Showing 18001 words to 21000 words out of 157423 words
dana gama ban bi takan wayata ba har sai da nayi azkhar ɗina na kammala na gyara ɗakina, lokacin kusan ƙarfe bakwai da wani abu, na nufi ɗakin Mamah ina buɗe wayata, message ɗinsa ne na gani har guda biyu sun shigo, na farko na fara buɗewa na karanta, ɗauke yake da tarin kalamai na so da ƙauna da suka jefani a cikin shauƙi marar misaltuwa, na biyun kuma sake jaddada mani irin kewata da zai yi yake haɗe da yi mini bankwana, nan take nima na ji cewa tabbas zanyi kewarsa duk da ba wani shaƙuwa muka yi dashi ba. Text message na rubuta masa nima ina mai yi masa addu'a tare da fatan Allah ya saukesa lafiya sannan na tura ina sauke ajiyar zuciya.
Da ma zaune na isko Mamah tana karatun alkur'ani na zauna zaman jiran ta ƙarasa, tana kammalawa ta ɗago kai tana cewa. "Janaam har kin tashi?" "Na tashi Mamah ina kwana, an tashi lafiya?" Tana rufe alƙur'anin ta amsa mini da "lafiya ƙalau Janam , halan yau ba school?" "Akwai amma sai zuwa ƙarfe sha biyu". "Allah ya kaimu". Mamah ta faɗa tare da miƙewa ta nufi kitchen, ni kuma tsayawa nayi na fara gyara mata ɗakinta na share na goge sannan na dawo palour shima na gyara shi na goge na turara turaren wuta na ɗan fesa room freshener yadda ƙamshin zai yi irin daɗin da Ya Jameel ke so, don sam baya son shigowa yaji ƙamshin turaren wuta da hayaƙi na tashi. Kitchen na wuce na samu Mamah na riƙa mata aikin da take yi muka ƙarasa haɗa breakfast ɗin a tare, bayan mun gama ta wuce ɗaki ta yi wanka ni kuma na kwashi abincin na kai dining na jere na sake dawo kitchen na gyara inda muka yi aikin na wanke kayan da muka ɓata, sai da naga yayi Mani tas yadda nake buƙata sannan na fito na wuce ɗakina nima na shiga wanka.
Nu'aym kuwa bai ga message ɗin Janaam ba sai da ya shiga jirgi yana ƙoƙarin tashi, sosai ya ji daɗi kafin a gurguje ya tura mata da, _"thank you kyakkyawata, zanyi kewarki sosai, Please ki kula mini da kanki". _
Muna breakfast saƙon Nu'aym ya shigo, da yake wayar na a hannuna nayi saurin buɗewa na karanta, murmushi na saki bayan gama karanta sakon sannan na ajiye wayar na maida hankali ga cin abincin da nake yi, amma fa zuciya ta kasa daina tunani haɗe da hango fuskar Ya Nu'aym yana mini murmushi, Allah ya sani tsakanin jiya da yau ya shayar dani madarar ƙauna sannan ya tsuma ni da salon zazzafar soyayyarsa ta yadda bansan lokacin da nima na kamu da soyayyarsa ba.
