umma take kiran wayar maryam sai dai da zarar ta duba taga itace sai taki dauka dan bata son mami ta fahimci wani abu sallah ne kawai yake tashinsu daga hirar da suke . karfe bakwai ATA ya dawo har lokacin suna a d’akin ya shiga ya ajiyewa mami qaramar jaka da wasu ledodi wanda ko baa fad’a nama rago ne aciki dan tuni kamshinsa ya bayyana “ sweetheart ga magungunanki har da kayanki na hado miki dashi da naman rago “lallai adamcy yau abun ya motsa bai ce komai ba yasa kai zai fice daga d’akin tace “na gode allah yayi albarka .”yana zaune a falo yana kallon labarai suka fito tare da maryam suka hau sama har kusan karfe shadaya saura suna hira .”


cikin wani irin yanayi ATA ya shigo d'akin maryam wanda ranar ne karo na biyu daya shiga dakin ya tsaya yana kallon mami wacce fuskata ke kwance da annurin farinciki  tamkar mai koyan magana ya bude bakinsa yana wa mami sallama "Sweetheart ni zan shiga na kwanta  sai da safe  ya soma taku cikin isa da kasaita don barin dakin, cikin sanyi murya mami  ta kira sunanshi adamcy !d'an tsayawa yayi tare da juyowa suna fuskarta juna da mami  idanunta ta xuba mishi kawai Tana kallonsa tare nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sake sauyawa cikin dan kankanin lokaci meke damunka naga yanayinka haka ?"babu komai sweetheart "hakika mami  tafi kowa sanin koshi waye ta fannin halayyarsa da abinda ke tattare dashi bata rai mami tayi tare da ajiye wayar hannunta "meke damunka ?dan qaramin tsaki yaja "kaina Ke dan min ciwo shiyasa nake son na kwanta da wuri tunda taji haka bata sake cewa komai ba dai ina da sabo ta rigada tasa ba da rashin son hayaniyarsa daman shi mutun ne ba mai san hayaniya ba ballanantana gashi yau tasashi magana "allah ya tashemu lafiya ta fad'a adaidai lokacin daya kusan fita daga dakin "kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ,yasoma cire kayan jikinsa yaja towel ya daura Tare da shigewa bathroom ya sakarwa jikinsa shower byn ya gama wanka ya dauro alwala yana fitowa bai wani tsaya shafa mai ba ya bude wordrob dinsa sai kamshi turaren ne ke tashi a gurin , ahankali yasa hannu ya zaro jallabiya milk colour ya zira a jikinsa ba qaramin kyau ta maisa ba ya qarasa inda daddumar salla take ya dauka ya shimfida shafi’I da wutiri ya gabatar sannan yayi addua ya mike batare daya nade daddumar ba ya zare Jallabiyar jikinsa yayi fillinging daita ya sanya vest da boxcer ya canza wutar dakin zuwa mara haske ya d’auki remut ya qara karfin ac sannan ya fad'a Kan bed dinsa ya lullube jikinsa da bargo mai taushi ."



Bangaren mami kuwa har karfe shabiyu ta buga suna tare da maryam wacce bacci ya soma daukarta kasa kasa ta soma kiran sunanta "maryam ki tashi kije dakin mijinki mana kema fa na fahimci baki kulawa dashi kamar yadda nake zato maryam ta mike ta zauna tana duban mami da fuskarta da d’an mamaki ,sosai mami ta shiga mata fada tare da bata shawarar hanyoyin da zatabi gurin shawo kan mijinta cikin sauki , sosai jikin maryam   yayi sanyi likis ita kanta tasan" inda mami  bata kasance yar,uwa,ce ga mahaifinta  ba ,hakika bazata dinga damuwa akan damuwarta ba kullum burinta ta gansu suna zaman lafiya tare da nusar daita yadda zata sake mallakarsa a tafin hannuta cikin ruwan sanyi batare da biye biye ko wani abu ba, hakika mami dabance acikin mutane km zuciyarta may kyau ce ba kmr  irin ta mahaifiyarta ba  km gashi Allah yayi ta may tsananin zumunci ce mami takarasa zanceta " da maza tashi ki sake shirya kanki kije ki kula da mijinki "km cire wannan tsoron nasa da nake hangowa acikin kwayar idanuki da kyar maryam  ta samu ta mike tana may dagawa Mami kai alamun taji .”


