Showing 21001 words to 24000 words out of 157423 words
gaba haɗe da cewa, "Oh my God! yanzu Momy don na ɗauki motar Dady wani abune? Menene aciki ni fa dansa ne, don wa yake siyen motar ko tara kuɗin ba don mu ba?" Momy ta sauke ajiyar zuciya tana cewa. "Nima dai haka na gani, amma tunda baya so kadena ko kuma ka riƙa tambayarsa idan zaka ɗauka, yanzu ba don Allah ya taimaka ka dawo gidannan dawuri ba haka zai mana cin mutumci daga ni har kai acikin gidan nan don cewa yai ya bani awa uku na faɗa maka kadawo masa da motarsa". "To ya yi Momy, ga key ɗinsa nan, dama na ɗauka motar zata ɗauki hankali, but babu ma wanda ya damu da ita ga shi nan na ajiye". Ya faɗa cikin ɓacin rai yana ɗora key ɗin motar a saman center table dake tsakiyar paloun tare da miƙewa ya fice daga paloun, yana jin takaicin abinda Dady keyi masa tamkar ba shine ya haifesa ba, kullum cikin yi masa faɗa yake da hantararsa ko gajiya baya yi, wannan abun na matukar taɓa masa ziciya shi yasa yafi son Momy a kansa...
Call/WatsApp
07040402435
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
13.
Ni da Nu'aymah kuwa har muka iso gida babu wanda ya sake cewa wani abu har sai data ajiye ni gida, bayan na fito cikin motar ta kalleni murmushi kwance akan fuskarta ta ce, "Karki manta dai an ɗaga lecture ɗin gobe 4-6 zamu yi ta, don Allah kada ki taushe hannu." Nayi rolling eyes ɗina tare da sauke su kanta sannan nace. "Shikenan amma dai sai nayi sallah la'asar tukuna zan fito". Bata ce komai ba ta tada motarta tayi reverse tabar wajen ni kuma na shige cikin gida.
A palour na tadda Mamah zaune tana gyaran alayyahu nayi mata sannu da gida sannan na wuce ɗaki, watsa ruwa na fara yi kafin na fito nasa ƙananan kaya na shan iska na samu Mamah a falo na karɓar mata aiki ina yi muna fira, bayan na gama muka shiga kitchen tare, sinasir zata yi, haɗinsa ta fara ni kuma na soma haɗa miyar, Cikin hikima take sake koyar dani salon yadda ake girke-girke don kuwa Mamah ba daga baya ba in dai wajen iya girki ne tare da bashi muhimmanci, zan iya cewa tun ina da shekara takwas take shiga dani kitchen tana koya mini girki kuma har yau bata dena ba, a cewar ta iya girki shine mace kuma yana da wani kaso mai girma acikin rayuwar auratayya, haka ma tsafta da iya magana, a duk lokacin da muke aiki da ita to irin wuɗannan nasihohin da dabarun zaman gidan aure sune firarmu da ita, a matsayinta na uwa bata ɓoye mini komai kuma bata barin kunya ta shiga tsakanina da ita in dai ta wannan fannin ne, a cewar ta nice madubinta aduniya da idan nayi abu kai tsaye za'a tuno da ita ko kuma a ambaceta.
