Showing 93001 words to 96000 words out of 157423 words
ɗaga ina cewa, "Pls Aunty do something don Allah ki rani dashi, ki faɗa masa ya rabu dani bana son sa". "Ki natsu Janaam ki faɗa mini abinda ke faruwa ni wallahi duk kun daga mini hankali, shi ya kirani yana haukan idan baki ɗaga kiransa ba zai isko ki har gida koma me zai faru ya faru, ke kuma na kiraki kina kuka, me yake faruwa ne?" Sai dana share kwalla sannan na ce, "Yanzu Aunty Nidrah har tambaya ta abinda ke faruwa kike yi bayan kin san abinda ya aikata jiya? Shin ana soyayya dole ne da zai ce banda ikon tsayawa da kowa ne namiji Saboda gashi ubana". "Subhanallahi me kike nufi Janaam, kar dai ace yaron da aka tsinta an yiwa duka jiya aikin Umar Farouk ne?" "Shine mana saboda ɗai ya ganni tsaye tare dashi muna magana shine ya sa akai masa haka, Aunty Nidrah idan ba shi ba to waye zai aikata hakan?" "Ya Salam! Indai haka ne bai kyauta ba, kiyi hakuri zanyi maga dashi amma don Allah kidena wannan kukan haka kin ji ko?" "Toh". Na faɗa tamkar ƙaramar yarinya ina kashe wayar.
A nan falo kuwa ko dana wanko fuskata na fito na nufi kitchen, ina ji su Mamah na sake maimaita zancen Mamah na cewa, "Ai yaron ya yi hankali daya ce ya yafe abar zancen, ba don haka ba da babu wanda yasan inda wannan tashin hankali da fitinar zai tsaya tunda ba'a san ko waye ba". Ban iya cewa komai ba sai hango fuskar saurayin nan nakeyi da murmushinsa a fuska lokacin da yake faɗa mini so na yake yi kuma da aure ba da wasa ba, tausayinsa ne ya kamani na ji ina ma ace bai tsaya dani ba da duk hakan bata faru dashi ba. Addu'ar samun lafiya nayi masa da Ubangiji ya bi masa hakkinsa don an zalunce sa ba kaɗan ba, Allah kaɗai yasan ko wace irin barazana Umar Farouk ke yi masu da suke cewa sun yafe bayan akwai yadda za'a yi a bi masu haƙƙinsu, haka akabar zancensa shima kamar dai na Ya Salis ba'a sake tadasa ba ya wuce.
Tsakanina da Umar Farouk kuwa wata tsanar sa ce ta sake mamaye mini zuciya naji ko ganinsa bana son yi, ranar Monday muna komawa school muka fara jarabawa, nakan riga shi shiga school sannan kuma nakan yi kokari naga na riga shi gamawa yadda ina fitowa zan wuce gida abina ba tare da mun haɗu ba, duk lambobin wayarsa da na san yana kirana dasu na goge nayi blocking ɗin su, gidan ya Jameel ko da wasa ban taɓa attempting zuwa ba tun bayan bukin kasancewar Aunty Nidrah yar uwarsa ce, hanyar duk da zata hada mu dashi na toshe ta don shafawa kaina lafiya, a ɓangaren Nu'aymah kamar yadda nake gujewa haduwata da Umar Farouk haka itama take guje wa haɗuwarta da ni, ina jin ba daɗi yadda ni da ita muka koma tamkar wasu makiya da basu taɓa son juna ba ko zama waje ɗaya, sosai Saleem ya yi ƙoƙarin sasantawa tsakanin ni da ita amma Nu'aymah taƙi saurarar sa, hakan yasa na hakura Nima na zuba mata idanuwa don ya Nu'aym ma da na kaiwa ƙorafin shariyar da take yimin cewa yai ya mata magana tace ba komai kawai zuwan abu ne, ranar da muka gama exam ko wa na murna amma fuskata cikin kunci da rashin walwala take saboda abokiyar da zamu taya junan mu murna an riga an shiga tsakanina da ita, bayan mun