Gaban mirrow dinta ta qarasa ta feshe ilahirin jikinta da turaruka masu sanyi kamshi sanna ta dauki hijab ta daura a saman rigar baccin dake jikinta ta fito zuwa dakinsa sai datayi addua sannna ta tura kofar dakin ta shiga ."acikin hasken da bai gama haskaka dakin ba ta hangosa kwance cikin bargo ahankali ta dinga daga kafafunta dan kar mostinta ya tayar dashi ta dan tsaya gabansa tana kallon kyakkwar fuskarsa ahankali yake sauke numfashi inda tasan mami zata bukaci tazo dakinsa data zuba masa magani acikin coffe ya sha ta samu natsuwar kwana tare dashi cikin salama ta zare hijab dinta ta ajiye bayansa ta  zagayo ta hau saman gadon ta dan yaye bangon dake lullube dashi ta kwanta bayan ta cire hijab din jikinta bai motsa ba  hakan yasa tayi tunanin baccinsa yayi nisa ta sake matsosa tana shakar kamshi jikinsa da kamshin turarensa. jikinta daya hadu danashi yaji kamar an ta’ba shi da wuta yayinda ita kuma sauyin yanayi taji a ilahirin jikinta kusan awa daya da wani abu suna kwance haka yadda bata runtsa ba haka shima bai runtsa ba .”


Zuciyarta ce ta bata kwarin gwiwar kai hannunta jikinsa ta soma shafasa tana aika masa wasanni stil bai motsa ba kuma bai ji komai ba sai tarin bakinciki mamaki da karfin halinta ya kamata shi Kmr ya tashi ya rufeta da duka amman ya kyaleta saboda darajan sweetheart dake gidan ganin bai motsa ba yasa maryam tayo kasa da hannunta daidai kasan marasa nan ne fa yaji bazai iya barin ta cigaba da iskancinta data tsiro dashi ba a yau ,zaraf ya damke tsintsiyar hannunta tare da jijiyo ya zabura ya mike zaune tamkar wani zaki mikewa tayi zaune Kmr yadda yake ,kallon da yake mata yasa qirjinta dokawa da sauri sauri saboda kallon ne mai tattare da tsana da gargadi ."a matuqar tsawace yace "uban wa yace ki shi go min daki ?kinga nayi kama da wanda zaki ta'ba? Ko jikina saanki ne ?yayi mata tmbyr ajere nan da nan yasa maryam ta gigice "tmbyarki naki "tayi shiru wallahi komai zaki min bazan ta'ba jin komai ba saboda bana kallonki amatsayin mace kmar yadda nasha fad’a miki idan kika sake gangancin kai hannunki jikina wallahi sai cakawa zuciyarki wuka .”kallonsa tayi da bayananen tsoro “wannan ya zama karo na qarshe da zaki shigo min daki domin har abada bazaki zamo abokiyar rayuwata ba jikina ma bazaki samu ba bare zuciyata fuskarsa babu annuri ya nuna mata  kofar fita oya get out from this room kafin na miki mugun bugu cike da sanyi jiki ta rarumo hijab dinta ta soma qoqarin jirawa ajikinta sai dai ta kasa fita daga dakin tana tunanin me zata koma tacewa mami ganin taki fita ya sauko ya kamo hanuta bai tsaya wata wata ba ya soma janta ya bud'e kofar tare da hankadata waje da sauri ta tokare hannunta da bango batayi mamaki ba dan tasan zai iya aikata fiyye da haka ."


