Showing 141001 words to 144000 words out of 157423 words
kamar waccan ranar, don haka bata ce komai ba ta miƙe bayan ta kwashi robar alayyahun da suka gama gyarawa ta bar palourn, tana fita Janaam na shigowa ɗauke da tray da gorar ruwa da kwalin lemu da kuma kofi akai, wannan karon ta sako hijabi ajikinta da alama tsayawar da tayi wajen sashi shi yasa ta ɗan jima bata dawo ba, a gaban Momy dake bin ta da wani kallo ta ajiye tray ɗin, har ta juya zata fita Momy tace, "Ki zauna mana wajenki nazo muyi magana". Gaban Janaam yai wata irin faduwa don har ga Allah gaba-daya ita tsoron wannan matar take yi amma sai ta dake bata nuna hakan ba ta juyo ta nemi ɗaya daga cikin kujerun da ke gefen ta Momy ta zauna, kallonta Momy keyi cike da mamaki da ganin tsantsar rashin ɗa'arta data iya zama akan kujera kamar yadda take, ita dai Janaam kanta na ƙasa tana wasa da zoben yatsanta da Nu'aymah ta bata bata masan tana yi ba sai da taji muryata tana cewa, "Gani nazo yau agareki ba'a matsayin jami'ar dake aiki da gwamnati wajen kare hakkin ɗan Adam ba ko kuma nace lauyan dake kare Umar Farouk, na zo ne a matsayina na uwa data sha wahala wajen ɗaukar cikin ɗanta har na tsawon watanni bakwai, ta juri laulayi da yunwa acikinta, rashin lafiya da rashin bacci don tabbar data haifo jaririnta lafiya, ta kuma sadaukar da duka rayuwarta ranar haihuwarsa don wanzuwar tasa rayuwar aduniya, ta renesa cikin so da kauna tare da alfahari samunsa, ta hakura da farin cikinta domin nasa farinciki, na san duk da baki san zafin rashin ɗa ba ko shigarsa a wani yanayi kinsan yadda uwa ke shiga damuwa da tashin hankali idan yana cikin damuwa balle kuma ace za'a rabata dashi, kamar dai yadda naga mahaifiyarki tsaye akanki saboda rashin lafiya kaɗai ta sadaukar da komai ciki har da lokacinta ta zauna dake a asibiti don tabbatar da kin samu lafiya bata rasa ki ba, Umar Farouk ɗana ne da nake matukar kauna aduniya da nake jin tamkar ubangiji ya haɗa lumfashina da nasa waje ɗaya ne da idan har na rasa shi nima zan iya rasa kaina, na san duk wasu dabi'u da kuma halaye nasa da ake kallo a matsayin rashin ji da abinda zai iya aikatawa da wanda bazai iya ba, hakan yasa na kasa yardarwa kaina har yanzu cewa shi ya aikata kisan da ake zargin da da shi har sai da na gano gaskiya, a bayananki da binciken da mukayi na tabbatar bashi yai wannan kisan ba kece wacce kika yi kuma kema kin san hakan, na gano cewa kin je gidan su ƙawarki Nu'aymah kin tadda gidan ba kowa, a tunanina wani abu yayi kokarin faruwa a lokacin tsakanin ki da wanda aka kashe wanda hakan yasa kika aikata abinda ya faru, a lokacin shi kuma Umar yazo anguwar wajenki sai aka sheda masa cewa kina gidan su ƙawar taki, kasancewar gidanku da nasu babu nisa kai tsaye sai ya nufi gidan, bisa bayanin da yaiwa kotu a tunanina akwai abinda ya alamta masa cewa akwai matsalar da har ta kai shi ga shiga gidan ya isko abinda ya faru..." shiru Momy ta yi tana jin wasu kwalla da takaicin yaron nata daya jefa kansa acikin halin da yake ciki kafin taci gaba da cewa...
ALLAH YA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
67.
