Showing 129001 words to 132000 words out of 157423 words

Chapter 44 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

520

mun hadu a kotu, ka tabbata ka zo wajen jibi idan ba haka ba zargin kisan zai iya dawo a kanka". "N.na..na'am ranka shi daɗe, kotu fa kace?" "Eh Indai har ka tabbatar da abinda ka faɗa gaskiya ne to muna bukatar ka awajen, yan tambayoyi kaɗai ne zaka amsa mana gaban kotu ba wani abu ba a sallame ka". Barrister Nazir na gama fadar hakan yabar wajen, mai gadi ya koma ciki jiki a sanyaye yana ji tamkar ya tattara inasa-inasa ya komawar sa kauye don tunda yake bai taɓa zuwa kotu ba ya tsaya gaban alƙali. Barrister Nazir bai bar anguwar ba sai daya yi bincike sosai ya kuma samu tabbacin lallai Umar Farouk ya shigo anguwar ranar, ya so ya nemi gidan su Janaam amma sai yaga babu bukatar hakan domin dole ta can ɓangaren zasu gabatar da ita a kotu, su kuma zasu iya yin amfani da wannan damar su yi mata duk tambayoyin da suka dace acan, daga nan school ɗin su ya wuce nan ma ya yi bincike mai kyau, abubuwan daya samu akan Umar Farouk ko kadan basu yi masa daɗi ba don har ya sare da cewa bashi ne ya aikata kisan ba, kai tsaye gidan Momy ya nufa ya kirata ya sanar da ita yana kofar gida tayi masa izinin shigowa ta buɗe masa falon kasa na bangaren Dady ya shigo, bayanan duk daya hado ya yi mata bayani yana ƙare zancen da cewa, "Am sorry to say Barrister Maryam yaron nan ya wuce duk wani tunanin mu, idan na fahimci yadda cáse ɗin yake akwai yarinyar da yake soyayya da ita, a yadda na ji labari dana bincika baya barinta tsayuwa da kowa ne namiji, yakan yi amfani da karfin ikon kujerar da mahaifinsa ke kai yai wa duk wanda ya gani tare da ita dukan mutuwa, abincike na na samu cases da yawa a school ɗin su da ya aikata hakan, kuma takan yiyu shi wannan ɗin ya kashe shi ne saboda ganinsa tare da yarinyar?" Kai Momy ta shiga girgizawa tana cewa "how Barrister? Taya zai shiga har cikin gidan su yaron saboda yarinyar ya kashesa, taya zai yi hakan?" "Shine abun tambaya da bamu gane ba, amma muna da hanya daya da zamu iya fahimtar komai idan aka koma kotu". "Wace hanya kenan Barrister Nazir?" "Mai gadin gidan tunda shi ke da alhakin sanin duk wani shige da ficen masu zuwa gidan". Shiru Momy tayi tare da fadawa tunani anya zata iya zame masu hujja a kotu, maganar Barrister Nazir ta katse tunaninta dake cewa, "Ba muda wata hanya sai ita da zamu iya jan case ɗin nan don faɗaɗa binciken mu saboda idan kin lura a zahiri ta kowace fuska shi ya aikata kisan nan". "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Barrister Nazir i have confused nima, me yasa Umar Farouk zai kashe mutum saboda mace?" "Koma Meye muyi addu'a kuma mu sake tsananta binciken duk da ni nafara sarewa akan lamarin yaron nan". Mommy ta sauke ajiyar zuciya ba tare data ce komai ba tana jin ta tsani ko wacece wannan yarinyar datai silar faruwar wannan tashin hankali akan danta, Da wannan tunanin suka yi sallama da Barrister Nazir, bayan ya tafi Momy ta shiga zagaye falon tana kai da komowa, bata taɓa tsammanin cewa akan mace yaronta zai iya koda daga hannu ya daki wani ba balle har akai ga kisa, yanzu idan ta tabbata haka ne ya zatayi ta bawa danta kariya? Me zai shiga kan Umar Farouk da har zai iya aikata irin wannan danyen aiki da ake zarginsa dashi?.

