Showing 12001 words to 15000 words out of 157423 words

Chapter 5 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

497

binneni ko na binneki". Suka sa dariya ita da ya Jameel tana cewa, "Bana fatan hakan ai Janaam". Na turo baki cike da shagwaɓa ina bubbuga ƙafafuwa ƙasa, Ya Jameel ya buɗe baki yana kallona kafin yace. "Iyeee...idan aka ce maki auta kice ba haka ba, yanzu Mamah wannan abinda take yi maki kina wani shafa kanta idan ba auta ba wa zai yi hakan yaci duka? Ai in kika ga nadena ce maki auta to gaban 'ya'yanki ne, shima don kar su riƙa fadar hakan ne, sai dai su ce maki Momy." "Tab! Allah Yaya a yadda nake kwaɗayin ƙanne bazan yadda su kirani Momy ba sai dai ko Aunty, idan ba haka ba ko na zugewa yaro". "Saboda ke zuge maki muka yi ko?" Ya Jameel ya faɗa yana kallona, cike da kunya na ɓoye fuskata a bayan Mamah ina dariya, Mamah tace ku tashi muyi taking dinner kafin ayi sallah. Cikin farinciki da soyayyar juna mukayi dinner munayi muna fira gwanin sha'awa, yadda Mamah ke sake mana baza ka taɓa cewa mu 'yayanta bane sai dai ko ƙannenta. Muna kammalawa ana gama kiraye-kirayen sallar isha'i Ya Jameel yayi masallaci Mamah ta wuce ɗakinta ni kuma na fara gyara wajen da muka ci abinci na wanke kayan da muka ɓata sannan na wuce ɗakina nayi sallah, bayan na gama na dauko littafaina na dudduba karatun da muka yi yau, ina gamawa na shiga wajen Mamah muka ɗan taɓa fira sannan tace naje na kwanta tunda nace dawuri zan fita, nayi mata seda safe sannan na koma ɗakina na kwanta.

Washe gari da nayi sallar asuba ban koma na kwanta ba ganin Mamah a kitchen sai dana rirriƙa mata ta rage aiki sannan naje nayi wanka na shiryo, ina fitowa har Mamah ta haɗa mani samosa da soyayyen biredi da kwai, sai kunun aya a ɗan ƙaramin flaks, side hug na bata haɗe da cewa. "Mamah you're the best Mom, thank you so much." Na karɓa sannan na fito zan wuce mamah ta rakoni tana faɗin, "Ki kula da kanki sosai Janaam Allah ya tsare ki ya kaiki lafiya". "Amin". Na faɗa sannan na wuce, abun mamaki ina fitowa naga motar Ya Jameel ya fiddo yana zaune a ciki, "Ya Jameel ina kwana". Na faɗa zan wuce ya ce, "lafiya klw Janaam, zo na saukeki school zan tafi wani wuri ne, so i think hanya ɗaya ne". "Amma Ya tare zamu tafi da Nu'aymah." "Saboda ke babu mota a gidanku ko? Dallah Malama shigo na saukeki karki ɓata mani lokaci". Raina a ɓace na zagaya na buɗe front seat na zauna ina faman haɗe rai, yai banza dani haɗe da tada motar ya ja ya bar wajen.....

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 1000 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (MONIEPOINT)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

0907 927 4454 KO 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @Billysfari

*IDO A DUHU*

07040402435

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            8.

Har cikin school Ya Jameel ya shiga dani ya tambayeni inda zai ajiyeni na nuna masa sannan ya yi parking ɗin motar na buɗe na fito, kuɗi ya ciro gaban aljihunsa ya miƙo mani yana faɗin. "Gashi sai kiyi amfani dasu ga dawowa, ita wacce kike zancen tare zaku zo ta jima da shigowa makaranta don haka sai ki maida wuƙar ki saki dan". hannu nasa na karɓi kuɗin ina yi masa godiya sannan ya ja motar sa yabar wajen.

