Showing 69001 words to 72000 words out of 157423 words

Chapter 24 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

522

tana ɗagawa Umar Farouk dake kwance ya tashi da sauri zaune yana faɗin, "Nu'aymah kin haɗu da Janaam kun yi magana?" Wasu hawaye suka shiga silalowa Nu'aymah a ido suna bin fuskarta masu matuƙar zafi da ƙunar zuciya, yau bata shiga school ba amma Umar Farouk bai iya tambayar ta dalilin rashin shigar ta ba sai Janaam da take da tabbacin ya haɗu da ita a makaranta! Kasa amsa masa ta yi har sai da ya sake cewa, "Hello Aymah kina jina? Nace kun haɗu da Janaam kuwa? ta yi maki zance na?" Cikin ƙarfin hali Nu'aymah ta ce, "Mun hadu ta zo duba ni saboda bata ganni a school ba, amma.." shiru ta yi ta kasa ƙarasa abinda take so ta faɗa da sauri Umar Farouk cikin kakkaryewar murya ya ce, "Am..ma..ma me Nu'aymah?". "Kayi hakuri bata mun maganar ka ba.." tun kafin ta karasa ta ji Ƙit Umar Farouk ya kashe wayar sa ba tare daya sake ƙara kalma ko ɗaya ba, wayar ta ciro daga kunnenta tana kallon sunan data yi saving ɗin lambar sa dashi "MY DREAM❤️" Ji kawai tayi kuka ya kwace mata ta fashe da shi haɗe da faɗawa kwance saman gado tana jifa da wayar. A ranta faɗa take yi Umar Farouk ya iya jurewa kiran Janaam har sau uku duk da bata ɗaga masa kiran nasa ba, amma ita second daya ya kasa jurewa saurarar ta saboda kaɗai ta faɗa masa Janaam bata yi mata zancen sa ba? Shin meye laifinta sannan da me Janaam ta fita da ita bazai so ta ba?.

Umar Farouk kuwa dafe kai yai yana tunanin ta wane yare zai sake bayyanawa Janaam soyayyarsa tunda ya fahimci ta kasa gane wanda yake yi mata yanzu, bazai iya fitowa fili ya faɗa mata yana son ta ba saboda bai san kalar amsar da zata bashi ba, amma zai bi duk hanyar da zai bi ya gwada mata so kuma ya isar mata da sakon zuciyarsa.

(Hmmm! Inji mai ciwon haƙora, kayi dubara Umar Farouk amma bana tunanin idan har kana ganin idan ka furta mata kalmar so bazata saurareka ba ci gaba da nuna mata son zai sa ta fahimceka, amma dai muje zuwa).

