Showing 57001 words to 60000 words out of 157423 words
yadda hawaye ke tsere akan fuskata haɗe da cewa. "Ikon Allah! Daga magana sai kuka? Ke baki san wasa bane da zaki faɗa mana hakan saboda shashanci? Idan ma nakin ne Jamil bai isa ya samo miki mijin da zaki aura ba ne sai wanda kika zaɓa?" "A'a Mamah ƙyaleta, da gaskiyarta fa taya rana ɗaya kwatsam za'a ce mata haka ta kasa shiga damuwa bayan tasan ni da kaina na hanata sauraren kowa, na kuma hanata tsaida miji har sai ta kammala karatun ta saboda ta samu cikakkiyar natsuwa har ta gama". Kusa dani ya zo ya zauna yana murmushi tare da riƙo kafaɗuna ya ce, "Autah ki kwantar da hankalinki wasa nake yi miki, in sha Allah baza mu taɓa yi miki auren dole ba sai wanda zuciyarki ke so kuma kika kawo mana shi, wuɗannan kayan na Auntynki ne dasu baffa zasu je su kai na jin magana da yarinyar da nake so, shine nafara kawowa Mamah ta gani ta sa albarka". Na ɗago kai ina kallon sa ya jinjina mini kai alamun tabbatarwa, ban san lokacin da murmushi ya kince mini ba na rungumesa ina faɗin, "Kai Ya Jamil wace mai sa'ar ce tayi nasarar yi mana wuff da kai, amma shi ne ko ka faɗa mun ka haɗani da ita mu riƙa gaisawa". Na faɗa ina sakin sa tare da ɗagowa cike da wata sabuwar rigimar ina turo baki, karan hancina Ya Jamil ya ja yana faɗin, "Ho.ho..ho Janaam ba dai rigima ba, yanzu kuma nayi laifi don ban faɗa miki ba?". Na ɗaga masa kai ya ce, "To shikenan yi hakuri tunda gashi yanzu na goge laifina na faɗa miki, in sha Allah kuma yau ba gobe ba zan haɗaki da ita". "In dai sakalcin Janaam zaka biyewa to zaku kai dare ne tana yi maka ƙorafi, ƙara tun wuri ka tashi kaje ka ɗauko su baffan naka su tafi yamma na sake yi". Mamah ta faɗa tare da barin wajen, na kalli Ya Jamil na ce, "Ya Jamil Allah ya sanya alkhairi, bari naje gun Mamah na san haushina take ji". "Maza ki je ki wanke laifin da kika yi nima bari na tafi nayi yadda tace." "Adawo lafiya Yaya". Na faɗa haɗe da miƙewa ganin yabar wajen nima na nufi ɗakin Mamah, a yadda nasan halin Mamah tabbas yau zan sha fama, ba abinda ta tsana irin taga kukan ɗaya daga cikin mu ni da Ya Jamil, hakan na hurting ɗinta sosai, Ni kuma a yadda na ji zuciyata na ƙokarin tarwatsewa ɗazun jin za'a saka katanga tsakanina da Ya Aym bazan iya jurewa ba sai na zubar da ƙwalla, da wannan tunanin na ƙarasa ɗakin Mamah, tana jin shigowa ta amma ko kallona bata yi ba taci gaba da abinda take yi, sai da nayi da gaske sannan na samu ta kulani tana cewa, "Janam bana so ki sabawa rayuwar ki cewa dole sai abinda kike so ni ko yayanki zamu yi miki, ki tuna cewa amana kuke a hannuna haka kema amana kike ga yayanki, dole duk abinda zamu yi mu tabbatar cewa mun kula da wannan amanar taki daga ni har shi saboda babu wanda zai yimiki abu don ya cutar dake, don Allah don annabi Janaam ko da Yayanki zai yi miki makamancin abinda ya gwada yimiki wasa dashi yau kada ki bijire masa, hakan zai haifar mani da tashin hankali da damuwa musamman da na san halin Yayanki da kafiya akan duk abinda zai faɗa ko kuma yi". Tausayin Mamah ne ya rufe ni sanin cewa har yanzu bata dena alhinin rashin mahaifin mu ba, mu kadai ne take kallo ta ji zuciyarta ta rage mata raɗaɗin mutuwarsa shiyasa bata son ganin damuwar mu ko kaɗan kamar dai yadda ta sha faɗa mana hakan akoda