*******

A bangaren Nu'aymah kuwa tana gama waya da Janaam ta jawo kayanta ta shiga ciro duk wani abu daya shafi Janaam tana wurgi dashi, kama daga kan sutura da take saya masu tare, littafan makaranta, wasu abun ƙawa, hotuna da duk wani abu daya shafe ta, yadda take wurgo kayan daga cikin dakinta suna gangarowa ta ƙasan upstairs ɗin tana kuka yasa Ummi fitowa daga dakinta, da sauri ta shiga dakin Nu'aymah taga yadda ta hargitsa sa tamkar wata mahaukaciya tana kuka, ƙarasowa tayi cikin dakin ta duka ta janyota ajikinta ta rungume tana lallashinta, "Ummi na tsani Janaam bana son ta nayi nadamar sabunta arayuwata, na tsani duk wani abu daya shafe ta Ummi bana son ganinta ta cuce mu ta zama silar rabamu da dan uwan mu da kuma farincikin mu, don Allah kusa akamata itama Ummi domin laifinsu daya da Umar Farouk ɗin don na tabbata hadin baki suka yi suka kawar mini da dan uwa don su cika burin su, Ummie taci amanar tare ta yaudare mu ta yanke yarda da amincin dake tsakanina da ita ta yadda bakin cikin data sakani aciki kullum nake ji yana kashe ni ina sake dawowa". "Ya isa haka Nu'aymah, koma meye bamu da wata hujjar da zata saka a rufeta sai dai shi wanda muke da hujja akansa, sannan karki manta ita cin amanar data yi maki taimakon ki ne tayi da yanzu cewa za'a yi wanda ke sonki ne ya kashe maki yaya, amma shi kisan kan dan uwanki yai kin ga kuwahar abada laifinsu bazai taɓa zama ɗaya ba domin shi ne ya rabamu da farincikin mu na har abada ba ita ba"..

*KOTU*

Kallo ɗaya zaka yiwa Barrister Shamsu da Barrister Aysha ka hango tsantsar farincikin dake dauke a fuskokinsu saboda nasarar da suka yi ta haɗo duk wasu hujjoji da zasu tabbatar da laifin da ake tuhumar Umar Farouk shi ne ya aikata. Bayan gama sauraren ƙararraki da dama aka gabatar da cigaban saurarar ƙarar da ake yi ta Umar Farouk, a yau kotun ta samu halartar mutane masu yawa tare da sabbin fuskokin da suka haɗa da Janaam, ya Jameel, Mamah, Dr Abdullahi gwaram, Nu'aymah da kuma Ummie mahaifiyarta da suke son suga wane kalar hukunci Justice Ibrahim zai yankewa ɗansa. Barrister Shamsu ne ya fara tashi bayan alƙali ya basu umurnin gabatar da hujjojin da suka zo dasu, cikin girmamawa ya ce, "Ya mai girma mai Shari'a muna bukatar kotu ta bamu izinin yin tambayoyi ga wasu mutane kafin gabatar da hujjojin mu". Justice Ibrahim ya yi masa alama da an bashi izini, sake cewa yai "ina so wannan kotu mai albarka ta bada izini a shigo mana da Saleem Abubakar". "Kotu ta bada dama a shigo da Saleem Abubakar" alkali ya faɗa yana rubutu a jikin takardun dake gabansa. Saleem ne abokin Umar Farouk aka shigo dashi ya tsaya acikin akwatin da wudanda ake ƙara ko suke yin ƙara ko suke sheda ke tsayawa aciki suna fuskantar juna shi da Umar Farouk da bai yi mamakin ji ko ganin ankira abokin nasa a wajen ba....

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:10 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            61.

