Showing 51001 words to 54000 words out of 157423 words
faɗa ta can ɗaya ɓangaren tun kafin yai magana, Muryar da ya ji ta tabbatar masa da Nu'aymah ce kamar yadda yai tsammani, murmushi ya ɗan saki haɗe da cewa, "Hello friendy ban kira ba na ji kun wuce ko kuna nan ba ko?" Yadda yai maganar cikin sanyin murya yasa Nu'aymah jin daɗi tana sauke ajiyar zuciya tace "Ba komai ai baka laifi friendy kuma baza ka taɓa yinsa ba indai awaje na ne", "Na gode sosai kuwa ya kike ya U.k ɗin don na tabbata kun isa tunda naga number waje". "Haka ne friendy ya jikin naka?" "Alhamdulillah na warke, ya kike?" "Fine, na kuma ji daɗin jin cewa kai ma ka warke, Allah ya ƙara maka lafiya". "Amin". Ya faɗa yana zaunawa gefen gado yayin da tunaninsa ya fara tafiya wajen ƙawar tata da a yanzu haka yake hango su tare a lokacin school, wannan ya sa yaba Nu'aymah lokaci suka ɗan taɓa fira kafin suyi sallama yana faɗin. "Aymah pray for me akwai wani abu dake damu na, zuciyata ta kasa gasgata abinda nake ji amma ina da yaƙini akan ko meye zaki iya taimaka mini idan har zargina ya tabbata". "Meye Umar Farouk? Me zuciyarka ta kasa tabbatar maka friendy ka faɗa mun ko meye zan taimaka maka har sai ka samesa, i promise you that in Sha Allah". Ta ƙare zancen zuciyarta na wani irin bugawa tana so taji ko abinda take ji akansa shima yana ji akanta, Umar Farouk yai baya ya kwanta yana sake hango fuskar Janaam lokacin da take masa masa masifa a waccan ranar ya saki murmushi haɗe da shafa kansa sannan ya ce, "No ba yanzu ba friendy, nasan zaki taimakeni no matter what". "Shikennan zan jira har lokacin da zaka buƙaci hakan". Nu'aymah ta faɗa cikin sanyin jiki don ba haka ta so ba sannan sukayi sallama.
Suna gama wayar ta kira Number Janaam bugu ɗaya ta ɗaga, "hello Besty ai har nayi fushi". Janaam ta fada tana gyara mayafinta tare da jakarta za su fita tare da ya Jameel gidan kawunsu saboda an soma yin hidimar 'yar wajen sa da zata yi aure yau ake sa lalle, tamkar Janaam ɗin na agabanta Nu'aymah ta ɗan harareta tana cewa, "Au! Rigana zakiyi don kada nayi ƙorafi? Ina zaune fa zan ji kina waya da Ya Nu'aym ko tambayata baza kiyi ba balle ma kice a bani". "Laaahhh..ta nan kika ɓullo kuma? Ai naga ke Ya kamata kifara nema na tunda banda number ki ta can ƙasar, amma shine zaki yi saurin lauyeni ko?" "Ehmm..Ni dai mubar wannan zancen tunda ba kida bakin kare kanki, ya Mamah take da Ya Jameel?" "Duk suna lafiya, ni baza ki tambayi ya nike ba". "Love bird ɗin Ya Nu'aym, ke kam ai nasan lafiya ƙalau kike tunda gashi muna magana dake, ko bayan haka ma kullum fa ina jin kuna waya da Ya Nu'aym, da akwai wani abu nasan bazai bari na zauna lafiya ba nima, ke ni ba wannan zancen na kiraki muyi ba, yanzu muka gama waya da mutumen ki.." kafin taƙarasa Janaam ta ce, "A'a mutumen ki dai, Allah dai ya rabani da wahala". Nu'aymah tayi dariya haɗe da cewa, "Ho..ho..ho Besty bakya shanye raɗa wallahi, ke da Umar Farouk ban san ranar da ɗayan ku zai yi mini kara akan ɗaya ba, gashi dai daga cewa mutumen ki har kin gane shi nake nufi". "Ba dole ba tunda shi kaɗai ne mutumen da ke kanki kika san ya tsaneni". "Ehm Allah dai ya yi muku magani Besty, ni dai ki taya ni addu'a na kusa zama matar Umar Farouk, don da alama abinda nake ji akansa shima shi yake ji akai na". "Tooo... Allah ya taimaka, Ni dai bazan yimaki fatar zama matar wannan mugun ɗan...". "Ya isa haka Besty, matsalata dake kenan bakya taɓa