Showing 78001 words to 81000 words out of 157423 words

Chapter 27 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

526

cin amanar yayana ba, saboda haka ki kwantar da hankalin ki zai sauko kawai kin san halinsa da zafin kishi sosai". "Shikenan Besty Nagode but kema na fahimci kina cikin damuwa kawai kina boye mun ne, ko meye kiyi addu'a sannan ki roƙi sassauci awajen Allah, da sannu zai sama maki mafita". "In Sha Allah zan yi haka". Nu'aymah ta faɗa kafin taji ta katse kiran. A jiyar zuciya na sauke haɗe da gyara kwanciyata cike da tsammanin ya Nu'aym zai hakura ya neme ni.

Nu'aymah kuwa na gama waya da Janaam ta kira yayan nata, sun ɗan yi magana dashi ya kuma fahimce ta kafin ya iya jin zuciyar sa tayi masa sanyi, yana son Janaam bai ƙi yau a ɗaura masu aure ba ta zama mallakin sa ko zuciyarsa ta huta amma taƙi ta bashi wannan damar, taya zai iya jurar kiranta na tsawon mintuna ashirin ana faɗa masa line busy ba tare daya kawo aransa cewa da wani take waya ba duk da irin yaddar da yai mata, sun ɗan taɓa fira da Nu'aymah kafin sukayi sallama tana jin ziciyarta na sake wani nauyi tunawo da nata masoyi da shi bata ma gabansa. Wasu hawayen ne data wuni tana yi yau suka sake zubo mata a hankali ta zame ta kwanta saman gadon nata tana jin gaba-daya duniyar tayi mata ɗaurin goro.

Umar Farouk kuwa ɗan ƙaramin hauka ya dinga yi cikin asibitin lokacin da Janaam ta kashe wayarta, daya sake kokarin kira kuma sai ya ji line busy, hakan ya sa duk ya ci cire bandage ɗin dake kansa haka ma daurin dake hannunsa, yana ƙoƙarin cire na kafar Allah ya kawo nurse ita da Momy data dawo yanzu a ɗakin suka rirriƙe sa, tuni gyaran da akayi masa a hannu ya lalace amma duk da haka baya jin zafi a hannunsa kamar yadda yake jin zafi a zuciyarsa, ya rasa ya zai yi da soyayyar Janaam data kasa fahimtar sa, gashi bazai taɓa iya hakura da ita ba balle ya yi tunanin yin hakan, duk girman soyayyar da Momyn ke yi masa haka ta rufe idanuwa tayi ta zabgar faɗa dashi, Umar Farouk bai iya cewa komai ba don shi kaɗai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa, idan yace zai buɗe bakinsa yai magana to kuwa tabbas raunin sa ne zai kara bayyana. Haka Momy ta ƙaraci faɗan ta ta gama nurse ɗin kuma ta basa taimakon da zata iya tana cewa, " Ka ga ka ɓalla aikin da akayi maka yanzu dole sai an sake wani aikin, kuma Dr Nasir kaɗai ne zai iya yi maka ni bazan iya ba". Har ta dasa aya Umar Farouk bai iya cewa komai ba sai ma juyar da kansa gefe da yai ya ɗora hannunsa a saman goshin sa. Godiya Momy ta yiwa nurse ɗin ta fice Momy ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Umar Farouk ɗin cikin tausasa murya ta ce, "Ka tashi ga abincin na kawo maka kaci". Ba tare da Umar Farouk ya juyo ba ya ce, "Bana ci am ok" ya faɗa cikin muryar dake nuna shima cikin fushi yake da ɓacin rai...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

https://www.arewabooks.com/chapter?id=6894e7bd8ebf53d524760d91

                            44.