"Malam Saleem, kotu zata so ka sake faɗa mata cikakken sunan ka da kuma danganta ko alaƙar dake tsakaninka da wanda ake tuhuma da aikata kisan kai wato Umar Farouk Ibrahim". Barrister Shamsu ya faɗa yana dai-daita tsayuwar sa agaban akwatin da Saleem ke tsaye, ajiyar zuciya Saleem yai yana dauke idanuwansa daga kan Umar Farouk daya ƙi bari su haɗa ido dashi haɗe da cewa, "Sunana Saleem Abubakar, ni abokin Umar Farouk ne tun yarinta har zuwa girma". "Kenan duk wasu ɗabi'un. sa da halayen sa ka sani?". "Eh kusan hakan kamar yadda shima ya san nawa". "A binciken da mukayi mun samu bayanai masu yawa akan cewa lallai Umar Farouk zai iya aikata kisa saboda halayensa da dabi'unsa da yadda ma yake mu'amalantar mutane, wanda hakan ya karfafa zargin mu akan cewa tabbas shi ɗin ya aikata kisan da ake zarginsa dashi, me zaka fadawa kotu akan hakan kasancewarka abokinsa tun na yarinta?" "Eh to, tabbas Umar Farouk mutum ne mai zafin rai sosai da idan ransa ya ɓaci to koma me zai iya yi zai kuma iya aikatawa musamman akan abinda yake so, amma batun kisan kai bana tunanin zai iya hakan". "To amma yayin bincike mun gano cewa ya sha yiwa mutane duka ba sai ɗaya ba ba sai biyu ba, shin baka ganin hakan zai iya haifar da kisan kan idan dukan yai yawa?" "Objection my Lord! ya kamata abokin aikina yaje kai tsaye ga tambayoyin daya dace yai wa Saleem ba ya tsaya bamu labaran da duka jita-jita da anyi ance ne saboda maganganun sa gaba-daya ɗauke ke suke da labaran da bamu da tabbaci akan su". Barrister Nazir ya faɗa haɗe da miƙewa, kai justice Ibrahim ya kaɗa kafin ya maido kallonsa ga Barrister Shamsu ya ce, "Barrister Shamsu je kai tsaye ga tambayoyin da kake son yi mas". Kallon Saleem Barrister Shamsu yai sannan ya ci gaba da cewa, "Malam Saleem Ranar tara ga watan daya gabata a binciken da mukayi ta ɓangaren wayoyin hannun Umar Farouk, mun samu bayanan wayar da kuka yi dashi har sau biyu na tsawon mintuna uku da second tara da kuma na minti ɗaya da second huɗu, kwatsam sai kuma bayan kun gama wayar da wasu sa'o'i aka kiramu aka ce an samosa a gidan Dr Abdullahi gwaram ya aikata lafin kisan kai, shin kun haɗa baki ne wajen aikata kisan ko kuwa ka taimaka masa ne".  Rudewa Saleem yai cikin tsananin tashin hankali ya shiga girgiza kai yana kallon alƙali ya ce, "ranka shi daɗe babu hannuna a wannan kisan wallahi kuma ban masan hakan zata faru ba" "to me ya faru?" Barrister Shamsu ya faɗa yana kallonsa, sai da Saleem ya share zufan daya keto masa ta goshi da rigarsa kafin yace, "Tabbas munyi waya dashi har sau biyu amma duka akan zancen bukin ƙarewar mu ne da ake yi a ranar, kira na farko bayan mun gaisa ya tambayeni ne akan ina ina ne na sheda