Showing 45001 words to 48000 words out of 157423 words

Chapter 16 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

500

ba daɗi a ranta, yau tunda safe ta shirya ta faɗawa Ummi zata je duba Janaam daga nan tayi mata sallama kasancewar gobe zasu wuce U.k kamar yadda Abba ya alkawar ta idan suka kammala exam, Allah ya tsare hanya tayi mata tana cewa ta gaisheta in ta je, bata yi wani wahalar daukar motarta ba kasancewar gida huɗu ne tsakaninsu sai kawai ta taka da ƙafa zuwa gidan, ina zaune ɗakina ina waya da ya Nu'aym na jiyo sallama daga palour, jin kamar muryar Nu'aymah na gaisawa da Mamah dake palour suna taking breakfast ita da Ya Jameel yasa na yi saurin yin sallama da Ya Nu'aym ina sheda masa cewa nayi baƙi sannan nayi saurin miƙewa na fito, a bakin ƙofar dakina na tsaya nayi folding hannayena a kirji ina kallon Nu'aymah da gaisawa kaɗai suka yi da Ya Jameel ya miƙe ya fita, Mamah kuma taci gaba da tambayar ta ya karatu sun gama exam lafiya ta amsa mata da lafiya ƙalau sannan ta miƙe ta nufo inda nake tsaye, juyawa na yi na shige ciki Nu'aymah ta biyo ni a baya, bakin gado na nuna mata da hannu ta zauna sannan na koma gefe ina kallonta cike da mamaki, don har text message na tura mata bayan kiran da na yi mata amma ba reply, sai da Nu'aymah ta zauna tare da cire mayafinta ta ajiye gefe sannan ta ɗago tana kallona tace, "Wannan kallon fa?" Ganin irin kallon da nake yi mata don ba ƙaramin mamaki ta bani ba, ta yi maganar tana ɗan haɗe rai, murmushi na saki haɗe da cewa, "Dole na kalle ki Besty har yanzu mamakin ki nake yi, halan baki ga kirana bane?" Sai da Nu'aymah ta ja ajiyar zuciya ta sauke sannan tace, "Na gani". "Good! Message ɗina fa?" "Shima na gani". Ta faɗa kai tsaye idanuwanta cikin nawa don Bama iya yiwa junanmu ƙarya, na ce "Yanzu har kina faɗa da bakin ki duka kin gani besty shine kika kasa mun respond ga ko ɗaya saboda na taɓa abinda kike so? Ai Shikennan Nagode". Na faɗa ina jin babu daɗi a raina haɗe da ƙoƙarin barin ɗakin, da sauri Nu'aymah ta riƙo hannuna tana faɗin, "Sorry Besty ai shi yasa kika ga takanas nazo don na baki hakuri, abinda kike tunani kuma ba haka bane, in har fushi zanyi akan abinda ya faru to ba ke kaɗai zanyi fushi dake ba dukan ku ke dashi ne, Musamman ma shi dake da kaso saba'in bisa ɗari, kaso talatin shine naki". Na juyo ina kallonta har lokacin mamakinta bai bar fuskata ba musamman yanzu data sake tabbatar mini da cewa nayi kuskure ga abinda na yi, ta sake cewa "Ki dena yimun wannan kallon Besty, gaskiya na faɗa maki kenan duka kunyi laifi, fuska abu ce mai daraja da bai kamata ace duk lokacin da rai ya ɓaci akanta ake sauke hukunci ba, 100% Umar Farouk bai kyauta ba abinda yai, amma hukuncin da kika yi masa gaskiya ya yi tsauri, shiyasa dake dashi gaba-daya na rasa me zan ce maku, musamman a lokacin da duka rayukanku suke a ɓace". Kwace hannuna nayi daga riƙon data yimini na fice daga ɗakin ina ƙoƙarin kwantar da ɓacin ran dake taso mini, sai dana ɗauki ruwa masu sanyi a fridge na sha sannan na ɗauko mata drink da wasu ruwan na biya kitchen na dauko cup na kawo mata, ruwan na fara tsiyaya mata na bata sannan na zauna kusa da ita na dafa kafaɗarta, sai da naga ta shanye ruwan ta ajiye cup ɗin kafin na sauke ajiyar zuciya na ce, "idan har marin Umar Farouk da nayi a fuska kuskure ne to ki shirya ci gaba da kallon kurakuraina ba adadi kafin mu kammala karatun mu, in dai bazai dena cutar da