A daren daƙyar Umar Farouk bacci ya iya ɗaukarsa saboda tunani, yana son Janaam son da shi kansa tsoro yake bashi, farar ɗaya ya yi masa mugun kamun da yake nema ya zautar dashi, washe gari duk wanda ya kallesa ya san sai ya fahimci irin damuwar da yake ciki, School ma daƙyar ya samu ya tafi saboda ita kadai ce hanyar da zai iya bawa zuciya abincinta wato ganin Janaam, baya fahimtar komai a yanzu kuma baya gane komai idan ba duk wani motsi na Janaam ba, ko me take yi akan idanuwansa, a yanzu komai take yi burgesa take, a da ba abinda ya tsana kamar shigar da take yi da saka niƙab haɗe da rashin shiga sabgar kowa, a yanzu ko hakan da take burge sa yake yi domin yana samama masa natsuwar babu namijin da zai gane masa ita ko zata saurarà, sannan bazai rika kishi da wasu ba saboda sun kula ta tunda bata basu fuska ba, Jabir ma tun daya sha duka a hannunsa tare da ƙwaƙƙwaran kashedi da jan kunne daya bisa daga baya yai masa akan Janaam bai koma bari ko hanya ta haɗasa da ita ba, waya ma data gwada kiransa sau ɗaya ta bashi hakuri tun daga ranar yayi blocking ɗinta, a aji ma Umar Farouk ya kasa ya tsare babu wani namiji dake iya kuskuren tunkarar ko da kusa da seat ɗin ta ne, sosai hakan ya ba Janaam mamaki haɗe da ɗaure mata kai, amma da yake dama can bata shiga sabgar su sai kawai ta ci gaba da tata sabgar ba tare data nuna damuwa ba, don a zaton ta Umar Farouk yai haka ne don ya takura mata bai san ita hakan ma daɗi yayi mata ba, Nu'aymah ta isheta rayuwa har su karasa kammala karatun su, ta yiwa Umar banza da shi da babu duka ɗaya agunta, duk wata hanya daza ta haɗata dashi ta datseta ta maida hankalinta ga karatu sosai ba ruwan ta da sabgar sa duk da yadda taga yana ƙoƙarin shige mata a yanzu tare da nuna mata shi na ƙwarai ne, don ba laifi ya gyara kaso mafi yawa daga cikin dabi'unsa sai dai yan wuɗanda ba'a rasa ba, Nu'aymah kam hakan ya yi mata daɗi sosai don ba laifi garin son ji daga Janaam ko yin magana da ita Umar Farouk na yawan kulata tare da bata lokacin sa, duk da tasan yana yin duka hakane don Janaam amma hakan na taimakawa wajen rage mata raɗaɗi ganin Janaam ɗin ba kulasa take yi ba.

Bayan sati biyu kana kallon Umar Farouk zaka ga yadda ya rame ya yi wani irin baƙi saboda azabar so, gabaɗaya Janaam tayi biris da soyayyarsa ta nuna bata ma san yana yi ba, hakan yasa tsawon sati ɗaya yau kenan daya dena zuwa makarantar cike da tunanin hakan shine mafita agun sa tunda Janaam taƙi ta fahimce sa, Momy ta yi tambayar duniya ya sanar da ita abinda ke damun sa ganin yadda yake rama amma ya ƙi, hatta Dady daba wata jituwa suke ba sai daya tambayesa dalili daya ga ya dena zuwa makaranta, da Umar Farouk ya ga matsa masa zai yi yafara takurasa sai kawai ya ce masa ya gaji da karatun ne shi yasa ya ajiye, hohoho ranar ina wuta Dady ya kaɗa Umar Farouk saboda yadda ya manna masa hauka ya yi ta yi mai faɗa yana cewa bazai maida shi dan iska ba ya biya masa kuɗin makaranta har