Raina ne ya ɓaci sosai jin wai Nu'aymah ta jima da shigowa school amma shine ko ta neme ni a waya ta sanar dani, wayata na ciro a cikin handbag da niyar kiranta sai ga message ɗinta na gani, hakuri ne take ban akan yau bata samu ta fito da mota ba saboda tata da aka fasama glass Abba ya kaita wajen gyara tun jiya, Ummi kuma ta hanata ɗaukar mata tata, shine fa da za'a ajiye Nihla a school Abba yace tafito itama a ajiyeta, a cewar ta takira lambar tawa switch up shine ta turo mani saƙo don kar naji ba daɗi, murmushi na saki sannan na ƙarasa shiga cikin class ɗin, Nu'aymah na ganina ta taso ta rungumeni, harara na maka mata da wasa ina cewa, "Ai ni har nayi fushi, wlh Banga text message ɗinki ba sai yanzu da Ya Jameel ya ajiye ni, ina ciro wayar zan kiraki naga saƙonki." "Ai kuwa dawuri na tura maki saƙon don karki zauna jirana kiyi missing lecture." Na ajiye small box din da Mamah ta sako mani breakfast a ciki na ɗora handbag ɗina akan table ɗin sannan na zauna ina cewa, "Haba! Ai ko da kece zaki koya mani duk abinda akayi wajen lecture ɗin da nayi missing, ya garin?" ta amsa da alhamdulillah idanuwanta na a tacan ɗaya ɓangaren da tun ɗazu naga tana kallo, juyawa nayi don ganin ko me take kallo haka da har bata ji abinda na faɗa ba yanzu.

Umar Farouk na hango a seat ɗin baya shi kaɗai kamar mai tunanin wani abu, sai ƙawayensa yan mata dake gaban seat ɗinsa suna fira, ban gama koƙarin tantance kallon da Nu'aymah keyi masa ba naji ya daka masu tsawa yana masifa wai surutun su ya damesa sai kace tsuntsaye, idan baza suyi shiru ba su tashi su fita waje, nan kika ji tsit duk sun kama bakunan su sai faɗin suke, "Sorry sir." Sai kace wani malamin su, takaici ne ya rufe ni har bansan lokacin da na ja wani irin dogon tsaki ba da sai da sautinsa ya karaɗe class ɗin, cike da mamaki kowa kallonsa ya koma akaina, ni kuwa nayi tamkar bansan me ke faruwa ba tare da juyawa abina, shigowar da lecturer ɗin da zai ɗauke mu yayi ita ta dakatar da faruwar duk wani abu da suke tunanin zai iya faruwa, ni kuwa ko ajikina sai ma maida hankalina ɗa nayi ga lecture ɗin da za'a fara.

Ɓangaren Umar Farouk kuwa shi kansa mamaki ne ya rufe sa lokacin da yaji sautin fitar tsakin da akayi bayan gama maganarsa, a hankali ya ɗago kai cikin ɓacin rai don ganin ko wacece, sai dai a lokacin ne Janam ta juya, idanuwan Nu'aymah dake kansa lokacin yasa yayi tsammanin ita ce tayi masa tsaki, hakan yasa ya riƙe fuskarta cike da son nuna mata kuskurenta na shiga gonarsa da tayi idan aka gama lecture.

