Showing 63001 words to 66000 words out of 157423 words
nice person". Wani kallo Janaam ta juyo ta yi masa jin abinda Nidrah ta faɗa wai nice person kafin ta saki murmushin yaƙe ganin Aunty Nidrah ɗin na kallonta tace, "Oh! nice person sannu ko". Ta ƙare zancen tare da haɗawa da 'yar dariya irin ta renin nan kafin ta kauda kanta ta ɗauki lemun dake gabanta da aka tsiyayar mata takai bakinta, cike da tsoro Aunty Nidrah ta kalli gefen da Umar Farouk ke zaune har lokacin idanuwansa na a rufe saboda yadda ta san halinsa ya tsani reni, kafin takai ga cewa wani abun taga ya miƙe rai a ɓace ya bar palourn, ya fahimci yarinyar na ba ƙaramin rena sa take son yi ba amma zai yi maganin ta, ya faɗa cikin ransa yana fita ya ja motar sa yabar gidan.
Ajiyar zuciya Aunty Nidrah ta sauke tana kallon Janaam dake kai samosa a bakinta, me yasa tayi hakan? Ta san shi ne ko akwai wata alaƙa ce tsakanin su? Tambayoyin dake bakinta kenan da take buƙatar amsar su awajen Janaam sai dai taga ita ɗin ko ajikinta abinda ya faru, hakan yasa ta ja bakinta tayi shiru ta ci gaba da dannar wayarta har Janaam ta gama sannan ta hau sama da ita zuwa ɗakinta. s
Sosai na saki jiki da Aunty Nidrah duk da ba tada son surutu amma tana da matukar daɗin zama da kirki, gashi in ka zauna da ita ko ƙaƙa ne sai ka ƙaru da wani ilimi, duk da zaune aunty Nidrah take a gidan su business takeyi sosai na kayan gyaran jiki da turarukkan wuta irin na yan Maiduguri, ta jima tana faɗa mani yadda ake haɗa wasu abubuwan kafin ya Nu'aym ya kirani a waya, wanda hakan yasa ta bani waje saboda naji daɗin yin wayar ta bar ɗakin....
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA 1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
36.
Duk da yadda nisa ya shiga tsakanina da Ya Nu'aym ina samun duk wata irin kulawa data shafi soyayya a hannunsa, bai bar wani gurbi ko ɗaya ba da zai bani damar na zauna nayi tunanin rashin masoyi akusa da ni ko kuma yasa nai kuka akan soyayya, ya san me nake so, ya san farin ciki na, ya san damuwa ta duk tsanin nisa bai sa ya gaza mini a soyayya ba domin kuwa hatta a maganata yakan fahimci ma'anar ko wace kalma da inda ta dosa, shi ne ainahin wanda ya kamata akira nice person da Aunty Nidrah ta faɗa ɗazu shi yasa jingina kalmar da Umar Farouk ya matuƙar bani dariya, ina wannan tunanin bayan kammala wayata da ya Nu'aym Aunty Nidrah ta dawo cikin ɗakin, farin cikin da na samu bayan gama wayata da shi kasa ɓoyuwa ya yi hakan ya sa data kalleni ta saki murmushi haɗe da cewa, "Sis meye labari naga fuskar ki sai wani annuri take?" Ta ƙare zancen tare da zaunawa bakin gado tana tsare ni da idanuwa, ƴar dariya na saki haɗe da dukar da kaina kafin na ɗago nace, "Abun sirri ne Aunty Nidrah ba yanzu ba, ki bari kina zaman ki zan zo na baki labari". "To ai shikennan ina jira, amma kafin nan bari na tambayeki". "To aunty Nidrah ina jin ki". Na faɗa