zana jarabawar karshe ina tsaye ni da Saleem yana bani hakuri akan yadda abubuwa suka faru tare da taya ni murnar ƙarewar mu na ce masa ba komai tare da yi masa godiya, muna nan tsaye sai ga Umar Farouk shima fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa, a take na haɗe rai ina kauda kaina gefe, wani kallo yai wa Saleem mai cike da tuhuma shima Saleem ya mayar masa kalarsa yana cewa, "Kai ka san Janaam classmate ɗina ce baka isa ka hanani tsayuwa da ita nai magana ba wallahi don ni ba.." bai ƙarasa ba kawai na ji Umar Farouk ya ja hannuna yabar wajen dani, turjewa na shiga yi ina neman kwace kaina amma na kasa don riƙo ne ya yi mini ba na wasa ba, hawaye ne suka shiga gangarowa a fuskanta ganin yadda mutane suke kallon mu amma na rasa mai taimako na, dai-dai lokacin kuma muka Nu'aymah ta fito daga hall ɗin da muka gama exam na shiga kiran sunanta amma tayi kamar bata gane mu ba tayi tafiyarta, haka na bita da idanuwa cike da mamaki har ta ɓacewa ganina don na tabbata itama yasan bana son Umar Farouk, haka ya ci gaba da jan hannuna ina turjewa haɗe da dukan masa hannu ya cika ni amma ko a jikinsa, bai tsaya ko ina dani ba sai bakin motar sa yana zuwa ya buɗe ya sani a ciki ya rufe, kafin na tattaro ƙarfina na yunƙura na fito har ya danna ma kofar key na shiga bubbuga wa ina ya buɗe mini ko nayi masa abinda bai taɓa tunani ba amma yayi banza dani, sai ma zagayo wa da yai ya buɗe gefen driver ya shigo ya tada motar ya fizgeta da ƙarfi yabar makarantar aguje, kaina na haɗe da cinyoyina ina rera wani irin kuka, cikin tsawa Umar Farouk ya ce, "idan baki dena wannan kukan ba narantse zan saki steering motar nan duk mu mutu kowa ma ya huta". Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka na riƙe kuka na jin abinda ya faɗa, a yanzu na gama tabbatar da cewa Umar Farouk bai da hankali tunda har yake tunanin kashe mu, sai da muka yi tafiya mai nisa muka fito cikin gari sannan Umar Farouk ya nemi guri gefen titi ya yi parking, yana fitowa nima na buɗe motar na fito raina a ɓace, ina zuwa na daukesa mari, kafin yace wani abun na sake daukesa mari ta ɗaya bangaren ina kuka tare da ci gaba da kai masa duka sannan na zube ƙasa akan guiwoyina a gabansa na haɗe hannayena waje ɗaya ina cewa "Don Allah ka ƙyaleni bana son ka na tsane ka ka mai sheni inda ka ɗauko ni". Umar Farouk da fuskarsa tayi wani ja idanuwansa suka kaɗa tamkar an watsa masa barkono aciki, lokaci ɗaya siffarsa ta can ja tamkar ba shi ba ya naushi iska da karfi tare da juyowa yana kallona ya ce, "Me nai miki haka da kika tsaneni Janaam? Menene nai da bakya so na? Meye laifina da zaki kasa karɓar soyayyata? Kin san me nake ji a zuciya ta akanki kuwa? Kin san ya nake ji aduk lokacin da kika ce kin tsaneni?" Yai maganar cikin ƙaraji tamkar zai rufe Ni da duka. kasa amsa masa nayi sai ci gaba da rera kukana nake yi durƙushe a gabansa, juyawa yai yana dafe goshinsa yana ji tamkar ya fashe da kukan shima saboda yadda yake jin raɗaɗin kukan da take yi acikin zuciyarsa, amma yasan yin hakan ba ƙaramin zubewar jarumtaka da kimarsa bace a matsayinsa na ɗa