Showing 156001 words to 157423 words out of 157423 words
Ya mai girma mai shari'a, wuɗannan takardu ne dake ɗauke da bayanan kwanan watan da aka fitar da wanda aka ce an kashe a ƙasar waje bayan gano cewa bai mutu ba, wannan ya faru ne tare da haɗin bakin Inspector Ashir da wasu yan sanda da sukayi ƙaryar cewa su suka ɗauki gawar wanda aka kashe suka kai asibiti domin ayi bincike, inda muka gano cewa lallai ba asibiti aka kaishi ba kuma rahotonnin da suka haɗa suka gabatar wa kotu na ƙarya ne". Shiru ya danyi kafin ya sake komawa wajen da yake zaune ya ɗauko Flash sannan yaci gaba da cewa, "wannan kuma flash ne ya mai girma mai shari'a dake ɗauke da bayanan duk abubuwan da inspector Ashir da Dr Abdullahi suka kulla aciki, sai kuma hotunan da muka ɗauke sa a lokacin da muka gano gaskiya muka fara bibiyarsa a kokarinsa na zuwa airport ya goge rahotonnin fita da ɗan nasa, a taƙaice dai duk wannan abin da ya faru an shirya shi ne don tozarci, sharri da kuma yin ƙage ga wanda ake zargi". Ya ɗan juyo zuwa wurin masu tuhuma cikin ɗaga murya yace, "Da mu daku duka mun san cewa tunda Babu hujjar gawa, babu rahoton likita, babu takardar kisan kai to babu tushen wannan Shari'a kawai ɓatawa kotu lokaci ne idan har ta ci gaba da sauraron wannan shari’a, menene zai zama ginshiƙinta? Duhu da zato kawai, mu kuma munsan cewa doka bata gina a kan zato, tana gina ne a kan tabbatacciyar hujja". Daga Barrister Shamsu har Barrister Aysha ƙasa suka yi da kawunan su don a yanzu sun tabbatar suma gaskiya ta gama bayyana ba zasu iya ci gaba da jayayya ba. Nan Barrister Nazir ya koma ya mika takardun da kuma flash ɗin zuwa ga alkali sannan ya koma ya zauna.
Tsit kotu tayi kowa ya tsare alkali da ido suna jiran hukuncin da zai yanke, yayin da zuciyar Momy ta shiga bugawa da wani irin speed tasa hannuwa ta rufe baki tana kallonsa itama tana jiran taji wane hukunci zai yanke. Justice Ibrahim kuwa sai da ya saka Flash ɗin a jikin system ɗin Momy dake gabansa ya saurari duka maganganun da Inspector Ashir suka yi shi da Dr. Abdullahi cikin natsuwa yana jin wani sanyi na ratsa masa ta wani ɓangare na zuciyarsa saboda tabbacin daya samu cewa dansa bai aikata kisa ba, ya ɗauki hotunan ya duba su ɗaya bayan ɗaya sannan ya ɗago kai yana gyara zaman gilashin idonsa ya dubi kotu gaba-daya, cikin murya mai nauyi ya ce, "Bayan dubawa da kuma tantance hujjojin da aka gabatar, kotu ta tabbatar da cewa wanda aka ce an kashe yana nan raye a wata ƙasa, kuma wuɗannan hujjojin gaskiya ce da aka tabbatar da ita da takardun hukuma masu sahihanci."
Shiru ya ɗanyi sannan yaci gaba da cewa "A tsarin doka, idan babu mutuwa to babu kisa, tunda babu wanda ya mutu, babu laifin da za a ci gaba da yin Shari'a a kansa. Saboda haka…"
Ya ɗauki alkalami yayi rubutu mai tsayi kafin ya ɗago yaci gaba da cewa.
"Wannan kotu ta tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ba shi da laifi. An yi masa sharri, an kusan hallaka rayuwarsa, alhalin wanda aka ce an kashe shi yana raye a wata ƙasa. Wannan babban makirci ne da ya nuna mugunta, rashin tsoro ga Allah, da kuma ƙin mutunta dokokin ƙasa, an kuma kulla wannan sharri ne da nufin durƙusar da rayuwar ɗan adam marar laifi. Saboda haka kotu ta soke wannan ƙara gaba ɗaya ta koreta, ta kuma sallami wanda ake zargi nan take tare da wanke sa daga kowace irin tuhuma da ake yi masa, sai dai duk da haka kotu baza ta bari ya tafi a haka ba har sai ta tanadar masa wani hukun don jan kunne agaresa bisa ikirarin da ya yi na amsar karya wato (false confession / perjury) da kuma ƙoƙarin katse adalci (obstruction of justice) wanda hakan zai iya rikitar da bincike, a tsarin doka duka wudannan abubuwan daya aikata laifi ne, don haka kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya kacal a gidan yari ko kuma biyan tarar Naira dubu ɗari (100.000.00), domin hakan ya zamo jan kunne da kuma darasi garesa da sauran jama’a".