******
Kallonsa Momy keyi tun daga sama har ƙasa ganin shigar dake jikinsa, kuma a hakan shirin zuwa makaranta ne yayi yazo ya faɗa mata ya tafi, girgiza kai tayi kafin tace. "Umar Farouk amma dai bada wannan shigar zaka tafi makarantar ba ko?" Kallon kansa yai sama da ƙasa shima, saye yake cikin gajeren wando da amless ɗin riga na kamfanin Puma, sai wata irin rafkekiyar sarƙa daya saka a wuyansa, a gefen aljihun wandonsa kuma ya soka handkerchief a ciki, ga wata sarƙa mai manyan duwatsu daya saka a hannayensa, sai kuma jaka mai dogon hannu daya ratayo ta wuyansa zuwa ƙarƙashin kafaɗa, sai yan kunnaye daya saka a kunnuwansa da wani kyalle daya daura a saman kansa daya sha wani kalar aski dasu Felicia suka rakasa akayi masa jiya, snickers ne a ƙafafuwansa fuskarsa tasha baƙin glass, kallo ɗaya zaka yi masa ka gano babu mutunci a tattare dashi ga duk wanda ya shiga gabansa yau, murmushi ya saki ganin yadda Momy ta haɗe rai tana jefo masa tambayar haɗe da cewa. "Menene laifin shiga ta Momy? Na rufe inda ya zama dole na rufe a jikina so me zai hanani fita haka?" "Haba Umar Farouk! Kai baka rabuwa da abinda zaka janyo mini magana ne? Ka fa san halin Dadynka idan ya ganka da wannan shigar ba lallai ya ƙyalesa ba, idan tani ce wannan ba abun damuwa bane, amma surutun da zai yimaka ne kasan bazai mun daɗi a rai ba". Rungumeta yai yana dariya haɗe da cewa. "Momy ƙyalesa, ki nemi kaɗa kawai ki toshe kunnuwanki, in da sabo kuma ni na saba da faɗan sa, so bazai ɓata mun rai ba ko da ya ganni ya yi mun faɗan". "Ka tabbata?" Momy ta faɗa tana kallonsa don duniya ba abinda ta tsana sama da ɓacin ransa, yai mata murmushi yana kada mata kai alamun tabbatar mata da hakan, addu'a tayi masa Allah ya tsare sannan ya fice, jakar dake jikinsa ya buɗe ya ciro key ɗin motar Dady sabuwa daya ɗauko ba tare da Momy ta sani ba, mai gadi yakira yasa ya cire rigar dake jikin motar, ba tada wata datti don shekaran jiya aka kawo masa ita ya buɗe ya shiga sannan ya tayar, sai daya bata wuta sosai kafin yai wani irin reverse da ƙarfi, dai-dai lokacin Dady da fitowarsa wanka kenan Momy na taimaka masa yana gyarawa yaji ƙarar tada mota da ƙarfi hade da yin reverse, da sauri ya fito Momy na biye dashi gabanta na faɗuwa, suna kawowa Umar Farouk na jan motar da karfi, cikin ɗaga murya Dady ya shiga cewa mai gadi ya rufe masa gate amma inaa.. kafin mai gadi yakai ga rufewa har Umar Farouk ya fice aguje, cikin ɓacin rai Dady ya juyo yana kallon Momy tare da nuna gefen da sabuwar motarsa take ajiye daba komai wajen sai rigarta a ƙasa yana cewa. "Kin gani ko? Yaron nan sam baya da hankali, sabuwar motar tawa da aka kawo shekaran jiya zai ɗauka ya tafi da ita wajen shashancinsa? Har ya akayi yaga makullan motar ya ɗauka kuma baki hana shi ba?" Shiru Momy tayi haɗe da sadda kai ƙasa ba tare data ce komai ba don ita kanta bata san lokacin daya ɗauki makullan motar ba, tsawar da Dady ya daka mata ta sa ta ɗagowa a ɗan zabure tana kallonsa, "ba dake nake magana ba?" Ya sake tambayarta ransa a ɓace, ganin mai gadi na kallon su yasa Momy juyawa ta koma ciki ya yi saurin bi bayanta yana cewa, "Au renin har ya kai haka ina magana kina tafiya? wato ke da ɗanki na fahimci so kuke yi ku maida ni mahaukaci acikin gidan nan ko?" "Haba Alhaji wace irin magana ce kakeyi haka fisabilillahi? Shin wai yaron na ba ɗanka bane da zaka ce bazai yi iko da abinka ba? Menene don ya dauki motarka ɗanka ne fa? Kuma tunda kaga ya ɗauki motar ina ga tashi ta samu matsala ne". "Oh k! Na fahimci da saninki kenan yai haka? To wallahi daga ke har shi na baku awa biyu kacal ya dawo mini da motar nan ko ku haɗu da fushi na da baku taɓa gani ba". Yana gama faɗar hakan ya juya ya fice daga gidan ba tare daya bi takan breakfast ɗin data haɗa masa ba, so take yi ta dakatar dashi amma yaƙi saurarenta, ranta a ɓace tace, "menene fisabilillahi don ya ɗauki motarsa, idan bai dauka ba to tawa yake so yaje ya dauka? Mtss.. Allah ni bana son wannan halin da kake wa yaron nan ko kaɗan". Tayi maganar tamkar mai yi da wani kafin ta wuce ɗaki ta ɗauki wayarta ta shiga laluben lambarsa.