masa ina school shi nake jira ya ƙara so ya sheda mini cewa gashi nan zai fito gida shima, kira na biyu kuma ya kirani ne yana sanar damu cewa zai fara biyawa ya dauko Janaam su taho tare kafin ya ƙaraso". "Wacece Janaam?" Barrister Shamsu ya faɗa wanda hakan yasa Umar Farouk ciro kai a lokacin yana kallon Saleem, Saleem da gabaɗaya ke a tsorace ya ce, "Budurwarsa ce wacce yake so" "to sai me yafaru bayan nan?" "Nima ban sani ba kawai tsinta zancen tuhumar da ake yi masa kawai nayi". "Ka tabbata duk abinda ka faɗa mana gaskiya ne?" Saleem ya jinjina kai a tsorace tamkar zai rugo saboda tashin hankali, juyawa Barrister Shamsu yai ya koma wajen zamansa ya fito da wata takarda ya miƙawa alƙali yana cewa, "Ya mai girma mai Shari'a wannan takardar na dauke da bayanan da duka Saleem ya bamu akan wayar da sukai da Umar Farouk, kamar yadda ya faɗa Umar Farouk yaje ɗauko Budurwarsa Janaam su tafi taron bukin kare makarantar su, wacce sun kasance anguwa ɗaya suke da Nu'aym Abdullahi Gwaram, a binciken da muka yi mun gano ita wannan yarinyar ƙawa ce ga ƙanwar shi wanda aka kashe mai suna Nu'aym, har wayau ita yarinyar tana soyayya dashi yayan ƙawar tata da aka kashe, shi kuma Umar Farouk yana matukar son yarinyar wanda hakan yasa ko a makaranta yake yiwa duk wani daya gani tare da ita barazana ko kuma shegen duka saboda kishi, kamar dai yadda aminin nasa ya faɗa cewa Umar Farouk mutum ne mai zafin rai da zai iya aikata komai akan abinda yake so ko kuma aka ɓata masa rai, wanda hakan na iya zamowa dalilin daya sa bayan ya je anguwar ya sameta tare da shi yayan kawar tata ya bishi har cikin gidansu ya kashesa". "Objection my Lord". Momy ta faɗa jin yadda ake tsaro labaran da zasu tabbatar da ɗanta yai kisan, ba tare da Justice Ibrahim ya ɗago ba ya ce, "Objection rejected Barrister Maryam". Sannan ya ɗago kansa yana kallon Barrister Shamsu ya ce, "zaka iya ci gaba da bayananka Barrister Shamsu kotu na saurarenka". "Na gode ya mai Shari'a " Barrister shamsu ya faɗa yana murmushin jin daɗi, wani irin gumi ne Momy ta ji ya taso mata zufa na tsattsafo mata ta duk wata kusurwar gashi dake jikin ta saboda tsananin tashin hankali, a hankali ta ja iska ta furzar ta baki tana dafe goshinta haɗe da lumshe idanuwanta jin zafi tako ina na taso mata. Barrister Shamsu ya gyara rigar jikinsa haɗe da yin gyaran murya sannan ya ci gaba da cewa, "Ya mai Shari'a ina so kotu ta sake bani dama na sake gabatar mata da wasu mutane da zasu tabbatar da abinda ake zargin Umar Farouk ya aikata". "Kotu ta baka dama". Justice Ibrahim ya faɗa tare da ɗagowa ya kalli Umar Farouk sannan ya maida kansa ga takardun dake gabansa ya ci gaba da rubuce-rubucen da yake yi.