Muna gama lecture mun fito Nu'aymah na amsa waya ni kuma nayi gaba, 'yan matan Umar Farouk ne ta ga sun zagayeta, shi kuma ya yi tsaye gabanta yana ƙare mata kallo don yama rasa wani kalar hukunci zai yi mata, sai daya ja iska ya furzar sannan ya ɗago kai fuskarsa a haɗe tamkar wanda aka yiwa mutuwa ya ce, "Ke maimaita abinda kika yi ɗazu". Nu'aymah da gabaɗaya ta kasa controlling kanta sai kallonsa takeyi murmushi kwance akan fuskarta tace, "Me kenan Umar Farouk?" Wani mugun kallo yayi mata kafin yace, "Karki bari na sake maimaita kaina, idan ba haka ba na rantse sai na saka an tozar taki a filin makarantar nan, ta yadda gobe baza ki sake kwasa ba idan har ban kasa dake ba." Sai a lokacin Nu'aymah ta fahimci inda ya dosa, ta buɗe baki kenan da niyar magana ta ji Umar Farouk ya wanka mata mari yana faɗin, "An faɗa maki ni sarki ne ina da lokacin ɓatawa zaki tsaya kina wani bangare tunani?" Daga nan ya shiga nuna yan matan yana cewa, "Kuyi mata abinda kuka san zai yi maku ciwo in akayi maku shi acikin makarantar nan, idan ba haka ba wallahi ni zan yi maku shi". Yana kaiwa nan yabar wajen ya koma can gefe ya zauna yana kallon me zasu yi mata, ita kuma Nu'aymah na dafe da kuncinta kanta a ƙasa tana jin wata irin kunya ta rufeta, dai-dai lokacin ni kuma na juyo ganin bata ƙaraso inda nake ba har lokacin, mayafinta na hango ɗaya daga cikin yan matan Umar Farouk na ja amma Nu'aymah batayi yunƙurin hanata ba, zuciyata na tafasa da sauri na ƙaraso wajen, ina zuwa na tura yarinyar da ƙarfi ta faɗi tare da mayafin Nu'aymah ɗin dake hannunta, duƙawa nayi na ɗauko mata na yafa mata sannan na shiga ture sauran yan matan dake zagaye da ita da kusan duka Christian ne, cikin harshen turanci na shiga yi masu masifa ina cewa sun ji kunya 'yar uwarsu mace suke yiwa hakan saboda wani ƙaton banza da bazai taɓa amfanar dasu ba sai dai su su amfane sa ya lalata masu rayuwa a banza, cikin kakkausar murya na shiga nuna su da yatsa ina cigaba da cewa duk wanda yaƙara taɓata a cikinsu sai nayi reporting ɗinsa ga school authority, daga nan na ja hannun Nu'aymah tamkar wata sakarai muka nufi inda muke zama, muna zuwa na rufeta da masifa akan barin su da tayi suke ƙokarin ci mata zarafi a tsakiyar makaranta, sai dai Nu'aymah fa ko ajikinta sai ma murmushi takeyi kafin naga idanuwanta na saukar da kwalla, ta ce "Da ace Umar Farouk zai san irin tarin soyayya da kaunar da nake yi masa wallahi da bazai ɗau hannunsa ya mareni ba, da bazai sa wuɗan can karnukan suyi ƙoƙarin zubar mani da mutunci ba". Ɗan zaro idanuwa nayi ina kallonta kafin nace. "Me kike faɗa? Mari! Shi Umar Farouk ɗin ne ya mareki? Akan me? Cewa kikayi kina son sa ne?" Na watso mata wuɗannan tambayoyin a jere ina yi mata wani irin kallo mai ban mamaki, hannu ta saka ta share hawayen fuskarta sannan tace, "Besty bana tunanin zai mareni akan nace ina sonsa, kawai dai akasi aka samu ya dauka nice nayi masa tsaki ɗazu". "Mtss.. Wannan ai shirmene, bari ni naje idan har shi makaho ne bai san wacce yake nema ba zan cire niƙaf ɗin ya ganeni da kyau kuma na sheda masa cewa nice wadda nayi masa tsakin naga me zai iya". Na faɗa a fusace ina ƙoƙarin barin wajen tayi saurin riƙeni tana cewa. "Please Besty don Allah ki ƙyalesa, ko ma meye naji na ɗauka indai akanki ne". "Wannan ba a kaina bane Besty akan soyayya dai kika yi". Na faɗa ina sake jin wani zafi ƙasan zuciyata, Nu'aymah ta jawoni ta zaunar dani akusa da ita tana cewa, "Na ji ɗin mu barshi a haka saboda soyayya nayi, ina shikennan ko?" Takaicin tane ya sake rufeni na wafce hannuna tare da juyar da kai na gefe, yadda nake jin tsanarsa azuciyata ya bala'in lunkuwa saboda abinda yayiwa Bestynah, na kuma saka a raina in har na samu dama wallahi sai na yi masa fiye da abinda ya yi mata, ina da sanyin hali sosai amma bana son reni kuma na tsanesa, ga kowa ban daukar wulaƙanci sannan bana jurar ganin an wulakanta wani gabana, sai naji tamkar zuciyata zata fashe, sai da Nu'aymah tayi da gaske sannan nabar abun har muka samu mukayi breakfast sannan muka koma class.