Umar Farouk kuwa yana kawowa bakin gate ɗin shigowa makaranta ya hango motar Nu'aymah a gaba, sai data shiga sannan ya shigo shima yai saurin jerawa da motarta haɗe dayin horn yana sauke glass, kamar ance Nu'aymah ta juyo idanuwanta suka sauka akan Umar Farouk ya sakar mata wani shu'umin murmushi daya saka zuciyarta kaɗawa, hannu ya ɗaga mata yana faɗin. "Hi Aymah Good morning". With so much happiness Nu'aymah ta rage taka motar tana cewa, "Morning Umar Farouk, how are you doing?". Ya amsa mata da "Fine", sai daya kalli gabansa da yake tuƙi yana sake riƙe steering wheel ɗin motar kafin ya juyo ya kalleta yace, "You look so cute". "You too looking so beautiful Umar Farouk ". Nu'aymah ta faɗa cikin rawar kai da wani maɗaukakin farin ciki, Janaam kuwa dauke kai tayi cike da takaici da ganin Nu'aymah zata ɓata masu lokaci su makara shiga class har azo afara lecture bada su ba...
Call/Watsapp 07040402435
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
12.
Murmushi Umar Farouk ya saki haɗe da cewa. "Friends?" yana miƙoma Nu'aymah hannu ta jikin motarsa, Nu'aymah tayi dariya haɗe da cewa, "Are you kidding me?" Umar Farouk ya amsa da "No can we be friends?" Dariya ta sake yi tana sake riƙe steering motar tace. "Yeah why not?" Tayi maganar cike da farinciki tana miƙo masa hannu kamar zasu tafa suka sa dariya. Gaba Umar Farouk yai yana jin daɗin yadda yaga Janaam ta cika tayi fam saboda ɓata masu lokaci da yai, ita ko Nu'aymah ji tayi tamkar an gafarta mata, ganin abinda ya faru takeyi tamkar a mafarki, wai Umar Farouk ne da kansa zai ce su zama abokai? Wow! wace irin rana ce yau mai sa'a ta taka? Ta tambayi kanta cike da jin daɗi tana cewa Janaam, "Ai na faɗa maki he's very nice person besty baki yadda ba, don Allah duba kiga abinda kika yi masa jiya amma duk da yasan tare nake dake bai kullace ki arai ba ya tsaya munayi magana, gaskiya ki cire wannan tsanar da kika yimasa don abinda ya faru jiya tsakanin ku kece mai laifi kuma baki kyauta ba". Kauda kai nayi ba tare dana tanka mata ba har muka iso department ɗin mu, kai tsaye class muka shiga saboda har anfara lecture zuciyata sai ƙuna takeyi akan wulakancin da Nu'aymah ta yimun.