namiji, Controlling kansa ya shiga yi kafin ya juyo cikin tausasa murya kamar ba shi ba yace, "pls Janaam kiyi hakuri ki yafe mini ki karɓi soyayyata, ji nake yi zan iya mutuwa idan har na rasa ki don Allah ki tausaya mini Amaahh..". Kasa amsa mishi nai saboda yadda kuka ya ci karfina sai dai na girgiza masa kai tabbacin ba zan iya ba, idanuwansa ne suka sake kaɗawa ya daga kansa sama yana ƙoƙarin shanye abinda yake ji acikin zuciyarsa, ƙasa ya zauna a gabana ya lankwasa ƙafafuwansa tamkar mai shirin ɗaukar karatu yana kallona ya ci gaba da cewa, "Fadamun me ye bakya so Janaam? Me yasa kike jin tsanata har hakan ki faɗa mun i promise you daga yau zan dena in har zaki so ni ki bani dama to duka zan watsar da dabi'una da duk wasu halayena da baya so na canja zuwa yadda kike so". Nan ma shiru nai masa bance komai ba sai sauke ajiyar zuciya nake yi, Allah ya sani ba halayensa da dabi'unsa kadai ba shi kansa bana son sa kwata-kwata bai yimin ba, amma taya zan iya fadar hakan daga ni sai shi akan hanya sai ɗaidai kun motoci dake wucewa a guje?, cikin muryar dana sha kuka na ƙoshi na ce "Ni kawai ka ƙyaleni bana.." kasa ƙarasawa nai ganin yadda yai wata irin miƙewa na ɗauka ma kashe ni zai yi numfashina na kokarin daukewa. "Ya isa haka Janaam, kiyi shiru ba sai kin karasa ba bana son ji, a yanzu na fahimci ke, bakya so na ni kuma ina son ki, baza ki iya yafe mun ba ni kuma bazan iya barin ki ba, kin tsaneni ni kuma ina son rayuwa a tare dake! Sai ki faɗa mun ya kike so ayi? Ni dai bazan iya haƙura da nawa ra'ayin ba amma ban sani ba ko ke zaki hakura da naki, idan ma baza ki hakura ba to ki sani zan ci gaba da bibiyar ki sannan zan bayyana kaina a gidanku a matsayin wanda ke sonki ko kina so ko bakya so, na sani kin gama cika burin ki tunda kin kammala karatunki don haka ni ma zan bawa kai na dama kamar yadda zaki bawa wasu damar zuwa su je su nemi aurenki Nima nake na nemi auren naki na cika nawa burin ko kina so ko bakya so". Yana kaiwa nan ya buɗe motar ya shiga ya tayar, sanin idan ma naki shiga motar zai iya yimun ta karfi kamar yadda yai mun ɗazu yasa na miƙe a mutunce na shiga motar ba tare dana kalli inda yake ba, ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya tayar da motar yabar wajen, har kofar gida ya kai ni ya ajiye a raina ina mamakin yadda akayi ya san gidanmu, ko kallonsa ban yi ba na buɗe motar na fito jikina a mace ina jin sabon bakon abu na tashin hankali a duniyata, ina fara tafiya na ji ya kira sunana, "Amaahh". Kamar bazan tsaya ba amma sai na ji na kasa ɗaga kafata ko da da taku ɗaya ne, ban juyo ba shi kuma hakan bai hana shi faɗar abinda yake son faɗa ba, "Ina sanki, ina matukar kaunar ki kuma ki ajiye hakan a ranki cewa bazan iya daina son ki ba har ƙarshen numfashi na". Tun daya fara faɗar hakan na runtsu idanuwana ina jin saukar kowace kalma tasa a cikin zuciyata tamkar ana zuba mini narkakkiyar dalma tsabar yadda nake jin zafi da yadda take ƙona mini zuciya har ya gama ya ja motarsa ya tafi, na fi mintina uku a haka kafin na iya daga ƙafafuwana na shiga cikin gida cike da rashin ƙwarin guiwa..