ni ba haɗe da tozarta ni ba to ni kuma bazan dena sauke masa wuɗannan yan yatsun nawa biyar a fuskarsa ba". Na ƙare zancen ina ware mata yan yatsun hannuwan nawa adaidai saiti fuskarta, ajiyar zuciya ta ja ta sauke tana girgiza kai kafin tasa hannunta ta riko hannun nawa ta ce, "Shikennan na ji kiyi hakuri, amma don Allah dai kibi komai a hankali". "Idan yabi komai din a hankali nima zan iyayin hakan duk da na tsanesa tsanar da ban taɓa yiwa wata halitta irinta ba, wlh ko sheɗ..." Saurin rufe bakina Nu'aymah tayi haɗe da cewa, "Haba besty! Yanzu idan shi na aura sai kici gaba da yi masa tsana haka? Kenan idan jinina ya surku da nasa sai ki tsani abinda zan haifa saboda ubansa? Me yasa baza ki tausasa wannnan tsanar da kike yi masa ba ko don ni?" Yadda naga ranta ya ɗan ɓaci ya sani cewa, "Shikennan kawai mubar wannan zancen Besty, nima kiyi hakuri kin ji ko? Hope kuma kina lafiya?" Ta ɗan harareni da wasa sannan ta ce, "Gashigani tunda na kawo kaina gunki sai maganganu kike yaɓa mini, Allah gaba-daya kun hargitsi mini tunani, gobe zamu wuce Uk wajen Ya Nu'aym, kina da sako?" Murmushi na saki haɗe da kallonta na ce, "Ni kuwa nake da sako babba agaresa amma dai abun sirri ne". Nu'aymah ta taɓe baki tana ɗan hararata da wasa tace, "Ku dai kuka sani, wannan ɓoyayyar soyayya ɗin taku na kusa fallasa maku ita kowa ya sani tunda munafurci ya hanaku ku bayyana, ni na rasa me Ya Nu'aym ke jira da bazai fito gabaɗaya ba asa mana rana musha bikin mu ba sai mun kammala karatun ba, wataƙil ma hakan yasa takun saƙar dake tsakanin ku da Umar Farouk ya yanke". Saurin zaro idanuwa nayi ina rufe mata baki na ce, "Don Allah ki rufa mun asiri da wannan zancen naki kar Ya Jameel ya ji, wata nawa suka rage mana? Da mun kammala komai zai fito fili aji, soyayyar mu zatayi amsa kuwa a faɗin duniya har inda baki taɓa tsammani ba, amma dai yanzu bama buƙatar bayyanata, a hankali muke ci gaba da ginata irin ginin da baza'a taɓa iya rushewa ba". Na ƙare zancen cike da jin kunya ina cire hannuna a bakinta, murmushi tayi sannan tace, "Allah ya sanya alkhairi kuma ya nuna mana lokaci, amma ko yanzu kam ai ke kin gama ginin taki tsaf don ba ƙaramar soyayya Ya Aym ke yi miki ba, a duniyar sa babu wata mace face ke, ke kaɗai". "Zan so hakan Besty saboda nima shi kadai ne aduniya ta, shine first love ɗina kuma last in Allah ya yarda". Nu'aymah tayi dariya tana ɗan hararata da wasa haɗe da cewa, "Wato da wannan daɗin bakin baki kika sacewa yayana zuciya, wai first love ɗinki duk ina samarin da suke tare ki su ce suna sonki idan mun fita".  "Kai Aymah! Baki ji me kika ce ba? Su suka ce suna so na ba wai ni nake son su ba, shi kuma ya Aym da kaina na ji na amince ina son shi har a kasan zuciyarta". Na faɗa ina dariya ganin kallon da take yi mini na shakiyanci, kasa yin shiru tayi har sai da tace, "Hmmm lucky him, to Allah yabar ku tare har gaban abadan". Na amsa mata da "Amin ƙawata." Cike da jin daɗin addu'ar ta, daga haka muka ci gaba da firar mu har aka kira sallar azahar muka tashi muka yi, bayan mun kammala muka shiga kitchen tare ina aiki tana taya ni har muka kammala na diba mana namu na zube sauran a warmer nakai kan dining sannan muka wuce ɗaki muka ci namu, Nu'aymah sai santi takeyi tana yaba girki na tana cewa yayanta ya huta da zuwa cin abinci waje dama gashi acici, ba ita tafi ba sai bayan sallar la'asar mukayi bankwana saboda jirgin su gobe tunda sassafe zai tashi.

Bayan sallar magrib Nu'aymah ta dauko wayarta ta kira Umar Farouk kusan missed call biyar bai ɗaga ba ta ji tamkar tasa kuka, tana so ta ji muryarsa ko da sau ɗaya ne ko da bazata samu ganinsa ba kafin tabar ƙasar gobe amma gashi yaki ɗagawa, Saleem ya faɗo mata arai da sauri ta lalubo lambarsa ta kirasa, bugu ɗaya ya ɗaga takai wayar a kunnenta tamkar zata yi kuka tace, "Saleem Barka da dare". Ya amsa da "Barka Nu'aymah ya gida ya hutu kuma?" "Alhamdulillah, Umar Farouk fa? Kana da labarinsa kuwa kwana biyu ban ji sa ba gashi baya so na kirasa har sai idan shi ya kira, ina so muyi magana saboda gobe zamu bar ƙasar nan da iyayena zanyi hutu na acan". Kallon Umar Farouk yai dake kwance ya ƙurawa gu ɗaya idanuwa, kana kallon sa kasan ya faɗa wata duniyar daban don gabaɗaya ɗabi'arsa yanzu ta koma haka, bai da wani aiki sai tunani wanda hakan ne ya hanama gangar jikinsa samun lafiya yadda ake buƙata, ajiyar zuciya yai sannan ya ce, "Yana nan Nu'aymah amma kwana biyu yana fama da rashin lafiya but Alhamdulillah duk da dai har yanzu ba wai ya gama warkewa duka ba".  Cike da tashin hankali Nu'aymah ta miƙe daga zaunen da take tana cewa, "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Saleem ya akayi baka sanar damu ba? Me yake damunsa haka? Kuna kuna ina ne yanzu?" Yadda Saleem ya ji ta ruɗe ya sashi cewa, "Calm down Nu'aymah ya ji sauki fa." "No don Allah Saleem kada ka mun yawo da hankali, pls kuna ina ne yanzu?" Ware idanuwa Saleem yai cike da mamaki jin abinda ta faɗa kafin yace, "Tooo! Ina dai ba wani abu bane Nu'aymah ko? Meye tsa.." bai ƙarasa ba ta kashe wayar a ɗan ruɗe ta ɗauki mayafinta da makullin motarta ta fito, Ummi na zaune ita da wata ƙanwar Abbansu ta ce, "Ummi zan ɗan fita bazan jima ba zan dawo". "Ok adawo lafiya". Ummi ta fada tana ci gaba da firar da suke yi, horn Nu'aymah ta yiwa mai gadi bayan ta ɗauko motar ta ya buɗe mata ta fice....

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402425 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

                            27.

A kan hanya ta fara tsayawa ta sayi fruit sannan ta tsaya a wata super market ta sayi katam ɗin ruwan gora da maltina ko wane ƙwaya biyu, sai a lokacin ta sake kiran Saleem dake faman tambayar Umar Farouk meye alakarsa da Nu'aymah ko soyayya suke yi yai banza dashi, wayarsa dake ruri ya ɗaga yana faɗin, "Hello Nu'aymah". "Saleem wane wuri kuke gani kan hanya na fito". Jin har ta riga data fito yasa ya faɗa mata address ɗin inda suke sannan ya kashe wayar yana cewa, "Umar Farouk yarinyar nan fa da gaske zuwa zata yi duba ka, Ni na rasa gane wannan abun wai dai ko soyayya kuke yi ne? Ka ji yadda duk ta ruɗe daga cewa ba kada lafiya?" Nan ma Umar Farouk bai ce komai ba ya shiga tunanin da shine kadai ke sama masa natsuwa yanzu idan yana yi wato tunanin Janaam daya zame masa tamkar abinci.

A ɓangaren Dady mahaifin Umar Farouk kuwa yau baƙi yai tun safe, akwai zama da suka gudanar a office na musamman da bai samu ya sami kansa ba sai dare bayan sunyi sallar magrib, restaurant ya biya dasu kasancewar dare yai bai samu ya kira can gida ba balle a samu shirya masu abin da zasu ci ba, suna kammalawa ya nufi gidan gonarsa dasu don yi masu masaukin da zasu kwana kafin gobe su wuce.

Mintuna goma suka kawo Nu'aymah address ɗin inda Saleem ya faɗa mata, wayarta ta fito ta kirasa ta sanar masa cewa gata ta iso, da kanshi ya taso ya yi mata iso har ciki, a bakin gate ta ajiye motarta saboda ba jimawa zata yi ba kasancewar dare ne, tare suka shiga ciki Saleem na gaba tana bayansa har suka iso cikin paloun, Umar Farouk na kwance saman doguwar kujera yana jin sallamar Nu'aymah yai saurin runtse idanuwansa tamkar mai bacci. Makullan mota Nu'aymah ta ba Saleem dake ƙoƙarin fita ya basu waje tace akwai kaya a mota don Allah ya taimaka ya shigo dasu ciki, ya karɓa ya fice ita kuma ta tsurawa fuskar Umar Farouk idanuwa tana sake yaba kyan da Allah ya yi masa, magana take so tayi masa amma ta kasa ganin kamar bacci yake har Saleem ya gama kwaso kayan kaf ya shigo dasu ciki, ta kallesa haɗe da cewa. "Bacci ma yake yi, wai meke damunsa ne Saleem?" "Ina tunanin dai zazzaɓi ne". Saleem ya bata amsa yana danne dariyar da yake son yi ganin yadda ko matsawa Umar Farouk yaƙi yi, "Allah ya bashi lafiya". Ta faɗa tana sake maida kallonta akan fuskarsa, bayan mintuna goma sha biyar ta miƙe tana cewa, "Saleem dare nayi bari kawai na tafi Allah ya bashi lafiya, naso muyi magana dashi amma naga bacci yake yi sosai". "Eh haka ne akwai maganin dake saka bacci acikin magungunan da yake sha shi yasa, amma bari na tashesa". "Noo don Allah ƙyalesa Allah ya bashi lafiya, zan wuce idan ya tashi sai ka faɗa masa nazo dubasa, but don Allah ya bani dama idan na isa can ƙasar muyi magana ko hankalina zai kwanta, in sha Allah zan kiraka sai naji yadda kuka yi". Ta ƙare zancen tare da miƙewa tana sake kallon Umar Farouk ɗin da ganinsa ya sake haifar mata da wata irin matsananciyar ƙaunarsa, har bakin mota Saleem ya raka Nu'aymah ta buɗe ta shiga ya rufe mata yana yi mata godiya, wanda hakan ya yi dai-dai da shigowar motar Dady a layin, gabansa ne yai wata irin mummunar faɗuwa hango mota da macce ciki abakin gate ɗin gidan gonarsa ana rufe mata kofa kafin ta ja motar tabar wajen, shi kuma Saleem ya koma ciki, wanda hakan yasa Dady tsammanin ko Umar Farouk ne, don haka ko daya iso ta saiti da gidan kasa tsayawa yai sai kawai ya wuce gaba saboda tsoron kar ayi abin kunya, bai san me zai tadda ba shi da baƙinsa a gidan idan ya ce zai tsaya, sai da yai zagaye dasu kafin yai karfin halin cewa. "Kuyi hakuri wani mutum naso gani anan kafin na kai ku ma saukin ku, amma gashi ya ɓata mana lokaci ban samesa ba, ina ga kawai bari na wuce ku samu ku huta ku ma". Ya ƙare zancen yana hawa wani titi da zai sada shi da wata babbar hotel da zai iya kama masu wani masaukin.

Saleem na komawa ciki ya isko Umar Farouk zaune ya dafe kansa, buɗe da baki yake kallonsa kafin yace, "Amma dai kasan baka kyauta ba, yarinyar nan don ka fa tazo wajen nan kuma kana ji kasar zata bari amma kayi banza da ita, wannan fa ba dai-dai bane". "Mtsss..Look Saleem, karka sake jawo mini mace a gidan nan, kafi kowa sanin halin Dady bana so na sake shiga matsalarsa, be side da kake zancen don ni ta zo, ni na gayyato ta? Pls kada ka sake mun haka bana so, da kake zancen alaƙa kuma to ni babu wata alaƙa tsakanina da yarinyar nan, she's just my friend kai ka sani". Saleem ya ce, "Oh k, kasan friend dinka ce me yasa ka yi mata hakan? Ai sai ka tsaya ku gaisa tunda ganinka ta zo yi ba wani abu ba". A ɗan hasale Umar Farouk ya miƙe yana jifar sa da wani kallo kafin yace, "Naƙi nayi haka ɗin ko zaka sani dole ne?" Saleem ya daga hannayensa sama alamun surrender yana cewa, "Nooo...ni na isa ne? Allah ya baka haƙuri". Sai daya maka masa harara sannan yabar palourn a hasale ya koma bedroom, ko daya shiga kasa zama ya yi ya rika kai da komowa, abinda yake ji ya fara girmamar masa a zuciya irin girman da bazai iya jurewa ba, wayar sa ya ciro gaban aljihu sai kuma ya tsaya saboda rashin sanin takamammen abinda zai yi da ita, Janaam kwakwalwar sa ta ambato masa amma kuma bai da lambarta, idan ma yana da ita ya zai yi ya kirata? Me zai ce mata maa idan ya kira, 'kawai kaji muryarta' zuciyarsa ta bashi amsa kai tsaye, iska ya furzar ta baki ya shiga jujjuya wayar yana jin kamar bazai iya ba, 'Give a try' zuciyarsa ta sake faɗa masa a karo na biyu, tamkar wanda aka tsikara ya fito palour da sauri, Saleem na riƙe da wayar sa yana latsa ya fizge ya shiga jerin sunayen dake cikin wayar yana dubawa ko zai samu number Janaam, sai dai har yai dube-dubensa ya gama bai ga ko mai kama da sunan nata ba, ɗaga wayar yai zai bugata ƙasa Saleem yai saurin miƙewa yana zaro idanuwa haɗe da saurin riƙe masa hannu yana cewa, "Easy wannan fa wayata ce ba taka ba ko ka manta?" Ya ƙare zancen tare dasa hannu ya karɓe wayar sa sannan yasa hannu a gaban aljihun Umar Farouk ya ciro masa wayarsa ya damƙa masa yana cewa, "Karɓi wannan zaka iya buga ta a kasa yadda kake so". Yana kai nan ya fice daga paloun gabaɗaya cike da jin haushi, a 'yan kwanakin nan ya rasa me ke damun abokin nasa, sai wasu abubuwa yake yi tamkar wanda ya zare, Umar Farouk ya kalli wayar tasa sannan yai wurgi da ita saman kujera tare da zaunawa daɓas akan kujerar shima yana jinsa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa.

Dady ko sai daya tabbatar da baƙin nasa sun samu kyakkyawan masauki sannan ya yi masu sallama ya wuce gida zuciyarsa na wani irin suya, daƙyar da taimakon Allah ya kai kansa gida cike da tsantsar baƙin cikin abinda idanuwansa suka gano masa don tuƙin kawai yake yi amma ko gabansa baya gani, yana isa sashen Momy ya nufa duk da ba ita take da girki ba, tana zaune tana waya da wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login