Showing 126001 words to 129000 words out of 157423 words
kai balle kuma shi kaɗai, bazan iya ba kawai kayi hakuri". "Look Maryam wannan halin na Umar Farouk shiyása ban wahalar da kaina ba, kina gani a gaban kotu ma ya kasa russinar da kansa to me za'a iya yi masa, sannan ke kanki kin ji irin tarin hujjojin da suka kawo da 60% ɗin su abun dubawa ne, gashi ya kafe akan shi ya aikata kisan to meye amfanin tsayuwar ki idan ba tarin damuwa kike so ku sake haifar mini ba". Hawaye ne suka zubowa Momy tace, "Don Allah kabar ni na tsaya ma yarona, yanzu haka Barrister Nazir ya cire hannunsa akan case ɗin saboda taurin kai na Umar Farouk, nasan kowa zai iya gujewa damuwarsa amma kayi tunani a matsayina na uwa ko da ace ni ba lauya bace bazan iya gujewa damuwar Umar Farouk ba, dole na tsaya dashi acikin kowa ne yanayi". "Har da na rashin gaskiya?" Dady ya faɗa yana kallonta cikin idanuwa, lumshe idanuwan tayi ta rufesu tare da haɗe hannayenta waje ɗaya tace, "Pls don girman Allah kabar ni". "Shikenan". Dady ya faɗa tare da juyawa ya shige toilet, Momy kuwa bakin gado ta faɗa ta fashe da kuka. A haka Dady ya gamo wanka ya fito ya sameta, bai ce mata komai ba ya shirya ya fice daga ɗakin zuwa daya part ɗin matarsa don duba lafiyarsu, Momy kuwa sai da taci kukanta mai isarta ta gaji sannan ta tashi ta wuce part dinta ta shirya wa Dady abincinsa akan dining sannan ta koma ɗakinta ta shiga tunanin ta inda zata fara kamo bakin zaren kafin zama na gaba...
******
Kwance nike na rasa abinda ke mini daɗi a duniyata, har yanzu na kasa dena tunanin Ya Nu'aym, ganin komai nakeyi tamkar almara, na kasa imanin cewa dukkanin abubuwan da suka faru gaskiya ne ba mafarki ba, ji nake yi ina ma bai mutu ba za'a sake dawo dashi duniya, soyayyarsa, kulawarsa da kaunar daya nuna mini duka sun kasa fita kwakwalwata, kalamansa sun tsaya mini a zuciya matuka da idan na tuna nake jin duniyata tayi min girma, da nasan idanuwana a duhu suke da na tsaya tun farko na saurari Umar Farouk ba tare da mutuwa ta wanzu akan ya Nu'aym ba ta silarsa ba. Ina tsakar wannan tunanin na ji wayata ta ɗauki kara, jiki a sanyaye na daga ba tare dana duba lambar ko waye ke kiran ba, cikin taratsi da tsananin kuka na ji muryar Besty Nu'aym na ji tana cewa, "Allah ya isa tsakanina dake Janaam bazan taɓa yafe abinda kikai mini ba, kin ci Amanata kin cuce ni sannan kin zo kinyi amfani da wanda nake matukar so kin raba yayana da rayuwarsa saboda zalunci da cin amana, in Allah ya yarda sai kin tozarta kin wulakanta kamar yadda kika tozartar damu ni da yayana kuma baza mu taɓa yafe miki ba, duk abinda kikai mana Allah yayi miki lunkinsa kema ya rabaki da farincikinki na har abada". Wani irin kuka ne ya kwace mini lokaci ɗaya na sake shiga tashin hankali tare da sakin wayar jin kalaman Nu'aymah, take na ji a hankali idanuwana na lumshewa in gani dishi-dishi dakin ya shiga juya mini, daga nan ban sake sanin ko me ya faru ba sai dai farkawa na yi na ganni a saman gadon asibiti....
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:10 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
59.
Ya Jamil da Mamah na gani a kaina lokacin dana farka na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi ina cewa.