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
Masu son Vip ku bibiyi Arewabook@billysfari ta wannan link https://www.arewabooks.com/chapter?id=689b69e619700231f1502019
53.
Umar Farouk kuwa ashe wasu daga cikin ɗalibbai sun je sun sanar da student affairs halin da ake ciki lokacin daya dauki Janaam ya fita da ita, a take aka shiga kiran wayarta daga ita har shi aji inda suke amma dukkansu basu ɗaga ba a lokacine suka yi parking suka fita cikin motar, hakan yasa student affairs nan take yakai report zuwa ofishin shugaban makaranta, ba tare da ɓata lokaci ba aka kira mahaifinsa aka sanar dashi abinda ke faruwa, lokacin yana tsaka da aiki kuma ba damar ya katse, dole yai hakuri ya turawa mahaifiyarsa kawai sako, Momy na ganin sakon ta yi tsuki haɗe da cewa, "Ai indai zaka biyewa ta mutanene baza ka taɓa zama lafiya da yaron ka ba, sun san me yarinyar tayi masa ne ko sun san tsakaninsa da ita, wannan ai gulmar ce da munafurci". Ta ƙare zancen cike da masifa tana faɗa, wayar Umar Farouk takira bai daga ba har sau biyu sai kawai ta kira Saleem , yana ɗagawa ta ce, "Saleem meke faruwa a school?" Sai daya gaisheta jin bata amsa ba sannan ya ce "Umar Farouk ne ya ɗauki.." tayi saurin dakatar dashi tana cewa, "Kafin wannan nake tambayarka, zai dauki yarinya ne ba tare da tayi masa wani laifi ba? Wai me yasa mutane basa neman zaman lafiya Saleem? Mtsss". Ta kashe wayar ta cike da ɓacin rai ba tare data tsaya taji ko meye ya jawo wanna samuwar ba, Mamaki ne ya kashe Saleem ya kasa cewa komai don bai taɓa ganin uwa kamar Mommy ba, son kanta yai yawa har ya kai bata taɓa iya hango laifin ɗanta sai na ya'yan wasu.
Rai a ɓace Dady ya dawo gida yana shigowa motar Umar Farouk na shigowa, tsaye yai har sai daya fito yana kallon sa, al'amarinsa yanzu tsoro yake basa case biyu kenan wannan ne na uku da aka kawo masa kwanaki na ya daki ya'yan mutane akan mace, ganin zai wucewa ya sashi cewa "Zo nan Umar Farouk". Ya maganar yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa, Umar farouk ya karaso wajen yana yi ma Dadyn kallo ɗaya, canjin da ya gani a tattare dashi ya tabbatar masa da cewa har an kawo ƙarar sa kenan kuma sai ya sha faɗa wajensa, a mamakinsa sai ji yai Dady ya ce, "ina yarinyar mutane?" "Na mayar da ita gidan su". "Me kayi mata?" Umar Farouk ya ɗago kai ya kallesa cikin rashin fahimta, idanuwan Dady na akansa ya sake cewa, "answer me, me kaiwa yarinyar mutane?" "Ban yi mata komai ba". "Menene alakarka da ita? Ban faɗa maka idan aure kake so ba ka samo yarinyar da zaka aura nayi maka ba? Wato ka fi so kaje kayi ta zubar mini da mutunci a gari kana ɓata mini suna ko? Shikennan na gode Allah ya shiryeka amma na baka wata ɗaya idan har son yarinyar nan kake yi kaje ku daidaita kanku in tana son ka kazo ka faɗa mani na tura a nemo maka aurenta, idan ba haka ba ka kuskura na sake jin wani case ya taso a kanka zan nuna maka ɓacin raina matuƙa, na gaji da matsaltsalunka Umar Farouk, na kai lokacin da nake bukatar na huta ka zamo mini ma taimaki madubin yan uwanka dake da rauni amma sai shashanci kake faman yi a gari kana jawo mini abun faɗi kullum tare da kara mini damuwa, kai ne ka daki wancan ka wulakanta wancan kasa a daki wancan wannan wace kalar rayuwa ce kake yi haka? zan matukar yin farin ciki dakai idan ka sauya wannan bahaguwar rayuwar taka idan kuma kaƙi to zan fidda hannuna a lamarin ka gaba-daya kaji na faɗa maka". Dady na kaiwa nan ya bar wajen ba tare daya sake ƙara kalma ko ɗaya ba, jikin Umar farouk.ne yai sanyi karo na farko ya ji cewa tabbas Dady yana da bukatarsa kamar yadda yake da bukatar Janaam kafin ya iya zama yadda Dady ke bukatarsa, don haka zai yi yaki a soyayyarsa matuka don ya tabbatar daya cikawa Dady burinsa bayan ya mallaki wacce yake so ya cika nashi burin shima.
