Showing 36001 words to 39000 words out of 157423 words

Chapter 13 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

507

zan cutu to tabbas sai ya bi ta ya cutar dani, don yanzu Nu'aymah ta ajiye motarta saboda kusan kullum shi yake sauketa gida da motarsa, hakan kuma bai dameni ba tunda dama na dena jiranta, ya Jameel na kokari sosai wajen saukeni school ga dawowa ne kaɗai nake hawo abun hawa na dawo gida, sosai na mai da hankali na ga karatu saboda mun kusa fara exam ɗin da daga ita sai ta karshe, duk wani abu da yake yi mini na dena damuwa wanda na lura da baya jin daɗin hakan, a maimakon ya sani damuwa sai naga shi yake shiga damuwar saboda rashin ganin ya cimma burinsa na son baƙanta mini, na fita sabgarsa sosai wanda kuma ban bari hakan ya taɓa alaka ta da Nu'aymah ba, a haka har muka zo muka fara exam, duk da zaman Umar Farouk tsagera daya gagari kowa a makarantar yana da bala'in ƙoƙarin da kai tsaye bazan iya cewa ga na biyun sa a ajin mu ba, duk da wasu da dama kan ce nice guru ɗin ajin na mu amma ni ban yadda da hakan ba saboda shi ko karatu baza ki taɓa ganinsa rike da littafi yanayi ba, amma duk semester idan exam ta fito shine overall, da yawa suna faɗa karfin arzikin iyayensa kesa yaci exam ba wai kokarinsa ba, amma ni dai ban yadda da hakan ba, kawai na ɗauka yana cikin gifted ne yan baiwa da basa zaman yin karatu kamar yadda muke yi ba, amma kuma ko da wasa idan ba dole ba ban taɓa ganin lecture ta wuce sa ba, sannan shi introvert ne acikin aji amma na sha zauna exam tare da shi tun a shekarar mu ta farko ina ganin yadda yake rubuta exam dinsa cikin natsuwa kuma yake cike handout ɗinsa tsab har ya nemi ƙari, wanda wasu ke ganin kamar satar amsa ce yake sai dai ni ban taɓa ganinsa da exco ba.