sai da aka zo ƙarshe yace bazai ƙarasa ba saboda haka dole ya zaɓi ɗaya, ko ya koma school, ko ya fito da mata yayi masa aure idan haka yake so tunda yaga harkar mata ya sa agaba ko kuma yabar masa gida, a cikin hukuncin da Dady ya yanke babu wanda ya ɗagawa Umar Farouk hankali saboda yanayin da yake jinsa aciki a ganinsa yafi ƙarfin duka wudancan hukuncin, da farko ya ɗauka abun zai zo masa da sauki idan ya nisanta kansa da Janaam yabar ganinta, sai daga baya jikinsa ya tabbatar masa da shine abu mafi wahala da zai illata masa zuciya da gangar jiki cikin sauƙi, ya ji a ransa cewa bazai iya jurewa rashin Janaam ba saboda haka ko ba don faɗan da Dady yayi masa ba dole zai koma makarantar don bayyana soyayyata saboda ya gaza bazai iya ci gaba da ɓoyewa ba, wannan shawarar da zuciyarsa ta yanke masa ya yi na'am da ita sosai ta kuma faranta zuciyar Momy ganin sa da ta yi cikin shiri yau tunda safe da niyar komawa makaranta, sannan ta yayyafawa fitinar da Dady keyi kullum akan ya renasa baya jin maganarsa sai ta mahaifiyarsa, da murmushi kwance akan fuskar Momy ta kallesa ta ce, "Umar Farouk ka faranta mini da zaka koma makaranta kai ma Allah ya faranta maka, ka yi hakuri ka jure ka ƙarasa karatun nan zai taimaka maka nan gaba ka ji ko?" "In Sha Allah Momy". Ya faɗa yana gyara zaman hular kansa, ganin hakan ya sake ba Momy mamaki ta shiga tunani a a zuciyar ta ko dai yaron nata ya faɗa soyayya ne saboda shi ɗin ba ma'aboci son manyan kaya bane ko ga sallah sai ta yi da gaske yake saka wa, shi yasa yau tayi mamakin ganinsa da su kuma sun matukar yi masa kyau sosai, musamman yar ramewar da yai ya ɗanyi haske sai tasa yadin da yai wa ɗinkin kaftan yai matukar yi masa kyau ba kaɗan ba. "What mommy?" Umar Farouk ya faɗa cikin basarwa ganin irin kallon da take yi masa, fuskarsa ta shafa haɗe da yin murmushi tana cewa, "Da zaka riƙa yin wannan shigar zan fi jin daɗi don tayi maka kyau sosai,duk da waccan ɗin ma tana yi maka amma wannan is the best". Murmushi kaɗai Umar Farouk yai bai ce komai ba ya ƙarasa kan dining ya yi taking breakfast ɗinsa sannan ya wuce school, a kan hanya ya dauko wayoyin sa da gabaɗaya ya kashe ya kunna, sakonni suka fara shigowa duka bai bi takan kowane sako ba sai na Nu'aymah da sun fi kwara ashirin, driven yakeyi yana bin saƙonnin yana karantawa, dukkanin su babu wanda ya samu abinda yake son ji a cikinsu game da Janaam sai tambayarsa lafiyarsa kawai da take yi da kuma rashin jin daɗin zuwan nasa makaranta daya daina yi, duk da ba hakan ya so ba ya ji dadin kulawar ta saboda haka bai wofantar da tarin saƙwanninta ba sai daya rubuta mata thanks sannan ya ci gaba da duba sauran saƙwannnanin dake da muhimmanci yana basu amsa a takaice, a kasan ransa kuwa ya ji zafi sosai na rashin ganin ko da kalmar a ce daga wajen Janaam duk da yasan zai yi wahala ta ji rashin daɗin dena ganinsa balle har ta turo masa saƙo ko da kuwa kowa ya damu da rashin ganinsa to banda ita.

