Showing 72001 words to 75000 words out of 157423 words
awon gaba dani.
Washe gari kasa shiga school nayi saboda fargaba, gabadaya na ji duniyar bata yimin daɗi ko Ya Nu'aym da muka yi waya haka ya yi ta tambayata meke damuna amma nakasar sanar dashi saboda gudun abunda zai iya faruwa, na san halinsa yana da wani irin fitinannen kishin da bazai tsaya ya fahimci abun da ya faru ba kawai zai yi focusing ne wajen son jin dalilin bibiyar da Umar Farouk ke yi mini a baya har hakan ta faru, ni kuma bana buƙatar hakan a yanzu kawai buri na ya tashi kar ya mutu a sanadiya ta, WatsApp ɗina na sake shiga ko zan samu wani labari akan lafiyarsa, sai gashi a group an turo hotonsa an ɗaure masa kai da bandage, haka ma hannunsa da alama ya ji ciwo don an naɗe masa shi an saƙalo zaren ta wuyan sa, ƙafarsa ma naɗe take da bandage daga wajen guiwa, kwance yake akan gadon asibitin ko motsi baya yi da alama yana jin jiki sosai don har vedio Salim ya turo kowa yana fadar Allah ya bashi lafi, ni kuwa da kyar na iya daurewa na rubuta Allah yaba Musulmi marasa lafiya lafiya gaba-daya.
********
Umar farouk ko da aka ɗaukesa wata private hospital dake kusa aka nufa dashi, student ɗin daya kaisu da mota shi ya kira Saleem ya sanar dashi abinda ke faruwa don yau bai zo school ba saboda wani kasuwanci da mahaifinsa ya turasa, da sauri Saleem suna gama waya ya kira Momy ya sanar da ita halin da ake ciki tun da shi baya gida, hankalinta a tashe tana kuka ta kira Dady ta sanar dashi abinda ke faruwa, sanin irin soyayyar da take yi ma yaron nata yasa ya shiga bata baki yadda ya jita a ruɗe yana tabbatar mata da yanzu zai kira Saleem ɗin ya tambayesa a wace asibitin aka kai Umar Farouk ɗin, kafin ya rufe baki Momy ta sanar dashi a asibitin da yake don Saleem duka ya faɗa mata, Dady ya ce "shikennan ki kwantar da hankalin ki yanzu can zan je mu haɗu acan". Da to ta amsa masa kafin ta kashe wayar ta zaro mayafinta da key ɗin mota ta fito tana kwalawa mai gadi kira ya buɗe mata, a guje ta fizgi motar ta fice daga gidan, sarautar Allah kadai ta kaita asibitin lafiya da ita ma wani abun ya sameta, ganin yanayin da yaronta ke ciki bayan ta shiga asibitin wajen da aka kwantar dashi shi ya hanata yin masifa ko yin faɗa da kowa a lokacin ta kama bakinta ta yi shiru, amma ranta cewa take daga wanda ya kaɗe mata yaro har zuwa wanda yai sanadiyar faruwar hakan baza ta taɓa ƙyalesu ba, bata jima da shigowa ba Dady ya shigo, "Alhamdulillah, alhamdulillah da sauki abun ashe". Ya faɗa yana kallon Umar Farouk ɗin da har lokacin bacci yake yi, Mommy ta ɗago kai idanuwanta cike da kwalla ta ce, "Sauƙi Alhaji? A wannan yanayi da nake kallon ɗana a ciki zaka ce da sauki? Kasan raɗaɗin da yake ji acikin jikinsa na wuɗannan raunin dake tare dashi kuwa? Hmmm walh bazan bar ko wanene ya yi masa hakan ba". "Ikon Allah! Yanzu ke baki ga sauƙi a lamarin nan ba Maryama? da Allah yasa ya mutu gaba-daya ya zakiyi kenan?" Saurin rintse ido ta yi haɗe da cewa, "Auzubillahi minasshaiɗanirrajim, Dady wane irin zance ne kake yi wannan fisabilillahi? Ni dai kawai kaje idan baza ka faɗi alkhairi ba akan ɗana, in sha Allah kuma ɗaukesa zanyi na maida shi asibitin da za'a bashi kulawar da tafi ta wannan asibitin". buɗe da baki ya bita yana kallon kafin yace, "Kar ki yadda ki aikata wannan kuskuren, abune ya riga daya faru kuma anyi kokarin kawo sa asibiti mai kyau yana samun kulawa, in sha Allah kuma zai samu lafiya don haka da izinina da kuma yawun bakina ban yadda ki ɗaukesa daga wannan asibitin ba ki kai shi wata asibitin idan ba so kike na saɓa miki ba". Yana gama fadar hakan ya fice daga asibitin yana sake jinjina irin so da ƙaunar da Momy ke yiwa Umar Farouk sai kace shi kaɗai ne ta haifa...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
Masu son vip ku bibiyi Arewabook @billysfari I just published "056" of my story "IDO A DUHU"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68926e51a9466b1b79a0206f.