Sai da Umar Farouk ya kwashe sati biyu a asibiti kafin aka sallamo sa, kallo ɗaya zaka yi masa ka tabbatar daga jinya ya taso, jinyar ma bata gangar jiki kadai ba har data zuciya don duk iya ƙoƙarin da zai yi wajen ganin ya shawo kan Janaam ta karɓi soyayyarsa ya yi amma bai yi nasara ba, hakan ya haifar masa dayin wata irin rama duk da irin tarin kulawar da yake samu wajen likitoci da kuma Iyayensa, hatta Dady dake fushi dashi sai daya sauko ganin irin ramar da yai , gaba-daya an ɗauka matsalar ciwon hannunsa daya samu karaya da ƙafa ne ke damunsa don har Dady ya soma shirye-shiryen ko za'a fitar dashi waje saboda yadda Momy tabi duk ta ɗaga hankalinta, gashi anyi masa tambayar duniya akan meke damunsa amma yaki buɗe baki ko da likita yai wa bayani, wanda hakan yasa da likitan ya dudduba sa yaga ya samu sauki ya basu sallama tare da yiwa Momy bayanin cewa su kula da kyau akwai abinda yake tunani wanda shi ya haifar masa da damuwa har ta yi masa yawa har yake wannan ramar, idan kuma bai dena ba to komai zai iya faruwa dashi nan gaba. Hankalin Momy sake tashi yai bayan sun dawo gida ta ci gaba da lallaɓa Umar Farouk tamkar wani ƙaramin yaro don tasan ko meke damun sa amma yaƙi bata damar hakan, daga karshe ta kira Saleem ta tambayesa amma sanin halin Umar Farouk bai iya ya faɗa mata gaskiyar abinda ke faruwa ba saboda rashin sanin ta ina ma zai fara sheda mata cewa yarinyar da a ranar ya hango tsantsar tsanarta a idanuwanta har ta kasa hakuri ma ta furta da bakinta ta tsane ta ita ɗanta Umar Farouk ke so har take wahalar dashi, ya san da kamar wahala idan zata karɓi zancen musamman ma idan ba shi Umar Farouk ɗin ya sanar da ita da kansa ba, yasan komai Momy zata iya yima Janaam musamman yadda taga ɗanta ya shiga wani hali ta dalilin ta, Momy tasan halin Umar Farouk tunda bai yi niyar buɗe baki ya faɗi abinda ke damun sa ba to fa duk abinda za'a yi bazai faɗa ba, don haka ta sashi agaba tana sharar hawaye tana fadar tunda ya fiso ya rasata saboda damuwar sa da bata so to ya je yai duk yadda yaga dama baza ta sake tambayarsa ba. Duk taurin kan Umar Farouk babu abinda ya tsana aduniya sama da ɓacin ran Momy, saboda haka yana ganin ranta ya ɓaci sai ya soma karfafa kansa ya rage tunani da damuwar da yake ciki har ya soma fita tare da Saleem saboda ya nuna mata ba komai kamar yadda yake faɗa mata akoda yaushe, ya yi kokarin canzawa sosai yadda Momy zata cire wa kanta damuwa kuma ba laifi ya yi nasara, sai da yai sati ɗaya da sallamo wa daga asibiti sannan ya koma school.