(Akwai matsala har yanzu a kwakwalwarka Umar Farouk gaskiya, wato sai ka cika burin ka sannan zaka cika na mahaifinka, let see Umar Farouk ko zaka yi nasara🏃)
Bayan kwana biyu anata shirye-shiryen bukin karewarmu amma ya Nu'aym shiru ban ji ya ce mun zai zo ba, daga karshe ma na neme sa a waya na rasa don tun sakon tayani murnar daya turo mini ranar da muka kare school da daddare bamu sake yin waya ba kuma bai koma turo mini da wani sakon ba da zai tabbatar min da zuwansa ban sani ba ko bazata yake son yimin amma dai ni bana buƙatar hakan, babbar damuwata yanzu ita ce idan na kira wayarsa bana samun sa sai ace mini a kashe take, tun ina jurewa har hankalina ya soma tashi, yau aunty Nidrah tazo ita da Ya Jameel gaishe da Mamah muna zaune a palour sai ga mai gadi ya yi sallama wai Janaam tazo ana yimata sallama tayi baƙo, kallona ya Jameel yai haɗe da cewa, "Baƙo kuma? Kar dai nace har kin fara tara samari daga gama school ɗin jiya-jiya?" "To me take jira zaunawa zata yi mu jiƙata mu sha ko muyita kallonta? Kai dai ba ta gama makarantar ba kamar yadda kake so yanzu ai sai abata dama ta saurare su, ko akwai wanda ka tanadar mata ne?". Mamah ta karɓe zancen cikin fushi tana tambayarsa, dariya Ya Jameel yai haɗe da cewa, "Allah ya baki hakuri Mamah, ni ba wanda na tanadar mata kawai dai don ta samu ta maida hankali ga karatun ta ne yasa nayi hakan, idan ma har akwai wanda ya taɓa yimun zancen yana sonta to Anish ne abokina, na kuma sheda masa ya jira har sai ta ƙare karatu sai ya tuntuɓeta, idan ta amince shikenan idan kuma bata amince ba yai hakuri don bazan wa ƙanwata auren dole ba, kawai dai mamaki abun ya bani yau fa gama karatun nata kwana biyu kacal". Dariya Mamah ta yi haɗe da cewa, "Yawwa dama ai kai ka tsaida su, ki tashi ki je kar kibar mutum na jira". "A'a Mamah bari nafara zuwa kinga dare ne". Ya Jameel ya faɗa haɗe da miƙewa ya fice, Ni kuwa gaba-daya ma hankalina baya jikina don ina can ina tunanin ko lafiya ya Nu'aym yake na dena jinsa, ba'a jima ba Ya Jameel ya dawo murmushi ɗauke akan fuskarsa, kallonsa Mamah ta yi ta ce,