yaushe. Hannuwan ta na riƙo haɗe da cewa, "Kiyi hakuri Mamah in Sha Allah hakan baza ta sake faruwa ba, na kuma yi muki alƙawari duk rintsi zaku sameni mai yin biyayya a gare ku keda Ya Jamil, kiyi mini addu'a Allah yasa na kammala karatu na lafiya kuma na kawo mijin da zan aura da kaina ba tare da an zaɓo mini ba". Na ƙare zancen cikin jin kunya ina noce kaina ƙasa." Dungure mini kai Mamah tayi tana dariya haɗe da cewa, "Ja'ira Allah dai ya shirya mini ke ya baki wanda zaki so kuyi ingantacciyar rayuwa dashi cikin kwanciyar hankali da kaunar juna ba tare da fitina ba, wani lokacin idan kika yi wani abun sai naga kamar an yi mini musanya ba Janaam ɗina ba ce". Nayi saurin fadawa a jikinta ina ɓoye fuskata cike da tsananin soyayya marar misaltuwa agareta.
ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
33.
Sanin gobe ina da school yasa tunda asuba na tashi nayi ayukkan dana dana yi har breakfast sai dana ɗora sannan na koma ɗakina na shiga wanka, ganin akwai sauran lokaci kuma yauce ranar farko da zamu koma ba lallai ne ayi karatu ba ya sa na yi shiri na a natse, ɗaya daga cikin abayoyin da Ya Aym ya aiko mini dasu na ɗauko na saka na yi rolling kaina da mayafinta, ya subhanallah! Ko ni dana kalli kaina a madubi sai dana yaba irin kyan da nayi musamman da naga abayar mai yalwace bata kama mini jiki ba, ban fiye amfani da abaya kai tsaye idan zan fita ba amma soyayyar da nake yiwa ya Nu'aym ta kwaɗaitar dani da yin hakan yau musamman da abayar ta kasance fara gashi ina son farin abu, kai tsaye ma zan iya cewa is my Best colour, sake kallon kaina nayi a madubi na sake godewa Allah daya tsara mini halittata ya kuma kyautata sura ta, wayata na ɗauko na ɗauki hotuna a gaban mirror da nake tsaye Sannan na ɗauko niƙab ɗina na ɗaura na saka flat shoes ɗina farare dake ajiye a inda nake jere takalma na sannan na ɗauki handbag ɗita na fice ina fitar da wani sanyayyen ƙamshi na ɗaya daga cikin turarukkan da Ya Aym ya hado mini dasu. Ko dana fito falo na samu har Mamah ta ƙarasa kammala breakfast ɗin dana ɗora ta jere akan dining, Ya Jamil na tadda zaune cikin shirinsa shima yana taking breakfast da alama yau fitar sassafe zai yi, kujerar dake kallonsa na ja na zauna ina faɗin, "Good morning Ya Jamil". "Morning Autah kin tashi Lafiya?" "Lafiya ƙalau". Na faɗa ina janyo flaks ɗin ruwan tea na buɗe na tsiyaya a cup na haɗa tea ina juyawa a hankali saboda zafin sa ya fita, Muryar Ya Jamil na ji yana cewa, "A ina kika samu wuɗannan kayan Autah? Sun matukar yi miki kyau sosai". Ya ƙare zancen yana kallona, dariya na saki cike da jin daɗi ina cewa, "Da gaske Ya Jameel? Nu'aymah ce ta kawo mini tsaraba da suka dawo". Ga mamaki na sai naga bai ce komai ba ya ci gaba da breakfast ɗin sa, jikina ne yai sanyi ganin hakan tare da ɗaukar cup ɗin tea ɗin dana haɗa na soma sipping a hankali don har yanzu zafinsa bai fita ba, na rasa me yasa Ya Jamil baya son yan gidan su Nu'aymah ko kuma zancen su duk da tarin soyayyar da suke nuna mini, har ya kammala taking breakfast ɗinsa bai sake cewa komai ba sai ma miƙewa da yai, adai-dai lokacin Mamah ta fito na ɗago kai ina kallon ta na ce, "Mamah barka da safiya, ina kwana?" "Lafiya ƙalau Janaam, har kin fito kema?" "Eh" na bata amsa ina ture sauran tea ɗin dake gabana haɗe da miƙewa