fadar alkhairi indai akan sa ne". "To tunda kinsan hakan Aymah me yasa zaki riƙa faɗan abinda ya shafesa?" "Ai Shikennan sai an jima, ki gaida Mamah". Nu'aymah ta faɗa tana jin haushin yadda Janaam ta tsani masoyinnata, taɓe baki Janaam ta yi bayan sun gama wayar tare da ƙarasawa dakin Mamah ta yi mata sallama tana faɗa mata saƙon gaisuwar Nu'aymah sannan da sauri ta fice don tun ɗazu ya Jameel ke faman yi mata horn. Buɗe gaban motar ta yi ta shiga tana faɗin. "Am Sorry Ya Jameel". "Kin kuru da nayi tafiyata, me ya tsaida ki bayan naga tun ɗazu kika shirya". "Nu'aymah ce ta kirani kasan halin ta da shegen surutu". "Kamar ke ko?" Ya faɗa yana tada motar haɗe da juyowa ya kalleta yana ci gaba da cewa, "Kin san sai hali yazo ɗaya ake ƙawance". Janaam dai bata ce komai ba har suka bar wajen, dama ta san indai zancen Nu'aymah ce da yan gidansu ya Jameel bazai taɓa faɗa mata mai daɗi ba.
Bacci Umar Farouk yai sosai kafin ya tashi yai wanka yai sallah sannan ya fito palour, zaune ya samu Momy tana kallo ya gaisheta sannan tace ga abincinsa can ta shirya masa akan dining, wajen ya nufa ya zuba ya ci, bayan ya kammala ya dawo palourn ya zauna shima suna ci gaba da kallon tare suna ɗan taɓa fira shi da ita har aka kira sallar la'asar, yana zaune Momy ta tashi ta je yin sallar shi kuma ya nufi dakinsa yai arwala ya fice, bayan ya dawo ya samu Tauheedah a palour zaune da littafanta a gabanta, kai ta ɗago ta gaishesa kafin tace, "Ya Nu'aym don Allah zaka mun Assigment?" Bai tanka ta ba ya nemi waje ya zauna ya kunna kallo yana yi yana kallon yadda take Assigment ɗin ta gefen ido, sai daya tabbatar da baza ta iya ba sannan ya yi mata alama da hannu, cike da jin daɗi Tauheedah ta miƙo masa littafin ya karɓa yana karantawa, Assigment ne aka basu na Chemistry under Empirical formula and molecular formula ya shiga koya mata, bayan ya gama yimata bayani ya ɗago yana kallon ta haɗe da cewa, "Kin gane kuwa?" Tayi murmushi tana cewa, "Eh ya Umar na gane." "Ok tunda kin gane what is the empirical formula of a hydrogen carbon containing 0.08 moles of hydrogen?". Dariya ta saki kafin tafara yi masa bayani daki daki tare da fitar masa da calculation ɗin yadda yake, "Wow!". Umar Farouk ya faɗa saboda yadda tayi shi dai-dai yana cewa,"Very good". Yana miƙa mata hannu itama ta miƙa masa hannu su tafe, tana dariyar jin daɗi tace, "Ya Umar I'm very sure wannan karon ni zan yi beaten Janaam, duk lokacin da akayi Assigment ita take zuwa first nazo second kuma fa da mark kaɗan take tsere mun". Umar Farouk tamkar wanda aka yiwa shocking ya ɗago da ƙarfi yana kallon Tauheeda jin sunan data ambata kafin ya ce, "Janaam? A in kika santa? Waye ita?" Ya kare zancen yana riko hannuwan Tauheedah da karfi, da kallo ta bishi cike da mamaki kafin tace. "Ya Umar Janaam fa yar school ɗin mu ce, Class ɗinmu ɗaya ita take zuwa first position nazo second, she's very intelligent". Umar Farouk ya runtse idanuwa na mintuna kafin ya buɗe yana kallon Tauheeda ya ce, "Try to become first always not second, winner not a loser kin ji ko? Daga yau bana so ki koma barin tana zuwa First position ke kuma second domin hakan na nufin tayi winning a kanki and I hate that kin ji ko?" Ya kare zancen yana jan cheeks dinta haɗe da miƙewa ya bar palourn...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRA N1000 KI KARANTA HANKALI KWANCE.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
030.