ina tattaro duka hankalina a kanta, shiru ta ɗan yi kafin tace, "Da alama akwai wani abu tsakanin ki da ɗan uwana don abinda ya faru ɗazu ban ji daɗin sa ba, sanadiyar hakan ma kinga ko sallama basu yi da Mamie ba duk da dai kusan haka yake shi abu kaɗan sai ya ɓata masa rai, musamman idan abun ya zo da reni, kuma kema dai kinsan reni bai da daɗi, ki faɗa mun shin kin san shi ne da kika yi masa hakan ko kuwa?" Yi nai tamkar ban fahimci me take faɗa ba haɗe da cewa, "Wai waye kike zance Aunty Nidrah?" Harara ta yi da wasa kafin tace, "Sis joke aside, Umar Farouk nake magana kin san shi ko baki san shi ba?" "Na san shi Aunty Nidrah school ɗin mu ɗaya dashi". "To meye tsakanin ku dashi?" Dariya na saki haɗe da cewa, "Ba komai". "Amma shine ki kai masa hakan ɗazu? Baki san zai iya haifar da ƴar tsama tsakanin ku ba?" Ai sai dai kar a ƙara, na faɗa cikin zuciyarsa kafin a zahiri nace, "Ta me Aunty Nidrah? Ni fa ba abinda nai". "Shi kuma ya tsani reni, kamar yadda na faɗa miki Umar Farouk mutumen kirki ne". "Shi ya ban dariya saboda nasan dai faɗa kawai kika yi saboda yana ɗan uwan ki, a kallo ɗaya kuma cikin dakika ɗaya zaka iya fadar ko wane ne shi, kuma nasan kema kin san hakan, kin ga kuwa dole nayi dariya". Wayar Aunty Nidrah ɗin ce da tayi ƙara ta katse zancen da muke yi, cikin muryarta mai sanyi bayan ta ɗaga wayar ta kai a kunne na ji tace, "Ba dai har ka iso ba?"Ban ji me aka faɗa daga cikin wayar ba na dai ga ta ɗan bata rai ashagwabe tana cewa, "To ka tafi mana sai ta kwana anan". Jin hakan data faɗa ya tabbatar mini da cewa Ya Jameel ne don haka na sauko daga kan gadon haɗe da gyara mayafin abayata ina jiran ta kammala wayar, bayan ta gama ta ɗago kai ta kalleni haɗe da cewa, "Eh lallai, wato kin gaji da ganina kema har da wani tashi kina shirin tafiya?" Dariya na saki haɗe da cewa, "Gwara haka Aunty Nidrah kar na kashe hanyar gobe ina son zo miki wani lokacin yaki kawo ni" "Tom ai Shikennan, muje sai kuyi sallama da Mamie." Ta faɗa haɗe da miƙewa ni kuma nayi gaba, sai dana sauko ƙasa sannan Aunty Nidrah ta sauko itama ɗauke da leda a hannunta, ɗakin Mamie dake can gefe ta nufa tana cewa nazo mu tafi, wani ɗan madaidaicin palour muka nufa, muna shiga wani irin ƙamshi mai ratsa zuciya da daddaɗan sanyin a.c ya tarbe mu, lumshe idanuwa na nayi na buɗe ina sake buɗe kofofin hanci na saboda na shaƙi ƙamshin dai kyau don ba ƙaramin daɗi ya yi mini ba, kujera Aunty Nidrah ta nuna mini alamar na zauna kafin ta wuce ciki ta shiga ta wata ƙofa ta kira Mamie, ba'a jima ba suka fito tare Mamie na biye da ita a baya, "Janaam ba dai har zaki tafi ba?" Mamie ta faɗa tana ƙarasowa cikin palourn haɗe da zama akan kujerar dake kallona, ina murmushi na amsa mata da "Eh wucewa zan yi". Miƙewa ta yi ta koma cikin daki sai gata da wata bag mai ɗan girma ta miƙo mini tana cewa, "Gashi idan kin je kya gaida Hajiya sosai kin ji