Misunderstanding ɗin da muka samu da Ya Nu'aym ta sanadiyar Umar Farouk yana da yawa saboda yawan kiran da yake yi mini da akoda yaushe hakan bata faruwa sai lokutan da Ya Nu'aym yake kirana, duk da magana mai daɗi bata taɓa haɗa ni da Umar Farouk ba bai taɓa jin cewa zai daina kirana ba, a yadda yake nuna mini ko zaginsa zan yi indai zan ɗauki wayarsa yaji muryata to zai ji daɗi saboda jin murya ta kaɗai na bashi natsuwar zuciya tare da samun farinciki, hakan daya faɗa shi ya hankaltar dani kuskuren ɗaga wayarsa da nake yi har muna samun matsala da ya Nu'aym sai kawai na rufe duka layoyan sa da yake kirana dasu ta yadda bazai sake samuna ba ko ya kira, bayan na tura masa ƙwaƙƙwaran jan kunne tare da baƙaƙen maganganu, daga lokacin na samu lafiya kuma muka dena samun matsala ni da ya Nu'aym, kyakkyawar alaƙa da kuma shaƙuwa ta sake shiga tsakanina dashi muka sake komawa tamkar sababbin masoya, kullum muna lake dashi a waya ko kuma vedio call, yayin da kwanaki keta shuɗe wa lokacin ƙarewa makarantar mu nata matsawo, da kansa yake kirgar ko kwanaki nawa suka rage mana mufara exam, inda yai mini alkawarin cewa tare dashi za'a yi shagalin bukin graduation ɗin mu don zai shigo kuma bazai koma ba har sai anyi mana baiko an tsayar da ranar bikin mu, ina son ya Nu'aym da duk wasu dabi'u nasa saboda mutumen kirki ne uwa uba ga soyayya da yake nuna mini tamkar zai hadiye ni, shi yasa duk wani abu da zai sa yai fushi ko ransa ya ɓaci ina nisanta kaina dashi musamman wanda zai hada alaƙata da wani namijin saboda tsananin kishinsa akaina yana da yawa, na kuma fahimci ba komai yasa yake yin haka ba sai don yana so na da yawa kuma yana kaunata fiye da kima, ban sani ba ko Nu'aymah ta fahimci Umar Farouk na so na shi yasa tayi baya-baya da alakar mu duk da muna gaisawa idan muka haɗu kuma muna zaunawa muyi fira, sai dai duk wani abu daya shafi sirrin juna da ada muke fadawa junan mu yanzu ta dena, ko firar ya Nu'aym na dauko mata sai dai kawai tayi murmushi tace wannan tsakanin ku ne, tun ina jin ba daɗi har na hakura na dena, duk wanda yasan yadda nake da ita ada ya san yanzu ba haka muke ba, ita kanta na san bawai tana jin daɗin irin zaman da mukeyi yanzu bane saboda tayi wani irin sanyi sannan kuma ta rame, ko da yake ban sani ba ko har da soyayyar Umar Farouk ke damunta data dena gani, don haka na kudurta a raina koma menene zan yi amfani da damata idan Umar Farouk ya dawo school na ajiye tsana da komai a gefe na nuna masa tarin ƙaunar da Nu'aymah keyi masa na kuma tabbatar masa da ina da wanda nake so kuma na tsaida da zan aura, na tabbata hakan zai sa ya hakura dani ya koma gareta.

(Anya Janaam kina ganin zaki iya? Kar fa kije ki ɓallowa kan ki ruwa🧐).