41.
Bayan Dady yabar asibitin da kusan awa uku sai ga Saleem ya shigo ya samu Momy ranta a ɓace saboda gargaɗi da jan kunnen da Dady ya yi mata, har ga Allah ita wannan asibitin bata yi mata ba dan son samunta ne takai ɗanta asibitin da za'a iya kula mata dashi fiye da haka, sai dai babu yadda ta iya tunda mahaifinsa ya riga ya yanke hukuncin barin sa anan ɗin sai dai ba haka taso ba, gaisheta Saleem yai cikin girmamawa kafin ya shiga duba lafiyar abokin nasa, "Allah ya sawaƙe ya baka lafiya". Saleem ya faɗa tare da komawa gefe ya tsaya, kallonsa Momy ta yi ta ce, "Saleem wai ya aka yi har hakan ta faru dashi? Ina motarsa ne?" "Ban san komai ba sama da abinda na faɗa maku Momy saboda yau ban shiga school ba". "Shikennan ka binciko mini yadda akayi hakan ta faru saboda bazai yiwu ace yana da matorsa ba ace ya haɗu da hatsari a tsakiyar titi mota ta bugesa ba da motar tasa ba, idan ma wani abun zai faru kamata yai ace accident ne yayi a motarsa ba wai mota ta kadesa a saman titi ba, saboda haka kayi duk yadda za kayi ka gano mini gaskiyar zancen nan don ko waye ya kaɗesa bazan ƙyalesa ba". "To momy za'a yi hakan in Sha Allah". Saleem ya faɗa a takaice don ya yi mata yadda take so amma shi ya san babu ta inda zai iya samo wanda ya kaɗe Umar Farouk ɗin yanzu tunda wudanda suka kawosa sun ce mutumen bai tsaya ba, motsin da Umar Farouk ya fara yi da hannu kafin a hankali ya shiga buɗe idanuwansa yana bin dakin da kallo har ya sauke su akan Saleem shiga dawo da hankalinsa agaresa, yunkurawa yai da niyar zai tashi ya saki wata irin ƙara saboda zafi da zugin da kariyar dake hannunsa da gurɗewar daya samu a ƙafa ke yi masa a lokaci ɗaya yasa Saleem yai saurin riƙasa ya koma ya kwanta yana sauke numfashi da ƙyar, hannun da ya ji a saman kansa ana shafa sumarsa a hankali haɗe da yi masa sannu ta gefensa ya sashi ɗago kai yana sauke idanuwansa akan Momy da idanuwanta suka cika da ƙwalla, ji takeyi tamkar ta cire ciwon dake jikin yaron nata ta maidosa a jikinta saboda ganin yanayin da yake ciki, Umar Farouk ya ɗan shagwaɓe fuska tare da lumshe mata idanuwansa ya buɗe su yana girgiza mata kai alamun kada tayi kukan daya ga tana ƙoƙarin yi, ya ƙaƙaro murmushi da kyar don kwantar mata da hankali yana ɗora hannunsa ɗaya mai lafiya akan hannunta ya ce, "Kar ki damu Momy i will be fine". Hawayen da take ƙoƙarin riƙewa ne suka sauko mata a fuska ta rumƙe hannunsa cike da tausayi irin na uwa da ɗa tana cewa, "Ina fatar hakan yarona amma ya kake ji yanzu?" "Da sauki". Ya faɗa duk da shi kaɗai yasan me yake ji cikin jikinsa, "Zaka iya na taimaka maka ka tashi ka samu ko wani abun ne kaci kafin akawo abinci?" Momy ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga sa don yadda ta ruɗe bata tsaya ɗauko komai ba banda mayafinta ta yo