na ƙaraso inda suke tsaye suna magana, sai da suka gama sannan Mamah ta juyo ta kalleni tana cewa, "Masha Allah Autah rigar nan yadda kika san don ke aka yi ta, ta yi miki kyau sosai, ka ga Nu'aymah ce ta kawo mata tsaraba da suka dawo u.k". Mamah ta ƙare zancen tana faɗawa Ya Jamil, na ɗago kai ina kallon sa nima don in ji me zai ce "Ta gode". Ya faɗa haɗe da juyawa zai ficewa Mamah ta ce, "Ba tare zaku je ba ka ajiye ta?" "No Mamah taje ta ajiye ta". "Wa kenan?" Mamah ta faɗa tana ɗan haɗe rai, Ya Jamil ya ce, "Wacce ta je rokon kaya awajenta mana". Sinne kai na ƙasa nayi jin yadda hawaye suka cika mini ido akan maganar da Ya Jamil ya furta, Mamah kuwa cewa ta yi, "Ka ga Jamil wannan abun naka yai yawa, menene tsakaninka da bayin Allah nan daka ɗauki tsanar duniya ka ɗora akansu, ina laifin wanda ya so naka fisabilillahi? Kana tunanin ni zan bar Janaam tayi wani makamancin abinda kake cewa tayi ba tare dana tsawatar mata ba?". Ganin yadda ran Mamah ya ɓaci ya sashi tausasa murya haɗe da cewa, "Mamah ni fa wulaƙanci nake guje mata kinsan halin..." Kafin ya ƙarasa ta dakatar da shi ta hanyar cewa, "Bana son jin wannan zancen Jamil ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, ya kamata ka sassauta wa kanka wannan kiyayyar da kake yi masu kar ta koma hasada, ita kuma hasada da kake gani lalata al-amurra take yi". Shiru Ya Jamil yai da alama zantukan Mamah ne suka dakar masa zuciya musamman kalaman ƙarshe, jiki a sanyaye yace, "Kiyi hakuri Mamah hakan baza ta sake faruwa ba, in sha Allah ba su ba kowa ma bazan bari hasada ta shiga zuciyata tsakani na dashi ba". Ya ƙare zancen tare da juyawa ya fice, saurin juyawa nai da gudu zan koma ɗakina da niyar cire kayan na sauya wasu Mamah ta dakatar dani tana cewa, "Ina zaki je?" "Zan cire kayan ne na sauya tunda baya so". "Bana son shashanci zaki zo ki wuce ne ko sai na saɓa miji kema." ba ni da zaɓin da ya wuce nayi abinda ta ce don haka na juyo ba tare dana bari taga kukan da nake yi ba ina cewa, "Na tafi". Ta amsa mini da "A dawo lafiya". Tana barin wajen ni kuma na fice na samesa a mota yana jirana, gaba na buɗe na shiga na zauna ya tayar da motar ya fice daga gidan, sai daya tsaya ya fita ya rufe gate sannan ya dawo ya tayar muka tafi, har muka kusa isa school ɗin mu ya Jamil bai ce komai ba haka bai kalli inda nike ba, wasu hawaye na ji sun sake cika mini idanuwa haɗe da yin nasarar saukowa akan fuskata, a hankali na juyo ina kallon sa da gaske fushi yake yi kuma nice silar hakan abinda bai taɓa faruwa tsakanina da shi ba tun ina ƙarama, na ce "Ya Jamil don Allah kayi hakuri, tunda baka son alaƙata dasu nayi maka alkawari daga yau bazan sake ba, kayan ma data bani idan na koma gida zan maida mata dasu". Na ƙare zancen ina fashewa da wani irin kuka, juyowa yai ya kalleni kafin yaci gaba da tukinsa har muka iso school, sai daya kawo ni bakin department ɗin mu sannan ya yi parking tare da kallona yace, "Ya isa haka kidena kukan komai ya wuce, dama ina yin magana ne saboda ki rage shigewa jikinsu amma na fahimci Mamah bata fahimci me nake nufi ba shi yasa har ta kwatanta hakan da nake yi da hasada, amma in Sha Allah daga yau bazan sake cewa komai ba akan alakar ki da su saboda kaucewa ɓacin ranta, kawai abinda zan ce ki kula don mutunci yafi