Showing 96001 words to 99000 words out of 157423 words

Chapter 33 - Ido A Duhu Book One Complete Hausa Novel

25 Oct 2025

525

"ka dubo ko waye?" Ya kalli Nidrah da kanta ke ƙasa tana latsar wayarta ya ce, "Baby wai kin san ko waye?" Ta girgiza kai tana kallon sa ya ce, "Umar Farouk ne fa". Kallona Aunty Nidrah tai cikin tashin hankali nima ita nake kallo kafin tace, "Umar Farouk kuma?" Ya Jameel ya amsa mata da "Eh shine". Ba tare daya lura da shock ɗin data shiga ba, idanuwa na shiga ƙyakkyaftawa sai ga hawaye, ban san lokacin dana fara buga ƙafa ina cewa, "Ni bana son sa wallahi ina da wanda nake so kawai yai tafiyarsa". Da mamaki Ya Jameel ke kallona jin abinda na faɗa kafin ya sauke idanuwansa akan Mamah dake cewa, "Wai waye wannan Umar Farouk ɗin? Dama duk kun san shi ne?" Ajiyar zuciya Ya Jameel ya sauke haɗe da cewa, "Eh Mamah ɗan uwan Nidrah ne da mahaifiyarsa da mahaifinta uwa ɗaya uba ɗaya". "Toh ikon Allah kace na gida ne, tashi ki je kafin na saɓa maki a ina kika ga wanda kike son banda shashanci ke da yayanki ya hanaki saurarar kowa, zaki tashi ki tafi ko sai na saɓa miki". Ina kuka na mike na shiga ɗaki na sako hijabi na, ko minti biyar banyi da fita ba na dawo don ina zuwa ya kalli yanayin dana fito ciki dashi yai murmushi haɗe da cewa, "Bazan yi fira da matata ba fuskarta na a haka dama zuwa nayi in fara tabbatar miki da alkawari na kuma na duba lafiyarki, alhamdulillah na ganki na kuma ga Ya Jameel, abu daya ya rage shi ne ki bani dama mu fahimci juna.." ban bari ya karasa ba kawai na yi tahowa ta don tsabar takaici, da kallo duka suka bi ni Mamah sai zabgar faɗa take yi dani ban ce uffan ba na shige daki abina tare da fadawa kan katifata na jawo wayata ina sake gwada kiran ya Nu'aym don na dena ɗaukar Umar Farouk a cikin mutane masu hankali balle har na bari matsalarsa ta ci-gaba da sa mini damuwa , cillar da wayar nayi gefe ganin nayi kira har na gaji bata shiga ba, ga Nu'aymah da nake tunanin ta hanyarta kaɗai ce zan iya samun labarin ya Nu'aym bana samunta a waya itama, gaba-daya komai ya kwaɓe mini na rasa tudun dafawa saboda ya Nu'aym ya riga ya lalata ni da ƙaunar sa da a kullum nake ji a raina idan ba dashi ba bazan taɓa iya rayuwa ba...

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/20, 6:08 PM] Jiddah Aliyu: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

Masu son Vip ku bibiyi arewabook@billysfari ta wannan link https://www.arewabooks.com/chapter?id=689b69e619700231f1502019

                            54.