Kai tsaye Umar Farouk ya wuce ɗakin sa ya ɗauko key ɗin motar sa yabar gidan, tafiya ya yi mai ɗan tsayi sai da yaga yai nisa da gida sannan ya rage gudun motar yana tunanin inda zai nufa don ji yake babu abinda ke yi masa daɗi, wayar sa ya ciro cikin aljihu ya kira Saleem yana ci gaba da driven da hannu ɗaya, yana ɗagawa yace, "Kana ina ne?" Saleem da fitowarsa wanka kenan yana tsane jiki ya ce, "Ina gida yanzu na fito wanka nake cewa na kiraka idan na gama shiryawa, ya jikin naka?" "Naji sauƙi, ina zaka je ne? Ni yanzu haka na fito". "Ok kana ina mu haɗu so nake ka raka ni wajen bukin wani abokina". "Mtss..matsalata dakai kenan ka cika kwashe-kwashe Saleem". "Na ji dai, zaka zo mu wuce ne ko kuma na sameka a inda kake?" "Bari zan kara so kawai tunda ina bisa hanya". "Shikennan sai ka ƙara so". Saleem ya faɗa sannan suka yi sallama, a gurguje Saleem ya shirya sanin halin abokin nasa, yanzu ne zai hasala idan ya samu bai shirya ba zai iya tafiyarsa, dama Allah ne ya ɗorasa akansa ba wani son shiga jama'a Umar Farouk ɗin yake yi ba". Horn ɗin daya ji ya sashi saurin ficewa cikin shirinsa ya buɗe gaban motar ya shiga yana faɗin. "Ai kasan Uncle Shahid Yayan Umman mu ko? To yaron sa ne zai yi aure kuma kasan tare muka tashi dashi". Umar Farouk bai amsa shi ba ya ja motar kawai yabar ƙofar gidan, sai daya hau titi sannan ya juyo yana maido kallonsa ga Saleem ɗin ya ce, "Ina ne zamu je?" Sanin halin abokin nashi da ya yi da halin ko in kula yasa Saleem cewa. "Meenah event center a can ake bikin". Umar Farouk bai ce komai ba ya ɗauki hanyar da zata kai shi wajen, suna isa motocin ango na isowa wajen, juyin duniya Saleem yai da Umar Farouk ya fito su je amma yaƙi ya ce kawai ya shiga zai jirasa a waje har su kammala, ba don Saleem ya so ba ya fita ya barshi acikin motar shi kuma yabi jerin abokanan ango suka shige ciki da sai sautin kiɗa ke tashi, Umar Farouk kuwa wayarsa ya ciro yana latsa, ji yai ya gaji da latsar wayar kawai ya buɗe motar ya fito ya jingina a jiki, tsintar kansa yai da son kiran number da yai saving jiya da Amaah, don haka ya shiga lalubo lambar a jerin lambobin dake cikin wayarsa yana jin gabansa na wani irin faɗuwa, saurin dafe ƙirjinsa yai jin lambar ta shiga har ta fara ringing, sai dai har wayar ta gama ringing ba'a ɗaga ba, wani irin kwadaituwa ya yi da son sake kiran number a karo na biyu har lokacin ƙirjinsa bai dena bugawa ba, tana shiga ya hango wata yarinya na tahowa inda yake, tsuke fuska ya sake yi har yarinyar ta ƙaraso wajen, ganin cousin sister ɗin sa ce Jiddah 'yar ƙanwar babansa yasa ya ɗan saki fuska, "Ya Umar kai ne anan?" Jiddah ta faɗa fuskarta a sake tana kallonsa, da yake suna ɗan shiri da ita sai ya yi murmushi haɗe da cewa, "Ni ne Jiddah ina kika fito haka?" Wajen da ake bikin ta nuna masa tana cewa, "Wallahi bukin 'yar wajen ƙawar Hajiyar mu akeyi, shine fa Hajiya ta matsa sai na tako mata biki, ya gida ina Momy dasu Tauheeda?" "Duk