kuɗi". So nake na fahimtar dashi ko wacece Nu'aymah amma sanin ba lallai ne ya fahimta ba a yanzu ko nayi masa bayani yasa na kama baki na nayi shiru har ya gama magana, cikin dasasshiyar muryar dana sha kuka na ce, "Kayi hakuri kuma in sha Allah zan kula kamar yadda ka ce". "To shikennan amma kidena kukan haka kin ji". Na ɗaga masa kai alamar amsawa, murmushi ya saki haɗe da ciro kuɗi ya bani yana cewa, "Ga wannan ki ci abinci ki yi transport idan an tashi ko da yake kawai ki kirani na ɗauke ki kar laifina ya ƙaru gun Mamah nasaka mata Autah kuka da nayi". Murmushi na saki ina rufe fuskata cike da jin kunya kafin na karɓi kuɗin ina yi masa godiya, jin yace ya makara wajen aiki ya sa na bude marfin motar na fita na rufe masa ina cewa, "Allah ya tsare ya kaika lafiya". Tare da ɗaga masa hannu, shima ya ɗago mini yana murmushi sannan ya tada motar ya juya yabar wajen.
Duk wannan abun dake faruwa ashe akan idanuwan Umar Farouk dake zaune shi da Nu'aymah akan steps ɗin da za'a taka a shiga department ɗin na mu, don haka ina nufo wajen naga ya taso cikin ɓacin rai ya tare gabana.
Yau tunda sassafe yai wanka cikin wani irin madaukakin farin ciki ya shirya cikin ƙananan kaya tare da taje sumar kansa, wani irin lokaci ya dauka kafin ya gama tsara kansa yadda yake so saboda murnar haɗuwa da Janaam da zai yi, sosai shigarsa tayi kyau ta kuma fiddo masa da ainahin ƙwalisar da yake buƙata irin ta gayu da suka amsa sunan su, bai saka sarƙa ba yau amma ya laƙa yan kunnaye, ya kuma daura wata sarƙa a hannunsa, tsadaddun kaya ne ya saka da kana kallon sa kasan shi ɗin ɗan masu faɗa a jine saboda yadda ya fito cikakken gayensa, ko karyawa bai tsaya yi ba ya ɗauki key ɗin motar sa da wayoyinsa ya fice, a falo ya tadda Momy ya gaisheta, Dady na zaune saman dining yana latsar system ya karasa ya gaishesa shima, ɗago kai yai ya yi masa wani kallo tun daga sama har ƙasa kafin ya girgiza kai ya rufe system ɗin dake gabansa ya juyo yana kallonsa ya ce, "Yanzu wannan shigar da ita zaka fita school Umar Farouk sai kace ba ɗan musulmai ba, duba wannan wando na jikinka da wuɗannan yan kunnayen, meye amfanin saka su sai kace yan iskan mawaƙan nan da ake nunowa a tv". Umar Farouk bai ce komai ba sai ma haɗe rai da yai, yana ganin ya ƙure shiga da zai burge Janaam amma Dady ya zo yana yarfa shi, da Tauheeda na kusa shikenan sai yasa ta rena sha, jin maganganun da Dady keyi yasa Momy ta karaso wajen tana cewa, "Dady meye illar shigarsa? Yaran yanzu fa ba ɗai dana zamanin ku ba don Allah ka barshi ya je kar ya makara". Ta ƙare zancen tana shafa bayan Umar Farouk ɗin haɗe da cewa, "Maza jeka Allah ya tsare ya bada Sa'a". Ta faɗa tana bi bayansa ta rakasa har ya fice part ɗin sannan ta dawo ta samu har Dady yabar falon da alama ransa ya ɓaci da abinda tayi, koma dai meye ƙara hakan, ta faɗa cikin zuciyarta tana komawa kitchen don bata kammala abun karyawa ba shi yasa ma bata tsaida Umar Farouk ba yaci nasa kafin yatafi, Umar Farouk kuwa ko daya shigo School bai tadda kowa ba sai Nu'aymah da itama ta kwana da ɗokin ganinsa, sai kuma wasu yan tsirarun ɗalibai dake yawo a farfajiyar makarantar, cike da farin ciki Nu'aymah na ganinsa ta fito daga cikin motar ta tana zuba wani irin sanyayyen ƙamshi tana kallon yadda yake fitowa acikin motar...
