Showing 6001 words to 9000 words out of 157423 words
kauda kaina gefe, "Morning Janaam". Na ji muryarsa ta daki kunnena duk da maganar yayita can ƙasan maƙoshi tamkar baya son maganar. Ban iya amsa shi ba don nasan ya yi hakan ne saboda ban gaishesa ba. Shiriyar ajiyar zuciya ya sauke a sirrance yana sake riƙe steering wheel ɗin motar haɗe dayin gyaran murya yace.
"Aymah meke damun ƙawarki ne? Ko azumin magana take yi?" Nu'aymah dake baya ta turo baki kamar zata yi kuka tace, "Don Allah Ya Nu'aym kabar wannan maganar ka taka mota, wallahi mun kusa makara kuma duka laifinta ne". Nu'aym ya sake juyowa yana kallona, ni har mamaki yake bani yadda yake son kallon nawa duk da rufe fuskata take, ƙasa nayi da kaina ina wasa da yatsun hannuwana naji yace, "Wai haka ne Janam?". A maimakon na amsa masa sai na tsinci kaina da cewa, "Please Ya Nu'aym mun makara fa?" "Am sorry". Ya faɗa yana ɗan taka motar, da haka muka iso school, yana yin parking Nu'aymah ta ɓalle marfin motar tafita tana faɗin, "Bye Ya Nu'aym" "Bye Aymah". Ya faɗa yana ɗaga mata hannu, na ɓalle marfin zan fita Nima yai saurin dakatar sani ta hanyar cewa, "Janaam ina son yin magana dake, gashi tun da na dawo ƙasar nan banda wani lokacin kaina kuma jibi zan koma". "Kayi haƙuri muna da lecture yanzu in ba so kake a hanani shiga ba kaga Nu'aymah har ta wuce abunta ta barni". Daga haka ban jira cewar sa ba na fito na nufi cikin hall ɗin da zamuyi lecture, ina jin idanuwansa akaina amma ban iya juyowa har na shige ciki, Alhamdulillah ko da na shiga har lokacin malamin da zai mana lecture bai zo ba, na zauna ina sauke ajiyar zuciya haɗe da mamakin to wace magana yayan Nu'aymah ke son yi dani.
Bayan mintuna biyar da zamana sai ga malamin ya shigo yana bamu hakuri akan delaying da yayi, awa biyu muka dauka muna lectures kafin ya gama ya fita, bamu fita ba sai da Nu'aymah tasa na sake yi mata bayanin karatun da muka gama sannan ta ɗago ta kalleni tana cewa, "Janaam muje capteria wlh yunwa nake ji". Kusan haka take a wajena yunwa nake ji sosai, don haka muka mike tare muka fito, muna fitowa idanuwana suka sauka akan Umar Faruk a can gefe shi da ƙawayensu da duka mata ne sai abokinsa namiji ƙwaya ɗaya riko, yan matan sun zagaye su sai fira suke yi suna dariya shi kuma yana tafewa dasu, kallo ɗaya nayi masu na janye idanuwana saboda a kaf faɗin makarantar babu wanda na tsana kamarsu, bani ƙaunar abinda zai haɗa ni dashi koda kuwa alkhairi ne saboda yadda ya ɗauki kansa acikin makarantar, baya ganin mutuncin kowa kuma baya shakkar wulakanta kowa cikin mutane, ciki kuwa hadda malamai saboda yana ɗan ɗan wani babban attajirin mutum dake faɗa aji a gwamnati mai ci yanzu, mata sune abokansa aduk inda yake baka rabashi dasu, yana taka duk wanda yaso sannan ya daukaka wanda yake so ba tare da an taɓa dakatar dashi ba a makarantar, duk da wuɗannan ɗabiu nasa kuma ba kaɗan 'yan mata ke sonsa ba saboda kyan da Allah yayi masa da kuma iya wanka, uwa uba tarin arziki da yake dashi da kana kallonsa zaka san shi ɗin ba ɗan gidan ƙananan mutane bane. Umar Faruk wankan tarwaɗa ne wato chocolate colour, yana da manyan idanuwa masu launin ja kuma a shanye suke tamkar mai jin bacci, haka kuma yana da dogon hanci da loɓawar kumatu musamman idan yayi dariya duk da ba kasafai ya fiye yinta ba, yana da matsakaicin tsawo da kuma murɗaɗɗen jiki dake nuna yana motsa jiki, na fahimci duka hakan ne lokaci ɗaya saboda yadda 'yan mata ke yawan zancensa.