"Wauta da yarinta da kuma soyayya ta ɗebe sa ya amshi laifin da ba nashi ba a kansa ba tare da tunanin komai ba, ya manta cewa wani masoyi yafi guba dafi domin lokaci ɗaya zai zamo silar ajalinka, guba kuma zata yi maka lamuni tayi ta aiki jikinka sannu a hankali har lokacin da zatafi ƙarfin ka, idan har zai iya sadukar da rayuwarsa akanki ina tunanin yakamata kema kiyi masa halacci ki faɗi gaskiya, soyayya ba tana nufin a so ka kaɗai bane a kuma yi sadaukarwa a kanka, soyayya na nufin ka so a so ka, ka kaunata a kaunar ka sannan ka sadaukar a sadaukar maka, ka ji tausayi a tausaya maka, kayi halacci kaima ayi maka, so baya da ido, baya da tunani sannan baya da hankali, abu daya ya sani kuma yake fahimta shine a mayar masa da fiye da abinda ya bayar, mafi ƙaramci abashi dai-dai abinda ya bayar ba tare da tawaya ba, duka hujjojn dana haɗa na kuma tanada ba su da karfin wanke Umar Farouk kuma baza su iya kuɓutar dashi ba daga hukuncin kisa da zai fuskanta daga wajen mahaifinsa, ki hango tashin hankalin da mahaifi zai shiga a lokacin daya tabbatar da cewa ya bada umurnin kashe dan sa da ya haife da cikinsa kuma ya rene sa da hannuwansa har izuwa girma wane raɗi zai ji a zuciyarsa yayin yanke wannan hukunci don tabbatar da adalci? ki dubi raunin da uwar data jingine aiki na tsawon shekaru talatin da wani abu zata tsinci kanta acikin bayan ta dawo abakin aikinta don kare ɗanta idan har akace batayi nasara ba, na rokeki ki bayyanar da gaskiyar da ita kadai ce zata kubutar ɗana don Allah". Ta ƙare zancen tana haɗe hannayenta waje ɗaya alamun rokon Janaam sannan ta miƙe ta mayar da gilashin idanuwanta tabar gidan ba tare dako sallama ta samu sunyi ba, ta bar Janaam da nazari da tunanin kalaman nata da gabaɗaya sun gama sanyaya mata guiwa tare da sa jikinta mutuwa.
*******
Tun Nu'aymah na kallon abinda mahaifin nata keyi tamkar a mafarki har ta koma gasgata zancen dan kuwa ya saka mata takunkumi sosaibaya barinta fita ko nan da cen gashi ya karɓe mata waya, a palour ma ba tada ikon saukowa saboda in dai yana gida to kullum yana zaune a palourn, abun da ya daure mata kai hatta Ummie ma bata shiga sabgarta yanzu gabaɗaya iya kacinta da ita gaisuwa idan ta je gaisheta, tana buɗe baki kuma zata fara yi mata wata maganar daban zata tashi tabar mata wajen, gashi tana kirga kwanakin da suka rage a koma kotu a yankewa Umar Farouk hukuncin kisan da bai aikata ba yau saura kwana biyu, gabaɗaya ta rasa yadda zata yi, Nihal ce ƙanwarta ta shigo ɗakin tana faɗin, "Addah Nu'aymah wai Ummie tace me zaki ci akawo miki?" Ta riko hannunta ta zaunar da ita kusa da ita haɗe da cewa, "Nihal bana jin yunwa". "Me yasa Addah?, kin ga yadda kika koma kuwa? Me yake damunki ne?" "Ba komai Nihal, kin ga yanzu dai so nake ki taimaka mun kije ki dauko mini wayar Ummi zan tura sako kin ji? amma kar ki bari ta gani sai ki faɗa mata nace duk abinda aka kawo mun zanci sai ki zo mun da wayar". Kallonta Nihal ta shiga yi kamar mai ƙoƙarin gano wani abun kafin ta mike kuma tafita. Ba'a jima ba sai ga Nihal ta dawo ta ciro wayar acikin rigarta ta miƙa mata, jiki na rawa Nu'aymah ta karɓa ta rungumeta tana cewa, "Yawwa sis jeki anjima kadan ki dawo na gama ki mayar wa da Ummi wayarta". Nihal ta amsa da to sannan ta fice ta bar ɗakin, cikin