Makalewa tayi a bangon koridor hawaye masu dumi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta ta goge shi kuwa rufo kofarsa yayi ya murda key a galabaice ya fad'a bed dinsa ya runtse idanushi ya sake jan laulausar bargo ya lullube jikinsa maryam kuwa natsuwarta take qoqarin daidaitawa amman ta kasa dan hawayenta ya gagara tsayawa bata koma dakinta ba sai wajen karfe daya wanda a tunaninta zuwa  wannna lokacin  mami tayi bacci sannan ta nufi dakinta tana danne sheshekar  kukanta Koda tashiga dakin mami na kwance , maryam ta haye saman gado ta kwanta lamo abayan mami tare da kamkame jikinta wani irin kewa da son mijinta ce ke damunta amman shi babu halittar daya tsana kamarta , kuka take son yi dan rage damuwarta amman bbu dama domin damuwarta zata iya haifawar da mami damuwa , a dalilinta mami zata iya muzgunawa yaya Adam , ita km abinda bazata so ba kenan, batason abinda zai sake hassalashi akanta
ta kai hannunta ta dafe daidai satin zuciyarta dake mata ciwo bayan Kmr minti goma mami ta tashi zaune ta dubeta tana mata kallon tsab batare da tayi magana ba sannna ta sauko ta shiga bayi ta dauro alwala ta fara gabatar da nafilflii .”


" juyi tayi tare da sake kamkame jikinta “yanzu ita yaya zatayi da rayuwarta ?”mayye zatayi ?”ga soyayyarsa ga tsananin sha,awarsa duk sun taru sun hade mata ,take zuciyarta ta bata amsa da kima kama kanki da rashin hakurinki dan muddin kikayi kuskure sake zuwa inda yake zai iya kasheki tunda har ya rantse “ya allah ka taimakeni kasa na samu ciki a karon mu na biyu dashi yanzu ta shiryawa kowani rigima zaiyi idan ciki ya bayyana ajikinta a boye take goge hawayen dake bin kuncinta ,har mami tagama tayi laziminta da sauran addu'o,inta
.bacci bai yi nasarar daukar maryam ba kuka take qasa qasa . Tana jin motsin mikewar mami ta shanye kukanta Tare da goge hawayen idanunta amman hakan bai hana mami gane wani abu ba ,daidai inda fuskarta take tazo ta zauna tare da kamo hannuta ,"me kike tunanin maryam ko kuma nace me ya dawo dake dakin nan har ya hanaki bacci ?


Kafin maryam tace wani abu mami ta km jiho mata wata tmbyr “sai ma naga kmr kuka kika yi ko?
Maryam ta Mike zaune suna fuskartan juna da mami ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka yi nasarar zubowa...."mayye km abin kuka tmbyrki kawai nayi fa? sai km ki kama min kuka.” wani abu adamcy yayi miki ?ahankali ta girgirwa mami kanta “ki fad’a min idan wani abu yayi miki da kyar maryam ta iya bude bakinta ..." ammi me yasa yaya Adam ya tsaneni haka ?kullum so nake naga na rayu dashi har qarshen rayuwa amman shi kullum burinsa ya ruguza rayuwar gidan aurenmu da ni kaina bansan yadda zanyi abubuwa su dawo min daidai tamkar kowasu maurata ".


“basan abinda na aikata masa ba da kullum yake son ganina cikin qaqa na kanyi .Ida abubuwa da yake min suka cigaba da faruwa bana tunanin zuciyar dake kirjina zata cigaba da bugawa , mami tambayar min shi laifin me nayi masa ?”wallahi ni ina qaunar zama dashi muddin raina .”mami ta rungumeta ajikinta tana mai tausaya mata "kukan ya isa haka babu abinda kika masa halinsa ne haka
halin bakar zuciya irin tasa yana damuna ni kaina na gaji da halinsa ,amman matsawar Ina raye ba zaki taba kasancewa cikin bakinciki ba , bugu da qari har yanzu kina da sauran damar rabuwa dashi dan bazan cigaba da baki hakuri ki cigaba da zama dashi ba dan duk wani abinda zaa masa anyi masa idan dai ba rayuwarmu yake nema ba .”



Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login