Lokacin daya iso school har an fara lectures ya shiga class ya zauna aka ƙarasa tare dashi, duk da ba wata mu'amala mai kyau tsakaninsa da colleague dinsa sun yi masa kara sosai wajen nuna masa jin daɗin dawowarsa don wasu gaba-daya sun dauka bazai dawo makarantar ba sanin halinsa tare da samun cikakken yancin su da baya nan, don haka dawowarsa ta faranta ma wasu rai kamar Nu'aymah haka kuma wasu bata yi masu daɗi ba musamman wuɗan da ya sama takunkumi akan Janaam...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

Masu son V.I.P sai ku bibiyemu a Arewabook ta wannan link I just published "042" of my story "IDO A DUHU"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=687420f67befaef38b43026a

                            40.

Ni dai duk murnar da ake yi da zaƙewar da Nu'aymah ke nunawa ta dawowarsa ko kallon gefen da yake ban yi ba, hakan ya sake karya masa zuciya har ya ji bazai iya jurewa ba, ana tashi school ina kokarin karɓar handout ɗina a hannun Nu'aymah da tabi duk ta wani ruɗe ganin ya nufo inda muke tana kallon sa, sallama ya fara yi mana na ji kirjina yai wani irin bugawa da ƙarfi, cikin zuciya ta na amsa sallamar tunda hakkinsa ne akan mu ba tare dana juyo ba na karbi handout ɗin nawa a hannun Nu'aymah sannan na nufi hanyar fita, Da fara'ar Nu'aymah ta nufi wajensa tana ƙoƙarin yi masa magana yai saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu sannan ya juya yabi bayan Janaam yana kiran sunanta, A take Nu'aymah ta ji idanuwanta sun cika da ƙwalla wani abu ya zo mata a wuya ya tokareta. Da gudu tabar ajin tana share ƙwalla ta nufi wajen motar ta ta shiga ta tayar ta fizgeta da gudu tabar makarantar.