sauri Nu'aymah ta shiga rubuta lambar Janaam a wayar tamkar zata suɓuce ta faɗi a hannunta, kusan sau uku ta kira Janaam bata daga ba, kamar zata yi kuka ta koma jikin kofar dakinta ta saka key tana tunanin wa zata kira yanzu kuma na kusa da Umar Farouk ta sanar dashi gaskiya, Saleem ta faɗa da sauri kafin ta shiga rubuta numbersa acikin wayar, sau biyu tana rubutawa tana kira amma sai taji ba shi bane saboda bata saka lambar dai-dai ba, silalewa kasa tayi tana fashewa da kuka don gaba-daya ta kasa tuna yadda karshen lambarsa take bata haddace ta ba, wannan damar kaɗai take da ita da zata iya faɗawa wani gaskiyar da zai iya faɗa a kotu a wanke Umar Farouk, sake gwada rubuta number tayi tana tunano yadda take rubuce a wayarta, bayan ta gama ta danna kira tana runtsu idanuwanta, sai da kiran ya kusa katsewa sannan aka ɗaga, a hankali ta sauke wata irin ajiyar zuciya haɗe da faɗin, "Hello hello Saleem kana ji na? Nu'aymah ce ya Nu'aym bai mutu ba yana raye don Allah kaje ka kubutar da Umar Farouk a koto, na tabbatar maka da idan akai bincike za'a gano gaskiya kafaɗa Please..". Kiran ta ji ya yanke da alama ba service network ɗin bai da kyau, "hello hello.." ta shiga faɗa amma ina service ya yanke gashi ba tada tabbacin ko Saleem ya ji abinda ta faɗa, sake gwada kiran wayar tayi sau barkatai amma taki shiga, daidai nan aka yi mata knocking, wata irin zabura tayi haɗe da mikewa tana boye wayar kafin nan cike da tsoro tace, "w..wa.waye?' tana haɗiye wasu yawu masu karfi, Muryar Ummi ta ji tace "Ki buɗe mana". A take jiki na rawa ta kamo lambar Saleem data kira ta goge ta kuma yi blocking ɗin ta don kar a samu matsala haka ma ta Janaam ta shiga ta goge wajen dailing call sannan ta saita kanta ta buɗe kofar, ba tare da Ummie dake dauke da abincinta data hado mata ba Nihal na biye da ita abaya ta kalleta ba ta wuce ciki ta ajiye mata abincin tana cewa, "Meye na rufe daki Nu'aymah ni fa wannan lamarin ya fara bani tsoro tsakaninki da mahaifinki, ki fada mini wai me ke faruwa ne?" Ƙasa Nu'aymah tayi da kai ba tare data iya furta ko a ba tunawa da jan kunnen da mahaifin nata ya yi mata, Ummi ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa, "shikenan tunda rayuwar da kika zaɓawa kanki kenan sai kayita yi, shi ya yi mini iyaka akan abinda ke tsakaninki dashi ke kuma baza ki iya buɗe faɗa mini damuwarki ba a matsayina na mahaifiyarki, duk kin bi kin lalace so kikeyi na rasa ki kamar yadda na rasa ɗan uwanki". Tana kaiwa nan ta fashe da kuka tana kokarin ficewa daga dakin, Nihla ta miƙawa wayar da sauri tare da cewa, "Ummi.." kafin ta fadi abinda take son fada sai Muryar Abba kawai ta ji a hasale ya hawo saman yana kwala mita kira, gabanta na faduwa tayi baya tana jin tamkar zuciyarta zata fito daga ƙirjinta tsabar tsoro, yana hawowa ya kalli Ummi sannan ya kalle ta ya ce "wato har ni zan saka doka a gidan nan na faɗi yadda nake so ayi a karya saboda kun maida ni ɗan iska ko?" Ummie da tai saurin share hawayenta ta marairaice murya kama zata saka wani kukan tace, "haba Alhaji me kuma ya faru yanzun nan fa na hawo na kawo mata abinci". Bai bi takan ta ba yace, "Da wace wayar kika yi kira yanzu?" Kai Nu'aymah ta shiga girgiza kai haɗe da cewa, "Abba ni banyi kira ba, ban kira kowa ba wallahi" gun da