Showing 33001 words to 36000 words out of 157423 words
saboda lokacin shiga lecture ɗin ya kusa, ganin yadda take faman raba idanuwa yasa nayi gaba abina don nadan shi take nema, ni kuma baza'a yi wannan dani ba, ina kan hawa steps ɗin class ɗinmu na hango Umar Farouk tsaye a can karshen hawa steps ɗin, wani irin bugawa na ji ƙirjina ya yi lokaci ɗaya tsoro na shiga ta ina ji tamkar na juya na koma, wani ɓangare na zuciyata ne na ji ya karfafa mani don haka naci gaba da hawa steps ɗin hankali kwance, wanda a zahiri kaɗai ne ya bayyana hankalin nawa a kwance yake. Kaina a ƙasa yake don haka har na gama hawo wa bansan na iso inda suke ba, sai ji kawai nayi na bugi abu a gabana, ɗagowar da zan yi naga Umar Farouk ne, ashe lokacin da yaga na gama hawo wa shine ya taso ya shiga gabana, sosai na ji haushin hakan da yayi amma sai kawai nayi ƙoƙarin raɓawa ta gefensa na wuce, nan ma sake tare mini hanya ya yi na ɗago kai na zuba masa idanuwa ta cikin niƙab irin ya kake so nayi ɗinnan, kamar da wasa naga yafara tunkaro ni, ban motsa ba a tunanina duk haukansa bazai yi tunanin rungumata ba, sai dai ban an kare ba kawai na ji saukar numfashinsa akan fuskata saboda kusancin da muka yi dashi, da sauri na ja da baya shi kuma yaci gaba da tunkarata tamkar mai son rungumo ni. "Wai meye haka Umar Farouk". Na faɗa a tsawace cikin tsantsar ɓacin rai ina ci gaba da ja da baya, murmushi naga ya shiga yi irin murmushin da ban taɓa gani akan fuskarsa ba, abinda ban sani ba ashe dama tarko ne Umar Farouk ke haɗa mun akwai ƙetar da yake shirya mini, Kafin in kai ga yin wani abu ashe na ɗora ƙafata akan step ɗin farko da zaka sauka ƙasa don haka ina ƙara ja da baya sai ƙafata ta gurɗe, daga nan kuma ban koma sanin abinda ya faru ba sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti (School clinic), yunƙura wa nayi da niyar tashi naji kaina tamkar an ɗora mini dutse akai ya yi mini wani irin nauyi, saurin kai hannuna na yi sai na ji ashe naɗe yake da bandage, haka ƙafata itama an naɗe yatsun da bandeji, sai a lokacin na tuna da abinda ya faru dani na fashe da wani irin kuka, da sauri Nu'aymah data sallame sallah ta taso ta riƙo hannuna tana yimini sannu, "Wai me yasa sai ni? Me na tsare masa ne acikin makarantar nan da bazai ƙyaleni ba?" Nu'aymah ta riƙo hannuna sosai tana faɗin, "Waye kuma Janaam?" Na ɗago kai ina jifar ta da wani kallo haɗe da cewa, "Zaki ce baki san Umar Farouk ne silar faɗowa ta a saman steps ba bayan na tabbata agaban idon ki komai ya faru?" "Ya Allah! Kamar ya Umar Farouk Janaam? Hannu yasa ya turo ki kika faɗo ne ko kuma me yayi maki? Saboda yana wajen Shikennan ƙaddara baza ta sameki ba sai kice shi yai