*****

Yau muna zaune ni da wasu yan class ɗin mu ana fira kafin mu shiga C.A da zamuyi don tuni muka fara contentiour assessment ɗin mu, Nu'aymah bata shigo ba shi yasa na ji bazan iya tsabbace kaina a gefe ba na shige cikin su ana tattaunawa akan abinda ya shafi karatu don karawa juna sani, motar Umar Farouk ta shigo ta yi parking adai-dai ƙofar department ɗin mu, wanda hakan yasa tun kafin ma ya ƙaraso mazan da muke zaune tare dasu duk suka tashi suka koma gefe, dariya matan dake wajen suka sa masu ni kuma na haɗe rai ina dafe goshi, don har ga Allah in nace na ji daɗin dawowar sa to nayi ƙarya, ta wani ɓangaren kuma tunanin ko don Nu'aymah da nake son samawa maslaha akan soyayyar ta dashi shigowar tasa zatayi amfani, kai tsaye wajen da muke zaune Umar Farouk ya nufo bayan fitowarsa daga cikin mota, ina wannan tunanin sai ji nayi suna gaishe sa haɗe da yi masa ya jiki?  Ina jin yadda idanuwansa ke yawo akaina amma ban damu da ɗago kaina na kallesa ba balle yasa ran zan gaishe sa, ganin nayi sun miƙe zasu bar wajen don haka nima na miƙe na bi bayan su, cikin sanyin murya na ji Umar Farouk ya kira sunana, "Amaah..." Sunan da shi kaɗai ne ke kirana dashi duk fadin duniya kuma idan ya kira ni da sunan sai na ji gabana yai wata irin faɗuwa, runtsu idanuwana nai ba tare dana tsaya ba na ji ya sake cewa "Don girman Allah da soyayyar da kike wa mahaifin ki ki tsaya". Tare da biyo ni a baya, ba don raina ya so ba na tsaya saboda girman Allah daya haɗa ni dashi da mahaifina daya ambata, zagayowa yai ya tsaya a gabana kaina na ƙasa ina sake haɗe rai, tsawon minti guda muka ɗauka a haka Umar Farouk ya kasa cewa uffan sai kallona kawai da yake yi wanda ina jin haka ajiki na, ganin bai da niyar cewa komai yasa na ɗago kai da niyar faɗa masa magana idanuwana suka sauka cikin nasa, innalillahi wainna ilaihirrajiun, na faɗa acikin raina gabana na faɗuwa ganin yadda ya ɗan rame ya kuma yi duhu tamkar ba shi ba tare da jin wani iri a zuciyata, duk da dama can shi ba fari bane tas amma ya sake yin duhu sosai, duka a cikin yan sakanni nayi masa wannan kallon, take sai naji zuciyata ta karye ina tabbatarwa da kaina cewa ban kyauta ba tunda saboda ni ya shiga wannan halin yai jinya har ta tsawon wata ɗaya amma ko sau daya ban je na duba sa ba  kuma ban yi masa sannu ba balle na tambayesa ya jikinsa, ko ba komai shi ɗin musulmi ne dake da haƙƙi akaina daya kamata idan yai rashin lafiya na duba sa, sake ɗago kai nai muka sake haɗa ido, murmushi ya sakar mini a wannan karon kafin yace...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

Masu son Vip sai ku bibiyi Arewabook @billysfari ta wannan link https://www.arewabooks.com/chapter?id=6894e7bd8ebf53d524760d91

                            45.

"Kiyi hakuri Amaahh na tsaida ke, na san na yi miki abubuwan da basu dace ba, amma ki yarda ni ɗan adam ne ina kuskure don Allah ki yafe mini, na sani yanzu haka kina jin ina takura ki sosai shiyasa har kikai blocking ɗin layoyana, na ji ba daɗi na ji zafi a zuciya ta sosai amma ya zan yi? Ni ne na jawa kaina da kaina watakil da baki tsaneni ba kuma baki yimun hakan ba, shi yasa duk abinda zaki yi mini bazan iya fushi dake ba saboda Allah ya riga ya ɗora mini cutar son ki saboda haka dole nayi hakuri, pls Amaahh don Allah ki bani damar gyara kura-kurai na wallahi ina sanki". Ƙasa nai da kaina don yanzu ban san kuma me zan faɗa masa ba, Allah ma muna yiwa laifi ya yafe mana balle mu daya halitta, Allah ya sani har yanzu ina jin zafin abubuwan da yai mun acikin zuciyata idan na kallesa, zan iya hakuri na yafe masa amma bazan iya karɓar soyayyar sa ba, har ga Allah bazan iya soyayya dashi ba don bana sonsa. Ina son na samu damar fahimtar dashi komai akan soyayya ta da shi ba abu bane mai yiyuwa kuma na fahimtar dashi soyayyar da Nu'aymah ke yi masa zai fi dacewa ya koma gareta, na sani idan har ni ban bashi damar saurarar sa ba to shima bazai saurareni ba, don haka na dago kai na ce, "Shikennan ka ɗauka wannan zancen ya wuce na yafe maka, Allah ya ƙara sauki". Wani irin murmushi Umar Farouk ya saki ni kuma na raɓa ta gefensa na wuce wani ɓangare na zuciyata na faɗa mini cewa nayi abinda ya dace yayin da wani ɓangaren kuma ke nuna mini nayi kuskure, koma dai meye yakamata ace na sama ma kaina lafiya agun shi haka itama Nu'aymah na sama mata mafita.

