Showing 39001 words to 42000 words out of 157423 words
Na faɗa ina kallonsa cike da son ɓoye alaƙar mu da ya Nu'aym don kar ya fahimta, ba tare daya kalleni ba yace, "Ki kwantar da hankalin ki mijin ki na tafe, ke dai ki maida hankali ki samu ki kammala karatun ki ki fito da sakamako mai kyau wannan shine abu mafi muhimmanci a gareki yanzu, don da zaran kin fara kula samari to shikenan ba lallai ne kiyi abun ƙwarai ba". Murmushi kawai nayi tare da juyawa na shige kitchen da kayan dana karɓa hannunsa na adana kowane inda ya dace sannan na fito ina faɗin, "Ya Jameel yanzu zaka ci abincin Yaya?" "Ya akayi ne?". "Tuwo na ɗora maka kuma ban karasa kammalawa ba shi yasa nake so naji". "Ehmmm to, bari dai nafara watso ruwa nayo sallar isha'i tukuna, ya exam an kammala ko?" Na amsa da Alhamdulillah sannan na juya na koma kitchen na hado masu ruwa na kawo masu, kitchen na sake komawa na tuƙe tuwon sannan na ɗora miya, muna da sauran stew, don haka ita na ɗiba na sake soyawa na saka nama da crayfish sannan na sa niƙaƙƙen agushi da muke dashi ajiye na zuba sauran kayan hadi sannan na tsaida ruwa na rufe na koma palourn, kusa da mamah na je na zauna haɗe da cewa, "Wai Mamah ina kika je?" Kai ta ɗago tana kallona kafin tayi dariya tace. "Gidan kawunku naje tarbar lefen yar wajensa Suhaimah." Zaro idanuwa na yi haɗe da cewa, "Mamah Suhaimah fa? Yaushe aka haifeta da har za'a yi mata aure yanzu? Ko fa Secondary bata gama ba". Mamah ta ce, "Aikuwa dai aure za'a yi mata goma ga wani watan mai zuwa idan Allah ya kaimu, ai dama shi yaransa basa haura shekara sha shida bai yi masu aure ba, Suhaimah ɗin ce kaɗai bata karasa kaiwa ba saboda yaga kanta rawa yakeyi, a yadda ya faɗa mini wai shi saurayin nata har ɗaukarta yake yi da mota su fita yawon su cikin gari, kin ga kuwa ai ta zubar masa da mutunci tunda gwargwado Yaya ba abinda bai yiwa yaransa tunda yana da abun hannunsa, amma da yake yaran yau kullum hangen nesa ya yi masu yawa sai ta biyewa yaron, shine fa yace yaron idan da gaske yake yi ya fito a daura masu aure kafin ta janyo masa abun kunya, da yake yaron ɗan gidan masu arziki ne kuma da gaske yake son ta yau kinga kwana uku da zancen amma sun kawo komai har sadaki, baki ga akwatinan ba yadda kika san za'a bude shago, Ni dai ban tsaya ƙirgawa ba amma na ji ance akwati talatin da bakwai ne banda wasu basket da aka haɗo dasu, abun dai tubarkallah masha Allah, kema Allah ya nuna mini naki, son samu na ne Janaam da kin kammala karatun ki Allah ya kawo miji kada a wani dauki dogon lokaci kema kiyi aurenki ki huta, Kinga doguwar soyayyar nan faɗi banza faɗi wofi banga wani amfaninta ba, indai anyi bincike an gano yaro ɗan gidan mutunci ne kuma yana da abun yin lalurar auren to banga amfanin ɓata lokaci da wani soyayya da yan wayoyi ba, ƙara su je can su yita idan ma canye junansu zasu yi sai suyi".
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNA LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA N1000 HANKALI KWANCE KI KARANTÁ.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
23.