maki?" Murmushin takaici na saki haɗe da cewa, "Taya zaki yarda idan ma shi ɗinne Nu'aymah? Ai na san baza ki taɓa yadda dani ba indai a kansa ne". Na ƙare zancen tare da miƙewa ina dudduba hijab ɗina saboda na tafi gida ba zan iya zama a clinic ɗin ba don ba wani abu da nake ji ajikina, yar ƙara na saki jin wani zafi daga cikin yatsun kafata da aka naɗe ina dafa jikin ginin dake kusa dani, nafi minti uku a tsaye kafin cike da ƙarfin hali nafara ƙoƙarin yin tafiya, Nu'aymah ta ƙaraso da sauri ta ɗauki hijabi na ta saka mani sannan ta fara ƙoƙarin taimaka mani ina takawa na ce "miƙo mun niƙab ɗina na saka". Ta zaro idanuwa tana faɗin. "Ban gane na baki niƙab ki saka ba, a haka? wannan abun fa shine silar faɗowar ki akan stairs ɗin can Janaam, don Allah ki shafawa kanki lafiya kidena sakawa, wallahi a some muka kawo ki clinic ɗin nan kuma duk saboda shi tunda ba bari yake kina ganin hanya da kyau ba". Ban tanka mata ba don gaba-daya ma gani nake ta gama rena mani da hankali, taya ga gaskiyar abinda ya faru amma take ƙoƙarin maida wa akan saka niƙab ɗin da nake yi?, niƙab ɗina dana gani gefe ajiye na miƙa hannu na dauka na fara ƙoƙarin ɗaurawa ina faɗin, "Ni dai nasan silar faruwar wannan abu dani kuma ba zan bari ba wallahi, zan kai shi wajen student affairs a shiga tsakanina dashi, wannan abun ma da yayi mini Allah ya isa tsakani na dashi wallahi". "Subhanallahi! Janaam wace irin magana ce wannan kike yi? Ba dai kida sheda akan shiya turo ki kika faɗo, idan ma kina da ke kin sani babu wani acikin makarantar nan dake da courage ɗin zuwa ya bada sheda akan Umar Farouk ko da da gaske ɗin shi yai maki, don haka don Allah ko ma shi ɗinne kiyi hakuri ki yafe masa, zan yi magana dashi shima yayi hakuri wannan abun ya tsaya haka tsakanin ku saboda baya yimini daɗi". Ta ƙare zancen tana karɓar niƙab ɗin ta ɗaura mini ganin na ƙasa ɗaurawa sannan ta riƙa hannuna muka nufi office ɗin Dr daya duba ni, da alama dama sun bani damar tafiya idan na farka don muna shiga magunguna kaɗai ya bani muka fito.
Daƙyar nake yin tafiya zuciyata sai Allah ya isa nake faman yi masa don ni kaɗai na san abinda nake ji, a rai na kuma na san abinda Nu'aymah ta faɗa gaskiya ne ko da hannu Umar Farouk yasa ya turo ni na faɗo babu wanda zai iya bada shedar hakan balle ma ba hakan ya yi ba, don haka na yanke shawarar ƙyalesa kawai yaje shi da Allah.
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE
070404042435, GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUƁEMU A WANNN LAMBAR DON YA MALLAKI NASA.
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUDI NE BA KYAUTA BA, KI BIYA NAIRA 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435.
20.