Wasa-wasa rashin ji daga wajen sa yasa ƙunci da damuwa suka yi mini ƙawanya na rasa abinda ke yi mini daɗi don kuwa kusan kwana biyar ba batu ba labarin sa tamkar bamu taɓa rayuwa dashi ba, gashi gobe ake bukin graduation ɗin mu ɗaya alkawarta mini cewa zai zo, a ɓangare ɗaya Umar Farouk ya nace mini don kusan kullum sai ya zo, har wajen Mamah ya shiga suka gaisa da ita, a yadda ya sauya yake yin shigar mutunci da kamala ba Mamah kaɗai ba kowa ma zai yi sha'awarsa, ta haka ya samu karbuwa a wajenta Ya Jameel kuma dama can suna gaisuwar mutunci dashi a yadda na ji yana faɗa, duk yadda ake zancen rashin kirkinsa yace shi bai taɓa yi masa ba kuma bai taɓa gani yai wa wani ba amma duk da hakan bazai takura ni ba sai na so shi in har bana son sa, Mamah kaɗai ce kullum ke ƙwoƙarin nuna mini kirkin Umar Farouk amma fir na nuna mata ni fa bana son sa, washe garin ranar da za'a yi graduation din mu na ji bazan iya cigaba da jurewa ba, atleast ya kamata nasan halin da ya Nu'aym ke ciki mu kuma fahimci juna ni da Nu'aymah ko da wajen taron nan ne agan mu atare, masu tunanin namiji ya raba mu ni da ita mu basu kunya, sai da nayi wanka na shirya sannan na fadawa Mamah na tafi amma zan fara biya wa gidan su Nu'aymah kwana biyu na dena jinta bamu haɗu ba, don ko da wasa ban taɓa sanar da ita abinda ke faruwa tsakanina da Nu'aymah ba, addu'a Mamah ta yi mini a sauka lafiya don ita sai daga baya zasu je tare da Ya Jameel, gabana na faɗuwa na nufi gidan su Nu'aymah, ban tadda mai gadi ba abakin gate don haka kai tsaye sai na nufi cikin gidan tunda ba bakuwar zuwa nike ba na wuce ciki har palorn ƙasa ina sallama, na fi minti biyar a tsaye amma ban ji an amsa min ba kuma ban ji motsin kowa ba, hakan yasa ni juyowa da sauri da niyar fita ina tunanin ko sun riga har sun tafi tunda da karfe tara za'a fara gashi ko dana fito gida karfe tara saura kwata, juyowar da zanyi kawai naga mutum a tsaye ya bani baya naji gabana yai wata irin faɗuwa, yana juyowa naga ashe Ya Nu'aym ne yasa hannuwan sa cikin aljihu, kallona yake yi tun daga sama har ƙasa yayin da wani irin farin ciki ya rufeni na kasa sanin me zanyi sai murmushi kawai nake sakar masa ina ji tamkar na rungumesa tsabar farin cikin dana tsinci kaina a ciki, ashe ban sani ba wannan kallon da wannan ganin dana yi masa cike da sa ran cewa ya zo ne don cika alkawarin da yai mini tare da cika mana burinmu shi ne na karshe, muna tsaye sai ganin Umar Farouk mu kayi ya shigo gidan riƙe da wuƙa suka dinga kokuwa ina ihun neman taimako amma kafin a shigo har ya yi nasarar sokawa ya Nu'aym ita sai gani nayi ya faɗi ƙasa, kafin kace me kawai na ga jini yana malala ashe ya kashe shi...