asibiti, sanin hakan kaɗai zai yi ya kwantar mata da hankali ya sa ya ƙarfafa kansa da taimakon ta ya tashi zaune ta saka mishi pillow a bayansa ya ɗan jingina yanda zai ji daɗin zaman, ledar da Saleem ya shigo da ita ta janyo, fruit ne aciki sai lemun kwali guda biyu, kankana ta fara bashi ya ci kuma ba laifi ya ɗan sha kaɗan kafin ta ɓara masa ayaba ta kai masa a baki, guda ɗaya ya iya ci ya ce ta ishesa, Momy ta ɗauko kwalin lemon yai saurin kauda kai yana cewa, "Momy is okay duk ina zan kai su". Ta san halinsa don haka sai kawai ta maida kwalin lemun ta ajiye, sallama akayi tare da shigowa Mommy ta ɗago kai tana amsawa haɗe da kallon ƙofa, Nu'aymah ce tare da sister ɗinta Nihla a bayanta ɗauke da basket, tun da taga a group ɗin school abinda ya faru dashi ta ji hankalin ta ya kasa kwanciya gabaɗaya har sai ta zo ta dubasa, ta so kiran Janaam ko za su taho tare amma sanin halin ta da kuma yadda take ji a kanta yanzu yasa ta fasa kawai ta ɗauko Nihla suka taho tare da lafiyayyen abincin data shirya masa da kanta, bata sani ba hakan da tayi dai-dai ne ko akasin hakan ita dai kawai tayi ne don tasan mafi aksari hakan al'ada ne idan za'a tafi duba marasa lafiya akan je da kayan dubiya ko kuma abinci, wannan dalilin yasa da taimakon masu aiki ta shirya abincin da zata zo dashi wajen duba sa, cikin girmamawa Nu'aymah ta gaida Momy tana tambayar ta mai jiki duk da bata san matsayinta a wajensa ba, amma ganinta awajen da yadda suke satar kamanni da Umar Farouk ɗin ya tabbatar mata da ko waye ita matsayinta mai girma ne a gunsa, fuska a sake Momy ta amsa tana yi masu sannu itama Nihla ta gaishesu tare da tambayar ya mai jiki kamar yadda yayar tata tayi, Saleem ne ya zagayo ta gefen su yana faɗin, "Barka da zuwa Nu'aymah" "Yawwa Barka Saleem ya mai jiki?" Kallon Umar Farouk yai daya tsurawa kofar da suka shigo idanuwa cike da sa ran ganin masoyiyar tasa daya san duk inda Nu'aymah zata je suna tare wani lokacin, "Mai jiki da sauki alhamdulillah". Saleem ya bata amsa tare da ficewa don bai shirya ganin yadda Umar zai watsa mata ƙasa a fuska ba idan har yai mata zancen Janaam, da kallo ya bi Saleem har ya fice kafin ya maido hankalinsa ga Nu'aymah dake gaishe sa haɗe da yi masa ya jiki? Sai daya ɗan saki fuska sannan ya ce, "Jiki alhamdulillah Aymah ke kadai kika zo?" Duk da Aymah ta fahimci me yake nufi sai kawai ta saki murmushin yaƙe tana yi kamar bata san inda maganar tasa ta nufa ba tana cewa, "No tare muke da sister ta Nihla baka santa ba ko?" "Good". Ya faɗa kawai tare da kallon Momy ya ce, "Momy wannan ita ce Nu'aymah, abokiyar karatuna kuma class ɗin mu ɗaya muna shiri da ita sosai, Nu'aymah meet my super hero, my Mom". Ya kare zancen yana nunawa Nu'aymah Momy da daɗi ya kamata na yadda yaronta ya muhimmantata