"Na shiga uku Mamah me yasa kuka kawo ni asibiti? Ni kawai ku barni na mutu na huta da wannan rayuwar na tsani kaina Mamah da komai yake faru ta dalilina". Na kare zancen Mamah na rugumeni tana shafa bayana a hankali alamun lallashi, ya Jamil bai iya cewa komai ba amma kana ganinsa kasan yana cikin damuwa, can ya ja ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Janaam ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai zai dai-dai ta muna nan tare dake by your each side ni da Mamah kin ji ko? Mu dai yanzu abinda muke so dake ki natsu ki dawo hayyacinki, ki kwantar da hankalinki wannan kukan don Allah kidena shi kar ki je ki jawowa kan ki wani ciwo". Ya faɗa yana shafa kaina dake saman cinyar Mamah". Duk wanda ya san ni ya ga yadda na koma yanzu sai ya tausaya mini, nayi baƙi na yi wata irin rama saboda ba karamin tashin hankali da damuwa nake ciki ba, da zata na tuna da Umar Farouk sai na ji na sake tsanar kaina da komai na duniya, sai na ji dama tun farko ban san shi ba da wannan halin daya jefa mu duka aciki.
Sai da nayi kwana biyar a asibiti likitoci na kula dani kafin aka sallamo mu, babu yadda Ya Jamil bai yi Mamah ta bari na koma gidansa ba amma ta ƙi, musamman da itama Aunty Nidrah ɗin da tun data dawo daga tafiyar da tayi washe gari ta tashi da wani irin zazzaɓi tana ta amai, da alama laulayi ne don gida ta koma sai jiya ta dawo, bamu daɗe da dawowa ba mai gadi ya shigo yace ana sallamah a kofar gida, ko da Ya Jamil ya fita ya dawo ya sanar da Mamah cewa Barrister Aysha ce da Barrister Shamsu ta ce yai masu iso su shigo daga ciki, ina zaune na fito wanka kenan sai ga Mamah ta shigo, sannu ta tayi mini kafin tace, "idan kin kammala gyarawa kifito gasu Barrister Aysha can a falo suna jira". Cikin dakewa na amsawa Mamah da to don bana so taga tashin hankalin daya dirar mini jin kalamanta, mai kaɗai na shafawa jikina na dauko doguwar riga na saka na nufi parlour, kasancewar dukkaninsu zasu girme mini yasa na fara gaishesu cikin girmamawa kafin na nemi waje na zauna. Cike da kulawa da kwarewar aiki Barrister Aysha ta kalleni ta ce, "Sannu Janaam, ya jikin naki?" Kaina na a ƙasa ba tare dana bari mun haɗa idanuwa da ita ba na ce, "alhamdulillah na samu sauki". Barrister Shamsu ya ɗan zauɗo daga kan kujerar da yake zaune yana buɗe wasu takardu yace, "Kiyi hakuri Malama Janaam kina fama da jiki kuma muna damunki da tambayoyi in sha Allah daga wannan karon baza mu sake zuwa tambayar wani abu ba sai kuma wani sati idan mun haɗu a kotu don muna bukatarki a wajen a matsayin shedar gani da ido, amma kafin nan, kwanaki kin sanar damu cewa tabbas kina a cikin gidan komai ya faru, muna so kafin gabatar dake kotu a matsayin shedu ki bamu labarin me ya faru a wannan ranar da kika sani har zuwa mutuwar shi marigayi Nu'aym Abdullahi Gwaram". Shiru nai tare da jin wasu hawaye sun sauko mini masu matuƙar zafi da raɗaɗi da kuma ƙuna kafin na buɗe baki na basu labarin abinda ya faru a safiyar ranar tiryan-tiryan kamar yadda na labarta wa su Mamah, ina gamawa wani irin kuka yaci karfina mama tazo ta rungume ni tana cewa, "Barrister don Allah kubar zuciyar yarinyar nan ta huta haka, da mutuwar masoyinta kadai aka barta kunsan ba ƙaramin abu bane a zuciya". Barrister Aysha ta ce "Hajiya hakuri zaku yi ta amsa muna duka tambayoyin nan, ta hakan ne kaɗai zamu iya kawo karshen wannan shari'ar a wani mako mai zuwa tunda ita kadai ce shedar gani da ido, kuma a 'yan bayanan da tayi yanzu mun kara samun haske a case ɗin nan domin mun gano cewa shi wanda yai kisan yai haka ne sanadiyar yana son ta shi ma wancan ɗin yana sonta".
