Showing 138001 words to 141000 words out of 157423 words

Chapter 47 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

523

ba damuwa ki amsa mana wasu 'yan tambayoyi da muke son yi miki?" Irin kallon da Barrister Maryam kewa Janaam da Mamah ta zuba mata fura tana sha ya sanya hankalin Janaam ɗin ya soma tashi har tana kwarewa da furar da take sha ta shiga yin tari, da sauri Mamah ta karbi kofin furar ta miƙo mata gorar ruwa tana shafa bayanta a hankali, sai da ta gama shan ruwan tarin ya kwanta mata sannan Mamah ta dago ta kalli Momy ta ce, "Baiwar Allah ba wai ina so zan hanaku aikinku bane, amma don Allah da kuyi hakuri ku bari har wani lokacin daya dace tunda dai kunga halin da yarinyar nan take ciki ba wai ta warke bane har yanzu tana bukatar natsuwa sosai kafin ta iya amsa maku tambayoyin duk da kuke son yi mata amma don Allah ba yanzu ba". "Ba komai Mamah barta zan amsa mata". Janaam dake sauke lumfashi da ɗaɗɗaya ta faɗa ganin irin kallon da Momy ke yiwa mahaifiyar tata saboda gudun ta faɗa mata wata magana marasa daɗi, hakan yasa Momy kallon Janaam tace, "ƙara da kikai wannan tunanin saboda barin kashi ciki baya maganin yunwa". Ta ƙare zancen tare da fiddo wata ƙaramar takarda da biro sannan ta ɗago kai ta kalli Janaam tace, "Me ya kaiki gidan Dr. Abdullahi gwaram ranar sha tara ga watan bakwai wato watan daya gabata kenan?" "Na je gidan ne domin na biyawa ƙawata Nu'aymah mu tafi wajen bukin ƙarewar makarantar mu". Janaam taba Momy amsa da tunda ta fara magana idanuwanta ke a kanta ita kuma taki bari su haɗa ido, "Dama kunyi da ita zaku tafi tare ne duba da buki ne da kowa na zuwa tare da ahalinsa ko kuwa?" "Eh to kawai dai na biya mata ne saboda hakan zai sa mu Dan samu muyi magana akan wata matsala da muka samu da ita mu fahimci juna". "Wace irin matsala kenan?" Shiru Janaam tayi kamar bazata amsa ba sai kuma can tace, "wannan tsakanina da ita ne daya shafi rayuwar mu". "To da kika je baki iskota ba meya tsaida ki cikin gidan har aka zo aka aikata kisan a gaban idanuwanki?" "Ƙaddara amma a lokacin nayi ƙoƙarin guduwa nabar gidan don ko dana shiga ban san babu kowa aciki ba, da nasan abinda shiga ta gidan zai jawo mini wallahi da ban shiga ba...". Nan Janaam tafara sabbatu tana kuka wanda hakan yasa Mamah fita da sauri kiran likita don bata son abun ya zama tashin hankali tsakaninta da Momy, Barrister Nazir dake tsaye gefe ne ya ce, "ki natsu kiyi mana bayani kin shiga gidan kin tadda ba kowa sai mutum daya shine kika kashesa? Wane laifin yai miki da kika aikata hakan?" Toshe kunnuwa Janaam tayi da hannuwanta tana girgiza kai haɗe da sakin wata irin ƙara, wanda hakan yai dai-dai da shigowar nurse tare da Mamah tace, "Subhanallah me kukai mata haka ne? Akan me zaku zo ku takurawa patient din mu pls don Allah ku fita". Ta faɗa tare da riko Janaam dake faman ihu jikinta na wani irin ciccira saboda tsananin tsoro da tashin hankalin data shiga tunawa da abinda y faru tana kuka, "ku fita mana". Nurse ɗin ta faɗa a ɗan hasale Momy ta miƙe tana sauke ajiyar zuciya tare da barin ɗakin Barrister Nazir ya rufa mata baya, wata nurse ce ta shigo dauke da tray ta ajiye ta zuko ruwan allura a syringe ta yiwa Janaam, daya nurse ɗin dake rungume da ita na shafa mata baya a hankali da haka har tabar kukan bacci ya ɗauketa ta kwantar da ita haɗe da gyara mata kwanciyar ta tana cewa Mamah kar su kara bari wani yazo wajen ta da sunan yi mata tambayoyi, Mamah bata ce komai ba ta tsurawa Janaam kawai idanuwa cike da tausayi, tunda abun ya faru kullum cikin kuka take da tsorata ita ta rasa gane wannan al'amari yadda yake, wannan wace irin soyayya ce haka da bata amfani yarta da komai ba sai tashin hankali da masifa? itama Aunty Nidrah gefe ta koma tayi tagumi tana jin tsananin damuwa na halin da Janaam ke ciki, wanda in har ɗan uwan nata ne ya aikata hakan ya jefa yarinya a masifa ko kadan bai kyauta ba kuma wannan ba soyayya bace, ya kuma cutar da ita ba kaɗan ba.