ALLAH KA JIKAN IYAYENMU 👏
[10/10, 1:04 PM] ummul Husnah 2: *IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9
34.
Wajensa ta nufa yana tsaye jikin motar sa yana latsar waya tayi sallama haɗe da cewa, "Welcome back Umar Farouk, Good morning". Umar Farouk ya ɗago kai fuskarsa ba yabo ba fallasa don har lokacin akwai sauran ɓacin ran da Dady ya sa masa, "Wow thank you friendy ya kike?" Nu'aymah ta saki murmushi tana rausayar da kanta ta ce, "Am fine friendy sai dai nayi kewar School sosai ciki har da kai shi yasa nazo very early". "Ni ma kusan hakan, ya akai ban ganki tare da ƙawarki ba". Ya faɗa cike da basarwa, Nu'aymah ta sake sakin murmushi haɗe da cewa, "Na tabbata itama tana nan ƙarasowa yanzu, You look so good friendy". "Thank you, ya ƙasar u.k?" "Akwai labarai sosai sai mun zauna". "Ok muje can a fara bani ɗaya labarin nasha". Umar Farouk ya faɗa yana nuna mata matattakalar shiga department ɗin nasu, tana dariya suka nufi wajen tana jin wani irin farin ciki a ranta, Zaune suke suna fira wacce yawanci Nu'aymah ce take yi masa shi kuma yana latsar wayar sa suka ga motar Ya Jamil daya kawo Janaam tayi parking gaban department ɗin na su, wanda hakan yasa Nu'aymah na hango su tace, "Yawwa ga yar halak din can Janaam ta ƙaraso". Da sauri ya fizgo kai yana sauke idanuwansa akan motar inda ya hango Janaam aciki duk da tana cikin nikab, yanayin yadda suke magana da Ya Jamil da murmushin da yaga ya yi mata da yadda ta rufe fuska da hhannuwan ta, kudin daya bata ta karɓa da ɗaga masa hannu da tayi ya mayar mata bayan fitowar ta a motar ba ƙaramin dakar masa zuciya yaji wani abu mai mugun raɗaɗi da zafi yai ba, take ya ji wani duhu ya mamaye masa gaba da ko gani baya yi, baisan lokacin da ɓacin rai ya sashi miƙewa ya nufi wajenta ba a lokacin da itama take nufowa wajen ba, cikin matsanancin kishin da shi kansa bai san yana da shi ba yana isa gabanta ya ce, "Wane ɗan iskan ne ya kawo ki?" Ba tare dana damu ba ina kallon sa cikin ɓacin rai ni ma na ce, "Kai ne dai ɗan iskan ba shi ba, kuma tun wuri ka ɗaga mini hanya na wuce". Umar Farouk da idanuwansa suka yi jajir ya kafeni da su yana sake matsowa kusa da ni ya ce, "Bazan ɗaga