tare da girmamata, ɗan sake russunawa Nu'aymah tayi da ladabin da yafi na ɗazu ta ce, "Sannu Momy Allah yaƙara tsawon rai". Da murmushi akan fuskar Momy ta amsa da amin tana jin yarinyar ta shiga zuciyarta sosai musamman yadda taga tun shigowarta ta bata girma da kuma yanayin natsuwarta, waje Momy ta nuna masu tana cewa su zauna ba musu Nu'aymah duk da tayi niyar tafiya sai ta tsinci kanta da son zaunawa kamar yadda ta ce, a hankali Momy ke ɗan janta da fira saboda tana so tasan ko ita ɗin yar gidan waye da kuma alakarta da yaronta da har yake faɗa suna shiri da ita da kansa, ganin hakan yasa Umar Farouk gyara kwanciyarsa a hankali ya maida idanuwansa ya rufe, a zahiri idan ka kallesa zaka ɗauka bacci yake yi amma idon sa biyu kawai ya faɗa duniyar tunanin Janaam ne da yake sa ran ita ce ta farko wajen zuwa dubasa sai ga shi ya ga akasarin hakan.
Nu'aymah kuwa har aka kira sallar isha'i bata wuce ba sai kusan ƙarfe takwas da rabi na dare, lokacin ne bayan ta koma ta hau online har take yiwa Janaam tambayoyin data yi mata saboda ta gano ko Janaam ɗin tafara jin wani abu akan Umar Farouk ɗin sai dai bata iya fahimtar duka kalaman data bata amsa ba shi yasa ta amsa mata da hmmm kawai itama.
Washe gari kuma data shiga school ita Janaam bata shiga ba, bayan an tashi ta sake komawa ta dubo Umar Farouk dake ci gaba da samun lafiya a hankali sannan ta wuce gida.
Ni kuwa ban koma school ba sai bayan kwana uku da faruwar abun, ko dana shiga ba wanda na yiwa zancen rashin lafiyar Umar Farouk haka kuma babu wanda ya tunkare ni da zancen don ba'a ga fuskar yin hakan ba, Nu'aymah ma ƙinzil bata ce dani ba akan maganar har muka gama lecture muka tashi, na so yau ta wuce dani gida ta ajiye ni saboda tsoron abinda ya faru ta sanadi na daya shiga jikina sosai, wanda hakan yasa tsayawa taron abun hawan duk ya fitar mini akai, sai gashi kumakafin nayi mata maganar naga kawai ta yi mini sallama tana cewa zata tafi, ban iya tsayar da ita ba alokacin tunda dama nasan tunda muka bar tafiya tare da an tashi kowa kama gabansa yake yi, ina wannan tunanin naga Nu'aymah ta tsaya ta ɗauki su Billy da Felicia a motarta, kau da kaina gefe na yi na soma tafiya cike da mamaki don ban taɓa ganin ko da wasa ta ragewa ɗayar su hanya ba, ji nai anyi horn ta bayana nayi saurin juyowa tare da komawa gefe, Nu'aymah ce tana kawowa wajena ta sauke glass ɗin gefenta tana cewa, "Besty zamu je dubiya ne wajen Umar Farouk ko zaki je?" Na ɗan yi murmushin yaƙe ta cikin niƙab haɗe da cewa, "Bazan samu dama ba besty saboda ban faɗa a gida ba sai dai wani lokacin". "Shikenan". Nu'aymah ta faɗa tana maida glass ɗin sannan ta ja motar tabar wajen, araina kuwa dama banyi niyar zuwa duba shi ɗin ba saboda addu'ar da nake yi masa da dukkanin musulmi kaɗai ta wadatar.