Fuskar Umar Farouk kuwa tamkar an yi masa wahayi mai daɗi saboda farin cikin daya tsinci kansa aciki, dama ita magana mai daɗi sadaka ce, duk da Janaam bata nuna masa ta karɓi soyayyarsa ba hakan kaɗai data faɗa nan take ya ji ya rage masa kaso sittin bisa ɗari na damuwar sa, yau ne karo na farko da lafuzza masu daɗi suka taɓa fitowa daga bakin ta a kansa da bazai taɓa mantawa ba, hakan ya sa ya tsinci kansa cikin tsantsar farinciki marar misaltuwa da har ya kasa iya ɓoye hakan a fuskar sa ya kuma ji cewa tabbas yau rana ce mai muhimmanci a wajen sa da zai iya kira da ranar alkhairi, juyowar da zai yi kenan yaga Nu'aymah tsaye tana kallonsa, tun farkon tsayuwar sa da Janaam ta iso wajen idanuwanta na akansu har tayi parking ɗin motar ta fito, duk abinda ya faru tsakanin su akan idanuwanta kawai abinda suke faɗa ne bata iya jiyo su ba, murmushin da taga yai shiya tabbatar mata da Janaam ta gama cin amanar ta haɗe da jin wani irin zafin da kishinta a ƙasan zuciyarta, take ta ji wasu ƙwalla sun zubo mata a idanuwa, tana ganin Umar Farouk ya nufo wajen ta tayi saurin sa bayan hannu ta goge tana kauda kanta tamkar bata gane sa ba tabar wajen, Jikinsa ne yai sanyi ya ɗan shafa ƙeyar kansa yana jin wani iri kafin shima ya nufi cikin aji, nan ma gaishesa colleague ɗinsa suka shiga yi suna yi masa ya jiki yana amsa masu da ya ji sauki tamkar ba shi ba, wajen zaman sa ya nufa idanuwan sa na akan Janaam yana kallon duk wani motsi nata haɗe dayin murmushi, a haka malamin da zai yi masu c.a ya shigo wanda hakan yasa kowa yin natsuwa cikin ajin, ko mintuna goma ba'a yi da farawa ba Umar Farouk ya gama, gefen da Janaam take ya kalla hankalinta na wajen amsa tambayoyin dake gabanta wanda hakan yai masa daɗi kafin ya sauke idanuwansa akan Nu'aymah da seat ɗinta ke gaban tashi, zaune take takardar dake gabanta bata rubuta komai ba sai ma kifa kanta da tayi akan desk ɗin, kai ya girgiza haɗe da kallon malamin dake can bakin ƙofa yana amsa waya ya taso ya dauki takardar, ɗago kai Nu'aymah tayi bai kalleta ba ya je ya rubuta mata amsa, sai daya gama da zai yi submitting ɗin tasa ya je ya ajiye mata tata ba tare daya damu da malamin zai gansa ko bazai gansa ba, da idanuwa Nu'aymah ta bishi har ya je ya yi submitting ɗin tasa takardar ya fita, takardar gabanta ta kalla da gaba-daya ya rubuce mata amsa suna kaɗai zata rubuta ta ji kamar ta yage takardar saboda haushin sa da take ji, sai dai bazata iya ba saboda ba abinda ta karanta jiya, asali ma damuwa bata barta ta iya fahimtar komai ba lokacin da ta zo yin karatu, tana nan zaune tana faman karatun wasikar jaki har kusan kowa yai submitting

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login