Showing 27001 words to 30000 words out of 157423 words

Chapter 10 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

538

                16.

Nu'aymah ko da kallo ta bisa har sai data ƙurewa ganinta tana jin babu daɗi a ranta akan abinda ya yiwa ƙawar tata, sai dai duk da haka bata ji tana jin haushinsa a ranta ba sai ma wani irin kishinsa da taji ya taso mata na tafiyarsa da yai tare dasu Billy, a hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta juyo tana maido kallonta wurin da Janaam take, mamaki ne ya kasheta ganin bata wurin kafin ta tako wajen tana kiran sunanta, "Janaam, Janaam, Janaam..Ina kike ne?" Ta ƙare zancen tana leƙawa wani common room dake cikin wajen, sai dai anan ɗin ma bata gane taba, wajen masu kula da serving ɗin mutane ta nufi wajen wani saurayi tana cewa, "Bawan Allah don Allah ina wacce ke wajen can tsaye tayi?" Ta nuna masa inda suke zaune ɗazu, ya ce. "Ai tun ɗazu tabi ta wannan ƙofar ta fice". ya nuna mata ɗayar ƙofar da mafi aksari masu aiki wajen suka fi amfani da ita don dama kofa biyu ne a wajen, da sauri Nu'aymah ta fice tana fiddo wayarta a jaka ta shiga gwada kiran Nu'aymah, ringing tayi har ta tsinke bata ɗaga ba Nu'aymah ta ci gaba da tafiya tana sake gwada kiranta a karo na biyu, nan ma ɗin har wayar ta tsinke Janaam bata ɗaga ba, da sauri ta nufi department ɗin su ko zata sameta a can, cikin ikon Allah tana kawowa zata shiga ajin sai ga Janaam ta fito ɗauke da jakarta data ɗakko, saurin riƙo hannuna Nu'aymah tayi tana dawowa ta gabana. Na runtse idanuwana jin saukar hannunta a jikina saboda nasan haƙuri ne zata bani, sai dai duk da sanin da nake dashi cewa ba ita tayi mun laifin ba idan nace bana jin haushinta itama a wannan lokacin nayi ƙarya, saukar muryarta a cikin kunnuwana da nayi bayan ta dawo a gabana ya sani buɗe ido na ina juyar da kaina gefe. "Please Janaam ina zaki je? Don Allah kiyi haƙuri da abinda Umar Farouk ya yi miki, wallahi nima abun bai yimin daɗi ba". Ta faɗa cikin karyewar murya don har rawa muryarta keyi, na sauke ajiyar zuciya sannan nasa ɗaya hannuna na cire hannunta dake riƙe da nawa ba tare dana tanka mata ba na raɓa ta gefen ta na wuce, "Ya Salam! Don Allah Besty kada ki hukunta ni akan laifin daba nawa ba, na ji zai iya yiwuwa ta wani ɓangaren ina da laifi amma in kin lura shima zaki yi mini uzuri akai". Ban tsaya sauraren ta ba kawai na wuce abina dama kwana biyu na dena jiranta idan zan zo school ko kuma idan aka tashi saboda matsalar data faru ranar da bana so taci gaba da faruwa mutumci da kima ta na zube wa a banza, nakan hau abin hawa nayi tafiyata idan aka tashi ko kuma Ya Jameel ya kawo ni tunda sassafe idan zai fita wajen aiki, ranakun da kuma bana da lecture da safe sai zuwa ƙarfe goma ko sha biyu nakan hau adai-daita ne ya kawo ni haka ma idan aka tashi, Nu'aymah ko tayi ban hakuri har ta gaji dole ta zuba mini ido saboda na nuna mata hakan nake da ra'ayi yanzu don tsira da mutunci na. Kai tsaye wajen gate na nufa don gabaɗaya a jiƙe nake bazan iya ci gaba da zama school ɗin a haka ba duk da ina da wata lecture ɗin gaba, tsanar sa ce mai tsananin ƙarfi ta sake shiga zuciya ta lokacin dana tuna da hakan hawaye na sauko mini a fuska, da sauri nasa hannu na goge ina tare mai adaidaita, bayan ya tsaya na shiga  ya ja yabar wajen ina sanar dashi inda zai aje ni.