Barrister Nazir bayan sun fito ya kalli Momy ya ce, "Yarinyar nan gaba daya a tsorace take, ta tsorata matuka akan kisan nan shiyasa har yau ta kasa dawowa hayyacinta balle ta samu natsuwar da zata iya yin bayanin abinda ya faru". "Ni kuma ba wannan na fahimta ba Barrister Nazir, na soma gano wani abun daban kuma yanzu da ka yi mata wannan tambayar a yanayin da take magana da sabbatu ta iya yiyuwa ita ta aikata kisan ko shakka bana yi, shi kuma da yake wawa ne soyayya ta rufe masa idanuwa ya mayar da kisan a kansa". Dariya Barrister Nazir yai haɗe da cewa, "No kada kiyi overthinking Barrister Maryam, ni fa nayi amfani da wannan maganar ne saboda hakan ya tsoratata ta faɗa mana ainahin gaskiya, amma taya ƙaramar yarinya kamar wannan zata iya aikata kisan kai? Wannan yanayin data shiga ba kowa za'a aikata kisan kai a gabansa bai shigesa ba Barrister Maryam musamman mace dake da rauni, macen ma ƙaramar yarinya". "Haka kake gani? Shikenan let see". Ta ƙare zancen tare da wucewa gaba ta shige motarta shima ya shiga tashi suka tayar suka bar wajen, a daren Momy batayi kwana ba musamman ta dauko ƙatuwar carbon papper ta kafe ta shiga rubuce rubuce da zane zane akai, bayan ta gama ta ji kanta na wani matsanancin ciwo saboda yadda ta dau zafi matuka wajen zurfafa tunaninta, toilet ta shiga tayo arwala tunawa da maganar Tauheeda,  "You should pray first Momy". Tana addu'a amma dole ta sake dagewa wajen rokon Allah ya taimaketa akan case ɗin nan don sarke-sarken dake cikinsa nada yawa dole sai an bi komai mataki mataki, sallolin nafila tayi ta kuma yi addu'o'i sosai kafin ta haye gado ta kwanta, nan ma tunani kin sakinta yai maganganun Janaam kadai ke dawo mata a kunnuwa, me hakan ke nufi idan bayan ta shiga gidan ta yi ƙoƙarin guduwa kamar yadda ta faɗa? daƙyar dai ta samu bacci ya ɗauketa ba tare data samu haɗa gamsasshin hujjojin da zasu tabbatar mata da zarginta akan Janaam ba.