suna lafiya, nima abokina na rako shi nake jira yafito mu tafi idan sun gama". "Uhmm! Ya Umar manya shine kuma baza ka shiga ba?" "Nayo me Jiddah ko an gayyace ni ne?" "Ai naga ka ce tare kuka zo da abokin ka, kuma bukin na ka abokinsa ne kaga kuwa kamar an gayyace ka ne kaima tunda shi ya jawo ka". Taɓe baki Umar Farouk yai tare da sake kiran lambar da yake trying a karo na biyu yana kai wayar a kunnen sa, Jiddah ta yi murmushi haɗe da cewa, "Ya Umar kayi kyau bari mu ɗauki hoto". Bai hanata ba ta matso kusa dashi ta shiga ɗaukar hoton, dai-dai lokacin kuma Janaam da taga an matsa mata da kira kuma idan ta ɗaga ba lallai ne ta ji ba ta fito daga cikin wajen tana ƙoƙarin ɗaga kiran sai dai kafin tayi hakan ya tsinke, kamar ance ta ɗago kai idanuwanta suka sauka akan Umar Farouk da Jiddah ke nuna wa hoton data ɗauke su shi kuma ya duƙo ta fuskarta sosai kasancewar ba tada tsayi yana kallon hoton ta cikin wayarta, wanda idan ba mutum ya kalla sosai ba zai iya ɗauka kissing ɗinta ne Umar Farouk ke yi, "Innalillahi wainna ilaihirrajiun". Na faɗa ganin abinda idanuwana suka gano mani, na yi sauri juyawa na bar wajen ina mai sake jin tsanarsa a cikin zuciyata, a raina cewa nake wato shi duk inda ya je sai ya bayyana munanan halayensa, a cikin gari ma ba a makaranta ba bazai iya rayuwa ba sai da yan mata atare dashi, sai ya nuna wa mutane shi ba ƙaramin tantagaryar ɗan iska bane, Na ja tsaki karo na ba adadi ina mai dana sanin fitowa ta daga wajen tare da Allah waddaran hali irin nasa sannan na kashe wayar gabaɗaya na jefa a cikin jaka.
A nan waje kuwa Jiddah ƙin tafiya tayi bayan ta gama daukar hoto da Umar Farouk sai ma jansa da fira da ta shiga yi duk da yadda yake basar da ita yana cigaba da kiran lambar Amaah ba tare daya ji haushin rashin ɗagawar da bata yi ba, daga karshe ma sai ji yai ankashe wayar gaba-daya, wani irin haushin kansa ya ji yan mai ɗora laifin akansa, ya rasa me ya sashi kiranta tunda ba wata alaƙa bace tsakaninsa da ita, ɗan tsaki ya ja haɗe da kallon Jiddah ya ce, "Ya kamata ki tafi wajen abinda ya kawo ki kin san dai halin Aunty ba daɗi ne da ita ba idan bata hangoki awajen bukin nan ba, nima yanzu nan tafiya zan yi idan bai fito ba". Ya kare zancen yana jefa wayar a cikin aljihu, Jiddah ta kallesa ɗauke da murmushi akan fuskarta tace. "Shikennan Ya Umar agaida su Momy ". Sannan ta bar wajen ta nufi wajen da ake bukin, ba'a jima ba sai ga Saleem ya fito ya samesa a cikin mota zaune, magiya ya shiga yimasa akan ya fito su shiga ciki ko abinci su ci amma fir Umar Farouk ya ce bazai shiga ba, daga karshe sai ma cemasa da yai tafiya zai yi idan ba yanzu zasu gama ba don akwai inda zai je, ya fadi hakan ne don ya gaji da zama wajen ga wani bacin rai dake taso masa na rashin ɗaga wayarsa da Amaah bata yi ba, wanda yake kallon hakan tamkar zubewar ƙimar sa a wajen ta, ba don Saleem ya so ba ya ce ba damuwa yaje zai bi motar ɗaya daga cikin abokan ango ya koma gida.