Dariya na yi gabana na faɗuwa jin kalaman Mamah, tunda ta faɗi haka na san tabbas idan ta san alaƙar dake tsakanina da ya Nu'aym to fa baza ta bari har sai na kammala karatu na ba duk da ɗan lokaci kaɗan ne ya rage baifi wata uku ba, shi kuma Ya Jameel ya fiso ko menene dai ya zama sai na gama karatuna zan fara kule-kulen samari, hakan yasa na sake ɗaukar alwashin ɓoye alaƙa ta da ya Nu'aym har sai na gama karatuna kafin na bashi damar turowa don cikawa Ya Jameel burinsa. Haka muka ci gaba da firar mu da Mamah na sake tsoratar dani halin samarin yanzu da kuma ƙalubalen da yan mata ke ciki yanzu.
Kitchen na koma na duba miyar da nake yi naga ta nuna sannan na bude fridge na ciro ganyen alayyahu na yanka na zuba na saka mai na sake motsa miyar, bayan mintuna goma na kwashe na zuba a kula na kai masa akan dining sannan na shirya mana namu da zamu ci ni da Mamah akan dining shima na wuce ɗakina kafin ya Jameel ɗin ya dawo, don tuni itama Mamah ta wuce dakinta don gabatar da sallar isha'i.
******""
LOVE AT FIRST SIGHT💞🧐
Al-amarin Umar Farouk ba'a cewa komai domin kuwa tunda idanuwansa sukayi arba da fuskar Janaam gaba-daya ya rasa natsuwarsa, daya rintse idanuwa ba abinda yake hangowa sai ɗan ƙaramin bakinta lokacin da tana masifa, tun yana ƙaryata lamarin har ya ji cewa tabbas akwai wani abu da yake ji akan Janaam da bai taɓa jinsa akan kowace mace ba, tunaninta kaɗai sawa yake yi yana ji tamkar an jona masa shocking saboda yadda jikinsa ke wani irin zuba tare da amsawa, tunda ya dawo gida ya faɗa kwance saman gadonsa fuskarsa na kallon rufin ɗakin daya ƙawatu da wani irin design mai ɗaukar hankali, ya yi juyi ba iyaka don gasgata abinda ke faruwa dashi shin gaske ne ko mafarki yake yi, sai dai har yanzu ya kasa tantancewa saboda shi bai taɓa jin wannan yanayin da yake jin kansa aciki ba a kaf faɗin rayuwarsa, shi yasa ya kasa yadda ba mafarki ne yake yi ba, tashi yai zaune ya sa hannuwansa duka a ƙeyar kansa ya shafo zuwa fuska tamkar mai arwalar shafar kai, "Oh my God! Me yake shirin faruwa dani ne?" Ya faɗa yana furzar da iska ta bakinsa tare da tallabe fuskarsa da tafin hannuwansa yana ƙurawa kofar shigowa ɗakin nasa ido tamkar ance zai ganta, ajiyar zuciya ya sauke kafin a hankali ya furta sunan, "Amatul-Alim." Tare da saurin dafe saiti zuciyarsa da yaji ta wani irin amsa da karfi tamkar itace mai amsa sunan daya kira, menene haka? Ya tambayi kansa yana murza wajen a hankali kamar mai ƙoƙarin lallashin yaro ƙarami, ya fi mintuna hamsin a wajen yana abu ɗaya kafin ya ji an ƙwanƙwasa masa ƙofar ɗakin haɗe da turowa an shigo lokaci ɗaya. Tauheeda ce sister ɗinsa ta ce, "Ya Farouk wai kazo in ji Dady". Ya sauke idanuwansa a hankali kan Tauheeda yana hango tamkar fuskar Janaam acikinta, a hankali ya ce, "Zo Tauheeda". Ya faɗa cikin wata irin murya da kana ji kasan akwai damuwa tattare da ita, idanuwan Tauheeda akansa cike da tsoro ta fara takowa zuwa inda yake zaune bakin gadon, hannayenta ya riƙo duka biyun ya ɗora a saman kowane gefe na fuskarsa ya shiga marin kansa da hannuwan nata da ƙarfi yana cewa, "Wake me up, wake me up Tauheeda, wake me up, kice ba gaskiya bane abinda nake ji mafarki ne nake yi." A tsorace Tauheeda ta jaye hannayenta tana ja da baya tana kallonsa take faɗin, "Ya Umar are you ok?"