Babban kalubalen da nake fuskanta a yanzu da Umar Farouk shine aduk lokacin daya gama exam to sai ya yi sanadin da zai ja a amshi nawa booklet ɗin ko da ban gama ba kuma ko ban yi komai ba, sosai wannan abun ya dameni haka zan yita magiya amma a hanani booklet ɗina, dole haka nake submitting ban gama ba na fita raina a ɓace shi kuma yana dariyar keta ya shige motarsa ya bar wajen, sanin na ɗanyi abun ƙwarai ke sa ban fiye damuwa ba na kuma sake maida hankali sosai ta yadda zan riƙa kammala exam ɗina cikin lokaci kafin ya ƙulla mini shiren da zai ja a amshe Mani booklet, yau zamu ƙare rubuta exam ɗin ƙarshe ta semester ɗin nan, kasancewar karshen wata ne ina fama da matsanancin ciwon mara yasa ban samu nayi karatu sosai ba sai da asuba na samu na ɗan dudduba  sama-sama, cikin rashin jin kwarin jiki na shiga makaranta na koma can gefe ina sake duba karatun don sai sha biyu zamu shiga, har lokacin kuma ban dena fama da ciwon marar ba sai dai ya ragu sosai ba kamar jiya ba tun da na samu period ɗin ya zo mini. Karfe sha biyu na bugawa muka shiga exam, cikin rashin Sa'a kuwa aka ajiye ni kusa da Umar Farouk don empty kujera ɗaya ce ke tsakanina dashi, tun da na karɓi booklet ɗina na duƙe ina rubuta abinda na sani don questions ɗin sun yi tsauri, sai dai kilan hakan baya rasa nasaba da rashin samun wadataccen karatu da ban yi ba, ko mintuna ashirin ba'a yi ba na hango Umar Farouk ya gama, juyowa yai ya kalli gefena ina kallonsa ta gefen idanuwa sai dai ko da wasa banyi gangancin bari muka haɗa idanuwa dashi ba don tseratar da kaina daga makircinsa, babbar damuwata a kullum in rubuta abun ƙwarai a exam ɗina saboda duka 50% na courses ɗin banda attendance saboda Umar Farouk baya bari na rubuta. Ashe ban sani ba ko yanzu ba tsira zanyi da mugun nufinsa ba don kuwa yana submitting exam ɗinsa ya biyo ta gefena da zai fita, sai gani kawai nayi yasa hannu ya jawo booklet ɗin nawa, miƙewa nayi da sauri amma kafin nayi wani yunƙurin ya yaga booklet ɗin pieces ya watso mani ita a jiki, "What?" Na ji supervisor ɗin namu ya faɗa da ƙarfi yana nufo wajen da muke amma ko a jikin Umar Farouk daya zuba hannayensa cikin aljihu yai tsaye yana kallona murmushin jin daɗi kwance akan fuskarsa, yayin da ni kuma hawaye tuni suka cika idanuwana suna sauka akan fuskata ta cikin niƙab, supervisor ɗin namu na zuwa ya rufe Umar Farouk da faɗa akan bazai dauki wannan rashin ɗa'ar tasa ba dole sai yayi reporting nasa ga school management haka kuma shima sai ya kece booklet ɗin nasa sannan ya ce gaba-daya mu fito, cikin ɓacin rai ya ɗauki booklet ɗin Umar Farouk ya yaga shima sannan yace yafita yabar masa hall, ni kuma ya bani wani sabon booklet ɗin yace na je na sake rubuta wa kafin lokaci ya yi, duk da an yaga masa booklet shima ko kaɗan hakan bai faranta mini rai ba saboda ni kaɗai na san halin da nake ciki da ƙoƙarin da nayi wajen haɗo amsoshin dana bayar, wanda ba lallai ne yanzu na iya sake haɗosu ba, ina hawaye na karɓi booklet ɗin don ba ni da zaɓin daya wuce hakan na koma seat ɗin da nake na zauna.