Umar Farouk ko jin yai har yau bai cire haushin Janaam ba aransa tunda har ta iya ɗaga hannu karo na biyu tace zata maresa, kenan hakan na nufin duk abubuwan daya yimata sun tafi a banza tunda har basu saka mata jin tsoronsa ba, zaune yake tare da yan matan kowa an kawo masa abinda zai ci, tuna hakan yasa ya ture abincin gabansa nasa cike da ɓacin rai ya mike ya fice ya ja motar sa yabar wajen aguje, kallon kallo suka shiga yiwa juna, cikin gwarancin Hausa da bata gama zaunawa a bakin Felicia ba tace. "Na sane yaron can, tunda sir ya hadu dashi ya canza mana gebadaya". Billy ta saki tsaki haɗe da miƙewa ta bi bayansa, sai dai tana fita taga har ya ja motarsa ya bar gun, dawowa tayi tana kallon su ɗaya bayan ɗaya kafin ta saka dariya tana taɓe baki tace, "To yan wahala sai a fito da kuɗi abiya don Umar Farouk ya yi tafiyarsa, duk wata shegiya mai shigewa gaban mota tana yi mana kuri da iyayi yau sai aje a hau mashin a koma inda aka fito".  Ɗaya daga cikin su ce tayi tsaki kafin tace, "Ai ke ma ɗin yar wahala ce ba mu kaɗai ne yan wahalar ba". Billy ta sake kwashewa da dariya data kalli fuskar Felicia, tasan daƙyar in tana da kudi a jikinta da zata iya biyan kuɗin abincin har su maida ita school, aranta tace "Shegiya yau zamu yi maganin ki". Dama dukkansu haushinta suke ji ganin tafi zama very close da Umar Farouk, ko abu zai basu kusan ita yake kira yaba yace su raba, dawowa Billy tayi ciki ta zauna tana ƙarasa cin abincin ta hankali kwance kafin ta shiga raɗa masu magana cikin kunnuwa ɗaya bayan ɗaya amma banda Felicia, gaba daya suka sa dariya suna tafewa alamun sun gamsu da maganar da Billy ta faɗa masu, "what?" Felicia ta faɗa tana bin su da kallo, da sauri Billy na ɗaukar lemun dake gabanta ta miƙe tana cewa, "Nothing ke dai ci gaba da cin abincin ki mu zamu wuce".  Felicia tace, "ha'a wait for me mana". Wata cikin su ta sake cewa, "No we we're finish our own, so when you finish your own zaki iya biyo mu baya don baza mu iya jiran ki ba kin san muna da lecture". "Ok wa ze biya kudin kenan?" Felicia ta faɗa tana kallon su, Billy ta zaro idanuwa tana cewa, "Oho wa zai biya kuwa! Mu zamu je mu biya namu kema idan kin gama ki je ki biya naki". Felicia ta kalli biyu daga cikinsu suma Christian ne tace, "Abeg ku jirani mana kun ji". Suka yi mata wani kallo suka yi gaba abun su ba tare da sun tanka mata ba, ƙyalesu tayi taci gaba da cin abincinta hankali kwance don tana da yan canji a jikinta da tasan zasu iya biyan kuɗin abincin, sai dai fa idan ta basu ba tada na abun hawa da zata hau ta koma school. Tana kallon su suka nufi wajen payment sannan suka wuce, Felicia bata san me suka kulla mata ba, ashe ko da suka je cewa sukayi tare suke da ita itace zata biya kuɗin duka su zasu jirata a waje ne, su kuma ganin duka tare suka shigo yasa suka amince da zancen su ganin ba yau suka saba zuwa wajen ba, Felicia na gama cin abinci ta je wajen biya aka miƙa mata bill gaba daya kusan dubu goma sha biyar don dukansu abincin 3k ko wanensu yaci, zaro idanuwa tayi ganin adadin kudin da suka bata tana cewa ita nata kaɗai zata biya, suma ba tada complete dubu ɗaya da ɗari bakwai kaɗai take dasu, ta ciro kudin ta cikin aljihun wandonta tana miƙa masu tare da basu hakuri tana faɗa masu cewa ba ita zata biya kuɗin ba kowa shi zai biya nasa, nan fa rigima ta kaure tsakanin su da ita aka riƙeta akace lallai babu inda zata je sai ta biya kuɗin ko su riƙe wayarta da suka karɓe, magiya ta shiga yimasu amma suka ƙi saurararta wasa-wasa rigima ta kaure tsakaninsu ita tana faɗin su bata wayarta su kuma suna cewa ta biya kuɗin mutane sannan su bata wayar, duk wani turancin Felicia da bagwariyar hausar ta sai da suka ƙare wajen basu haƙuri amma suka hanata wayarta, ta samu waje gefe ta tsaya tana tunanin ya zatayi, gashi tace su bata wayar ko Umar Farouk ɗinne takira ta sanar dashi halin da ake ciki amma suka ƙi saboda suna tunanin zata iya guduwa, ai kuwa haka akayi bayan kusan awa ɗaya Felicia na tsaye taga sun ajiye wayar agefe tayi saurin kai hannu kafin su ankara ta wafce wayarta ta ruga da gudu, ihun ɓarawo suka shiga yi mata tana kaiwa waje wasu samari suka tare ta, basu tsaya saurarar komai ba suka rufeta da duka, nan take aka sauya mata kamanni kafin kace me an kira yan sanda suka dauki Felicia suka wuce police station da ita fuskarta tayi suntul saboda dukan data sha, ga bakinta ya fashe da gefen ido sai jini ke faman zuba...

WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE

070404042435, GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUƁEMU A WANNN LAMBAR DON YA MALLAKI NASA.

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            17.

Report yan sanda suka fara ɗauka tayi masu bayanin komai, jin ko ɗan gidan waye shi wanda ya kaisu waje yasa basu ɗaga case ɗin ba sai dai suka kira number mahaifinsa suka sanar dashi halin da ake ciki.

Duk inda ransa yake ya yi mummunan ɓaci, dama yana sashen kishiyar Momy uwar gidansa, ya miƙe ya nufi sashen na Momy ya shiga gidan a hasale yana kwalawa Umar Farouk kira, da Momy ya fara cin karo cikin ɓacin rai yace, "Ina wannan shashashan yaron naki yake?" "Yana ɗakinsa, Ina ga bai da lafiya don tun bayan azahar daya dawo makaranta ya shige ya kulle kansa bai sake fitowa ba, Amma lafiya irin wannan kira haka Dady?" Momy ta faɗa tana kallonsa, Dady bai tsaya bi takan ta ba yasa hannu ya jayeta daga gabansa ya nufi dakin na Umar Farouk, yana tura kofa ya jita a rufe ya shiga buga ta da ƙarfi yana faɗin, "kana ina ne? zaka buɗe kofar nan ne kafito ko sai na buɗe da kaina na sameka aciki na tattakaka". Yadda yake dukan ƙofar da ƙarfi yasa Umar Farouk dake barci ya tashi, da sauri ya sauko kan makeken gadon nasa ya fito daga bedroom ɗinsa ya nufi kofar palourn yana murza idanuwa ya buɗe, yana buɗe ƙofar Dady ya ɗauke sa da marin da bai san lokacin daya ja baya ba, hakan yaba Dady damar shiga cikin dakin nasa yafara yi masa faɗa yana cewa, "Tir dakai Umar Farouk ban taɓa tsammanin cewa shashancin ka har ya kai hakan ba, ni zaka je ka riƙa zubar wa da mutunci a gari? Yar gidan waye kaje ka ɗauka ka kai wajen cin abinci ka baro ba tare daka biya kuɗin ba har aka kamata aka ci zarafin ta saboda kai?" Umar Farouk ya yi shiru ya kasa cewa komai, sharabonsa da mahaifinsa yasa hannu ya dake sa har ya manta don bazai ma iya tunawa ba tun daga kan ƙuruciya har zuwa girmansa, iya kacinsa da mahaifinsa ya yi masa faɗa amma sai gashi yau ya ɗauki hannu ya maresa ba tare da sanin laifinsa ba har sai daya furta, gaba-daya ya manta da zancen baro su Felicia da yai agidan cin abinci saboda takaicin Janaam da yake ji, ya manta kwatakwata da bazai bar wajen sai ya biya kuɗin ko kuma daga baya ya tura ma Felicia ta biya, tabbas wannan ba mahaifinsa kaɗai ba har shi anci mutuncin sa, amma kuma me ya hana su su saka kuɗinsu su biya tunda sun san yafi ƙarfin ko nawa ne kuma zai iya basu lunkinsu daga baya,  amma shine suka zaɓi tozarta shi da su biya kudin to idan haka ne meye amfanin su a wajensa? Ya tambayi kansa kafin yaji Dady ya sake jeho masa wata tambayar a tsawace, "Wace yarinya ce nace?" "Ban san ko wacece ba a cikin su". "Very good! Wato yawan yan matan shashancin naka ma ya kai har bazaka iya tuna ko wacece ba daga cikinsu? Shikenan Nagode Umar Farouk da irin sakayyar da kake yi mini a matsayina na mahaifinka da kasan matsayina acikin wannan garin". Yana gama faɗar haka ya juya zai fice Umar Farouk yai saurin bi bayansa yana faɗin, "Dady ba haka bane Please..." Cikin wani irin ɓacin rai Dady ya juyo yana ɗaga masa hannu tare da nuna sa da ɗan yatsa yana cewa, "Mintuna