*******
Sai kusan ƙarfe takwas na dare na koma gida a gajiye, a can na haɗu da Saleem bayan an gama bukin inda motarsu ce ta kawo ni gida shi da abokinsa don na kira Ya Jameel ya a ce bazai samu damar zuwa ɗaukata ba saboda ya yi ɓaki a shago dake son kaya, daga can kuma akwai inda zai je saboda haka ya ce nayi ƙoƙari na koma gida akan lokaci, hakan ne yasa har na amince na shigo motar tasu musamman da naga Saleem aciki, wanda bayan mun gaisa da shi yake sanar dani ai tare suke da Umar Farouk wani uzuri yasa ya tafi da mun haɗu, cikin raina nace ba wani uzuri ya dai gama shashancinsa da yan mata shine yayi tafiyarsa, na gode Allah da bamu haɗu ɗin ba don bana son abinda zai sa aganni tare dashi, a zahiri kuwa cewa kaɗai nayi Allah ya kyauta saboda bana son muja firar da tsawo, wanka na fara yi kafin nayi sallolin dake kaina sannan na jawo wayata, lambar da akayi ta kirana da ita ɗazu na kamo na kira, sai data kusa katsewa sannan na ji an ɗaga amma ba'a yi magana ba, sallama na fara yi kafin nace, "Hello..hello". Ba'a amsa ba duk da ina jin alamar an ɗauka, sai nayi tsammanin ko matsalar network ne don haka na katse kiran na sake kira a karo na biyu, nan ma an ɗauka amma kuma ba'a yi magana ba har kusan second hamsin don haka sai na katse kiran gaba-daya na aje wayar. Mikewa nayi na saka kayan bacci na na shafe jikina da turaren kamfanin suratti, fitowa nayi na nufi ɗakin Mamah na sameta zaune tana karatun Alkur'ani, sai da na bari ta kammala sannan na karbi alkur'anin na ajiyesa a mazaunin sa ina faɗin, "Mamah ina wuni, barka da dare". "Barka Janaam kin dawo?" "Eh Mamah ai tun ɗazu". Daga haka ta miƙe ta ciro zuma mai kyau acikin roba ta miƙo mani tana cewa, "karɓa akwai magani na nan na ɗora a wuta ki zuba mini cokali uku aciki?" Na amsa da "To Mamah maganin meye halan?" Ta ce, "Jeki kiyi abinda na saka ki zan faɗa maki ko na meye daga baya". Na karɓa na fice daga ɗakin na nufi kitchen na bude tukunyar da naga wasu ganyayyaki da itace aciki na zuba mata zumar kamar yadda tace ina yamutsa fuska don ƙamshin maganin dake tashi bai mun ba, saboda in dai aka ce wannan maganin Hausa ne da za'a dafa asha to fa sam bana shiri dashi, shi yasa ina gama zubawa na rufe na ɗauki plate na bude warmer na debi abinci na wuce ɗaki abina, ina ci ina chart da Nu'aymah da har na so na bata labarin abinda idanuwa na suka gani ɗazu akan wanda take kira masoyi sai kuma na fasa don kada taji haushi na, in fact ma baza ta yarda ba ko na faɗa mata tunani zata yi sharri nayi masa ko ƙage, sai kawai na ci gaba da bata labarin yadda bukin ya kasance da kuma yadda ya