Ba mu muka gama aikin ba sai kusan ƙarfe biyu, a gurguje na shiga dakina na shiga toilet na ɗauro arwala nayi sallah, bacci nake ji sosai don haka na haye kan katifata, kafin kace me tuni baccin ya yi awon gaba dani, bani na tashi daga daddaɗan baccin da nake yi ba sai wucewar ƙarfe huɗu da rabi na marece, shi ma Mamah ce ta shigo ta tasheni tana faɗin."Wannan wane irin bacci ne haka da bazai barki ki tashi ki gaida ubangijinki ba, haba ace har an gama salloli bawa na kwance yana baccin asarar? Wannan abu ai yayi yawa". Mirginawa nayi ina sake juyawa daga kwancen da nake nace. "Kai Mamah baccin ne yayi mun daɗi fa wallahi". "To ai shikennan kije sai kiyta baccin na kyaleki sai kici gaba tunda bazaki tashi ba". Ta faɗa da ɗan ɓacin rai wanda hakan yasa na buɗe idanuwana a hankali ina tashi zaune tare dayin wata iri doguwar miƙa ina cewa, "Allah yahuci zuciyar ranki shi daɗe Hajiya Mamah, Allah ya baki haƙuri na tashi". "Ai na zata baza ki tashi ɗin ba ne naje na haɗoki da yayanki". Ina sauko da ƙafafuwana ƙasa nace, "Ni na isa ma! Bari kiga yanzun nan ma kuwa zan tashi". Na ƙare zancen ina miƙewa tare da shigewa toilet, sai da Mamah taga na kabbarta sallah sannan ta fice daga ɗakin, bayan na kammala na gyara katifata sannan na fito, a falo na samesu ita da Ya Jameel suna jiran fitowata muyi lunch, na ce "Mamah barka da wuni". "Barka Janaam har an gama sallar?" Bance komai ba shima ya Jameel na gaishesa, yana latsar wayarsa ya amsa mini da "Lafiya ƙalau Auta ya karatu?". "Alhamdulillah". Na bashi amsa ina ƙoƙarin serving dinsu sinasir ɗin da muka yi ni da Mamah, ƙwaya ɗaya na sakawa ya Jameel yace ya ishe sa, miya na ɗiba mishi a ɗan ƙaramin bowl na ajiye mashi a gabansa, haka ma Mahmah itama sannan na jawo kujerar dake kusa dani na zauna nima na zuba ma kaina na soma ci, ko rabin ƙwaya ɗaya ya Jameel bai ci ba na sinasir ɗin naga ya ture yana faɗin. "Mamah ni dai bana son wannan abun". Yai maganar yana ture plate ɗin gefe, kallonsa tayi kafin tace, "Wai kai kam har sai yaushe zaka dena tarar cin wasu abubuwa?, mutum kenan yace baya cin wannan baya cin wancan sai kace mace mai tsohon ciki? Shi yasa na damu da kayi aure ko na samu na huta da tsirfan nan taka" "To Mamah wannan abun ne shi ba masa ba shi ba wainar fulawa ba, ni dai sam bai mun ba". "Kai dai kace kawai bai ma ba, amma in dai baka haɗashi da masa ba tofa karka haɗashi da wainar fulawa, Janaam sai ki tashi ki sama mashi wani abun da zai ci idan kin gama". "A'a zan je na siya a waje Mamah, kawai tabar shi yaushe ta dawo makaranta akwai gajiya tare da ita". "Wace gajiya yarinyar data sha bacci yanzunnan ta tashi, kana ji ma ko Sallah sai yanzu tayi".
Saurin miƙewa nayi don bana son Mamah ta hau yin mita na makarar da nayi wajen sallah na nufi kitchen ina cewa. "Just a minute Ya Jameel yanzunnan zan kawo ma wani abincin". Na shige da sauri tare ƙoƙarin kunna gas, tunanin me zan dafa mishi da zai nina da sauri na soma yi, "Yes". Na faɗa ina ciro indomie ƙwaya ɗaya mai ɗan girma, tukuna na ɗora na zuba ruwa aciki sannan na bude fridge na ciro kifi na wanke, duk abinda zan nema sai dana haɗa waje ɗaya sannan na soma aikina, nan take gidan ya karaɗe da ƙamshi cikin mintinan da basu gaza goma ba na kammala na juye a plate na kawo masa.