**********
Ko da Nu'aymah suka je asibiti yau ba kowa wajen Umar Farouk saɓanin ko yaushe da idan kaje zaka isko wajen cike da mutane, yau Momy ta koma gida tayo masa tuwo da yace yana so, Saleem kuma ya yi masallaci wajen Sallah don haka wajen ya rage shi kaɗai, yana kwance aka turo ƙofa Nu'aymah ta fara shigowa fuskarsa ba yabo ba fallasa, yana hango su Billy a bayanta ya haɗe rai tare da kauda kansa gefe, jikin su a sanyaye suka ƙaraso ciki suna gaishe sa ɗaya bayan ɗaya tare da yi masa ya jiki, sanin don shi suka zo bai kamata ya wulakanta su ba yasa ya juyo ya amsa masu ciki-ciki, Nu'aymah ta ƙaraso wajen gadon tana kallonsa ta ce, "Kai friendy wannan fuska haka f..?" Wani kallo daya yi mata ya sata saurin haɗiye sauran kalaman ta tana komawa gefe gudun kar ya yarfata, bata ankara ba taga Felicia ta halba spray sama irin wanda ake wishing birthday ko marriage da shi, Billy ta duƙa ta ajiye ƙatuwar jakar data shigo da ita da Nu'aymah bata lura da ita ba ta ciro kwalin wani ɗan madaidaicin cake ta ɗora a gefen gadon tana fiddosa aciki a sama an rubuta "HAPPY BIRTHDAY U.F". Nan sauran suka ƙaraso gaban gadon suna ajiye masa abubuwan da suka zo dasu Felicia na sake halba spray ɗin a sama suka shiga tafi suna faɗin, "Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday happy birthday, happy birthday to youu...wish you quick recovery oga with good health and wealth". Wani kallo ya shiga yi masu ɗaya bayan ɗaya tamkar wanda ke shirin rufe su da duka yana sake tamke fuska, gaba-daya shan jinin jikin su suka yi kafin can suga ya saki murmushi haɗe da karɓar flower da Felicia ke miƙo masa yana cewa, "thank you so much felicia, thank you Billy i really appreciate, na gode na gode sosai, ai ni nama manta yau ne birthday na, thank you all". Ya faɗa cikin farin ciki da jin daɗi, da gaske kwatakwata ya manta da yau birthday dinsa in ba yanzu da suka tuna masa ba, A yadda yake da su ada shi kansa ya san ba abun mamaki bane idan basu manta da ranar zagayowar haihuwarsa ba saboda duk shekara tare dasu yake celebrating, tabbas kyautatawa na da daɗi wannan abu da suka yi masa ya sa ya ji ya manta da duka laifinsu a wajensa, ko ba komai tunda course mate ɗinsa ne zai yi kokari ya manta da komai ko gaisawa ce ya koma yana yi dasu.
Nu'aymah dake gefe tsaye ji tayi tamkar ta muzanta don ita ce yafi dacewa tayi masa hakan, sai dai ko sau daya bai taɓa bata damar da zata iya sanin wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsa ba kamar yadda ya bawa su Billy ada to taya ma za'a yi yasan ranar birthday ɗinsa, turo ƙofa akayi ana dariya, Dady ne tare da wasu manyan mutane abokansa daga wajen aiki suka zo duba Umar Farouk ɗin, turus yai ya kasa karasawa cikin ɗakin ganin yadda yan mata suka cika da alama ma wani celebrating suke yi..
(🥺Hmmm! Umar Farouk kana ruwa ban sanal kuma wane hukunci Dady zai yanke maka ba daga kai har su Felicia🥲Rest in peace hwaruku🏃).
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN