Showing 90001 words to 93000 words out of 157423 words
komai ya sake lalacewa tsakanina da ita". Na faɗa cikin muryar kuka ina jingina da kaina a jikin glass ɗin motar nima ina hawaye, a kullum nakan kwatanta kaina a matsayin Nu'aymah na ji ya zan yi idan hakan ta faru dani, ban da tsananin zafi da ƙunci tare da ƙunar zuciya ba abinda nake hangowa kaina, sosai jikina yai sanyi hakan yasa yana yi mini magana amma ban tanka shi ba har muka iso, bayan ya yi parking ya juyo ya kalleni ya ce, "Ki taimake ni ki tsaida kukan nan naki, dole ne nayi ƙoƙarin yaki da duk wani abu da zai shamakance soyayyata dake na kuma tabbatar na nuna masu ina son ki, bana so ki riƙa jin babu dacewa wani ya ganni a tare dake shi yasa nai kokarin dakile wannan bahagon tunanin naki, ki kula mini da kan ki idan an ƙare kuma zan zo na dauke ki, sosai na ji daɗin kasancewa ta atare dake yau, na ƙara sanin ko wacece ke, ban damu da tsiwar ki ba duk da na fahimci ke ɗin matsoraciya ce ta wani ɓangaren, a haka sai naji kin ƙara burgeni sannan kin sake shiga zuciyata, ina sanki Amaah don Allah kar ki bari ɗan wannan abun yasa naji kamar ban kyauta ba pls.." ban ce komai ba har lokacin hawaye nake yi, yana gama magana nasa hannu zan buɗe kofar sai na jita a rufe "Matukar baki dena hawayen nan ba sai dai na mai da ki gida". ya faɗa yana jingina a seat ɗin da yake tare da kunna volume ɗin wakar da yake sha ɗazu ya kashe, ganin da gaske bazai bude mini ba ya sa nayi kokarin tsaida hawayena, sannan na samu ya cire lock na buɗe motar na fito ba tare dana ce masa uffan ba.
Umar Farouk kuwa bai bar wajen ba sai da yaga ta shiga sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tada motar ya nufi gida.
A falo ya tadda Momy zaune sai masifa takeyi da Tauheeda ta fasa mata kwalaben khumras data saka ta tayi mata gyaran ɗaki, Tauheeda dake durƙushe a gabanta na hawaye sai hakuri take bata amma fir Momy taƙi haƙura sai zazzaga mata masifa take yi tamkar mai yi da babba, sai da Umar Farouk ya zauna ɗaya daga cikin kujerun sannan ya kalli Momy ya ce, "Momy this is too much fa, me tayi maki tun a waje nake jin muryar ki, ni kam wai ba ke ce kika haife mu ba ni da ita? Tauheeda fa yarinya ce bai kamata kina saka mata ciwon kai haka ba, zo nan ki zauna Tauheeda". Ya faɗa yana nuna mata kusa dashi, Tauheeda ta taso tana faman yin ajiyar zuciya don har dukan ta sai da Momy tayi, Momy na hararar ta ta ce, "Wannan yarinyar da kake gani ni haihuwar ta kawai nayi amma ta je can ta gado bakin halin kakar ta na munafunci ta dauko gaba-daya yadda kasan dashi aka halicce ta". Umar Farouk bai bi takan abinda Momy ke faɗa ba ya ce Tauheeda ta bata hakuri, cikin shesshekar kuka Tauheeda ta ce, "Momy kiyi hakuri". Momy ta watsa mata harara ta yi saurin sauke kanta ƙasa, "Je ki idan akayi la'asar ki shirya kayanki na kai ki gidan Uncle Shahid bukin Nidrah ki je ki yo kwana biyu". "Oh wato kam ga mahaukaciya ko Umar Farouk? So kake ka nuna mun kafi son ƙanwarka a kaina, to idan ka kaita can wa zai ci gaba da aikin gidan?" Umar Farouk ya miƙe haɗe da cewa, "Momy don ki huta fa zan dauke miki ita take tayo kwana biyu, Dady ya riƙa taya ki mana". Throw pillow Momy ta dauko ta jefe sa dashi yai saurin kaucewa tare da caɓewa yana dariya ya maida shi akan kujera ya ajiye, "Ka ci abinci kuwa?" Momy ta faɗa cike da kulawa tana kallon sa, ya ce "Eh na ci a gidan Mamie". Taɓe baki Momy ta yi jin abinda ya faɗa ba tare data sake cewa uffan ba don ba wani shiri take yi da ita ba, kawai don dai Umar Farouk ɗin na son ta kuma yayanta na nuna mata tana da muhimmanci a wajensa da bukin ma na Nidrah baza ta je ba, ban da halin yaro ma da mantuwa Umar Farouk da yana tuna yadda Mamie ke yawan haɗasa da Uncle Shahid ɗin takai ƙararsa yai tayi masa masifa da faɗa daga ni har shi akan ɗan abinda bai taka kara ya kawo ba da ko kusa da ita bazai je ba ta samu ta kwanta tayi bacci kafin akira sallar la'asar ɗin.
Umar Farouk na shiga ɗakinsa ya ciro wayarsa ya fara kiran Janaam, bata ɗaga ba ya tura mata message ɗauke da kalamai masu daɗi da kuma sanyaya zuciya sannan ya juya akalar kiran nasa ga Nu'aymah data kasa ƙarasawa gida ta shiga wani wajen shakatawa da wasannin yara tasha kukanta har ta gaji, ta rasa da wa zata zauna tayi wannan zancen na halin da take ciki, ta rasa wa zata fadawa damuwarta ya lallasheta, tana son Umar Farouk ta sani idan har ta fadawa Ummie abinda ke faruwa tana da zafi sosai, akan ɗan wannan matsalar zata iya cewa idan bata rabu dashi ta fita sabgarsa ba sai ta mugun saɓa mata, Nihla kuwa ko ta faɗa mata baza ta fahimce taba tunda bata kai girman da zata iya banbance ko meye damuwar ba. Kamar yadda Janaam take ba tada wasu ƙawaye sama da ita itama haka Nu'aymah take, ba tada wata babbar ƙawa abokiyar shawara da take fadawa kukanta da damuwarta sai Janaam gashi taci amanar ta ta kwace mata wanda yasan tana matukar so da kauna, ta rasa inda zata saka ranta taji sanyi kullum damuwarta sai daɗa ƙaruwa take, tana wannan tunanin kiran Umar Farouk ya shigo wayarta, kamar baza ta ɗaga ba amma sai ta ji zuciyarta ta kasa, ɗaga kiran ta yi takai wayar a kunnen ta, sai dai tana jin muryar sa ta tuno yadda ta gansu acikin mota shi da babbar ƙawarta kawai ta ciro wayar tayi jifa da ita tayi ratsa-ratsa tare da fashewa da kuka tana rufe fuskar ta da tafin hannayenta.
Jin kiran ya yanke yasa Umar Farouk ya sake gwada kiranta, sai dai tana shiga ya ji ance masa it's switch off. A jiye wayar ya yi ya mike ya shiga toilet yana mamakin me yasa Aymah ta kashe wayar ta bayan har ta ɗaga da farko?
(Lallai Umar Farouk ka cika gulmamme, ka daki yarinya sannan kuma ka koma tambayar dalilin yin kukanta?🤔 I feel your pain Aymah Gaskiya anci amanar mu😭).
Janaam kuwa tana ganin shigowar sakon Umar Farouk ko tsayawa karantawa bata yi ba ta goge tana jin zafinsa da haushinsa a ƙasan zuciyarta, ita kam Allah Allah take yi agama bukin Ya Jameel su fara jarabawa, suna kammalawa ya Nu'aym ya zo ayi ta ta ƙare ko ta huta da wannan masifar dake bibiyarta...
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
Ga masu son Vip ku bibiyi Arewabook @billysfari ta wannan link https://www.arewabooks.com/chapter?id=689b69e619700231f1502019
51.
Wannan karon ma ban ɓoyewa Aunty Nidrah komai ba akan abinda ya faru, dariya ta yi haɗe da cewa, "Sis wannan lamarin naku na rasa yadda zan yi maku, babbar damuwar yanzu ɗaya ce wato Nu'aymah, duk yadda za'a yi baza ta taɓa yarda cewa ba amanar ta kika ci ba, saboda haka kiyi kokari ki je kiyi mata bayani yadda zata fahimce ki, ina ga hakan shi kadai ne zai fi kawo maslaha tsakanin ku, Umar Farouk kuwa kiyi ta hakuri dashi kuma kiyi ta addu'a Allah ya zaɓa miki alkhairi tsakanin ki da shi". Na ciro kaina a ƙasa haɗe da cewa, "Aunty har wani alkhairi ne tsakanina dashi mutumen da tunda ya shigo rayuwata ya hana zuciyata samun natsuwa da kwanciyar hankali? Ni dai ko alkhairi ne shi a gareni bana so yaje can ya samu wata". Aunty Nidrah murmushi kawai tai bata ce komai ba har aka kammala mana gyaran kai da ƙafafuwa kafin aka hau yiwa aunty Nidrah kwalliya, sosai muka yi kyau musamman ita da kana kallonta kasan amarya ce don ta samu gyara abun har ba'a magana tubarkalla Masha Allah kawai za'a ce, Ya Jameel ta kira bayan an kammala mata kwalliyar ya zo da kan shi ya ɗauke mu don gudun abinda ya faru jiya ya sake faruwa dan shi kam abun ya bashi mamaki ya kuma bashi tsoro, sai da muka koma gida muka ƙarasa shiryawa duk inda amarya ta yi sai binta da kallo akeyi saboda yadda tayi kyau, ƙarfe biyar muka je wajen buɗan kai abun gwanin burgewa da ban sha'awa, an gudanar da komai cikin burgewa da kuma wayewa, dangin ango sun taka rawar gani sosai haka ma abokansa, Mamah ta je ta kuma zuba kudi masu yawa da suka sake jawo mata kima da martaba a wajen dangin amarya ta kuma nuna tsantsar soyayyarta ga amarya da kuma farincikina ga auren, ni kaina ba'a barni a baya ba Ya Jameel ya bani kudi lokacin da ya ajiye mu daya dauko mu daga wajen gyaran kai da zanyi amfani dasu, anci an sha an kuma cashe sosai cikin farin ciki da walwala, kana kallon yadda fuskokin dangin amarya dana ango dama saura abokan arziƙi kasan auren na so ne da kuma kaunar juna, ba mu muka gama shagalin ba sai ƙarfe takwas na dare kuma alhamdulillah an watse taro lafiya, Sosai Aunty Nidrah ta so na sake komawa gidan su na kwana amma naƙi saboda takurawar Umar Farouk da kuma gobe ake yinin biki da kuma ɗaura aure tare da dinner, nima zan fi jin daɗi na ganni cikin yan uwana cikin farin ciki da walwala, don haka ana gama buɗan kai na bi Mamah muka koma gida, washe gari karfe ɗaya da rabi na rana aka daura auren ya Jameel da Aunty Nidrah, kafe biyar na marece aka dauko amarya, sai da aka kawo ta wajen Mamah ta yi mata nasiha haɗe da rungumeta kafin aka ɗauketa aka nufi gidanta da ita, ƙarfe takwas na dare an gama shirya Aunty Nidrah zuwa wajen dinner da aka dauko mai kwalliya ta tsara mata ita, ina zaune a gefenta ina latsar waya ta, chart muke yi da ya Nu'aym ina tura masa hotunan da muka yi jiya wajen buɗar kai sai yaba kwalliyata yake yi ina dariya don ba kaɗan nake jin daɗin chart ɗin ba, wata yarinya da bazata wuce shekaru sha huɗu ba ta shigo da gudu tare da haye gadon Aunty Nidrah tana ɓuya a bayan mu, wanda hakan yasa wayata dake hannuna faɗuwa ƙasa saboda yadda ta faɗo mini da karfi, raina a ɓace na fizgo yarinyar ina jin kamar na kifa mata mari tayi saurin runtse idanuwanta tana sa ƙara ganin har na ɗaga hannu sama, yadda naga jikinta na rawa ya sa na saketa haɗe da cewa, "Idan kika dawo ɗakin nan sai na miki shegen duka". Tare da duƙawa na ɗauko wayata, ga mamaki na duk da yadda ta tsorata da dukan dana tashi yi mata bata bar wajen ba, cikin muryarta mai zaƙi na ji ta ce, "Sorry Aunty, Kamal ne ya biyo ni zai dake ni". Tsintar kaina nayi da yin murmushi ina dafa kanta na ce, "Sorry too da tsawar da nayi miki kin ji ko?" Murmushi ta sakar mini tana kada kai kafin tafice tabar ɗakin na bita da kallo don sosai yarinyar na ji ta burge ni, ina wannan tunanin aka ce a fito da amarya zuwa wajen dinner, da gudu yarinyar ta sake shigowa dakin tana riƙo hannun Aunty Nidrah tana dariya sai naga itama ta rike nata, a daya gefenta na tsaya nima bayan na miƙe ta riko hannuna muka fita sauran kawayen ta na biye damu a baya har muka sauko daga saman steps ɗin zuwa ƙasa, sai da muka kai Aunty Nidrah bakin mota yarinyar ta buɗe mata baya, ita naga ta fara shiga sannan aunty Nidrah ta shiga, so nake na tambayi wacece wannan yarinyar amma na rasa wa zan tambaya, gaban motar na buɗe na shiga ashe ya Jameel na ciki, ga mamaki na ina juyawa naga sun tafe da yarinyar, Ni dai ban san yarinyar nan ba don ba yar uwar mu bace sannan ban taɓa ganinta gidan su aunty Nidrah ba balle nace yar uwar su ce, haka na ja bakina na kama nayi shiru har muka isa Hall ɗin da ake dinner ɗin daya matuƙar tsaruwa, muna fitowa wannan karon naga yarinyar ta zo ta rike hannuna, juyowa nayi ina kallonta ta sakar mini murmushi ta jani zuwa bayan amarya da ango dake gaba sun rike juna za'a shiga ciki, ma'ana dai mu zamu yi masu rakiya, kasa haƙuri nayi sai da na ɗan duƙo yadda zata iya jin me nake faɗa ina cewa "Hello beautiful girl, who are you?" Na faɗa ƙasa-ƙasa ina kallonta, itama kallona tayi kafin tace "Tauheedah, bride sister and you what's your nam?" Ta faɗa can ƙasa-ƙasa kamar yadda taga nayi, dariya nai haɗe da cewa, "Janaam". Idanuwana na akan mc da sai faman wasa ango da amarya yake "Wow nice name, I have a friend Janaam, will you too be my friend?" Dariya nai jin ta faɗi haka dai-dai lokacin muka iso mazaunin amarya da ango, murmushi na saki bayan sun zauna tare da kallonta ba tare dana ce komai ba na riƙo hannunta muka sauko, hannuna ta rike tamkar wacce ke tsoron na gudu na barta tana cewa "Aunty Janaam Yayana yace masu sunan Janaam basa da kirki nadena ɗaga masu ƙafa, amma ke kina da kirki zan faɗa masa nayi sabuwar ƙawa Janaam kuma mai kirki ce". "Sure?" Na faɗa tare da sama mana wuri muka zauna, shaƙuwa sosai ta shiga tsakanina da yarinyar ina jin ina ma ace ita ɗin ƙanwata ce kamar yadda ako yaushe nake jin Nihla tamkar ƙanwata kuma nake matukar son ta, muna zaune aka kira yan uwan ango, bayan mun gama spreading kuɗi wata yar uwar mu ta jani gefe muna magana da ita sai ga wani kyakkyawan saurayi ya yi mana sallama, amsawa mukai muka ci gaba da firar mu, sai ji na yi yace "pls Baiwar Allah minti ɗaya?" Ba tare dana kallesa ba nace, "Kayi hakuri bawan Allah an tsayar mini da miji". Yar uwar tawa ta zaro ido tana kallona jin abinda na faɗa nayi saurin kauda kaina gefe, murmushi ya saki haɗe da cewa, "Hakan kaɗai ya tabbatar mini da wasa da zuciyata kike son yi amma don girman Allah ki bani aron lokacinki pls". "Haba ke kuwa Amatu girman Allah fa yace, ki je kiji dame ya zo". Yar uwar tawa ta faɗa tana kallona, hakan yasa na mike muka koma gefe dashi, ko minti biyar bamuyi ba na bashi hakuri ya kama gabansa, nan aka ci gaba da shagulgula zuwa ƙarfe goma da wani abu aka gama dinner ɗin kowa ya watse ya tafi gida suma ango da amarya aka kaisu ɗakin su, Tauheeda kuwa sai da akayi da gaske sannan aka samu aka rabata dani da zasu wuce gida.