ko". "In Sha Allah zata ji". Na faɗa tare da miƙewa ba tare dana ɗauki jakar data ajiye mini ba saboda kunya, Aunty Nidrah ce ta dauko mini suka rakoni ita da Mamie har bakin main palour na yiwa Mamie godiya sosai sannan ta juya ta koma ciki, Aunty Nidrah kuwa sai data kai ni har bakin mota na buɗe gaba na shiga ita kuma ta buɗe baya ta saka mani kayan tana cewa, "Ga saƙo nan ki kaiwa Mamah idan kika buɗe zaki ga naki a ciki". "Kai Aunty Nidrah wai har da wata hidima haka Allah tayi yawa". Kafin na rufe baki Ya Jameel ya ƙaraso wajen dama ko da muka iso bakin motar baya ciki yana waje can gefe yana waya. "Matata me ake faɗa ba da ni ba?". Ya faɗa yana kallon Aunty Nidrah, murmushi kawai na yi na dauke kai don indai soyayya ce to fa ya Jameel lamba ɗaya ne, kamar ance na juya na hango motar Umar Farouk a can gefen titi da yake gidansu aunty Nidrah ɗin akan titi yake, kauda kaina nayi ba tare da na damu ba tunda nasan dalilin da zai iya kawo sa anguwar, sai da suka shafe kusan minti goma kafin suka yi sallama Ya Jameel ya zo ya ja motar muka tafi Aunty Nidrah na ɗaga mini hannu,
Bayan na koma gida da daddare Aunty Nidrah ta kira ni tana yi mini ban gajiya kafin tace. "Janaam kin tabbata babu komai tsakaninki da Umar Farouk?" "Me ya faru ne Aunty?" Na tambaya don in dai ba tashin hankali ba ni nasan babu wata kyakkyawar alaka tsakanina dashi, ajiyar zuciya na ji ta sauke kafin tace, "Kin san ashe ɗazu bai tafi ba yana bakin gida duk jimawar nan da kika yi? Sai bayan kun tafi ne zan shiga cikin gida sai gashi naga ya fito daga cikin motar sa, nan nake tambayar sa dama bai tafi ba shine yace wai eh kika hana shi tafiya". Taɓe baki na yi haɗe dayin yar dariya ina zaro ido na ce, "Toh! Ni kuwa da nai masa me Aunty Nidrah?" "Nima dai ban sani ba don bai fadamun ba dana tambayesa, asali ma cewa yai shi bai sanki ba sai yau". Haushi ne ya kama ni jin renin hankalin da yai mata, kenan me yake nufi ni karya na yi mata, a ɗan hasale na ce, "Zai fadi haka mana saboda yana tsoron ki tambayeni na faɗa maki munanan halayensa da dabi'unsa, ko bayan haka babu jituwa sam a tsakaninmu shi yasa ya tsaneni kuma nima na tsanesa to the extend". "Easy Janaam, shi dai bai faɗi hakan ba, amma ni na hango wani abun tsakanin ku wanda daga ke har shi baku fahimta ba, kin san IDO A DUHU ba komai yake iya hangowa ba". "Tab! To ni dai wannan bayanin Aunty Nidrah ba fahimtar sa zanyi ba kawai mubar zancen, "Ai shikennan, idan ta yi wari ma ji". Dariya sosai aunty Nidrah ta bani don haka na shiga yi kafin nace, "Wari fa kika ce Aunty kuma tsakanin ni dashi? Hmmm over my died body wallahi!". "Ehm to ai shikenan ya kika isko Mamah?" "Tana lafiya gata can har ta kwanta nima zan kwanta naga kiran ki". "To bari na barki sai da safe na gode sosai". "Allah ya tashe mu lafiya best Aunt". Na faɗa haɗe da kashe wayar ina gyara kwanciyata don bacci nake ji sosai.