Kamar yadda yake a ƙa'idan ce awanni biyu ake ɗauka ana lecture kafin a gama koma sama ga haka, kasancewar ba muda wata lecture a gaba yasa a wannan lecture ɗin sai da muka buge kusan awa uku munayi, malamin irin lecturers ɗin nan ne masu tsanani da ba ko yaushe suke da time ba na zuwa karantar da ɗalibbai saboda wasu uzurukka na rayuwa, sai dai suna ba lokacin da suka samu na karantar da ɗalibban muhimmanci sosai. Shi yasa babbar matsalar malamin shine attendance, matukar ba kada 75% na attendance ɗinsa to baza ka taɓa passing course ɗinsa ba, yau ma yana gama lecture yasa a dauki attendance akai masa a mota bayan ya kidaya mutum ko nawa ne, Umar Farouk ya fiddo takarda ya fara rubuta sunansa duk da ko ba shi ne c.rep ɗin mu ba, ɗaya bayan ɗaya ya riƙa miƙowa ana rubuta sunaye, yana zuwa kaina ya tsallake, banza nayi masa da niyar idan ya gama zan karɓa na rubuta sunana ga wanda ya rubuta sunansa na ƙarshe, ba tare dana makare ba na karshe na gama rubuta sunansa ya wafce takardar, kafin na yunƙura nake na karɓa a hannunsa ɗin na rubuta sunana har yaje ya kaima malamin dake zaune cikin mota yana jira takardar, yana bashi kuma ya tayar da motarsa ya tafi, a bakin kofa mukayi clashing da Umar Farouk nayi folding hannaye na akan kirji cike da ɓacin rai ina kallonsa, wani shu'umin murmushi ya saki yana yi kamar bai ganeni ba tare da raɓawa ta gefe na ya wuce abunsa, kwalla na ji sun cika mani ido nayi saurin gogewa don bana son ya gani reni ya shiga tsakanin mu, kasa komawa cikin class ɗin nayi jin ihu da suke yi ana tafawa Umar Faruk tare da kambama wankansa da sam baya da maraba dana yan iska a idanuwa na, Nu'aymah kuwa tuni naji yana sanar dasu itace best friend dinsa a kaf faɗin makarantar kar wanda yayi kokarin ɓata mata rai domin hakan zai sa a haɗu da fushinsa, juyawa nayi na kalli Nu'aymah sai wani farin ciki take yi, murmushin takaici na saki kafin na koma na dauko handbag dina na fito daga ajin, don naga abun nata tamkar tana neman zaƙewa sai kace ta manta waye shi, da sauri na ji ta biyo bayana tana faɗin. "Janaam wait ina zaki je kuma?" Cak na tsaya ina kallonta ta cikin niƙab cike da takaici kafin nace, "Ina zan je kike tambaya besty? Wai me ya sami kanki ne? Umar Farouk ne fa da babu wanda bai san irin tsagerancinsa da rashin mutuncinsa ba acikin makarantar nan! Shine zaki ƙulla abota dashi har kina wani washe baki a gabansa? Kin manta da wulakancin da yayi maki a tsakiyar filin makarantar nan har zaki zo ki wani biye masa, Gaskiya kin bani kunya besty". Hannuna ta riƙo haɗe da cewa, "Oh my God! Besty me yasa abu baya wucewa a wajen ki ne? Ya fa bani hakuri don me zan riƙesa arai? Sannan kuma ai jiya agaban mutane kika maresa kema amma kina gani bai riƙeki a rai ba, don..." Saurin dakatar da ita nayi ina ɗaga mata hannu haɗe da cewa. "Ya isa haka Nu'aymah, ai ina ga ba wani abun zamuyi ba yanzu tunda mun gama lecture ko? To sai kizo mu tafi gida ni bazan iya kallon wannan kayan haushin ba?" "Shikenan na ji, amma Please ki saki ranki". Nu'aymah ta faɗa tare da riƙo hannuna muka nufi wajen motar ta muka shiga ta tayar muka wuce, bamu kai ga ƙarasa fita ba wayarta dake saman steering wheel ɗin motar tayi ƙara, "Please besty duba ki gani waye?" Ta faɗa ba tare data kalleni ba, ba musu n mika hannu na ɗauko wayar, *MY DREAM* naga an rubuta a jikin screen ɗin na zaro idanuwa haɗe da ɗago kai na kalleta ina miƙa mata wayar nake cewa, "Your dream! Yaushe kika fara soyayya ban sani ba besty?" Hannu ta ɗaga mani tana dariya bayan ta kai wayar a kunne, "Hello". Ban