A hankali na ci gaba da saukowa akan matattakalar wajen da muka gama ɗaukar karatun ina ma Nu'aymah magana, jin shiru bata amsa ni ba ya sani ɗago kai da niyar sake yi mata magana, abun mamaki sai na hangota a can matakalar farko ta saki baki tana kallon gefen da su Umar Faruk suke tana faman kallonsa, takai ci ne ya kamani na ɗan tsaya ina kallonta nima kafin na koma na riƙo hannunta muka shiga saukowa ina cewa, "Wlh Aymah bakiyi ba! Na rasa meye abun kallo a can". Nu'aymah dake yi tana juyawa tana kallonsa tace, "Baza ki fahimta ba Janaam, gayen can na matuƙar burgeni wallahi, ba don nasan halinsa ba tsab zai iya disgani da na je mun zama Friends ni dashi, Allah Janaam yana matuƙar burgeni sosai". Taɓe baki nayi bayan mun sauko ina cewa, "Lallai ba kida aiki Aymah, meye abun burgewa atattare dashi, bakya ganin dabi'unsa da halayyarsa ne? Ai sam ko kusa bai dace daya shiga rayuwarki ba don Allah tun wuri karki fara, mutum bai da aiki sai faɗin rai da zama cikin mata sai kace wani ɗan daudu". "Hmm! Bazaki gane ba, ai Wlh ni ko gaisawa ce mu riƙa yi dashi hakan ba ƙaramin faranta raina zai yi ba,". Nu'aymah ta faɗa tare da juyawa gefe, hango motar ta a inda mukayi parking ɗazu tayi, tayi saurin taɓo ni tana faɗin."Bar wannan zancen Janaam dama ya Aym ya bar mana motar anan bai tafi da ita ba?" Na juyo na kalli motar haɗe da cewa. "Gashi kin gani, amma nima ban san bai tafi ba gaskiya tunda bai bani key ba yana hannunsa, kin kuma san idan yasan anan zai bar maki ita dole ya bani key ɗin yace na wuce maki dashi". "Zo muje" Nu'aymah ta faɗa tana jan hannuna muka nufi wajen motar, tamkar wanda idanuwansa ke kanmu muna isowa wajen ya zuge glass ɗin gefensa fuskarsa ɗauke da murmushi yana cewa. "Har kun fito". Nu'aymah ta zato idanuwa tana kallon sa haɗe da cewa, "Can't believe wai da gaske kai ne yaya ka tsaya jirana? Muna fa da lecture ɗi 2-4". Ni kuwa a zuciyata mamaki ne yakama ni kar ace ya tsaya ne akan maganar daya ce yana so yayi dani? Ai kuwa sai ji nayi yace wa Nu'aymah. "Malama bake na tsaya jira ba, ƙawarki Janaam nake son magana da ita shiyasa ban tafi ba". Nu'aymah ta taɓe baki tana haɗe rai take cewa. "Dama ai na sani, kinga Janaam bara naje na samo mana abinda zamu ci, kai kuma ya Aym gaka gata amma ka sani dole sai ka biyo ta hannuna na buga maka stamp, idan ba haka ba na hana a saurareka". Nu'aym ya saki murmushi haɗe da ciro kudi a aljihunsa ya miƙa mata yana cewa, "Eh na dai ji, karɓa ki ƙara ki sawo maku abu mai kyau, in dai ke nasan halinki yanzun nan sai kije ki kwaso maku harkar kayan zaƙi da snacks, kuma sam basa maganin yunwa don haka kawai kiyi maku take away ɗin abinci mai kyau". Nu'aymah na dariya ta karba ta wuce, shi kuma ya ɗan leƙo daga cikin motar yace, "To Ranki shi daɗe shigo daga ciki muyi magana". "A'a ya Nu'aym nan ma ya isa". Na faɗa ina jin ƙirjina na wani bugawa da karfi, murmushi ya yi ya fito cikin motar shima ya jingina a jikinta kamar yadda nayi sannan yace..