Washe gari misalin ƙarfe sha daya na rana yan buki duka wasu sun watse ya rage daga ni sai Mamah da wata ƙanwarta Ya Jameel ya shigo gaishe su, nan yake fadawa Mamah jiya bayan har an watse wajen dinner misalin ƙarfe sha biyu da rabi na dare aka kirasa wai an tsinci wani saurayi bayan hall ɗin da akayi dinner cikin jini anyi masa mugun duka, haka ya fita lokacin ya je ya kira yan sanda aka zo aka ɗauki saurayin aka kai shi asibiti bai dawo gida ba sai da yaga an yiwa saurayin komai lokacin karfe uku da rabi na dare, dalilin da yasa kenan yau yayi rankon bacci bai samu shigowa tunda safe ya gaisheta ba, ya sheda mata yanzu ma haka daga asibitin yake, ya kare zancen yana nuna masu hoton saurayin a wayarsa kwance a saman gadon asibiti.
Sallallami su Mamah suka shiga yi a take na ji hanjin cikina sunyi wani irin murɗawa lokaci ɗaya tsoro na mamaye mini zuciya ganin hoton saurayin nan da yai mini magana jiya wajen dinner wanda hakan ya tabbatar mini da ba ko shakka wannan aikin na Umar Farouk ne, tsabar tashin hankali da tsoro wani fitsari na ji na shirin zubo mini da sauri na miƙe na nufi ɗakina ina rufo ƙofa, jikin ƙofar na jingina na silale ƙasa tare da fashewa da kuka, wannan wane irin bala'i ne da masifa haka Umar Farouk ke son jawo mani, saurin toshe bakina nayi jin kukan na shirin fitowa kafin nai saurin miƙewa na koma kan katifata na jawo wayata, sai dana share hawayen da suka jiƙa mini fuska sannan na kira wayarsa, bugu ɗaya ya ɗaga ban tsaya sauraren abinda zai cewa ba nace, "In sha Allah duk abin kayi mini. sai an yiwa ƙanwarka, me yasa zuciyarka babu imani da tausayi a cikin ta? Me yasa zaka riƙa zaluntar mutane da sunan kana so na kuma har kake tunanin zan so ka har na aure ka? Na tsane ka Umar Farouk bana son ka bana kaunar ka". Na ƙare zancen tare da kashe wayar ina sake fashewa da kuka...
WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.
ACCOUNT NO
7040402435 (MONIEPOINT)
ACCOUNT NAME
BALKISU SANI KAURA
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07040402435
09079274454
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
Masu son Vip ku bibiyi Arewabook@billysfari ta wannan link https://www.arewabooks.com/chapter?id=689b69e619700231f1502019
52.
Ya kirani yafi a kirga ban ɗaga ba kafin can kiran Aunty Nidrah ya shigo, cikin kuka na