Bayan kwana biyu Momy ta sake komawa asibiti, wannan karon ita kaɗai ta je kuma ta taki sa'a Janaam kadai ce zaune bisa gado ta miƙe ƙafafuwanta tana shan faten doya daya sha kifi da ganye sai ƙamshi ke tashi, ɗago kai Janaam tai tayi mata kallo ɗaya lokacin data ƙaraso wajen ta ɗauke kai, Momy ta ja kujera ta zauna ba tare da Janaam da gabanta ke wani irin faduwa ba ta kalleta ta gaida ita, Momy bata amsa ba sai kallon Janaam take yi tana sake nazarin ta, Mamah bata nan yanzu ta fita ta je pharmacy karbo wasu magunguna da aka rubuta, Aunty Nidrah kuma yau bata zo ba jikin ya ɗan motsa mata, kamar daga sama Janaam ta ji Momy tace, "Me yafaru acikin gidan da kika yi ƙoƙarin guduwa?" "Kisan kai". Janam ta faɗa kai tsaye, Momy ta ciri kai ta kalleta da kyau taga wannan karon babu alamun tsoro tare da ita, ta ce "kafin nan fa?" Janaam tayi shiru sai juya spoon ɗin hannunta takeyi tana ji tamkar ta zura da gudu saboda tashin hankalin da take ciki aduk lokacin da tayi ido biyu da Mommy, kawai dai dakewa takeyi don ba tada wani zaɓi sama da hakan, "shikenan mubar wancan zancen tunda bakya so, yanzu tsakanin ke da Umar Farouk waya aikata kisan? Ke ko kuma shi?" Da sauri Janaam ta ɗago kai tana kallon Momy, take idanuwanta suka cicciko da kwalla ta shiga motsa baki tana so tayi magana amma ta kasa, maganganun Umar Farouk ke dawo mata ta tabbata idan ta furta wani abun zai iya kasheta kamar yadda ya faɗa kuma ya kashe kansa, iska Momy ta fitar ta baki haɗe da cewa, "Ya kamata ki hutar da kowa ki buɗe baki kiyi magana ki fadawa kotu ke kika aikata kisan nan ba Umar Farouk ba, na fahimci cewa Umar Farouk na kokarin sadaukar da rayuwarsa ne saboda soyayyarki, yana ƙoƙarin kareki akan abinda bamu san dalilinki na aikatawa ba, idan kin so zaki iya faɗa mini abinda ya faru ni kuma nayi alkawarin zan taimakeki don na gama tabbatar da cewa ba shi yai wannan kisan ba ke ce, saboda haka idan kin shirya faɗa ina saurarenki". Janaam ta girgiza kai tace, "ban fahimceki ba me kike tunanin ya faru ne? Kamar ya ni na aikata kisan? Na rokeki don Allah ki tafi kibar nan wajen ki ƙyaleni naji da abinda nake ji". Janaam ta faɗa cikin wani ƙaraji tana fashewa da kuka, hakan yasa Momy ta mike tabar dakin tun kafin jami'an lafiya su zo suyi mata wulaƙanci, sosai mamakin Janam ke ƙara rufeta ta yadda take da karfin zuciya irin haka, wata irin tsanarta ta sake ji aranta don ta tsani makaryaci aduniya a muhallin da yasan gaskiya kuma ya boye hakan bayan ya san zai iya jefa mutane cikin matsala. Sai da Momy ta jima da fita Janaam ta sha kukanta har ta gaji sannan Mamah ta shigo, ashe dabata samu maganin a pharmacy ba sai ta wuce waje ta siyo sanin ana da bukatarsa a lokacin, ganin yadda ta isko Janaam yasa ta shiga yi mata faɗa akan yarda da ƙaddara da kuma hakuri idan musiba ta sameka tare da nuna mata kukanta bazai dawo da Nu'aym ba kuma bazai sauya komai ba, kawai tayi fatan Allah ya bata lafiya shi kuma Umar Farouk Allah yasa a yanke masa hukunci dai-dai da laifinsa, banda ajiyar zuciya babu abinda Janam keyi don bata fahimtar ma abinda Mamah ke faɗa har tayi fadanta ta gama..

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[10/4, 3:54 PM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            66.