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
5.
"Janaam ya lectures ɗin? Ina fatar dai laifina bai sa aka hanaki shiga ba?" Na ɗanyi murmushi daga cikin niƙab ɗina haɗe da cewa, "Ko ɗaya ya Nu'aym". Ya amsa da alhamdulillah yana gyara tsayuwar sa, shiru ya ɗanyi kamar mai wani nazari kafin yai gyaran murya yaci gaba da cewa, "Bansan ta wace fuska zaki kalli maganar da nake so muyi dake ba, amma ina rokonki daki taimaka ki yi mani kyakkyawar fahimta, kin sani ni ba mazaunin ƙasar nan bane amma ba tun yau ba nake jin ƙaunarki da soyayyarki acikin zuciyata, duk tsawon tazarar dake tsakaninmu dake, da yadda mukayi nisa ban taɓa jin ƙaunarki ta ragu a zuciyata ba, dake nake kwana kuma dake nake tashi araina har zuwa wannan lokacin". Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya kafin yaci gaba da cewa, "Ina sonki Janaam so mai tsanani da bana jin zan iya rabuwa dake, ina fatar samun alfarmar so a wurin ki ba tare da kin bari nasha wahala ba". Shiru nayi ƙirjina na wani irin duka da jin kalaman yayan Nu'aymah saboda ganin rashin cancantar tarayyarmu dashi, ita kanta Nu'aymah lokuta da dama duk da kasancewar muma muna da namu rufin asiri dai-dai gwargwado nakan yi ƙoƙarin nisanta kaina da ita, soyayyar da take yimani tasa ko nayi hakan zata sake janyo ni cikin jikinta da kuma rayuwarta, mahaifina har ya rasu mutum ne mai matsakaicin ƙarfi, saɓanin nasu mahaifin dake da matuƙar tarin arziki shiyasa ban fiye shige masu ba, muhimmancin da Nu'aymah ta nuna mani ina dashi a wajenta tare da bani matsayi mai gima shiyasa na saki jiki da ita sosai har ƙawancen namu yayi ƙarfi ta yadda zaka iya cewa gida ɗaya muke. taya kuma yanzu yayanta zai zo mani da zancen wata alaƙa ta soyayya tsakanina dashi! Jin nayi shiru ina wannan nazarin ya sashi cewa. "Janaam bazan maki dole ba nace sai kin amshi soyayyata yanzu-yanzu, zan baki lokaci kiyi tunani, idan kin amince dani sai na baki amanar zuciyata duka kiyi yadda duk kike so da ita, jibi zan koma ina fatar zaki bani izinin sake tuntuɓarki naji ra'ayinki kafin na tafi". "Shikenan ya Nu'aym ba damuwa Nagode ". Na faɗa ina ƙoƙarin barin wajen, "Ina kuma zaki tafi tunda ƙawar taki bata dawo ba?" "Zan jira ta ne daga can". Na nuna masa wani gurin da muke zama ni da ita, kasa bari yai na ƙarasa wajen ni kaɗai sai dai muka tafi tare yana cewa, "Nagode ma Allah daya sa kike rufe kyakkyawar fuskar nan taki Janaam, ba don haka ba da nikam na shiga uku". Nayi dariya haɗe da cewa, "Shiga uku fa kace Ya Nu'aym, na meye?" Ya Nu'aym dake kallon yanayin cikin makarantar tamu a natse yace, "Baki ga yawan samarin dake cikin makarantar nan taku ba? Ai inaga da zasu san yadda Allah ya kyautata halittar ki da kuma kyan da kike dashi da ban samu damar tsayawa tare dake ba don na tabbata wani zai rigani a fadar zuciyarki, saboda haka nagodema wannan niƙaf ɗin da ake sawa". Nayi murmushi haɗe da cewa, "Ehmm haka dai kafaɗa". "Haka