Ummien ke tsaye ya kalla yace "ina wayarki?" "Tana daki, me yake faruwa?" Bai tankata ba yace Nihla da cikinta ya ɗuri ruwa itama taje ta dauko masa wayar, a tsorace ganin yadda Abba ya sauya Nihla tafita ta je ɗakin Ummi, zaune tayi bakin gado tana dafe kirji kafin ta mike ta ciro wayar da Nu'aymah na bata ta tura cakin riga sannan ta koma wajen su ta miƙawa Abba wayar, dialling call da massages ya shiga ya dudduba, Allah ya taimaki Nu'aymah bai ga komai ba amma duk da haka ya kasa yarda sai daya kalli Ummi ya ce, "Don me kika bata wayarki bayan na karɓe tata? Idan ina bukatar tayi amfani da waya me zai sa na karɓe wayarta wato ke kike goya mata baya ta saɓawa umurnina to kije na sake saki ɗaya". Ya kare zancen ransa a ɓace tare da juyawa zai bar dakin Nu'aymah ta faɗi ƙasa da sauri ta riƙe masa ƙafafuwa ta baya tana fadin, "Abba kayi hakuri na tuba wallahi bazan sake ba, Ummie bata san ma na dauko mata waya ba don Allah kada ka kori Ummi na bazan sake ba Abba". Bai tsaya saurararta ba ya ture kafarta ya fice daga dakin, tabbas ta yarda mahaifinta komai zai iya aikatawa idan ta fitar da wannan maganar, Ummie da ranta yayi kololuwar ɓaci ta kalli Nu'aymah tace, "ai shikenan burinki ya cika tunda kunnen kashi ne dake, indai mahaifinki ne akan farincikinsa ya yarda kowa ya rasa nasa farinciki, me yasa baki yimun magana ba kafin ki ɗaukar mun waya? Me kikai da ita gashi yanzu da idanuwanki kin ga abinda kika jawo mun, shekara da shekaru bai taɓa cewa ko gidan mu na tafi ba amma gashi kin ja wo ya sakeni akan abinda ban ji ba ban gani ba". Tana kaiwa nan ta fice daga dakin ta bar Nu'aymah kwance kasa tana darzar kuka.
******
Tunda Momy tabar gidan su Janaam ta rasa me yake yi mata daɗi, ta shiga tunani shin me yakamata tayi yanzu, fadar gaskiya Umar Farouk ya kashe kansa kuma ya kasheta ko kuwa ci gaba dayin shiru a yanke masa hukuncin kisa? Da daddare kasa bacci tayi zantukan Momy sai yawo suke yi mata a kunnuwa, cikin kaifi da raɗaɗi take jin kowace kalma ta Mommy na sare mata gaboɓin jiki suna yanka mata zuciya gunduwa-gunduwa, gaba-daya ta rasa me zata yi sai kawai ta haɗe kai da guiwoyinta ta shiga rera wani irin kuka mara sauti, har ga Allah tana tsoron zuciyar Umar Farouk da halinsa, a nan cikin kotun zai iya aikata abinda ya faɗa kuma gaban kowa dan kai tsaye shi ya shiryawa mutuwa amma ita bata shirya ba, ko da zata zo mata bata fatan tazo mata ta hanyar da Umar Farouk yai ikirari, a daren bata yi bacci ba har garin Allah ya waye, a wunin ranar Mamah na lura da yadda take yin komai cikin sanyi amma bata haɗata da uffan ba dan kuwa bayan tafiyar Barrister Maryam Janaam bata faɗa mata komai ba akan yadda sukayi sai ita kuma sai bata tambayeta ya suka yi ba ta zuba mata idanuwa, da marece tana kitchen tana taya Mamah aiki Nu'aymah takirata da wayar Ummi, ko da akai sallar magrib ta shigo ɗakin bata bi takan wayar ba har sai bayan sallar isha'i ta ci abinci tayi wanka zata kwantawa, tana dauko wayar taga tarin missed call a ciki hadda na Ummi wato mahaifiyar Nu'aymah, da sauri tabi kiran sai dai wayar bata shiga ba ance kashe take don da ita Abba ya fita ya kashe ya jefata a wani safe inda yake ajiye takardu inda ta Nu'aymah take...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
68.