Umar Farouk na zaune shi da abokinsa Saleem sai gasu Janaam sun zo wucewa, yadda Janaam ke tafiya tana ɗingisa ƙafa ya sashi kwashewa da dariya har yana rike ciki, da hannu ya shiga nunata yana cewa, "Saleem dubi yarinyar can bata yi maka kama da guragu ba? Wai ita smart to yau ina jarumtar tata take? Kana ji sai dai kaji Timm...abu na gangara yadda kasan buhun masara." Cike da tausayi Saleem ke kallon Janaam kafin ya maido kallonsa ga Umar Farouk yace,
"Haba Umar Farouk! wannan ba halinka bane walla.." kasa ƙarasa kalamansa yayi saboda wani irin kallo da Umar Farouk ya yi masa kafin ya miƙe ya biyo bayansu, duk wannan abun dake faruwa akan idanuwansu kuma akan kunnuwansu, sai dai ita kanta Nu'aymah haushin rashin kulawa da yai tunda suka shigo school yasa ta ɗauke masa kai duk da zuciyarta cike take da mararin sa da kuma ƙaunar sa. "Jimana Nu'aymah magana nake yi dake". Umar Farouk ya faɗa yana jerawa tare dasu, Kamar Nu'aymah bazata kulasa ba amma sai naga ta ja ta tsaya, cikin ƙarfin hali na kwace hannuna da take riƙe dashi ina ƙoƙarin tafiya nabar wajen naji yace, "Easy! Dama ba dake nake ba yan mata, mintuna uku zaki bai zan sallameta, idan kuma baza ki iya ba Allah ya raka taki gona, ko ba komai za ki yi kyau da wannan tafiyar taki da kika koma tamkar gurguwa". "Ya isa Umar Farouk meye haka kuma don Allah? Ina ka manta da alaƙa ta dakai tun jiya daka kasa nemana, na kuma kira ka ba adadi amma ka ƙi ɗagawa daga karshe ma sai kashe mani waya kayi, haba Umar Farouk wannan shine abota? Kuma abotar ma ta gaskiya? Me zaka fadamun yanzu daka tsaida Ni?" Nu'aymah ta faɗa cikin ɗan ɓacin rai tana kallonsa, haɗe rai Umar Farouk yai yana yimata wani kallo daya sa cikinta murɗawa tare da sauke kanta ƙasa, tsaki yai kafin yace, "Ke! Waya faɗa maki ana yimin tsawa? Don na baki damar shigowa rayuwata da sunan abota ba shi ke nufin kin banbanta da sauran mutane da har zaki faɗa mini duk maganar data fito daga bakinki ba domin ni ba sa'an ki bane, banda mutunci zan iya yimiki fiye da abinda duk wanda ya shiga gona ta zan iya yi masa, wa yace ki kirani dama? kin ajiye ni ne da zaki yi tsammanin dole sai na ɗaga kiranki? Bana buƙatar damuwa ko kuma takurawa musamman akan abinda ya shafi waya, don haka kada ki sake kuskuren kira na, idan har ina bukatar hakan ni zan kira ki da kai na, and lemme tell you one thing, this will be the last da zaki sake ɗaga mini murya kin gane ko?". Jikin Nu'aymah ne ya yi sanyi lokaci ɗaya tsoronsa na dirar mata a zuciya tayi saurin cewa, "To kayi hakuri hakan baza ta sake faruwa ba". Bai tsaya tanka ta ba ya juya ya bar wajen don dama burinsa ya gama cika na son tsayar da Janaam tare da bata mata lokaci, Nu'aymah ta juya a sanyaye jikin ta ba ƙwari tana hawaye ta nufi inda Janaam ke ta ƙoƙarin takawa da kanta cike da ƙarfin hali.
Ban tanka ta ba koda ta ƙaraso ta riƙani saboda ina bukatar taimako muka nufi inda motarta take, ta buɗe mini na shiga sannan ta zagaya ta gefenta ta buɗe ta shiga ta tayar muka bar wajen, duk yadda zuciyata ke cunkushe da maganganun da Umar Farouk yai mini lokacin dana kalli yadda Nu'aymah ke driven tana faman share ƙwalla sai da tausayinta ya kama ni, a hankali na ɗaga hannuna na ɗora saman kafaɗarta, bata iya juyowa ba ta kalleni amma na tabbata hankalinta ya dawo a guna, cikin sanyin murya nace, "Besty don Allah kifita shirgin Umar Farouk, ki ƙyalesa wallahi rayuwar ki bata dace dashi ba, duk mutumen da bazai girmama wanda ya damu dashi ba wannan mutumen bai cika dan halak ba da zai iya ramakon Alkhairi da Alkhairi, pls don Allah ki rabu dashi Allah zai baki wanda yafi shi". Sai da Nu'aymah ta ɗauke kwalla ga idanuwanta sannan tace, "Bazan iya ba Besty, ina son Umar Farouk irin son da ni kaina tsoro yake bani, taya kike tunanin zan iya barin shi haka kawai ta cikin sauƙi? Bazan iya ba wallahi". Ta ƙare zancen tare da juyowa ta kalle ni cike da tausayi na ce da ita, "Allah ya kyauta." ta amsa da amin.