Umar Farouk kuwa ko da yan matan suka koma inda yake kallonsu yai a wulaƙance yace, "Wacece ita ɗin, ina nufin waccan mai niƙaf ɗin da kuka bari ta tafi da ita baku haɗa da ita ba?" "Amatul-Alim ibrahim sunanta, Amma Janaam ake kiranta, itace ɗazu tayi maka tsaki sir ba Nu'aymah ba". "Meye? Waye Nu'aymah?" "Wacce ka mara sir". Suka bashi amsa a tare. "Damn it!" Ya faɗa yana sakarwa iska kulli, a take yaji wani takaicin kansa ya rufesa na yin hukunci a inda ba nan ya dace ba, sosai ya ji ba daɗi a ransa har sai da yanayin sa ya bayyanar da hakan, tsanar yarinyar da aka kira Amatul-Alim ta rufesa dama yana neman hanyar da zai wulakantata saboda yadda take ɗaukar kanta tare da jin kamar ita wata ce, ba abinda yafi baƙin ta masa rai da itama sama da saka niƙaf ɗin munafurci da take yi sai kace tafi kowa musulunci, tabbas dole ya lunka mata wulakancin da yayi niyar yimata sau biyu bisa saka shi hukunta yariñyar mutane ba bisa laifinta ba. ɗago kai ya yi ya kallesu kafin yabar wajen su kuma suka rufa masa baya.

A ranar wuni Umar Faruk yai yana jin ba daɗi abinda ya yiwa Nu'aymah, mutum ne shi da baya shiga harkar kowa sai wanda ya shiga tasa, gashi yau yai abinda ya sha masa kai bai ji bai gani ba, ji yai bazai iya yafewa kansa abinda yai mata ba ba tare daya roƙe ta ba, at least hakan zai sama masa natsuwa a zuciya, wayarsa ya janyo ya shiga group dinsu na makaranta, number mai suna Nu'aymah kamar yadda ya ji sun faɗa ya shiga searching sai dai har ya gama duba contact ɗin bai samu ba, tsaki ya ja kafin ya kira lambar cikin yan matansa Felicia, bugu ɗaya ta ɗaga wani irin farin ciki na rufeta ganin wai yau itace Umar Farouk ya kira, tana ɗagawa yace, "Felicia ki turo mani Number wannan yarinyar ta ɗazu, ya ma sunanta?" "Sir Nu'aymah?" "Yes!" Ya faɗa yana kashe wayar, Felicia taji kamar ta fashe da kuka ko kuma kar ta tura masa lambar saboda haushin da ta ji, sai dai tasan ko sama da ƙasa zata hade baza ta iya ba don bata ma isa ba...

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 1000 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (MONIEPOINT)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

0907 927 4454 KO 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @Billysfari

*IDO A DUHU*

07040402435

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            9.