Umar Farouk kuwa magana yake yi Mani bayan ya fito ya cimma ni yana bina a baya amma naƙi sauraren sa sai ci gaba nake yi da tafiya ta, ko kaɗan kallon da mutane keyi masa bai damesa ba abu ɗaya ya sani dole yau ya fitar mata da abinda ke zuciyarsa cewa yana sonta koma me zata yi masa tayi domin ya gaji kuma hakan kaɗai ne zai haifar masa da salama acikin zuciya, Umar Farouk yasan ko Janaam bata tsaya ta sauraresa ba to tabbas idan suka isa wajen da take tsayawa tare abun hawa zata tsaya ta saurare sa, don haka ya ci gaba da bina duk da wayar da yaji ina yi da ya Nu'aym daya kira ni hakan bai sa ya dena bina a baya ba, ni kuma ban dena wayar ba hankali kwance nake fira da ya Nu'aym ina dariya duk don na bakan tawa Umar Farouk da yanzu na gama gano cewa yana ƙauna ta, wanda hakan babu abinda ya kara mini a zuciyata sai tsanarsa musamman da nasan irin son da Besty keyi masa amma yai biris da ita, dama ban taɓa jin ina son shi ba don haka na daukarwa kai na alkawari ko mazan duniya zasu ƙare bazan taɓa son sa ba, balle ga Ya Nu'aym daya kasa ya tsare ya hana zuciyata ganin kowa idan ba shi ba, da muka isa wajen da nake taren abun hawa sanin yana biye dani sai naki tsayawa na kuma ƙi kashe wayar don kar yai mun magana, gaba-daya na manta da titi zan hau ban tsaya duba kowane hannu ba kawai na haye titin, ban ankara ba sai ji nayi tamkar an wurga ni da ƙarfi zuwa tsallaken titin lokacin da manzo tsakiya, yayin da naji ƙarar abubuwan hawa da suka buga da juna, cike da tashin hankali naji 'yan makarantar mu dake tsaye a bakin gate ɗin da mutanen dake wucewa sun saka wata irin ƙara, wasu kuma suka shiga yinsallallami, a firgice na juyo cikin kiɗime wa sai kawai na hango Umar Farouk a tsakiyar titi cikin jini mota ta bugesa ashe shine ƙarar da naji mutane nayi, kasa motsawa nayi daga inda nake jikina sai rawa yake yi ganin yadda mutane suka tallabosa cikin jini suka tsallako da shi ta tsallaken da nake, amma duk da haka idanuwan Umar Farouk na kaina kafin yanayin da yake ciki ya bugesa, cikin ƙarfin hali naga yana motsa baki kafin daƙyar na ji ya furta kalmar, "Ina son ki Amaa.." bai ƙarasa ba kawai muka ga hannunsa ya faɗi jikinsa ya saki gaba-daya, wani student ne yazo da motarsa aka ɗauki Umar Farouk aciki suka bar wajen, sai a lokacin ne na ji tamkar an ta do ni daga bacci nayi firgigit jin wani daga cikin dattijan da suka taimaka aka dauko Umar Farouk tsakiyar titi dake wajen ya ce yana kallona, "Baiwar Allah idan wancan bawan Allah ya mutu ke ce da alhakin hakan saboda rayuwar ki yazo ceto ya rasa tashi rayuwar, ba don haka ba da yanzu ke ce a halin da yake ciki saboda ke mota ta zo bugewa ya rugo ya ture ki motar ta bugesa, fisabilillahi sai ku haye titi ba tare da kun duba ba sai kace na gidan iyayen ku, abun haushi ma kina waya ga ki saye da niƙab, wannan wane irin gangancin ne haka kika aikata". Ya ƙare zancen cike da takaici yai tsaki sannan yabar wajen, ni dai kasa sanin me zanyi na yi,  mutane sai zancen yadda abun ya faru suke yi suna nuna ni, ganin mai napep ya tsaya agabana yasa ban tsaya komai ba na faɗa ciki ina faɗa masa inda zai kai ni, jiki a sanyaye na iso gida na shige ɗakina tare da zubar da littafaina da jakata duka a tsakiyar ɗakin na zauna bakin ƙatuwar katifata ina cire niƙab ɗina, tokare guiwoyin hannuwa na nai akan cinyoyina haɗe da tallabe fuskata da tafin hannuwana kafin na rufe bakina wasu hawaye na sauko mini a fuska, ba ina kuka bane akan abinda ya faru ko tausayin abinda ya faru da Umar Farouk ba, kawai ina kuka ne saboda tsoron kada na zamo silar rasa rayuwarsa ko faruwar wani abu marar kyau a kansa kasancewar duk lalacewar musulmi ɗan uwan musulmi ne. Na jima a haka kafin na tashi na cire kayan jikina na faɗa toilet, ruwa na sakarwa kaina kafin na ɗauro arwala na fito na zura wata doguwar riga ta yadi na tada sallah, tsintar kaina nayi da addu'ar Allah ya ba dukkanin musulmi lafiya tare dashi yasa ba abinda ya samesa duk da naga jini sosai ya zuba ajikin sa, jiki a sanyaye na miƙe tamkar wadda ƙwai ya macewa a cikin ciki na nufi palour, abinci ma kasa ci nayi saboda tsoron abinda zai iya faruwa dashi ga shi duk mutanen wajen sun san ta dalilina abun ya faru, a ranar wuni nayi tamkar wata marar lafiya Mamah tayi tambaya har ta gaji amma na kasa faɗa mata, sai bayan sallar isha'i bayan na watso ruwa nayi shirin kwanciya na dauko wayata na kunna data, ina shiga WhatsApp group ɗin makaranta nafara budewa ganin tarin messages sama da ɗari biyar, a hankali na fara bi daya bayan ɗaya ina karantawa duka hira ce akan accident ɗin daya faru da Umar Farouk a ƙofar makaranta inda kowa keta faɗar albarkacin bakinsa tare da yi masa addu'a samun sauki, Nu'aymah dai bata iya cewa komai ba sai "hmmm Allah ya bashi lafiya" daga haka bata sake cewa wani abu ba sai dai ta biyo ni private ta ce, "Besty baki ji abinda suke faɗa ba akan ku ba game da abinda ya faru? Baza kije ki kare kanki ba ko ki karesa? Ko dai da gaske ne kece sanadiyar abinda ya samesa?" Murmushin da yafi kuka ciwo na saki don na tabbata haushi na take ji shi yasa ta faɗi hakan, kuma ban ga laifinta ba ko nice zan iyayin fiye da abinda ta yi, jiki a saliɓe na tura mata amsa da , "Me zan ce Besty idan ma gaskiya ko ƙarya suka faɗa, kowa yasan irin rashin jituwa ta da Umar Farouk saboda haka babu abinda zan faɗa na iya kare kaina ko a yarda dani, abu ɗaya na sani tunda Allah ya tsaro yau Umar Farouk zai yi accident ta sila ta ko bata sila ta ba to tabbas sai hakan tafaru, saboda haka Allah ya bashi lafiya ni shi kaɗai zan iya faɗa". "Hmm Besty kenan!" Nu'aymah ta faɗa kafin daga bisani naga ta sauka online, ji nai nima chart ɗin ya fita raina don haka sai kawai na sauka na ajiye wayar gefe, addu'ar bacci nayi sannan na gyara kwanciya ta ina sauke ajiyar zuciya a hankali kafin bacci yai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login