Umar Farouk kuwa yana ganin an yaga booklet ɗinsa ya ɗage kafaɗu irin i don't care ɗin nan sannan ya je ya zaro wani booklet ɗin da kansa ya koma ya samu waje ya zauna ba tare daya bi umurnin da aka bashi ba na fita yabar hall ɗin ya fara sake rubuta wata exam ɗin, sosai ran supervisor ɗin ya sake ɓaci ya ce bazai rubuta wata ba dole sai ya yi spill over ɗin course ɗin, shi kuma ya ce babu inda zai je sai ya sake rubuta exam kamar yadda aka bani na sake rubuta wa, nan fa rigimah ta kaure tsakanin shi da supervisor ɗin, supervisor na sai ya fita shi kuma yana bazai fita ba, sannu sannu hall ɗin yafara cika da malamai, duk wanda ya zo yaga da Umar Farouk ake rigima sai kaga ya koma ba supervisor ɗin haƙuri, daga karshe dai akafi karfin supervisor ɗin akan ya ƙyalesa, hakan ya tunzura sa matuƙa ya bar hall ɗin ya kuma ce lallai sai ya tabbatar da cewa hukumar makaranta ta hukunta Umar Farouk bisa wannan renin hankali da wulaƙanci da yayi masa. Wannan yar tsamar da aka samu tsakaninsa da supervisor shi ya ɗauke hankalin malamai a kanmu ya kuma taimaka mini wajen sake rubuta abun ƙwarai fiye ma da wanda na rubuta farko saboda taimakon dana samu daga wajen colleagues ɗin na da banyi tsammanin hakan daga wajensu ba musamman Saleem abokinsa. Sai dai duk da hakan ban dena jin zafin wutar dake ci a zuciyata ba ta wannan wulakancin da Umar Farouk ya yi mini, na ji araina cewa idan har ban rama abinda yai mini ba yau  nima bazan taɓa yafewa kaina ba saboda abun nasa ya wuce hankali, matukar zanci gaba da yi masa shiru to gaba zai mun wulakancin da yafi wannan kafin mu ƙare. Handbag ɗita na sagala a kafaɗata sannan na nufi wajen da yake tsaye a saman hall ɗin masu zugasa na sake yi masa zuga akan wai kada yabar supervisor ɗin ya kamata ya ɗau mataki a kansa saboda ba ƙaramin rena masa da wayo yai ba. Ina zuwa wajen Umar Farouk na ɗagowa yana kallona murmushi ɗauke akan fuskarsa ban tsaya wata ba na ɗaukesa da mari cikin ɓacin rai ina ɗage niƙab ɗina don na samu damar bayayana masa tsantsar ɓacin raina ina zaro idanuwa nake faɗin, "Umar Farouk ba burinka kaga ina hawaye ba na ƙuntata? Farin cikinka shine ka ɓakanta mini saboda kana ganin kafi kowa a makarantar nan, to shikennan kaci gaba da farin ciki kayi nasarar ƙuntata mini, ka ɓakanta zuciyata sannan kasa na zubar da hawayen da na yi alƙawarin bazan sake zubar wa ba saboda kai, sai ka zuba ruwa a ƙasa kasha, kaci gaba da yin farinciki sannan ka hanani zuwa matakin da Allah ya nufa zan kai a karatu na idan har zaka iya". Na dakata da faɗan tare dasa bayan hannuna na share hawayen da suka jiƙa mini fuska, yayin da gabaɗaya hall ɗin yai shiru hankalin kowa ya dawo akan mu, cikin karyewar murya da kuma yanayin da nake jin kaina aciki na rashin lafiya na ɗago idanuwana na zuba masa ina ci gaba da cewa, "Da farko nayi tunanin cewa watakil kuskuren nawa ne dana shiga gonar ka shiyasa kake mun duka wuɗan nan abubuwan, sai yanzu na gano cewa ba kuskure na aikata ba ina akan daidai abinda nayi maka domin zuciyarka sam bata san daraja da kimar ɗan adam ba, na shanye abubuwa da dama da kake mun ba wai don basa ɓata mani rai ba sai don na baka damar da zaka iya barin komai ya wuce saboda mun duwa ɗaya bata amo, amma na fahimci zuciyarka ba tada yafiya gani kake yi duk abinda akayi maka sai ka rama sannan zaka zama jarumi, shi kenan muje a haka, daga yau ni Amatul-Alim ba zan koma bari ka taka ni ba, ba zan koma bari ka wulakanta ni ba sannan ba zan ƙara ɗaga maka ƙafa ba acikin makarantar nan har zuwa lokacin da zamu ƙare, duk wani mutum da kake gani a duniya yana da negative side dinsa ba kai kaɗai kake dashi ba saboda haka ka shirya ganin nawa bangaren na rashin mutunci don daga yau duk abinda kayi min sai nayi maka linkin sa, don haka mu zuba ni da kai mu gani ɗan halak ka fasa". Na ƙare zancen ina yi masa kallon sama da ƙasa tare da ƙyasta masa hannu sannan na bar wajen ina ɗauke hawayen da suka zuba mini haɗe da sauke niƙab ɗina.

Umar Farouk kuwa kasa motsawa yai tun lokacin da idanuwansa sukayi arba da kyakkyawar fuskar Janaam da bai taɓa gani ba, lokaci ɗaya ya ji wani abu mai ƙarfi ya dirar masa a zuciya, daradaran idanuwanta masu matuƙar haske da kukan da tayi yasa suka garwaya da ja ya ƙurawa idanuwa, ya lumshe idanuwansa yana rufesu tare da sake buɗesu lokaci ɗaya ya sauke akan ɗan ƙaramin bakinta dake masifa, wani kaɗawa ya ji zuciyarsa tayi masa tamkar tana neman ɓallewa daga wajen zaman ta tafito, round ɗin fuskarta, dogon hancinta da loɓawar kumatun sune suka fi fizgar masa hankali, do tun da yake bai taɓa ganin mace mai kyan fuska ba kamarta, gashin idanuwanta kaɗai abun kallo ne balle kuma tausasan laɓɓanta da bakinta ke dauke dasu, gaba-daya Umar Farouk ya shagala da kallon Janaam har ta ƙare masifarta tayi gaba, a lokacin ne yai firgigit yana binta da idanuwa, ji yake yi tamkar tana tafiya tare da ruhinsa ne ta bar shi da gangar jiki kawa...

WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE

070404042435, GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUƁEMU A WANNN LAMBAR DON YA MALLAKI NASA.

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/10, 1:03 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA, KI BIYA NAIRA N1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

                            22.

Ji Umar Farouk yai gaba-daya jikinsa ya mutu bazai iya sake yin komai ba, don haka sai kawai shima ya fice ya nufi wajen motar sa, bayan ya buɗe ya shiga ciki ya zauna sai ya ji shi tamkar wanda aka zarewa lakka, ya rasa me ya shiga kansa lokaci ɗaya daya haifar masa da wata irin kasala, key ɗin motar yasa amma sai ya ji yakasa tada ita balle ya iya barin wajen. "Me ke faruwa dani ne?" Ya faɗa a zahiri tare da kife kansa a jikin steering wheel ɗin motar, tamkar wanda aka tsikara sai kuma ya yi saurin ɗago kansa tare da ba motar key ya ja yabar wajen aguje.

Ni kuwa dama ina fitowa hall ɗin kai tsaye na nufi gate ba tare dana tsaya jiran Nu'aymah ba, ina zuwa kuwa cikin ikon Allah na samu abun hawa na tare na hau, tun da muka fara samun yar tsama da Umar Farouk ban taɓa jin sanyi a zuciyata ba sai yau dana fitar da abubuwan dake dasƙare cikinta akansa, na kuma ji kaso 60 daga cikin damuwata ya gushe don a shirye nake da yi masa duk abinda yake tunanin zai iya yi mini don ya wulaƙanta ni. Ko dana iso gida na tadda Mamah bata nan don haka kai tsaye sai na wuce ɗakina na rage kayan jikina na shiga toilet don rage gajiyar dake tare dani, sai da nayi wanka mai kyau na gyara jikina sannan na fito na nemi katifata na haye kasan cewar fashin sallah nake ba tare dana tsaya yin komai ba, bacci nake ji sosai don haka ina kwantawa ya ɗaukeni, bani na farka ba sai kusan bayan la'asar na ji jikina ya saki sosai, toilet na sake shiga na watso ruwa sannan na fito na ɗauki man da nake amfani dashi na shafe jikina dashi, ban fiye son kwalliya ba sai kawai na ɗauki khumrah mai ƙamshin gaske na shafa na ɗauko wata doguwar riga fara data ɗan kama jikina na saka na feshe jikina da turare mai ƙamshin gaske, na yafa ƙaramin mayafina fari akaina sannn na ɗauki wayata na fito ina ƙoƙarin kunna waya ta na nufi ɗakin Mamah, ko dana leƙa har lokacin bata dawo ba sai na nufi kitchen na zubo abincin na dawo palour na soma ci bayan na kunna tv, Data na kunna na hau WhatsApp, ina hawa naga Ya Nu'aym na online na saki murmushi, tun kafin nayi masa magana sai ga saƙonsa ya shigo da sauri na buɗe, "Hi kyakkyawata". Shine abinda naga ya turo mini, cike da shauƙi da tsokana na mayar masa da amsa ina cewa "Allah ya taimaki yallaɓai." na tura masa, emojis ya turo mai hawaye tare da marairaice fuska, na saki dariya don sai na hango fuskarsa kamar gashi a gabana, ya Nu'aym akwai son shagwaɓa har mantawa yake da Ni nafi dacewa da nayi masa hakan, "Sorry Hayat". Na tura masa kafin ya maido min da ,"Ina kewarki kyakkyawata ya kike? Ya exam an kammala lafiya ko?" Na