"Am not Tauheeda". Ya faɗa yana dafe kansa dake wani irin sara masa saboda tunanin daya matsawa kansa dashi". Da sauri Tauheeda ta fice da gudu ta nufi sashen Momy, suna zaune palour Dady cike da ɓacin rai yana jiran shigowarsa, yana wajen aiki aka kirasa daga makarantar su aka sheda masa abinda ya yi da kuma nemansa da ake yi gobe school saboda za'a zauna meeting da Umar Farouk ɗin kan laifin daya aikata, wanda dakyar Dady ya gama abinda yake yi a office ya dawo gidan rai a ɓace. Tauheeda na shigowa palourn tace, "Dady Ya Umar baida lafiya.." bata ƙarasa rufe baki ba Momy tayi wata irin zabura haɗe da miƙewa tana faɗin. "Umar ɗin ne ba lafiya? Ina yake?". Ta miƙi ƙofar fita palourn har tana bangaje Tauheeda dake tsaye da ta faɗi har sai da Dady ya yi saurin miƙa hannu ya riƙeta, da mamaki yabi Momy da kallo yadda a take ya ga hankalinta ya tashi jin ance Umar Farouk ba lafiya, ya rasa wane irin kalar so take yi masa da ko rabin rabinsa bata yiwa Tauheeda da take ƙanwarsa, ba don a gabansa ta haifi tauheeda da kanta ba da yace ba ita ta haifeta ba shi yasa bata son ta kamar yadda take son Umar Farouk, ajiyar zuciya ya sauke tare da riko Tauheeda ya zaunar a gefensa yana faɗin, "Mamana a kwance kika isko shi?". "No Dady zaune yake amma ya riƙa hannuna yana dukan fuskarsa wai na tashesa, Dady me yake damunsa ne?" "Nima ban sani ba Mamana, nafi zargin kawai pretending ne yake yi yana so ya rena mani da hankali, zauna anan ina zuwa". Dady ya faɗa haɗe da miƙewa ya bi bayan Momy, yana shiga ɗakin ya tadda Momy zaune kusa dashi tamkar zata maida shi cikin ciki ya ɗora kansa saman kafaɗarta tana shafa fuskarsa a hankali, tsawa Dady ya katsa masa data sashi ciro kansa ba shiri yana cewa, "Meya maido dakai gidana? Bance kar na sake ganin kafarka cikin gidan nan ba idan har baza ka sauya halin ka ba? Wato don ka renani shine zaka je ka ɗauko wata fitinar ka dawo cikin gidana ka shige ko? Wato kai mai gata da ɗaurin gindi to bari kaji wallahi bazan daukar maka ba, sannan tunda baka son karatun zan basu dama su dauki duk hukuncin daya dace a kanka, kai waye da har zaka tsaya jayayya da malamin ka? Shin kana tunanin zan iya baka ilimin da su suke baka ne ko kuma zan yimaka gatar da suke ƙoƙarin yimaka wajen inganta rayuwarka? Na rasa me damunka Umar Farouk da sam kai baka son a zauna lafiya sannan ka dauki kowa ba a bakin komai ba wajenka". "Amma dai Dady kana kallon yaron nan kasan cikin damuwa yake bai kamata ace an ƙara masa wata ba.." "Will you Short up my friend". Dady ya faɗa cikin ɓacin rai yana kallonta. Shiru Momy tayi bata sake cewa komai ba, faɗa Dady ya ci gaba dayi masa sosai kafin Umar Farouk ya mike rai a ɓace ya fice yabar ɗakin, saurin tashi Momy tayi zata bi bayansa Dady ya dakatar da ita yana cewa, "Idan kika bishi kada ki kuskura ki dawo cikin gidan nan, na lura duk ke kike ɗaure masa kuma zanyi maganinku". "Amma Dady kasan wane kalar hali zai shiga idan ya tafi, ko baka ga yanayin da