Washe gari ko da na shiga school na samu har an fara yi mana lectures don na makara ban tashi ba tun dana koma bayan sallar asuba sai takwas da rabi, kafin na gama shiryawa har ƙarfe tara ta buge, ko da na ƙaraso cikin school kuma ƙarfe tara da kusan kwata, sosai gabana ya shiga faɗuwa sanin ba lallai ne malamin ya barni na shiga ba, sai gashi ina zuwa har na ja na tsaya abakin class yai mini izini dana shigo, seat dina da kowa ya sanni da ita na nufa, amma sai na hango Umar Farouk zaune akai, haɗe rai nayi ina jira ya tashi cikin tsawa malamin ya yi mini umurni dana samu waje na zauna, kamar zan yi kuka na shiga raba idanuwa sai dai ba seat ko daya da ba'a zauna ba in ba ta Umar Farouk ba da shima ya saba zama a can baya, kenan da sanin sa ya yi haka saboda ya tsokanoni? Ai ko ya tara ya samu, Na faɗa cikin zuciyarsa haɗe da yin kwafa sannan na nufi wajen kujerar na zauna, Allah ya sani na tsani zaman seat ɗin baya saboda bana jin abinda malami ke faɗa da kyau musamman idan ana surutu, haka nan dai na samu aka gama lecture malamin ya fita ba tare dana fahimci komai ba, raina a ɓace na taso na nufo wajen seat ɗina na ɗora littafaina akai ina folding hannaye na a ƙirji, ɗago kai Umar Farouk yai ya kalleni na sake tsuke fuska ina kauda kaina gefe, maida kansa ƙasa yai shima tamkar bai gane ni awajen ba yana ci gaba da duba littafin dake hannunsa, "kaga malam tashi ka bani wajena". Na faɗa cike da ɓacin rai don ji nake gaba-daya ya gama rena mini da wayau....
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
37.
Ganin ko motsawa bai yi ba yasa a hasale na sake cewa, "dakai fa nake malam". Nan ma bai tanka ni ba hakan yasa na fizge littafin dake hannunsa cike da masifa ina cewa. "Ka tashi malam ka bani wajena ina magana ka yi banza dani sai kace wata mahaukaciya, kowa ajin nan ya san wannan seat ɗina ce ba kada right ɗin zama akai saboda haka dole ka bani wajena". A mamaki na sai gani nai tsam Umar Farouk ya miƙe ya tashi, tsaye yai agabana yana kallon cikin idanuwana na yi saurin jaye nawa idanuwan, sai daya saki wani miskilin murmushi kafin na ji kawai ya riƙo hannuna dake riƙe da littafinsa, da sauri na juyo ina zaro idanuwa ganin abinda ya aikata, ba tare daya kalleni ba ya ɗago hannun nawa yasa daya hannunsa ya fizge littafinsa haɗe da cewa, "Yadda kika biya kuɗin makaranta haka nima na biya Madam ba daga gidanku kika zo da seat ɗin ba, idan kina son zama akai dole ki riƙa shigowa school akan lokaci, idan ba haka ba daga yanzu seat ɗin ta zama tawa". "Saboda daga gidanku kai ma kazo da ita?" Na faɗa ina kallonsa ido cikin ido ba tare da tsoro ba sannan na kwace hannuna daga riƙon da yai mi shi na kwashi littafaina na fice daga class ɗin rai na aɓace tamkar zan tashi sama.
Umar Farouk kuwa seat ɗin ya koma ya zauna yana jin wani abu na fizgar zuciyarsa, tafin hannunsa ya kalla daya riƙa hannun Janaam dashi haɗe da rumƙe hannu sai kace wanda ya kama wani abu.