zancen yake Janaam". Ya faɗa adai-dai lokacin da muka kawo kusa dasu Umar Faruk yana katsa ma wata budurwa tsawa, ɗauke kaina nayi nayi gaba amma ga mamaki na sai ban ji ya Nu'aym a tare dani ba, juyawar da zanyi don ganin ina ya tsaya na hango shi ya riƙe hannun Umar Faruk, ashe ina wuce ya ɗaga hannu zai mari wannan budurwar shine Ya Nu'aym ya ƙarasa ya riƙe hannun kafin taƙarasa marubuta, tsaye nayi ban ƙarasa wajen ba ina kallon ikon Allah, cikin sanyin murya naji Ya Nu'aym yana faɗin, "Haba kai kuwa ba girmanka bane, meye ribarka idan ka daki mace? Be wise wannan ai ƙauyanci ne". Rai a ɓace naga Umar Faruk ya ɗago kai yana watsa ma Ya Nu'aym wani irin mugun kallo kafin ya wafce hannunsa ya wani yarfi dashi gefe, budurwar data zube ƙasa akan guiwoyinta tana kuka ya nuna da rinannin idanuwansa da suka kaɗa sukayi ja saboda ɓacin rai yace, "Idan ki ka kuskura kika sake bayyana fuskarki a gabana sai na wulakantaki acikin makarantar nan irin wulaƙancin da ban taɓa yiwa kowa ba, wawiya jaka kawai zaki bar nan ko sai na taka ki?". Nayi saurin runtse idanuwa jin kalmar daya jefeta da ita ina sake jin tsanarsa mai ƙarfi a zuciyata, ko ta kan Ya Nu'aym Umar Faruk bai bi ba yabar wajen hannunsa riƙe da wayar sa daya karɓe daga cikin yan matan dake zagaye dashi, Ya Nu'aym ya ɗaga kafaɗu irin i don't care ɗin nan sannan ya baro wajen shima, "Me yasa zaka shiga sabgar wancan da bai san darajar mutane ba?" Na faɗa ina ci gaba da tafiya, Ya Nu'aym na biye dani yace "Abun da yai ne bai dace ba Janaam, da can ƙasar da nake zama ne za'a iya rufesa akan cin zarafin mace da yai, na rasa me yasa wasu mazan basa daraja mace bayan ita ɗin abu ce mai kima da daraja". "Wasu mazan dai ya Nu'aym, wancan da kake gani ya addabi kowa a makarantar nan, ka gode Allah da bai ma rashin mutunci ba". "Haba!" "Sosai". na faɗa ina zama daya daga cikin kujerun dake wajen da muke zama, shima ɗaya ya nema ya zauna yana jinjina lamarin Umar Faruk da naci gaba da basa labari, da haka Nu'aymah ta dawo ta tadda mu wajen don zata iya hango mu. "Wai baka tafi ba Ya Nu'aym?" Ta tambaya tana miƙo mani ledar takeaway ɗin data yimana tare da ruwa da lemu sannan itama ta nemi waje ta zauna ta ciro robar abincin ɗaya daga ciki ta soma ci, wayar Ya Nu'aym ce ta ɗau ruri ya ciro ta agaban aljihu, idanuwa ya zaro haɗe da miƙewa yana cewa. "Aymah bari na tafi Abba ne ke kirana, idan kun gama lecture ɗin sai ki kirani na ɗaukeku zan tafi da motar ki". Nu'aymah data jawo gorar ruwa tana sha ta cire gorar a bakinta tana cewa, "Allah Ya Aym ka takuramu da yawa gaskiya, yanzu don Allah sai mun tsaya jiranka idan muka gama baza kabar mani motata ba mu tafi da kanmu?" Bai tanka mata ba ya kalleni yace, "Janaam ni na tafi kada kimanta da saƙona". Ya faɗa yana ɗan zuba idanuwansa akaina, nima kallonsa nake yi don haka nayi saurin jaye idanuwana haɗe da cewa, "Allah ya tsare hanya". Ya amsa da amin sannan ya wuce.