yake ciki bane? A matsayin mu na iyayen sa haƙƙine akan mu mu san matsalarsa da kuma damuwarsa". "Oh shi kadai yake da haƙƙi akan mu mu bama da haƙƙi akansa? Ko ita waccan yarinyar da kike wofantar wa ba tada haƙƙi ne akanki da zaki ja ta ajiki kisan damuwarta sai wannan baligin yaron?" Momy na jin ya ɗauko zancen Tauheeda ta haɗe rai tare da barin wajen don ita bata ga abinda take yi mata ba daba dai-dai ba, amma kullum cikin korafi yake akan kulawar da take bata wai tayi kaɗan, kawai ta lura Umar Farouk ɗin ne baya so shi yasa yake ganin tafi son shi a kanta, kuma babu yadda za'a yi ta taɓa kwatanta soyayyar da take yi masu tunda shi tafara gani. Girgiza kai kawai Dady ya yi ganin Momy ta bar wajen, dama ya san tunda ya ɗauko zancen Tauheeda za'a yi haka. "Allah ya kyauta". Ya faɗa haɗe da barin wajen yana shigewa sashensa.
Momy kuwa tana shiga sashenta ta ɗauki wayarta ta kira Umar Farouk, ta yi masa missed call ya fi a kirga bai ɗaga ba, hakan ya matuƙar tayar mata da hankali saboda yadda ta ji ya fizgi motar da karfi lokacin daya fita, tagumi ta buga tana jin zafin irin yadda Dady ke nuna tamkar ba shi ya haifi Umar Farouk ba.
Da wani irin matsanancin gudu Umar Farouk ya bar gidan ya nufi gidan gona, gabaɗaya ya manta da abinda ya faru tsakaninsa da mahaifinsa kwanaki shi yasa har ya koma gidan, ya jima cikin mota yana jin zuciyarsa nayi masa wani irin zafi, a yanzu ba matsalarsa da mahaifinsa ce tafi damun sa ba, abinda yake ji akan yarinyar da zai iya cewa yafi tsanarta akan kowa cikin makarantar da bai san me zai kirasa ba shi yafi ɗaga masa hankali akan komai. Ya rasa wane irin al'amari ne mai girma haka ke shirin fuskantosa da bai shirya masa ba, daƙyar ya iya kashe motar ya fito ya nufi cikin gidan yana hada hanya, wanka ya shiga yai sannan ya fito ya ranka sallar azahar da la'asar da bai yi ba, yana gamawa nan take ya ji wani irin zazzaɓi ya taso masa ya miƙe ya hau kan gado ya duƙunƙune acikin bargo yana wani irin rawar sanyi, damuwa da zazzaɓi lokaci ɗaya sun rufesa har baya iya tunawa da yunwar dake cikinsa, don tun safe sharabonsa da abinci gashi har ƙarfe shida na yamma ya yi. A hankali ya lumshe idanuwansa haɗe da rufesu, nan take fuskar Janaam ta fara yi masa yawo ta cikin idanuwa yai saurin buɗe su yana jin duka jikinsa na amsawa, lokaci ɗaya kuma yaga ta fara yi masa gizo a idanuwa, wata irin ƙara ya saki tamkar mai shirin zaucewa yana rufe kansa har fuska da duvet wanda anan take yafara sakin wasu irin sabbatu da shi kansa bazai iya faɗar ko me yake cewa ba.
_(Ni kam nace sabbatun so ne Umar Farouk keyi, kuma da alama so bai zo masa da sauƙi ba, ko ya zata kaya tsakaninsa da Janaam idan har ya gama tabbatarwa da kansa cewa lallai sonta yakeyi? Ko ya zai ji idan ya gano yanayin da yake jinsa aciki soyayya ce mai ƙarfi da kuma ƙaunar Janaam ta shigesa?)_
Ku biyo ni muje don ci gaba da jin yadda zata kaya tsakanin su💃
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9.