ji me aka faɗa ba acan cikin wayar ba bayan sakanni da ɗaga warta sai gani nayi tayi parking gefe tare da cire wayar a kunnenta. Tsareta ɗin da taga nayi da idanuwa yasa tayi murmushi tana cewa. "Kai Besty! Wannan kallon fa? Sorry bani mintuna biyar ya karaso muyi sallama". "Wai waye Your dream ɗin naki? Zai shigo ne ko dama a makarantar nan yake?" Dariya ta saki tana kwantar da kanta a jikin seat ɗin motar kafin tace, "Umar Farouk ne fa, tun ranar daya kirani nayi saving ɗin number sa da wannan sunan, shine my dream man". Buɗe motar nayi da niyar fita sai gashi yayi parking dai-dai ta gefen da nake, rasa yanda zanyi nayi saboda tsananin ɓacin rai sai dai kawai na kawar da kaina, yana dariyar da nake da tabbacin yana yi ne don ya ɓata mini rai yace, "Haba Aymah waya faɗa miki haka ake abota, tafiya ba sallama!" Dariya tayi kafin tace. "Am sorry zan kiyaye yin haka gaba". Felicia dake gaban motar sa tayi tamkar zata fashe don takaici, wannan karon ba ita kaɗai ba gaba-daya yan matan nasa dake cikin motar daya ɗauko ji suke yi tamkar su fita su rufe Nu'aymah da duka saboda ganin ogan su ya fara maida hankalinsa kanta, a tunaninsu son ta yake yi ko kuma soyayya suke, motarsa ya ja yana ɗaga mata hannuhade da cewa. "Bye". Ta amsa da "Bye Farouk". Sannan ta ja motar ta muka fice, kasa jurewa nayi sai dana kalleta cikin ɓacin rai nace. "I think dole mu raba hanya dake Nu'aymah matukar zaki na yin haka dashi idan muna tare saboda bazan iya ɓata lokuta na masu matuƙar muhimmanci ba ina jiran ki akansa ba wallahi". "Ya Allah, ni kam na rasa me Umar Farouk ya tsare maki Besty, yanzu wannan yar tsayawar da muka yi har ya yi maki abinda ya ɓata maki rai? To koyi hakuri kin ji". Ta faɗa tana juyowa haɗe da kallona, harara kawai na maka mata na dauke kai don bansan kuma me zan sake cewa ba tunda ta rufe baki na ta bani hakuri.
Umar Farouk kuwa tsabar farin ciki kiɗa ya ƙure a motarsa yana jin daɗin yadda yau ya ɓakanta ran Janaam, duk da bai ga fuskarta ba idanuwanta kaɗai sun tabbatar masa da saƙonsa ya isa yadda yake buƙata, don haka kai tsaye wata restaurant ya wuce dasu ya siya masu abinci suka ci, tsabar farin ciki yasa ko wacensu ta ɗauki duk abinda take so a ɓangaren snacks da drinks aka sa musu a leda ya biya sannan suka fito, kuɗi ya rarraba masu ko wacensu ta kama hanyarta shi kuma ya shiga motarsa ya tayar yabar wajen aguje.
Ko daya iso gida a harabar gidan hango Momy tsaye, tayi kiransa a waya har ba adadi bai ɗaga ba gabaɗaya hankalinta ya tashi, abokinsa Ridwan kuma ta kira sa ta tambayesa ina Umar Farouk ya sheda mata cewa shi yayi tafiya kwana biyu bai shiga makarantar ba basa tar don ko waya basu yi ba, tsoronta ɗaya kar wani abu ya samesa tunda taga yadda ya fita aguje da motar.
Yana shigowa cikin gidan ta sauke ajiyar zuciya, wajenta ya nufa bayan ya yi parking ya kashe motar ya fito, "Momy lafiya?" Ya faɗa ganinta a waje tamkar mai jiran tsammani, ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa, "ina ka shiga Umar Farouk ina ta kiranka baka ɗaga ba duk kabi ka ɗaga mini hankali?" "Haba Momy, nifa ba yaro bane ki daina damuwa haka saboda ni Please, kiyi hakuri nabar wayar ne a mota". "To mu shiga ciki ka samu kaci abinci muyi magana". Ta faɗa tana kamo hannunsa suka shiga daga ciki, a palour suka zauna Umar Farouk na cewa "Momy a ƙoshe nake mun biya restaurant ni dasu Billy mun ci abinci, mu dai yi maganar kawai, me yake faruwa?" Cikin sigar lallashi Momy ta fara magana tana cewa. "Farouk me yasa ka ɗaukarwa Dadynka mota?". Yarfa hannayensa biyu ya yiwa a