A waje wayata na ciro cikin jaka ina sake jin ɓacin rai na ta so mini, gashi Nu'aymah bata shigo ba hakan yasa na kirata na ji ko lafiya, bugu biyu bata ɗaga ba sai ana uku na ji muryarta can ƙasa ƙasa, "Subhanallahi Aymah lafiya na ji muryarki haka?" Na faɗa cike da damuwa jin muryarta yadda ban saba jinta ba, shiru na ji ta yi na sakanni kafin tace, "lafiya ƙalau Janaam". "To ya akai baki shigo makaranta ba?" "Kawai dai". Ta faɗa a daƙile, mamaki ne ya kamani saboda daga ni har ita fashin zuwa makaranta ba ɗabi'ar mu bace har sai da wani ƙwaƙƙwaran dalili, jin yadda take amsa mun yasa nayi sallama da ita na kashe wayar ina jin babu daɗi a raina, tunani na shiga yi dalilin da zai sa Nu'aymah fashin zuwa makaranta idan har lafiyarta kalau amma nakasa gano komai, na ja tsaki ina tuna yadda Umar Farouk ya riƙo mani hannu tare dasa hannu na kakkaɓe wajen tamkar wadda datti ya taɓa, kasancewar ban fahimci lecture ɗin yau ba gaba-daya yasa na shiga warar idanuwa inda zan hango Jabir don shi kadai ne a class ɗin bayan wancan ɗan faɗin rai da zai iya zauna wa yai mini bayani na fahimta tamkar yadda malamin yai saboda shima yana da matukar kai sosai, yana gane karatu don a group ɗin su shi keyi masu tutorial, ina wannan tunanin sai gashi ya zo wucewa, da sauri na miƙe ina cewa, "Amm. Jabir don Allah minti ɗaya". Ya juyo rike da littafinsa yana cewa, "Janaam lafiya dai ko?" "Eh lafiya ƙalau don Allah lecture ɗin da aka gama nake so ka sake yimin bayani in ba damuwa kafin mu shiga next lecture". "Ok da Capteria zan shiga amma bari na gama miki sai na tafi, dame-dame ne baki fahimta ba?" Ya tambaya tare da zama gefen da na zauna anan gaban class ɗin mu, murmushi nai sannan na ce, "Komai ma ban fahimta ba kasan ko dana shigo anfara lectures, sai kuma ban samu seat ɗin gaba dana saba zama ba sai can baya". "Eh haka ne". Jabir ya faɗa sannan ya fara koƙarin yimani bayani, ko minti biyar bamuyi da farawa ba sai ganin mutum kawai muka yi agaban mu, ɗago kan da zamu yi ni da Jabir sai kawai gani nayi Umar Farouk ya shaƙo wuyan rigar Jabir, miƙewa Jabir yai cikin ƙarfin hali zai yi magana Umar Farouk ya daukesa mari, zai sake magana ya sake ɗaukesa ta ɗaya ƙuncin haɗe da finciko sa, da sauri na miƙe raina a ɓace ina faɗin. "Wai meye haka? Me yake damunka Umar? Me yai maka ne da kake dukansa?" Ko kulani Umar Farouk bai yi ba yaci gaba da dukan Jabir daya faɗi ƙasa, yana ja da baya yana dukan sa nayi saurin shiga tsakaninsu tare da fashewa da kuka, wanda hakan ya ba Jabir damar tashi yabar wajen da gudu, "Menene haka anya kai mutum ne ko dabba da baka san kima da darajar mutane ba? Akan me zaka dake sa karatu da yake koya mun?". Na ƙare maganar da ƙarfi wanda hakan yasa hankalin mutane dawowa a kan mu, kallo ɗaya Umar Faruk da idanuwan sa suka kaɗa tamkar an watsa masa barkono yai masu sai gashi kowawanen su ya kama gabansa, kaina ya yo yana yimin wani irin kallo cikin tsananin ɓacin rai da sai daya sa gabana faɗuwa amma na dake naƙi matsawa ko nan da can, sai da yazo dab dani ina jin lumfashi na tamkar zai ɗauke nayi saurin haɗiye wasu miyau masu kauri, cikin kausasshiyar muryar da ban taɓa jinsa da ita ba ya ce, "Idan kina so ki tantance mutum ne ni ko