Ganin haka yasa ta juya akalar kiran nata gata Nu'aymah itama wayarta a kashe, tayi shiru tana tunanin dalilin kiran da Ummi tayi mata, ko dai Nu'aymah ce? ta faɗa a ranta tana ci gaba da saƙawa da kuma warwarewa har bacci yazo ya yi awon gaba da ita.
Washe gari ana gobe za'a koma kotu jikin Momy yayi sanyi matuƙa domin har yau basu karasa samun wasu hujjoji da suke bukata ba domin samawa ɗanta mafita duk da yadda bincike ya tono masu wasu abubuwa da basu taɓa tsammani ba, koto hujja mai ƙarfi take bukata kuma wancan bangaren sun fisu hujjoji masu karfi musamman idan Janaam ta kafe ta tsaya masu a matsayin shedar su ta gani da ido, da safe Dady na shirin fita shima duka jikin nasa ba kwari tana zaune bakin gado ta ce, "Me kake tunanin zai faru a kotu gobe a matsayinka na mahaifi ba alkali ba?" Ba tare daya ɗago ya kalleta ba yana gyara clips ɗin hannunsa yace. "Samun adalci daga wajen wudan da aka zalunta ko da akan kaina ne". "Amma baka jin yanke hukuncin nan gobe yai wuri a matsayinka na alkali?" "Sam bana jin hakan domin duk wasu hujjoji da ake bukata wajen tabbatar da gaskiya da kuma yin adalci an samu, sheda daya ce nake jira wacce nake fatar bayyanarta gaban kotu ya zame mana alkhairi, hakika ban taɓa jin damuwa ko tashin hankali ba wajen tabbatar da hukunci na gaskiya kamar shari'ar nan ta Umar Farouk, hakan jarabawa ce garemu mai girma ina fatan kuma zamu canyeta". "Kenan kana nufin zaka yanke hukunci akashe mani ɗa bayan bai aikata abinda ake zarginsa da aikatawa ba?" "Hakan zai faru matukar ban samu hujjoji masu karfi daga wajen ku ba". "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un". Mommy ta faɗa tana fashewa da kuka tare da rufe fuskarta da hannuwanta, a hankali Dady ya tako zuwa inda take ya zauna a kusa da ita ya rungumota a jikinsa yana shafa gefen hannunta alamun lallashi, sunfi minti goma a haka kanta na saman kafaɗarsa, sai da taci kukanta har ta gama sannan ya mike ya fice daga dakin, gabaɗaya Momy ta sare duk da tarin abubuwan da suka haɗo na bincike sanin ba zasu taɓa sama hujjar da zata buge ta wancan ɓangaren ba idan Janaam bata iya warware komai ba ko kuma zarginsu ya gama tabbata a inda suka sa gaba gashi kuma lokaci ya riga daya gama ƙure masu, mikewa tayi ta shiga toilet ta ɗauro arwala tayi raka'a biyu, bayan ta gama ta karanta wata addu'a acikin ayoyin Alkur'ani da Ubangiji ke cewa,
*'AMMAN YUJIBUL MUƊƊARRA IZAA DA'AHU, WA YAKSHIFUSSU'A, WA YAJA'ALUKUM KHULAFAA'AL ARDI A'ILAHUN MA'ALLAH, KALILAN MAA TAZAKKARUN'*
Bayan ta gama ta haɗa da istigfari da salatin Annabi da tasbihi sannan ta roki Allah ya kawo mata mafita ya kubutar da ɗanta, addu'a ce sosai da idan bawa ya karantata ya kuma roki Allah yai masa alkawarin amsa masa kowace irin buƙata ce matuƙar anyi ta da ikhlasi, bayan ta gama ta