A ranar da marece aka bawa su Janaam sallama Ya Jameel ya zo ya ɗauke su suka koma gida, shima a mota nasiha sosai ya yi ma Janaam akan ta amshi jarabawar data zo mata hannu biyu ta kuma tabbatar a zama na gaba tayi iya kokarinta na faɗawa kotu gaskiyar iya abinda ta sani a wuce wajen ta samu ta huta kowa ma ya huta "hmmm!" Kaɗai Mamah ta iya cewa don cike take da takaicin yar tata, gani take yi ko tausayin kanta bata ji halin data shiga da kwanakin da suka shafe a asibiti wajen kulawa da ita amma taki ta natsu ta dena wannan kukan da take yi da bazai yi mata maganin komai ba, hakan yasa take jin haushinta sosai saboda yadda ta iskota ɗazu tana faman darzar kuka, bayan sun iso gida Jameel ya shigo masu da kayan su ciki sannan ya zauna ya tambayi Mamah ko akwai abinda suke buƙata kafin ya wuce tace a'a, sallama ya yi masu sannan ya tafi ita kuma Mamah ta shiga toilet ta watso ruwa, itama Janaam ɗin toilet ta shiga ta watso ruwa, bayan ta fito ta ɗauki wata doguwar riga armless marasa nauyi ta saka tare da samun gefen katifar tata ta zauna ta buga uban tagumi, ganin tunanin babu abinda zai haifar mata sai tarin damuwa yasa ta jawo wayarta da sharabonta da ita tun ana gobe graduation ɗin su, kasancewar ta jima batayi amfani da ita ba yasa har charging ya ƙare sai ta jona ta a jikin charger dake liƙe a jikin socket ita kuma ta miƙe ta fito don fa sam bata jin daɗin jikinta ko kaɗan, ɗakin Mamah ta nufa tana shiryawa kenan ta shigo ta haye saman gadonta ta ja duvet ta lullube, Mamah na kallonta ta jikin madubi da har baza tayi magana ba sai kuma can ta juyo tana cewa da ita "menene? In jin ba jikin ba?" "A'a kawai bana son ji na ni kaɗai ne, Mamah kiyi hakuri pls kukan da nake yi shi ke zuwa da kansa ba yin kaina bane". Sai da Mamah ta sauke ajiyar zuciya sannan tace, "Duk da haka kiyi kokari ki rage, ina shiga cikin damuwa idan na ganeki a cikin wannan yanayin, kiyi ƙoƙari don Allah ki sassautawa rayuwarki, with time ko mai zai wuce kin ji ko?" "Zan yi hakan in sha Allah". Janam tafada tare da lumshe idanuwanta tamkar mai kokarin yin baccci ita kuma Mamah ta ɗan karasa shirinta ta fice zuwa kitchen domin tanadar masu abinda zasu ci. Janaam ta so zuwa ta bita ta dakatar da ita tana cewa, "Kwanta abunki ki huta kafin akira sallah, amma kiyi koƙari kibi da azkar ɗinki". "In Sha Allahu" Janaam ta faɗa tana sake gyara kwanciyarta.

Bayan anyi sallar magrib sun kammala Mamah ta zubowa Janaam abinci ta kawo mata tace ta tashi ta daure taci ko ta samu jikinta yai karfi yadda ya kamata sannan ta kamata ɗakin ta rufe, sai da Janam ta ciro wayar ta dake chargy ta kunna sannan ta jawo abincin ta soma ci.

Sakonnine suka fara sauka cikin wayar Janaam ta buɗe akwatin messages ɗinta ta soma karantawa, gaba-daya ana yi mata tambaya ne akan abinda ya shafi kisan kai da kowa ke tambayar wai da gaske ne Umar Farouk ya aikata hakan agabana? kanta ne ya fara juyawa saboda tarin tambayoyin sun yi yawa  barkatai da bata san ta ina zata fara bada amsarsu ba, hakan yasa ta mayar da wayar a jikin chargy ta ajiye, tunanin rayuwarta da Nu'aym ta shiga yi har ta gangaro zuwa lokacin da Umar Farouk ya fara furta mata kalmar so, wani abu mai daci ta ji ya taso mata azuciya har zuwa tsakiyar harshen ta, cike da damuwa ta kwantar da kanta a jikin katifarta hawaye na sauka a hankali, lallai bawa baya taɓa wuce kaddararsa ba don haka ba da gaba-daya ta goge wanzuwar wasu abubuwan a rayuwarta ciki har da Umar Farouk da kuma Ya Nu'aym wanda a dalilinsa duka ta shiga wannan tashin hankalin da rigimar da take ciki.