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
24.
Daƙyar Umar Farouk ya samu bacci yai gaba dashi, baccin da shima kai tsaye zai iya fadar bai zo masa da sauƙi ba don cike yake da tarin mafarkai kala-kala da bazai iya cewa ga ma'anar su ba, wannan dai fuskar data hana zuciyarsa natsuwa itace ta sake bibiyarsa har a cikin baccinsa. Ga wani irin zazzaɓin dake sake taso masa sai sake rikicewa da sabbatu yake yi, jin an yaye duvet ɗin jikinsa ya sashi saurin farkawa daga baccin da dama zai iya cewa sama-sama yake yinsa, yadda taga yana rawar sanyi ya kasa motsawa ya sata matsowa kusa dashi takai hannunta ga jikinsa tana cewa. "Subhanallahi Farouk jikin naka har yayi nauyi haka? Wai menene haka yake damun ka?" Momy da a can gida ta kasa zaune ta kasa tsaye ganin magrib tayi har lokacin tana kiran wayarsa bai ɗauka ba ta faɗa tana ɗagosa daga kwancen da yake zuwa jikinta, sanin baici komai ba ko daya bar gidan ya sa ta shiga kitchen ta haɗa masa abinci sannan ta ɗauki makullin motarta ta fito, ɗakinsa ta fara biya wa inda nan ta isko wayarsa akan sofa ashe bai tafi da ita ba ta daukar masa wayar sannan ta jawo ƙofofin ɗakin nasa ta rufe, da kanta ta ɗauki abincin ta kai cikin mota sannan ta ja ta fice daga gidan, kana kallon ta kasan cikin damuwa take don tuƙin ma yi kawai takeyi, bata tsaya ko ina ba sai gidan gonar Dady, tayi parking ta fito tana sauke ajiyar zuciya ganin motar Umar Farouk ɗin a farfajiyar gidan, buɗe bayan motar ta yi ta ciro basket ɗin abincin ta nufi ƙofar shiga cikin gidan, ko data tura kofar ta jita a bude wani sanyi ta ji a ranta don ta sani da a rufe take ba lallai ne Umar Farouk ya buɗe mata ita ba, sallama ta yi tayi amma ba'a amsa ba, mamaki ya kamata ganin ya bar ƙofar a buɗe kuma baya cikin paloun, ajiye basket ɗin tayi ta ɗan zauna na mintuna tana tunanin ko ya shiga wanka ne amma sama ga mintuna goma sha biyar data buge zaune ko motsi bata ji ba balle tasa ran fitowarsa, hakan ya sa ta miƙe ta nufi hanyar da zata sada ta da bedroom ɗinsa gabanta na faduwa kar ace wani abun ya sami yaronta, da yake gajeren corridor ne tsakani bai fi minti biyu ba ta isa bakin kofar, tana kai hannu da niyar ƙwankwasa ƙofar sai ta jita a bude itama, da sauri ta faɗa cikin ɗakin ta hango ɗan nata kwance ya tattake cikin duvet sai sabbatu yake yi ƙasa- ƙasa, shine fa tayi saurin isa wajen ta yaye duvet ɗin daya lulluɓa dashi, tamkar zata yi kuka ta ɗago fuskarsa da kansa ke saman kafaɗarta tana faɗin. "Please Umar Farouk bana son shirun nan naka kayi mini magana ko meye zan taimakeka". Daƙyar cikin wani yanayi na masifaffen ciwon kai da yake ji ya iya buɗe baki ya ce, "Momy am fine". "Wane you're fine Umar Farouk? Dube ka yadda ka koma kamar ba kai ba! In wani abu ke damunka ka sanar dani idan ina da hanyar magance maka shi na magance ma ba ka kama baki kayi shiru kana cutuwa haka ba, gashi har zazzaɓi ya rufe ka, don Allah faɗa mun menene ke damunka haka?" Sake narkewa Umar Farouk ya yi zai komawa ya kwanta tayi saurin tarosa tana cewa. "No karka