"Haka ne Barrister Aysha ko bayan hakan akwai mutane da dama daya yiwa duka saboda kaɗai ya gansu tare da ita, aciki akwai abokina da wani matashi da hakan ta faru dasu". Ya Jamil ya faɗa yana gyara tsayuwar sa, Barrister Shamsu dake rubuta duka bayanan su ya ɗago kai yana kallon Ya Jamil yace, "zasu iya bayyana a gaban kotu a matsayin shedu?" "Zasu iya sai dai ba akan kisa ba". Numbobin su Barrister Shamsu ya karba sannan ya kalli Janaam yace, "kuyi hakuri in sha Allah za'a kawo karshen wannan zalunci nasa, zamu shiga makarantar taku za kuma muyi ƙwaƙƙwaran bincike da zai tabbatar mana da cewa lallai shiya aikata wannan kisan mu kuma tabbata an bima masoyinki hakkinsa". Wani kuka ne ya sake kwace mini na tashi da gudu nabar wajen na shige dakina ina jin wani sabon zazzaɓi na rufeni, da na san gaibi da ban taka kafata a gidan su Nu'aymah ba a waccan ranar balle har Umar Farouk yasan inda nake wannan al'amari ya faru. Anan falo kuwa sallama su Barrister Aysha suka yiwa su Ya Jamil bayan sun sanar dasu ranar da za'a koma kotu tare da yin musayar lamba su da Ya Jamil ya raka su har bakin gate sannan ya dawo suka ci gaba da tattauna zancen shi da Mamah kafin ya wuce gida.
A ta ɗaya ɓangaren Dady ya sake kiran Barrister Nazir ba tare da Momy ta sani ba ya bashi hakuri akan ko meye Farouk yai masa yai hakuri su karasa case ɗin saboda Momy na bukatar support a yanzu, sannan bazai iya jurar ci gaba da kallonta ita kadai tana fafutuka akan case ɗin ba a matsayinta na matarsa kuma mace dake da rauni duk da ko kadan baya da haufi akan jarumtarta da jajircewarta, kawai wannan karon yana ganin kamar bata dauki ɓangaren daya kamata bane shi yasa yake ji ajikinsa kamar bazata iya ba, gashi ta kwana biyu bata yi aikin ba wanda yana da tabbacin dole tana bukatar taimako ko yaya ne, girma da kuma mutuncin Dady yasa Barrister Nazir ya hakura sannan Dady ya roƙe sa akan kar ya faɗawa Momy shi ne ya bashi hakuri hakan zai sa ta jawa yaronta kunne kar ya sake yi masa abinda zai ɓata masa rai ya sake ajiye case ɗin. A ranar Barrister Nazir ya sake komawa police station don ganawa da Umar Farouk, bayan an fito dashi Umar Farouk bai kalle sa ba yace, "baka ji gargaɗin dana yi maka ba kenan! Ko kayi shawara da Momyn yawa ne ta hakura ta ajiye case ɗin". "Ba wannan ya kawo ni wajenka ba, so nake yi naji me ya kaika wannan anguwar har ka shiga gidan mutane aka zarge ka da kisan kai". Barrister Nazir ya faɗa aɗan hasale don kalamansa sun ɓata masa rai, wani kallo Umar Farouk yai masa tare da sakin murmushi, gani yake yi gaba-daya Barrister Nazir ya