Ya Salis aka shigo dashi abokin Ya Jameel, sai kuma Kamal ɗan ajinsu Janaam da kuma saurayin da Umar Farouk ya daka a Library da wanda aka yiwa duka a ranar dinner ɗinsu Ya Jameel, daya bayan ɗaya Barrister Shamsu ya shiga yi masu tambayoyi akan Umar Farouk suna bashi amsa har aka zo kan Ya Salis, nan shima ya sanar dasu cewa tabbas Umar Farouk ne yasa akayi masa dukan mutuwa saboda ya ganesa tare da Janaam ya ɗauko ta a mota ya kuma bishi har a asibiti ya yi masa ƙwaƙƙwaran jan kunne akan zai iya yi masa fiye da abinda yai masa idan har ya bayyana cewa shi yasa aka dakesa, wanda aka yiwa duka ranar dinner din su Ya Jameel shima ya bada irin bayanan da Ya Salis ya bayar na barazana da Umar Farouk ke yi masu wanda shi yasa suke cewa sun yafe ba tare da sun bari hukuma ta shiga cikin case ɗin ba, bayan duk sun gama bayanin su Barrister Shamsu ya ci gaba da cewa, "Ya mai girma mai Shari'a, ina so kotu tayi duba mai kyau akan bayanan wuɗannan mutane ta fahimci cewa Umar Farouk yana amfani da karfin iko da yake ganin yana da shi acikin garin nan yana taka duk wanda yaga dama ya kuma tozarta duk wanda yaso sanin hukuma baza ta iya aiki akansa ba". Wani abu Justice Ibrahim yaji ya dakar masa zuciya jin cewa ɗansa na aikata abinda hukuma bazata iya hukuntasa ba, abu mai zafi da matukar raɗaɗi da kuna a zuciya shine su dake hukunci da doka a hannunsa yau an wayi gari wai ƴaƴansu ne ke taka dokar, wannan abun kunya ne ba kaɗan ba agunsa da bai taba ji ba a rayuwarsa, Barrister Shamsu ya ci gaba da cewa "Bisa wannan dalilin yasa Umar Farouk bai ji nauyin shiga har cikin gidan Dr Abdullahi gwaram ba ya kashe masa ɗa dalilin ya ganesa tare da yarinyar da yake so, wanda iyayen yarinyar sun sheda mana cewa ta je wajen ƙawarta ne don su tafi wajen bikin kammala makarantar su tare shi kuma lokacin ya je gidansu ya aika kiranta sai aka sanar masa da tana can gidan, shine har ya same su acan ya aikata abinda ya aikata, saboda haka ina rokon wannan kotu data yi la'akari da shedun da muka gabatar daga wajen mutane daban-daban ta yarda ta kuma amince Umar Farouk shi ya aikata wannan kisan da ake zarginsa dashi" yana kaiwa nan ya je ya zauna kotu tayi tsit ko ƙwaƙƙwaran motsi baka ji saboda yadda Shari'ar ta dau hankalinsu, Justice Ibrahim ya ɗago kai ya ce, "lauyan wanda ake ƙara ko kuna da abun cewa?" Momy ta miƙe cikin ƙarfafa kanta tace, "Ya mai girma mai Shari'a, duk wudannan maganganu da abokan aikina ke faɗa har yau basu gabatarwa da koto hujja mai ƙarfi da zata yarda cewa Umar Farouk shi ya aikata kisan ba, kawai dai sun bayyanawa kotu halayen Umar Farouk ne da wasu dabi'unsa da ake ganin basu dace ba, amma in son kotu ta sani kisa bata ta'allaka ga mutum mai munanan ɗabi'u kaɗai bane, iwa, uba, ɗa, malami, likitoci, direbobi, mace, namiji har ma da malaman Arabia da alkalai da shuwagabannin gwamnati sukan iya aikata kisa bisa ganganci ko kuma akasi, wanda idan hakan ta faru ba dubi ake yi da shi malamin addini bane ko ita uwa ce kyawawan dabi'un su bazai bari su iya aikata hakan ba, hujja mai ƙarfi ake dubawa ko da mutum shi yafi kowa kafirci da rashin halaye masu kyau matukar bashi ya aikata kisan ba to baza'a ce shi ya aikata ba, haka koda mutum a masallaci yake kwana yana wuni azumi idan ta bayyana shirya aikata kisan baza ace bashi ya aikata ba saboda kyan halayensa, saboda haka ya kamata su gabatar wa da kotu hujjojin lokacin daya shiga gidan da wanda yaga sadda ya shiga gidan, da wanda aka aikata kisan kan gabansa da kuma wace asibiti aka kai gawar shi wanda aka kashe da bayanan tabbacin kisan kafin su tabbatar da laifin akansa". "Ina da korafi ya mai Shari'a". Barrister Aysha ta faɗa haɗe da miƙewa, Justice Ibrahim yace, "kotu na sauraren ki Barrister Aysha" "Ya mai girma mai Shari'a kamar yadda abokiyar aikin ta faɗa muna da tarin hujjojin da muka bayar akan wanda ya aikata kisa, na farko rahotannin da muka dauka daga bakinsa, na biyu rahotannin bayanan asibiti da muka bayar akan binciken da akayi wa gawar a zama na farko, na uku zanen shafin hannunsa da muka dauka a wuƙar da aka aikata kisan da ita wanda ya bada tabbacin hannun wanda ake tuhuma ne, sannan na karshe muna sake rokon kotu data bamu dama mu gabatar da shedar mu ta gani da ido wacce agabanta komai ya faru". "Kotu ta baku dama". Justice Ibrahim ya faɗa yana sauke wata sihirtacciyar ajiyar zuciya...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:10 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            62.

Janaam ce aka shigo da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login