Bayan ya tafi nake ba Nu'aymah labarin abinda ya faruwa tsakanin Umar Faruk da yayan nata, nan ta saka dariya tana cewa shima Ya Nu'aym ɗin da gangan ya shiga abinda bai shafesa ba, ina ruwansa tunda ba'a saka dashi ba? yan matanne sam ba class wallahi sai su yita binsa, ai ya yi maun dai-dai da yayi mata hakan gobe ma ta ƙara, baki na saki ina kallonta jin abunda take fada, sai da muka yi sallah sannan muka koma lecture, awa biyu muka yi muka gàma, muna ƙoƙarin fita naga kowa ya ja ya tsaya ganin Umar Faruk zai fita, aikuwa na ja tsaki na wuce abina don bana da lokacin ɓatawa akan wani, yadda nake jin gajiya atattare dani bana jin zan iya jiran har sai wani ya fita. Ina saukowa daga stairs na Hall ɗin na hango ya Nu'aym, sai dana jira Nu'aymah ta fito sannan muka nufi wajen motar, muna zuwa na buɗe baya na zauna, a maimakon ta zauna gaba sai itama ta buɗe gefen da nake ta shiga ta zauna. "Kuce na zama driver". Ya Nu'aym ya faɗa yana gyara zaman madubin dake gaban motar daga sama zuwa saiti fuskata, muna haɗa idanuwa na sauke nawa idanuwan na mayar jikin glass ɗin ƙofar da nake zaune. Murmushi Nu'aym yai haɗe da tada motar ya ja ya fice, muna kawowa bakin gate ɗin fita shima Umar Farouk na kawowa sukayi clashing, ƙin ɗaga masa Ya Nu'aym ya yi ya wuce haka shima yaƙi ya ɗaga masa, ga mutane a bayanmu sai horn suke yi, Nu'aymah ce naji tace "Ya Nu'aym don Allah ka ɗaga masa ya wuce". Nu'aym da ransa ya gama ɓaci a ɗan hasale cikin tsawata murya yace, "Shout up Nu'aymah karki sake yin magana akan wannan yaron, bari naga ƙaryar iskancinsa tunda shi marar kunya ne, idan yana tunanin shi tsagera ne zan gwada masa nawa tsagerancin yafi nashi". Sosai na ji daɗin hakan hadda kaɗa kai irin yayi daidai. Mutanen dake bayan mu dole suka riƙa juyawa suna komawa ta ɗaya gate ɗin don dukkansu babu alamar ɗaya zai haƙura yaba ɗaya waje, can bayan mintuna biyar na hangi Umar Faruk ya fito daga cikin motarsa ya buɗe Boot, bamu ankara ba sai gashi ya ƙaraso wajen motar mu a hasale, yana zuwa ya fara dukan glass ɗin motar mu, wata irin ƙara muka saki ni da Nu'aymah muka duƙe ƙasa, a hasale shima Ya Nu'aym ya buɗe motar ya fito, hannu ya ɗaga zai wankama Umar Faruk mari ya ji an riƙesa ta baya, "Don Allah kayi hakuri bawan Allah kada ka biye masa ku tashi hankali". Wasu mutane daga waje da suka ƙaraso wajen suka faɗa suna ba ya Nu'aym haƙuri, da yake shima zuciya ta rufesa kawai ya ture su gefe ya yi kan Umar Faruk ya turasa da karfi har sai da ya kusa faɗuwa, nan fa suka sulle da faɗa idan ya kai masa naushi shima ya kai masa, sai dai ga alamu ƙarfi ba ɗaya ba saboda Ya Nu'aym kana kallonsa kasan gaskiyar hutu tabi jikinsa, shi kuma Umar Faruk banda hutu akwai alamun ƙarfi tattare dash kasancewar kana kallon sa zaka ga ƙaƙƙarfan mutum ne saboda yanayin kirar jikinsa da ta bayyanar da hakan. Da kyar aka samu aka rabasu sun fasama juna baki, Umar Faruk bai tsaya saurarar kowa ba yabar motar anan yayi tafiyarsa, shi kuma ya Nu'aym Nu'aymah ce ta koma seat ɗin driver ta tada motar tayi reverse muka fita ta ɗaya gate ɗin fuskar ya Nu'aym da idanuwansa sun yi jajir saboda ɓacin rai sai faman ƙyacci yakeyi....
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
6.
Ko da Umar Farouk ya isa gida main palour ya nufa, Momy na kitchen tana aiki bata ji shigowarsa ba, sai daya buge kusan minti talatin sannan ta fito daga kitchen ɗauke da kulolin abincin data gama haɗawa ta nufi