*Back to story*

Kuka ne mai karfi yaci ƙarfin Janaam ta faɗa jikin Mamah tana yi, Mamah da ya Jameel suka dauki sallallami Mahmah na cewa, "Amma wannan yaro ya cuce mu ya ci amanar mu, ina ganinsa da siffar mutanen kirki ashe ban sani ba makashi ne shi, saboda soyayya idanuwanka su rufe ka kashe dan uwanka Musulmi har cikin gidansa wannan wace irin masifa ce haka?" Ta ƙare zancen tare da fashewa da kuka itama, Ya Jameel ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "wallahi Mahmah a iya sanina Umar Farouk yana da kirki ban taɓa yadda tsagerancinsa da ake magana ba ya kai zai iya kashe mutum sai yanzu, to yanzu meye ribarsa da yai hakan fisabilillahi?" cikin kuka nace, "hatta Ya Salis shi yasa akayi masa wannan dukan a lokacin da kasa ya kaini gidan su Aunty Nidrah, haka ma saurayin da aka yiwa duka ranar dinner din ku shine yai masa saboda dai ya ganni tare dashi, ya Nu'aym ko ban san ya akai yasan alakata dashi ba, ban san waya faɗa masa muna soyayya ba daya kashesa". "Tirƙashi! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yanzu Janaam tuntuni duk kin san da wannan zancen kika ja bakinki kika yi shiru? kina rayuwa da mutumen banza ɗan daba baza ki faɗa ba a shiga tsakaninki dashi? To menene amfanin mu a raye ni da yayanki idan har zaki shiga matsala irin wannan ki ɓoye mana, wannan irin damuwa da tashin hankali har ina?". Mahmah ta faɗa cike da takaicin abun tana ganin koma meye hadda laifin yar tata da bata faɗa ba, watakil da ta faɗa da duk hakan bata faru ba, cikin kuka nace, "Ya zanyi Mamah, na riga na saɓawa umurnin Ya Jameel na fara soyayya da yayan Nu'aymah, tsoron kar naje bayyana damuwata ya gano ina tare da ya Nu'aym ko ina saurarar shi Umar Farouk ɗin yasa na kasa faɗa maku, sau da dama idan Aunty Nidrah ta ce na sanar da Ya Jameel nakan samu kwarin guiwar yin hakan, amma dana tunkaresa da zancen sai naji kamar zan kashe masa mafarkin da yake da shi a akaina ne". Ya Jameel kasa cewa komai ya yi don ya fahimci shima yana da laifi a wannan damuwar, sai dai duk da haka shurun nata ya yi yawa da har zata iya ɓoye irin wannan al'amarin mai girma. "Dama Nidrah tasan da wannan zancen". Ya faɗa cike da damuwa, Mamah ce ta sake cewa, "wallahi Jameel da nadan hakan zata faru da ni kaina ban saki jiki da yaron nan ba, kuma jin da nayi kace ɗan uwan Nidrah ne yasa na bashi yarda ashe macijin sari ka noce ne, ranar da wannan abun ya faru ai nan gida ya zo ya aiko mai gadi wai Nidrah ta zo su tafi school, shine nace a faɗa masa tana gidan su ƙawarta Nu'aymah dake nan farkon layi bata daɗe da fita ba, ashe daya je illa yai masu su duka don yanzu babu wanda bai da tabonsa acikinsu, uwa uba shi wannan daya raba da rayuwarsa".

Wayar Ya Jameel ce ta ɗau ƙara ya ciro ta daga gaban aljihunsa ya ɗaga haɗe da kaiwa a kunne, Muryar Nidrah ce ya ji tana cewa.

"Beb mun dawo ina gidan su Mamie, zaka biyo ka ɗauke ni ne ko na tafi gida da kaina?" Don tafiya suka yi ita da mahaifiyarta zuwa Morocco Allah ya yiwa kakar ta rasuwa wato mahaifiyar Mamie, shi yasa ya dawo gida ya zauna kafin ta dawo sai gashi wannan tashin hankalin ya faru a gaban idanuwan sa, Jiki a sanyaye ya ce ta jira shi gashi nan zuwa sannan ya kashe wayar tare da yiwa Mamah sallama yana sheda mata Nidrah ta dawo, ta amsa masa da "Allah ya tsare ka yi mata sannu da zuwa, hankali ba kwance ba amma zan samu in lallaɓa idan abubuwa sun lafa in je in yiwa mahaifiyar tata gaisuwa". Daga haka Ya Jameel ya miƙe ya fice daga gidan har lokacin na kasa daina kukan da nake yi don ni kaɗai nasan irin tashin hankali da damuwar da nake ciki.