Wani numfashi Momy ta ja mai nauyi tana jin hawaye na cika mata idonta saboda farinciki a hankali tana furta "Alhmdulillah". Jama'ar kotu kuwa sai jinjina suke wa adalin alkalin nasu da tun farkon shari'ar suka tabbatar da zai yi adalci, Inspector Ashir ne ya miƙe yana kai waya a kunne don tun ɗazu gaba-ɗaya ya jike da gumi tsantsar tashin hankali, ganin hankalin mutane ya ɗauke wajen surutu haɗe da murnar tabbatar da adalci ya sashi ƙoƙarin miƙewa zai gudu sanin suma hukuncin na nan tafe a kansu, sai dai tuni wasu samari sun lura da hakan sai suka tare masa ƙofa, wanda hakan yasa hankalin kotu dawowa a kansa ana Allah ya waddaran masu hali irinsa. Barrister Maryam ta sake miƙewa tana ɗauke kwallan idanuwanta haɗe da cewa,
"Ya mai girma mai shari'a, ina roƙon wannan kotu bisa adalcinta data bayar da umarnin bincike da gurfanar da duk waɗanda suka shirya wannan sharri, domin adalci ya tabbata, idan ba a ɗauki mataki ba, to gobe wani zai iya fuskantar irin wannan mugun abu daga wajen wasu tsiraran mutane masu hali irin nasu saboda wannan abu da suka aikata ya kasance “kisan adalci” dabai kamata a yi shiru a kai ba. Shi kuma Adalci ba wai kawai a kare wanda ake tuhuma bane har da hukunta masu sharri da aka tabbatar suna da laifi".
Justice Ibrahim ya jinjina kai haɗe dayin yan rubuce-rubuce haɗe da cewa, "Barrister Maryam ai dama wannan kotu bazata ƙyale su ba tunda har aka samu cikakkun hujjoji akansu, saboda haka abu na farko, kotu na umurtar hukumar 'yan sanda nan take data kama waɗanda aka gano sun ɓoye wanda aka ce an kashe, abu na biyu har kotu na umurtar hukumar bincike ta musamman (Criminal Investigation Department da Human Rights Commission) da su buɗe sabon bincike mai zaman kansa akan wannan lamarin, sai abu na ƙarshe kotu zata bayar da takardar umurnin dawo da wanda akace an kashe dake wata ƙasar cikin gaggawa wato (Extradition warrant), za kuma ta tura takarda (request for extradition) ga Ma’aikatar harkokin tsaro na waje, ofishin jakadancin ƙasar da aka ɓoye shi da hukumar yan sanda ta ƙasa tare da haɗin gwiwar Interpol da kuma Ma’aikatar Shari’a. Wannan umurni ne daya zama dole don tabbatar da cewa wanda ya aikata laifi ya fuskanci hukunci shima dai-dai da laifinsa saboda adalci yaci gaba da tabbata a cikin wannan al’umma." Yana gama faɗar hakan ya ƙwanƙwasa gudumar dake gabansa yana kai karshen shari'ar inda nan take jami'an tsaro suka kame Inspector Ashir suka tafi dashi.
Momy da farinciki ya rufe ta nufi wajen Umar Farouk da wani ɗan sanda ya fito dashi ya cire masa ankwar dake hannunsa, Umar Farouk kuwa da tunda aka fara shari'ar yau bai san inda kansa yake ba saboda wani abu da yake ji ajikinsa da kwakwalwarsa dake juya masa, ga wani abu da yake ji na taso masa tun daga cikin ciki har zuwa makoshi sai faman jiri yake ji duniyar na juya masa, ana cire ankwar ya zube a ƙasa a tsakiyar kotun a sume, Momy na ganin haka ta yi watsi da takardun hannunta da gudu ta rugo ta ƙaraso wajen a rikice ta tallabosa a jikinta, ganin kumfa na fita ta bakinsa ya sa ta sakin wata irin ƙara haɗe da ƙanƙamesa ajikinta tana kuka...
*ALHAMDULILLAH*, _Anan na kawo karshen littafin IDO A DUHU BOOK 1, ku tareni a book domin jin yadda wasar zata kasance. Hmmmmm yanzu fa wasar zata fara karku sake baku labari_
ME YA SAMU UMAR FAROUK NE😳?
ME ZAI FARU DA UMAR FAROUK NAN GABA?
SHIN ZA'A YI NASARAR DAWO DA NU'AYM NAJIRIYA AN YANKE MASA HUKUNCI KO KUWA?
YA LABARIN MAHAIFIN NU'AYM DA NU'AYMAH? SHIN HUKUMA ZATAYI NASARAR KAMA SHI KO ZAI GUDU?
WACE RAYUWA JANAAM ZATA FUSKANTA ANAN GABA?
SHIN MAR FAROUK ZAI AURI JANAAM KO KUMA SUN RABU KENAN?
YA LABARIN SALEEM, INSPECTOR ASHIR, WANE HUKUNCI KOTU ZATA YANKE MASU.
WANE MATSAYI MOMY ZATA KALLI JANAAM DASHI ACIKIN RAYUWAR ƊANTA, MASOYIYARSA KO KUMA ABOKIYAR GABANSA?
_Ku kasance tare dani a book 2, anan ne zan zube maku duka baseerata domin warware maku zare da a bawa, kar kuma ku manta wasan yanzu ne zata fara💃💃💃_
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