"Yawwa auta sannu da ƙoƙari, yanzu Kinga wannan zanci na koshi har sai naji ba daɗi". Na saka dariya haɗe da cewa. "A'a Ya Jameel har sai dai ka barshi, ina zancen sai ka ji ba daɗi in har zaka iya ci?" "Lallai kam, faɗa masa". Mamah ta faɗa tana dariya itama, spoon na farko daya kai abakinsa naga ya wani yatsine fuska, haɗe rai nayi don nasan dai girkina yayi daɗi, kallona ya yai yana haɗiye lomar daya kai cikin bakinsa kafin yace. "Wannan wane kalar girki ne haka Janaam mai shegen daɗi". Nayi saurin sauke ajiyar zuciya ina dariya haɗe da cewa. "Ni dai nasan babu ta yadda za'a yi kace girkina nan bai yi daɗi ba duk wannan uban ƙamshin da yake zubawa". Mamah na dariya ta ce, "Ai ƙamshi ba shine daɗin girki ba Janaam, ni na ma ɗauka kwaɓa kika yi masa daya ɓata fuska haka". Ya Jameel yace. "Ai Mamah indai Janaam renonki ce babu ta yadda za'a yi takasa iya girki, shi yasa nake tunanin matar da zan aura dole sai tazo wajen ki tayi course ɗin girki na wata biyar kafin na yarda a ɗaura auren". Dariya muka sa ni da Mamah na miƙe naje bayansa na tsaya ina cewa. "Mamah bari nayi masa waigi ta baya kada ya faɗi don Allah wannan sanyi ne yake yi". "Mako ɗin ba komai sanyin ne". Ya faɗa yana sake kai indomie ɗin abaki, Nan ma dariya muka sake sawa cike da farinciki. A kullum rayuwar da nake yi tare da ahalina kenan ta farin ciki da walwala suna masu nuna mini ƙauna da soyayya, a tashina ban san wani abu hantara ko tsangwama ba awajen su, ko laifi nayi sai dai su zauna suyi mini nasiha, sai sunga abun na buƙatar jan kunne sosai za kaga sun zauna suna yi mini faɗa, ni kuma ina kiyayewa ba kasafai nafiye yin laifin da har zai kai suyi mini faɗa ba balle duka
Da daddare bayan na kammala komai munyi sai da safe da Mamah na kwanta ina ƙoƙarin saka wayata a caji sai ga kira na gani da sabuwar number ta ƙasar waje, ina gani nasan Nu'aym ne, ban ɗaga kiran ba har sai dana bari ya tsinke wani ya sake shigowa sannan na ɗaga a karo na uku. Sautin sanyayyar ajiyar zuciya na ji yayi daga cikin wayar kafin yace. "Har kin sa na fara tunanin sake yin wani booking gobe na dawo Nigeria da baki ɗaga wayar ba, ya kike kyakkyawata?" Nayi murmushi ina gyara kwanciyata yadda zan ji daɗin yin wayar haɗe da cewa, "Ina lafiya ya kuka isa?" "Ni da waye?" "Kai da zuciyata mana". Na faɗa ina murmushi haɗe da jin daɗin muryarsa, ya ce "Kin ganki ko? Har kinsa tsabar kishi na ji wani abu ya tsaya mini a wuya da kika fadi haka, yanzu sai kiyi ƙoƙari ki saukar mini dashi kafin ya shaƙeni yau nakasa yin bacci". "Taya kenan!" Na faɗa cike da son karin bayani akan kalamansa, "Kice kina sona da bakinki naji da kunnuwa na". "Ai tunda har kaga na amince maka to tabbas ina sonka, ko kana shakka akan haka ne". "Ehmmm to bazan ce a'a ba, amma zan ji daɗi sosai idan har na samu tabbacin haka daga bakinki, wannan zai kore mini fargabar da nake ciki cewa wani zai iya kwace mini ke". "To shikenan rufe kunnuwanka na faɗa maka". Dariya na ji ya saki haɗe da cewa, "Ranki shi daɗe anyi ba'a yi ba kenan, idan na rufe kunnuwana to taya zanji?" Cike da shauƙi na juya kwanciyata ina cewa, "zaka ji mana ko ka manta komai nawa naka ne, ni zan jiye maka da kunnuwana". "Na ƙi wayon". Ya faɗa a sakalce nayi murmushi haɗe da cewa, "Tom kabari zan kawo maka ziyara zan faɗa". "A ina kenan?" "A mafarki". "Me yasa baza'a faɗa yanzu naji ba?" "Kunyarka nake ji". "Iyyee kice akwai aiki agabana kafin nayi nasarar yakice wannan kunya da zata hana na samu tabbaci akan soyayya ta". "Ai ka riga ka samu tunda har na aminta dakai kuma na baka soyayyata, me yai saura kuma?". "A ɗaura mana aure na ganki acikin gidana, cikin dakina, a saman gado na kuma bisa ƙirjina, wannan shi yai saura tsakaninmu kyakkyawata, Kinga kuwa akwai sauran aiki a gabana". Nu'aym ya fa cikin wani irin sanyin murya, wata irin kunya ce naji ta rufeni da tasa na kasa cewa komai, haka yayita magana yana jana da fira amma na kasa cewa uffan, tun ina saurarensa har na dena saboda baccin da yai awon gaba dani....