Ko minti biyu basu yi ba da gama waya da Felicia sai gashi ta turo masa number Nu'aymah, sau uku yana gwada kiranta amma sai yaji kamar bazai iya ba don gudun reni saboda yadda yaga rawar kai ta yiwa yan mata yawa, tsaki ya saki a karo na ba adadi yana hango marin daya sauke mata a fuska ta cikin idanuwansa, ji yai zuciyarsa na sake tabbatar masa da bai kyauta ba don haka cike da ƙwarin guiwa ya sake gwada kiranta a karo na huɗu, yana danna lambar yai saurin runtse idanuwa, lokacin ita kuma Nu'aymah na zaune tare da Nihla tana koya mata aikin gida da aka basu a school, wayarta ta ji tayi ƙara ta miƙa hannu ta ɗauko tana kaiwa a kunnen ta ba tare data tsaya duba ko wa ya kirata ba. "Hello wake kan layi?" Ya faɗa tamkar bashi ya kirata ba, sai a lokacin Nu'aymah ta ciro wayar a kunnenta jin muryar namiji da irin tambayar da aka jefo mata, ganin sabuwar lamba yasa tayi kamar zata katse kiran sai kuma ta dakata jin ankira sunanta ta cikin wayar da wata irin murya da tasa gabanta faɗuwa. "Nu'aymah?" Aka faɗa ta sigar tambaya, tamkar tana gabansa ta shiga kaɗa kai a ɗan ruɗe jin muryar wanda duk inda zai shiga bazata taɓa mantata ba, "Hello". Umar Farouk ya sake faɗa, da sauri Nu'aymah tamkar wacce aka fizgo muryarta ta ce, "Na.na.na'am, hello nice, nice Nu'aymah". Ta ƙare zancen tare da miƙewa ta bar wajen, Nihla ta bita da idanuwa kafin ta maido hankalinta ga aikin gida da take yi. A bakin gado Nu'aymah ta zauna tana sauraren Umar Farouk cikin wata murya mai cike da natsuwa yana cewa. "Sunana Umar Farouk Ibrahim, na kiraki ne na baki hakuri akan abinda ya faru tsakaninmu dake ɗazu saboda a tsammanina kece kika.." da sauri Nu'aymah ta dakatar dashi tana cewa, "No.no ba laifi wallahi komai ya wuce a wajena". "No am Sorry please, nasan nayi hurting ɗinki so forgive me idan zaki iya". Murmushi ya kwacewa Nu'aymah ta lumshe idanuwa tana rufesu lokaci ɗaya ta buɗe tana jin wani sanyi da farin ciki a ranta, shiru tayi bata iyayin magana ba haka shima bai sake cewa komai ba har na tsawon wasu mintuna, ajiyar zuciya ta ja ta sauke sannan tace. "Shikenan na yafe maka kuma komai ya wuce in sha Allah". "Nagode". Umar Farouk ya faɗa, daga haka ya kashe wayar sa, sai a lokacin yaji ya samu cikakkiyar natsuwar da zai iya runtsawa yana cilli da wayar a gefen gado tare da kwantawa.

Nu'aymah kuwa tana jin ya katse kiran tasa wata yar ƙara haɗe dayin tsalle tana farin ciki, idanuwanta suka sauka akan Nihla dake tsaye a bakin ƙofa ta saka pen ɗinta abaki tana kallonta, hannunta tazo ta riƙo ta shiga yin juyi da ita kafin ta tsaya taja chicks dinta tana cewa, "My ɓakutu meye kike kallo na haka? Am so excited today faɗamun me kike so na baki?". "Adda kin fara soyayya ko? Allah sai na faɗawa Ummi". Ta ji Nihla ta faɗa ba zato ba tsammani, tana gama faɗar hakan kuma ta ruga da gudu ai kuwa ta bita abaya tana ƙokarin kamata taja mata kunne don bata shirya amsa tambayoyin Ummi ba.

A daren ranar tsabar farinciki Nu'aymah kasa runtsawa tayi, haka kuma bata iya yin haƙuri ba har sai safiya ta waye ta labartawa Janaam abinda ke faruwa, cikin daren misalin ƙarfe biyu da rabi na dare ta kirata, cikin magagin bacci na ɗaga Nu'aymah ta shiga bani labarin wai Umar Farouk ya kirata yana roƙon ta yafe masa abinda yayi mata, tsaki na ja haɗe da cewa. "Ba kida aikin yi Aymah sai da safe". na kashe wayata ina juya kwanciya ta tare da cigaba da baccin da nake yi ina jin ta bala'in takura ni data tayar dani a kan wannan zancen banzar.

Washe gari Nu'aymah fuskarta ta kasa ɓoye irin farin cikin da take ciki, burinta ɗaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login