amsa da lafiya kalau ina yi ina tsakura abincin don gabaɗaya hankalina yanzu ya koma ga masoyi na, vedio call ya kirani na ɗaga ina shagwaɓe fuska hango yadda ya sake yin wani kyau da haske tamkar wani bature ina cewa. "Hayat ya naga haka! Kaga yadda ka ƙara kyau da haske kuwa? Anya kana tunanina?" Bai tanka ba sai kallona kawai naga yana yi ya kura mini idanuwa tamkar wanda bai taɓa ganinsa ba, baki na turo ina cewa, "Meye haka Hayat ina ta yi maka magana ka yi mini shiru?" Ya ɗago kai tamkar wanda aka tada daga bacci yana sauke narkakkin idanuwansa akaina haɗe da cewa, "Me kika ce kyakkyawata?" "Eh'ehmm ni Allah bana son haka Hayat, kana nufin baka ji me nace ba? Ina tunanin ka ya je ne halan?" Na faɗa aɗan shagwaɓe ina sake turo bakina gaba, Pointing ɗin hannunsa naga yai saiti ƙirji na da sauri na zaro idanuwa tare da jan mayafina na rufe jikinsa sosai cike da jin kunya ina sadda kaina ƙasa, Sai da Nu'aym ya saki murmushi sannan yace, "Kin ga, ni fa ba can nake nufi ba, ina nufin ke nake tunani". Yai maganar yana yi mini dariya tare da kashe mini ido, saurin sake maida kaina ƙasa nayi ba tare da na sake haɗa idanuwa dashi ba, hira mukayi sosai tun ina jina a takure har na ɗan saki saboda yadda yake ja na da ita so romantic, bamu kare vedio call ɗin ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar magrib sannan muka yi sallama yana cewa zai je yai sallah idan ya dawo zai sake kirana, miƙewa na yi nima ina mamakin ina Mamah ta je da har yanzu bata dawo ba, ɗakina na shiga na ɗauko azkhar ɗina na karanta, bayan na gama na fito na shiga kitchen, muna da sauran abincin da zamu ci ba sai na sake ɗora wani ba, amma na san ba lallai ne Ya Jameel ya iya cin shi ba, sai kawai na ɗora masa tuwon semo ɗan kadan da bazai wuce iya bakinsa ba don Mamah bata cin abu mai nauyi da daddare, WhatsApp ɗina na sake hawa ya Nu'aym na online muka ci gaba da charting dashi, sallamar Mamah na jiyo daga palour nayi saurin yi masa sallama ina sauka bayan na kashe data tare  fitowa nayo palour, muna haɗa ido da Mamah na turo baki haɗe da cewa, "Sannu da zuwa Mamah ina kika je haka kika yi zamanki har wannan lokaci baki dawo ba?" Na kare zancen ina karɓar handbag ɗinta da mayafin da ta cire, Dariya tayi tana zama kan kujera kafin tace, "Ai dama na san zakiyi ƙorafi shi yasa naso dawowa tun la'asar don na san zakiyi ta zama ke kaɗai, laifin yayanki ne shi yace na jira har ya tashi wajen aiki sai ya biya ya ɗauko ni". Ban kai ga yin magana ba Ya Jameel ya shigo ɗauke da kaya, na yi saurin zuwa na karɓar masa ina ajiye jakar Mamah da mayafinta a gefenta nake faɗin, "Ya Jameel sannu da zuwa". "Yauwa auta, wato daga shigowar Mamah har kin soma yi mata ƙorafi, ke fa ba yarinya bace balle kice an barki a gida ke kaɗai kina jin tsoro, bayan haka kwana nawa ya rage maki acikin gidan mu aurar dake kije gidanki kuma ki zauna ke kaɗai?" "Aure ya Jameel! An taɓa aure ba miji?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login