A ɓangaren Momy sosai ta ci gaba da tsananta bincikenta tunda ta fahimci tabbas Janaam ce ta aikata kisan don gano dalili da makasudin da yasa tayi hakan, kuma ba laifi tafara samun tsiraran hujjoji da zata riƙa don duk wani abu da inspector Ashir ke tattaunawa da Abba a wayarsa ana turo mata bayanan, sai dai har yau takasa gano inda suka nufa domin ko inspector Ashir ya yi kokarin sakin layi Abba na saurin dakatar dashi, hakan yasa suka bata tazarar da har yanzu ta kasa gano abubuwan da suke kullawa, abu ɗaya ta fahimta akwai wasu ƙulle-ƙullen da Dr Abdullahi gwaram ke shiryawa kuma tabbas zata bibiyesa ta kuma bi diddiginsa har sai ta gano ko meye don tabbas suna da alaƙa da shari'ar da suke yi, kwana huɗu da sallamar Janaam ana saura kwana uku a koma kotu Momy ta shirya ta nufi gidan su Janaam don ta fahimci Janaam nada wani irin taurin kan da duk abinda za'a yi bazata fadi gaskiyar abinda ya faru a shari'ar nan ba saboda ba tada gaskiya itama, sannan a halin yanzu ita kadai ce zata bayyana agaban kotu ta wanke ɗanta daga zargin kisan da ake yi masa, dole ta zauna da ita a karo na farko ta roketa ko hakan zai sa jibi idan aka koma kotu ta fadi gaskiyar abinda ya faru, a ɓangare ɗaya tuni suka fara binciken yadda akai da gawar Nu'aym bayan mutuwarsa, wanda Barrister Nazir ne ya ɗauki ɓangaren kuma cikin nasara yafara gano bakin zaren, wanda hakan ya matuƙar tayarwa da Dr. Abdullahi gwaram hankali ya shiga bibiyar duk wasu hujjoji da zasu iya samu yana goge su.

Momy na isa a bakin ƙofar gidan tayi parking ta samu yaro ta tura ciki tace ace Barrister Maryam na sallama da mahaifiyar Janaam, ba'a jima ba yaron ya dawo yace, "Wai ance ki shiga daga ciki". Godiya tayi masa sannan ta fito daga cikin motar ta mayar da marfin ta rufe, tsaye tayi tana ƙarewa anguwar kallo cikin doguwar riga abaya baƙa ta saka glass baki daya kusa rufe mata rabin fuska kanta kuma na yane da mayafin doguwar rigar dake jikinta, tayi matukar kyau da kuma kwarjinin da kallo ɗaya zaka yi mata kasan babu wasa a fuskarta don bada ita tazo ba, su Mamah na zaune a falo suna gyaran alayyahu Barrister Maryam tayi sallama, Mamah bata ɗago kai ta kalleta ba ta amsa sallamar tana cewa Janaam dake zaune gabanta, "tashi ki kawo mata ruwa". Kamar Momy zata ce a'a sai kuma tayi shiru tuna cewa yau a matsayin uwa ta zo gare su ba'a matsayin lauya dake kare wanda ake zargi ba, Muryar Mamah ta ji na fadin "Bisimillah ƙaraso daga ciki ga waje nan ki zauna". Jiki a sanyaye Mamah taƙaraso ta zauna haɗe da cewa, "Barka da rana ina wuni?" "Lafiya ƙalau". Mamah ta faɗa tare da ɗago kanta ba, hakan yasa Momy ta zare glass ɗin idon ta haɗe da cewa, "ina fatar kin waye ni". "Kwarai da gaske, da fatan ba wata matsalar bace kika sake zowa yaran nan da ita?" "Eh to kin san indai aka ce bincike baza'a rasa matsala ba ko kaɗan ce, na zo ne na roƙi wata alfarma da ita kadai ce zata iya yimini ita a yanzu ba nazo don na tayar mata da hankali ba don na hango a shirye kike da kiyi komai akan yar ki don hana faruwar matsalar da kike guje mata, kesan da ɗa uwa sai Allah kuma hakan ya dace kowace uwa tayi akan ɗanta". Ajiyar zuciya Mamah ta sauke don ta fahimci magana ce Momy ke son sakar mata, sai dai a yadda ta ganta yau ba alamar jiji da kai atare da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login