070404042435
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU👏
[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
14.
Ta ɓangaren Nu'aym kuwa jin saukar lumfashinta a hankali ya tabbatar masa da tayi bacci, hakan yasa ya kashe wayar yana jin gabaɗaya jikinsa ya saki wata irin masifaffiyar soyayyarta na taso masa, bai ƙi jinin ace yau ya mallaki Janaam ba ta zamo mallakinsa, Yana jin wani irin kishi a kanta da baya tunanin zai juri wani ya raɓeta, shiyasa nan da 3month dole zai sake komawa don ya tabbatar da babu wani abirnin zuciyarta sai shi.
********
Washe gari misalin ƙarfe biyu Umar Farouk ya kira Nu'aymah, cikin jin daɗi ta ɗaga tana faɗin, "ɗan halak yanzu nake cewa bari na taɓoka na ji". "Ki ji me?" "Ba komai". Nu'aymah ta faɗa gabanta na wani irin faɗuwa, sosai take son bayyanawa Umar Farouk soyayyarta amma wata zuciyarta na gargaɗinta akan haka, tsoronta ɗaya kada tazo ta faɗa a samu matsala ko gaisawar ma su dena yi. Jin tayi shiru ya sashi cewa. "Aymah zaku shigo school dawuri kuwa?" "Anya? Sai anyi sallar la'asar kasan an maida lecture din 4-6". Umar Farouk ya amsa da "Ok! to shikenan ba damuwa". Har zai kashe Nu'aymah da jin muryarsa kaɗai ke haifar mata da wata irin natsuwa haɗe da tsumammen farin ciki ta ce, "Ya akayi ne Umar Farouk? Idan kana bukatar hakan ni sai na shigo kafin lokacin, dama dai Janaam ce ta so mu bari sai anyi sallah". Murmushi Umar Farouk ya saki tare da cewa. "Hakan zai fi gaskiya, idan kuka ce sai anyi sallah ba lallai ne ku samu farkon darasin ba, anyway duk yadda kuka yi, sai mun haɗu". Ya faɗa tare da kashe wayar yana kwashewa da wata irin dariya, shi dama bawai son shigar su yakeyi da wuri ba, shi kansa ba zai shiga da wurin ba so kawai yake ya kuntatawa Janaam don yana da tabbacin Nu'aymah baza ta jirata ba, juya kwanciyarsa yai yaci gaba da baccinsa da yake yi hankali kwance.
Nu'aymah kuwa suna gama waya dashi ta kira Janaam kusan sau biyar bata ɗaga ba hakan yasa ta haƙura da kiran ta miƙe ta shiga wanka kasancewar lokacin har ƙarfe biyu da rabi tayi, ko data gama shiri karfe uku da kusan mintina bakwai ta fito tana ta zuba ƙamshi abunta, Ummi ta kalleta tace. "Nu'aymah ina zuwa haka?" Saboda ganin irin adon data chaɓa, murmushi Nu'aymah ta saki sannan tace, "Ummi nayi kyau ne?" Tana wani jujjuyawa gaban Ummi, Ummi ta taɓe baki tana cewa, "Nu'aymah bakya da kunya ko? Ni kike cewa haka bayan ina tambayarki ina zaki je baki bani amsa ba!" "Oh God! Kema fa Ummi kinsan babu inda zan je idan ba makaranta ba". "Au! shine kika zuba wannan uban kwalliyar?" Hugging ɗinta Nu'aymah tayi ta baya tana dariya take cewa, "Ni dai ki min addu'a karki saka na makara." "To a sauka lafiya, Allah ya tsare". "Amin Ummi." Nu'aymah ta faɗa tana gyara mayafin data saka ta nufi hanyar fita, da gudu Nihla ta bita abaya tana cewa, "Adda Nu'aymah don Allah in zo mu tafi?". "Ba yau ba Nihla sauri nake yi". Ta faɗa tana fiddo key ɗin motarta daga cikin jaka ta buɗe ta shiga ta tayar sannan tabar gidan, Nihla ko harara ta bita da ita har ta fice daga gidan sannan ta koma ciki tana ƙunƙuni.