rena masa da wayau da zai tsaresa da wannan tambayar sai kace shi yaro ne ko shiya aike sa, bai ce masa komai ba yasa kai zai bar wajen Barrister Nazir yai saurin cewa, "wannan karon saboda mahaifinka kaɗai na dawo wajenka, idan kasa taurin kai ina tabbatar maka da cewa zaka rasa rayuwarka ne a banza a wofi domin kai kake da hasarar rayuwa ba mu ba". Tsayawa Umar Farouk yai na sakanni tare da juyowa ya kallesa, nan ma shiru yai sai bayan wasu sakannin sannan yace, "Bana tsoron mutuwa shi yasa na aikata abinda na aikata, saboda haka zan fi kowa farin ciki idan har abinda ka faɗa ya tabbata". Yana kaiwa nan yabar wajen ba tare daya sake bi takan Barrister Nazir dake kiransa ba, haka ya juya yabar Police station ɗin ba tare daya samu bayanan komai a wajen Umar Farouk ba yana jinjina tsageranci da zafin kansa, yana barin police station ɗin tamkar hadin baki sai ga Momy ta iso, bata bi takan Umar Farouk ba sai data zanta da inspector Ashir ya sake bata wasu bayanan da suka haɗa tare da duk wasu evidence da suka gabatar a kotu sannan ta nemi ganinsa, bayan an fito dashi ta ajiye masa abincin data zo masa dashi tace, "Kada ka kuskura ka sake cin zarafin daya daga cikin duk wani lauya da zai zo zantawa dakai domin hakan karawa kanka laifi ne, sannan ka tabbata kaci abinci ka kuma sha magani" tana gama fadar hakan ta miƙe zata bar wajen, jikin Umar Farouk ne yai sanyi ganin yadda ranta ya ɓaci haɗe da cewa "Momy.." tayi saurin dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu tana cewa, "Bana bukatar jin komai a wajenka domin ba shi ya kawo ni ba, ka samu kaci abinci zan dawo gareka kada kuma ka kuskura kai mun wannan taurin kan naka" tana gama fadar hakan ta bar wajen, da kallo Umar Farouk ya bita har tabar cikin police station ɗin, a hankali ya yi baya da kansa ya jingina ajikin ginin da yake zaune kusa dashi yana lumshe idanuwa tare da rufesu.
A daren ranar Momy batayi kwana ba haka ta watse duka takardun bayanan da police suka naɗa a gabanta, idan ta zana wannan ta zana waccan ta haɗa wannan da waccan ta sake daukar wannan da waccan tana dubawa, sai dai duk yadda taso ta gano wani abu akasin cewa Umar Farouk yai kisan ta kasa, ta ko ina ƙarara ta bayyana shine makashin, wani irin kuka ta fashe dashi tana jifa da biron dake hannunta tare da ture takardun duka suka watse a tsakiyar ɗakin, taya Umar Farouk zai aikata haka? Me yasa? Ta tambayi kanta tana jin wani irin tashin hankali na sake mamaye mata zuciya...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:10 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
60.
Washe gari tunda asuba ta nufi ɗakin Umar Farouk, abakin gado ta zauna ta rufe bakinta da hannuwanta tana bin ɗakin da kallo ta kowace kusurwa ɗaya bayan ɗaya, wajen da kayansa suke jere ta nufa ta shiga watse su daya bayan dayan kafin ta koma jerin inda yake ajiye belt da kayan adon sa, ɓangaren takalmin sa da sauran abubuwan amfanin rayuwarsa na yau da kullum, sosai ta bincike ɗakin ko zata samu abinda zai bata tabbacin zargin da ake yiwa ɗan nata amma bata ga komai ba, sashenta ta koma ta dauki wayarta takira Saleem, bugu ɗaya ya ɗaga tace, "Saleem when last kayi waya da Umar Farouk kafin a kama shi". Saleem da tun ranar da abun ya faru yake cikin damuwa ya ce, "Momy ranar da zamu yi bukin graduation a ranar da abun ya faru kenan ma munyi waya akan zamu haɗu dashi school". "To sai me ya faru?" "Eh to ya sake kirana lokacin daya fito ya ce zai je ya dauko Janaam sai su sameni a can school ɗin". "Wacece Janaam?" Shiru Saleem yai kafin yace, "Yarinyar da yake so?" "A ina ne gidan su?" "Kawar wacce Umar Farouk ya kashe yayanta ce, babu tazara gidansu da ita". Cikin sanyin murya Momy da zancen Saleem na karshe ya dakarwa zuciya ta ce "Saleem kai ma ka yarda kenan Umar Farouk zai iya aikata kisa?" Saleem yai shiru don bai san me zai ce ba, ya tabbata a halayyar da Umar Farouk ke nunawa akan Janaam zai iya yin komai, jin bai amsa ba yasa Momy kashe wayar. Ta jima a zaune har Dady ya shigo jiki a sanyaye ta gaishesa, cikin dauriya don shima yana jin damuwar lamarin a kasan ransa ya kalli Momy ya ce, "Hajiya lafiya dai ko?" Ta ɗago kai ta kallesa sai kuma tayi saurin maida kanta ƙasa hawaye na sauko mata, ganin haka yasa Dady yin sallama da ita, wayar Barrister Nazir ta sake gwada kira ko Allah zai sa ya hakura, bugu ɗaya a na biyu ya ɗaga ta sauke ajiyar zuciya, sai bayan sun gaisa sannan Momy ta shiga sake basa hakuri, murmushi yai haɗe da cewa, "shikenan Barrister Maryam na hakura komai ya wuce". Cikin jin dadi tayi masa godiya sannan ta sanar dashi jiya ta karbo bayanan da aka hada a police station tayi duk wani binciken daya dace amma bata samu hanyar da zata iya riƙa a matsayin hujja ba wajen kubutar da ɗanta, ta ƙare zancen tana sake fashewa da kuka, ko kadan bata iya rike zuciyarta idan ta tuna da halin da danta yake ciki shiyása take kasa dakatar da zubowar wayen idaniyarta. Kwantar mata da hankali ya yi kokarin fara yi don dama dan uwan ta ne matsayin yayanta yake saboda dan kanen mahaifinta ne kafin ya shiga karfafata, nan ta sanar dashi bayanin data samu a wajen Saleem ya ce mata ba damuwa zai je anguwar yai bincike shima, in yaso tayi ƙokarin bibiyar abubuwan da yayi a ranar kafin abun ya faru tana sanar dashi a waya, ta hakan zasu iya samun wata hujja da zasu riƙe zuwa jibi da za'a koma kotu. Godiya tayi masa sosai tana jin ta sake samun ƙwarin guiwa a tattare da ita. Suna gama wayar Barrister Nazir ya nufi anguwar su Janaam, kai tsaye gidan Dr Abdullahi gwaram ya nufa wato gidan su Nu'aymah, parking yai haɗe da yin sallama a bakin gate mai gadi ya fito, hannu ya miƙa masa suka gaisa yana tambayarsa ko mutanen gidan na ciki, mai gadi ya amsa masa da eh bari ya shiga ya yi masa sallama da maigidan, saurin dakatar dashi yai haɗe da cewa, "A'a kyalesu ba wajen su nazo ba wajen ka". Ya fito da ID card dinsa cikin aljihu ya nuna masa kafin yaci gaba da cewa, "sunana Barrister Nazir, lauyan wanda ake tuhuma da kisan yaron gidan nan". Ya kare zancen yana nuna gidan tare da mayar da ID card dinsa a cikin aljihu, hankali kwance mai gadin yace, "to to na fahimta, ai ba tuhuma bace ranka shi daɗe saboda an kama shi hannu da hannu, anan gabana jami'an tsaro suka cukuikuye sa suka jefa a mota suka tafi dashi hannunsa duka jini" "ka tabbata?" "Sosai ranka shi daɗe". "Shikenan Nagode sai