talatin na baka kayi gaggawar zuwa kafito da yarinyar mutane, idan ba haka ba zakaga abinda zanyi maka". Yana gama faɗar haka ya juya ya bar wajen cikin ƙunar rai, da sauri Momy dake tsaye wajen ta janye ya wuce sannan ta shigo cikin dakin tana kallon Umar Farouk ya kasa motsawa daga inda yake tsaye, hannunsa ta riƙo ta zaunar dashi bisa kujera tana cewa, "Ya akayi haka Umar Farouk? Ba kada kuɗi ne da zaka kaisu wajen cin abinci ka kasa biya." Bai iya cewa komai ba Saboda ransa ya yi kololuwar ɓaci, dama tasan bazai yi magana ba tunda tasan halin abunta don haka taci gaba da cewa, "Koma dai meye baka kyauta ba, akwai ɓacin rai  acikin wannan abun daka aikata da kuma nuna gazawarka, ka tashi kaje kayi abinda mahaifinka yace". Umar Farouk ya miƙe ba tare daya ce komai ba ya shiga bedroom ya ɗauko wayarsa da key ɗin mota ya fice, Momy na jin yadda ya tada motar ya fice aguje ta bishi da addu'a tare da nema masa tsari a duk inda zai je, a maimakon Umar Farouk yayi abinda mahaifinsa ya sashi kai tsaye sai ya wuce gidan cin abinci, yana shiga ya nemi a gwada masa Manager ɗin wurin, baya nan sai wanda ya barwa kula da wajen kafin ya dawo, wanda shine ya kira police suka tafi da Felicia, ba tare daya tsaya wani abu ba kai tsaye ya tambaye sa waye yasa akama yarinyar ɗazu da bata biya kudin abinci ba ya amsa da shine, bai tsaya wata ba tun kafin ya rufe baki ya daukesa da mari sannan ya fiddo ATM ya jefa masa yana cewa ya cire kudinsa ko nawa ne, cin mutumci ya yi masa sosai kafin yace, "Kuma ka tabbata duk abinda ya sami yarinyar nan sai ka kuka da kanka". Yana gama faɗar haka ya ja ATM dinsa da suka ajiye bayan sun cire kuɗinsu sannan ya fice daga wajen. Ja yai ya tsaya tunawa da bai san a wace Police station ɗin ce aka kama ko wacece ba a cikinsu, juyowa yai da hannu ya kira daya daga cikin ma'aikatan wajen da gaba-daya suka sha jinin jikinsu, ya zo a ɗaɗɗare cikin girmamawa yace, "Ranka shi daɗe gani". Tambayarsa yai wace police station ɗin ce aka kai yarinyar ya faɗa masa sannan ya sallamesa, wajen motarsa ya nufa ya shiga ya tayar ya nufi Police station ɗin, wanda ya karɓi case ɗin baya nan sun tafi wajen wani case ɗin da aka kirasu sai dai ya isko wani wajen, fuskarsa a haɗe ya yi masa bayanin yarinyar da yazo beli, kallon ƙasa da sama ɗan sandan ya shiga yi masa kafin yace. "Kune yan iskan samarin dake daukar yaran mutane kuna lalata dasu kuma ku gudu ku kasa biyan kudin inda kuka je ku ka k.." bai ƙarasa ba Umar Farouk da dama a hasale yake ya kai masa wani naushi a baki, wasu yan sandan ne suka yo wajensa da niyar rirrike shi ya ɗago ya watsa masu wani irin mugun kallo daya sa suka ja da baya, don gaba-daya ya rikece masu ya koma tamkar ɗan ƙaramin zaki, jin hayaniya yasa dpo fitowa, ganin abinda Umar Farouk ya yiwa yaransa yasa ran shi ɓaci, mahaifinsa ya kira ya sake kora masa bayanin abinda ya zo ya aikata tare da tabbatar masa da cewa ba don yana ganin mutuncin shi ba da yasa shima an rufesa bisa laifin faɗa da hukuma har cikin wajen aikinsu, Haƙuri Dady ya shiga bashi duk da irin matsayinsa Kafin yai masa godiya bayan ya tabbatar masa da za'a bashi belin yarinyar yanzu.

Bayan sun gama wayar dpo ya kalli Umar Farouk yace, "Idan kai tsagera ne hukuma dai-dai take da kai, mutuncin mahaifinka yau ya kwace ka a hannunmu, amma idan ka kuskura ka sake shigowa hannunmu to ka kuka da kanka don sai ka yabawa aya zaƙi". Ya kare zancen tare da yin rubutu yasa aka fito da Felicia da ko gane fuskarta ba'ayi saboda dukan data sha, littafi aka turo masa yasa hannu, ya dauki biro ya yi signing sannan ya juya ya fice daga police station ɗin, yanayin da yaga Felicia aciki ya sashi kasa daukar kowane hukunci a kanta, jiranta ya yi acikin mota har ta fito, a yadda ta ganesa yasan yau sai buzun ta idan ya rikata don sai yayi mata wulakancin da bata taɓa tsammani ba, hakan yasa ta kasa matsa wa wajen motar tayi tsaye, ga mamakin ta sai taga an buɗe gefen seat ɗin mai zaman banza a gaba, jiki ba ƙwari ta ƙarasa wajen ta shiga ta rufe ya figi motar aguje ya bar wajen, "I'm sorry sir." Ta faɗa cikin sanyin murya, jin bai ce komai ba yasa ta fahimci me yake nufi, nan ta shiga yi masa bayanin abinda ya faru, juyowa yai ya kalli fuskarta, wata Chemist ya nufa da ita aka dubata aka bata magani, ya fiddo da kuɗi masu ɗan yawa ya bata sannan ya fice ya ja motar sa yabar wajen yana jin sai ya yiwa su Billy abinda basu taɓa tsammani ba, a ɓangare ɗaya yana kallon Janaam a matsayin wacce ta haifar da duka matsalar (Ni kuwa nace taya malam Umar Farouk?🤔...

*******

A yau wuni nayi duk wani motsi nawa ina tuna abinda ya faru dani, dana rintse idanuwa ina hango

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login