Gidan su Janaam ta nufa da niyar ɗaukarta su wuce tayi parking a ƙofar gidan ta fito ta shiga ciki, da Mamah sukayi karo a palour cikin girmamawa da ladabi ta gaisheta, Mamah ta amsa tana yimata sannu da zuwa take cewa.
"Aikuwa kinga mutuniyar taki bata nan Yanzun nan na aiketa gidansu baffanta, halama har lokacin makarantar ya yi?" "Kusan haka Mamah, bana so ne mu makara, gashi ina ta kiran wayarta bata ɗaga ba,". "Ai kuwa ina ganin ta bar wayar a gida tana chargy ne". "To shikenan Mamah bari na tafi, kice mata na wuce." "To zata ji Allah yai maki albarka, gashi zaki wuce ko ruwa baki sha ba". Nu'aymah tayi murmushi sannan ta miƙe tana cewa, "Ba komai Mamah sai anjima". Mamah ta rakota har kofar gida tana sa mata albarka, sai da taga ta tafi sannan ta juya ta koma ciki tana yaba halin kirki na Nu'aymah tamkar ba yar masu kuɗi ba. Ko data isa school tsirarun mutane ne aciki kasancewar ba'a fiye saka lecture ɗin 4-6 ba, kai tsaye department dinsu ta nufa tana faman dube-duben inda zata hango Umar Farouk, sai dai ga alama ta fahimci kamar bai shigo ba, wuri ta samu tayi parking tare da ciro wayar ta. Kiranta daya shigo wayarsa shi ya tashe sa daga baccin da yake yi lokacin ƙarfe huɗu, cikin Muryar bacci ya ɗaga yace ,"Nu'aymah?" "Na'am, wai baka fito bane gani cikin school tun ɗazu ina jiranka". Ta faɗa cikin sigar shagwaɓa da bata san lokacin da ma tayi ba, tsaki yaɗan ja yana cewa, "wallahi bacci ne ya ɗauke ni, bani nan da mintuna kadan kina ganina". Daga haka ya kashe kiran ba tare daya jira cewar ta ba, wanka ya shiga ya fito ya shirya ya yi sallah anan ɗaki sannan ya ɗauki key ɗin motarsa da wayoyinsa ya nufi makarantar, tafe yake ya ƙure sautin disko dake tashi cikin motar yana bi yana rausaya kai har ya ƙaraso, yana zuwa bakin gate mai adai-daita sahu na ajiye Janaam zata sallamar sa, wani irin murmushi ya saki tare da rage tafiyarsa har sai da Janaam ta gama sallamar mai adai-daita ɗin ta nufi cikin makaranta sannan ya biyo bayanta, sai daya zo saiti da ita sannan ya zuge glass din motar yana yi mata wani irin kallo cike da shaƙiyanci kafin yace, "Ya dai yan mata? Yau ba'a samu lift ɗin bane? Ko da yake na manta motar bata tsoho bace ashe hanya ake rage miji da ita, sorry tunda kin iso, watakil da akan hanya ne muka haɗu zan yi tunani ko zan iya rage maki hanya nima, anya ma zan iya? Bye sai kin iso yan mata". Ya faɗa yana ɗage glass ɗin daya sauke tare da shiga cikin wasu ruwan sama da suka kwanta a gefe da ƙarfi duk suka ɓata mata jiki gabadaya, tamkar an dasa Janaam haka tayi tsaye wajen zuciyarta na tafasa tana ganin kamar hadin baki ne sukayi da Nu'aymah don su tozarta ta,