Yau Umar Farouk ransa fari tas yake saboda abinda ya yi wa Janaam ba ƙaramin faranta ransa yai ba, tafe suke shi da Saleem suna dariya da alama ko firar me suke yi tayi masu daɗi suna nufo wajen motarsa, hango su Billy a jikin motar tasa ya sashi saurin haɗe rai, tun safe suke binsa suna yi masa magana yai banza dasu, duk inda ya je sai sun bishi shi kuma sai ya tashi ya bar masu wajen ba tare daya yimasu magana ba, daga karshe ne ya buga masu kwakkwaran jan kunne akan duk wacce ta sake zuwa inda yake sai ya wulaƙanta ta, wannan shine dalilin daya sa da suka gama lecture ɗin ƙarshe suka zo suka tsaya jikin motar sa suna jiran fitowarsa.
Yanzu ma ko kallon su bai yi ba ya buɗe motarsa ya shiga, roƙonsa suka shiga yi suna ƙoƙarin duƙawa ƙasa tare dayi masa magiya amma yai kamar bai gane su ba yana tada motar sa, kallonsa Saleem yai haɗe da cewa, "Su kuma me suka yi maka ne? Please ka saurare su don Allah". Cikin fushi Umar Farouk ya juyo yana kallon sa yace "Nafi son duk yar iskar data shiga gabana cikin su na take ta na wuce akan na tsaya na saurare su, kasan abinda sukayi ne? Mtsss...Ba na da lokacin ɓatawa tsayawa faɗa maka ko mene, Yana gama faɗar hakan ya ja motar da ƙarfi yana baɗe su duka da ƙurar wajen, tari suka shiga yi suna kakkaɓe jikinsu, sun san duka wannan fushin yana yin shi ne akan abinda ya faru jiya wanda suma sun san ba suda gaskiya musamman da suka ji abinda ya faru da Felicia, shi yasa suka nace da bashi haƙuri ko zai sauko ya hakura amma daga ƙarshe ga abinda yayi masu.
Kwana uku Felicia tayi bata zo makaranta ba har sai data samu sauƙi, rana ta uku data shigo bayan angama lecture ta samu Umar Farouk cikin motarsa ya kure volume sai sauti yake sha, yana ganin Felicia ya rage volume tare da ɗan sakar mata murmushi kaɗan wanda yasa su Billy dake gefe mamaki kusan kashe su, cikin girmamawa ta ɗan russuna tana gaishesa, ya amsa yana yimata ya jiki ta amsa masa da taji sauki, ganin haka yasa su Billy tamkar munafukai suka ƙara so wajen suka gaishe sa suma, ga mamakin su sai gashi ya amsa masu, a kwanaki ukun da Felicia bata zo ba ko kallon su baya yi balle ya amsa gaisuwarsu idan suka yi masa, asali ma ko haƙurin da suke daman bin shi suna bashi ƙin saurarsu yai sai yau da Felicia ta shigo, ƙoƙarin rufe motarsa yai bayan ya maida ƙafafuwansa ciki zai tayar sukayi saurin riƙe marfin suna yin nile down ƙasa haɗe da sake bashi haƙuri, Felicia ya kalla dake gefe ta ce, "Please sir." Ya mai do kallonsa garesu sannan ya kashe motar ya fito ya yi tsaye agabansu yana kallon su ɗaya bayan ɗaya fuskar nan ba alamun wasa, hannunsa ɗaya na cikin aljihu ya shiga nuna su da ɗaya hannunnun yana cewa, "Ashame of you Wllh duka kun bani mamaki, kuna mata ace kun kullawa mace yar uwar ku makirci don ku cutar da ita, wannan ba ita kuka yiwa ba ni kuka yiwa, and i know what to do, To wallahi bari kuji, dubu goma akayi treating ɗinta kuma sai kun haɗa mata su duka, sannan suma kuɗin abincin da kuka ce ita zata biya sai kun haɗa su yanzun nan indai har kuna so na saurare ku". Da sauri Billy ta ciro dubu biyar tana faɗin, "zamu bada, wannan nawa ne, ku haɗo naku don Allah bazan iya da shariyar boss ba". Ta faɗa tana miƙa masu hannu kowa ya ciro abinda yake dasu ya bata, kuɗi ne masu yawa yai murmushin jin sunan da Billy tayi masa kafin ya sa ta miƙawa Felicia kuɗin, hannun Felicia na rawa ta karɓa tana kallon sa ya ce, "Kije ki cigaba da kula da lafiyarki, but lemme tell you one thing, dake dasu kar wacce ta sake zuwa inda nake, i have don with you people saboda ba kuda amfani a tare dani, mind you kar wacce ta kuru tace zata bani hakuri cikinku don zan iya takata da mota". Ya kare zancen yana nuna su su duka sannan ya shige motarsa ya ja yabar wajen, sai daya fice daga makarantar sannan ya fito da wayarsa ya kira Nu'aymah, suna bayan hall ɗin da suka gama ɗaukar lecture ita da Janaam suna sake duba handout ɗin da zasu rubuta C.A an jima taga shigowar kiransa, kwana biyu kenan data fita harkar sa duk da ita kadai tasan wahalar da take sha na rashin kulawar da bata yi masa, kamar baza ta ɗaga ba sai kuma ta kai hannu ta ɗauki wayar daga kan table ɗin da take ajiye ta ɗaga tana kaiwa a kunnen ta. Ƙin yi masa magana tayi data ɗaga kiran haka shima sai bai ce mata komai ba ya ci gaba da driven ɗinsa, kusan mintuna biyar suna a haka kafin can Nu'aymah tace, "zan iya ajiye wayar?" "Idan kina buƙatar hakan, amma kafin nan ki sani ni ba'a kashe mini waya idan na kira, kina ina ne?" "School mana". "Ya akayi da aka gama lecture ban gaki ba sai dai ƙawarki mai sa niƙab? Ashe ta warke zamu ci gaba da game ɗin mu daga inda muka tsaya, har yau 1-0 muke da ita?" Nu'aymah dai bata ce komai ba tana saurarensa ya ci gaba da cewa, Anyway na fita me zan siyo maki na san bakiyi breakfast ba". Rasa me Nu'aymah zatai ta yi, farin ciki ko kuma akasin hakan domin idan tace yar wannan kulawar daya bata yanzu bata faranta mata rai ba tayi karya, "Hello Nu'aymah kina jina?" "Eh". Ta faɗa tana kallona, kiran daya shigo a waya ta nima ya sani daukar wayar na miƙe na bar wajen, daga haka ban san yadda suka ƙare wayar ba ita dashi sai gata ko dana dawo na iske ta tare da wata course mate ɗin mu tana dariya, wanda zan iya cewa kusan kwana biyu kenan ko murmushin Nu'aymah na dena gani in ba tunani da kuka ba akan mutumen da nake ganin ba ƙaramar hasara bace zaunawa tana zubar masa da hawaye..
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA, KI BIYA NAIRA 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
21.
Sosai a 'yan kwanakin shaƙuwa ta shiga tsakanin Nu'aymah da Umar Farouk da muka ga ya yi fatali da ƙawayen nasa wato su Felicia da Billy, wanda kai tsaye zan iya cewa wataƙil saboda shirin da suke yi da Nu'aymah ne don kai tsaye na san zata nuna masa bata ra'ayin tarayyar sa dasu, a ɓangare na kuma dashi babu abinda ya sauya, duk hanyar daya san