Ko kadan Ya Jameel bai sanar da Nidrah abinda ke faruwa ba sai data dawo anan gidan su Mamie take jin labari wajen mai aikin su, cikin tashin hankali ta shiga kiran Umar Farouk ɗin bata samosa ba don gaba-daya an karɓe wayoyinsa kuma chargy ya kare sun mutu, Ya Jameel na zuwa ɗaukarta tasha kuka har ta godewa Allah ko gaisawa basu yi ba tace, "Beb ina Janaam? Hope she's fine?" "She's" ya iya faɗa kaɗai haɗe da tada motar suka nufi gida, kasa jurewa Nidrah tayi tana kallon yanayin da yake ciki, ta ɗora hannunta a saman nasa a hankali ya juyo ya kalleta ya sake maida idanuwansa akan fito, idanuwanta cike da ƙwalla ta ce, "Beb da gaske ne?" A maimakon ya amsa mata sai ya ce "Me yasa baki sanar dani abinda ke faruwa tsakanin Janaam da Umar Farouk ba tun a waccan ranar bayan ta sanar dake?" "Beb taya zan iya bayan wannan family issue ne bai kamata na saka bakina ba, the only thing shine na bata shawara and i did that ka tambayeta ka ji". "Kenan family dina is not yours Nidrah? Irin wannan babban al'amari yana faruwa kuma kin sani ki kasa sanar dani saboda family ɗina ake cutarwa ba naki ba? Kan me Umar Farouk zai takurawa Janaam da irin wannan soyayya marar ma'ana ki kasa sanar damu, I feel disappointed from you Nidrah". A hankali ta zare hannunta daga saman nashi hawaye na sauko mata a fuska tace, "Ya Allah! Beb bai kamata ka fadi hakan ba, idan ma kana tunanin abun da nai kuskure ne think? Taya zan iya yin kirari na cakawa cikina yuƙa da abinda zai jawo mana matsala acikin family, you don no his mom akansa komai zata iya aikatawa ko da ran kowa zai ɓaci". Wani burki ya Jameel ya taka da ƙarfi yana kallon Nidrah, murmushin takaici ya saki haɗe da cewa, "baki yi kirari kika cakawa kanki yuƙa ba baby amma shi ya haukan zuwa ya cakawa ɗan wasu yuƙa har acikin gidansu ya mutu har la'ila da sunan wata banzar soyayya ta shi, ke ga yanzu sai ran mom ɗin nasa ya ɓaci fiye dana kowa, don wallahi mahaifin yaron nan ya fita uzza, isa da kuma son ya'ya, zai iya kashe ko nawa ne don abi masa jinin ɗansa". Kumshe idanuwa Nidrah ta yi tana sauke su akan ya Jameel haɗe da cewa, "Beb I beg you mubar wannan maganar, ubangiji ya bayyana gaskiyar mene faruwa tsakanin su amma don Allah kada mu kawota cikin marriage life ɗin mu, nayi accepting laifinta na rashin faɗa maka kayi hakuri ka gafarceni ban yi da wata niya ko manufa ba Allah knows that, saboda haka ka yafe mini idan hakan ya ɓata makarai". Ya Jameel bai ce komai ya tada Motar suka bar wajen yana sauke ajiyar zuciya a hankali...

WANNAN LITTAFIN KUƊI NE BA KYAUTA BA KI BIYA NAIRAN 1000 HANKALI KWANCE KI KARANTA.

ACCOUNT NO

7040402435 (MONIEPOINT)

ACCOUNT NAME

BALKISU SANI KAURA

SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR

07040402435

09079274454

ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU 👏

[8/21, 11:05 AM] Queen Qee's💎: *IDO A DUHU*

         *NA*

*BILLY S FARI* 💎

Arewabook:-billysfari

Wattpad:-billyfari9

                            55.

Da daddare dady na tsakar shirin zai kwanciyar bacci wayarsa ta hau ƙara, Momy dake gefen gado zaune ko kallon wayar bata yi ba duk da tana kusa da ita sai 'yan cike cikenta takeyi a system, Dady ya kara so wajen yasa hannu ya ɗauki wayarsa yana kallonta, gabadaya tun da abunnan ya faru ta sauya masa, yar kulawar da take basa duka ta dena kullum cikin latsar system da buge bugen waya akan matsalar dan gaban goshinta take har yabar part ɗinta, yau kwana huɗu kenan da barin part ɗin nata gashi ya dawo ya taddata akai, wayar ya ɗaga yana kaiwa a kunnensa, ɗaya daga cikin yan sandan police station ɗin da aka kulle Umar Farouk ne ya kira, abinda ya faɗa masa ne ya sashi zaunawa bakin gadon jikinsa a mace, tattaro duka kwarin guiwarsa yai haɗe da cewa, "ok to Shikennan babu matsala Allah yakai rayuwarmu, kuyi duk abinda aka saba yiwa kowa gaskiya daya ce kuma a ko yaushe muna bayanta, za kuma mutabbatar da ita akan ko waye". Shiru ya danyi na sakanni yana sauraren ɗan sandan kafin sukayi sallama. Bayan ya ajiye wayar ya gyara kwanciyar sa yana azo kafafuwansa a samanan gadon, sai daya ja duvet ɗin zuwa saman cikinsa sannan ya zauna yana jingina da kan gadon, kallon Momy yai kafin yace, "police station ne suka kira akan case ɗin yaron nan, ashe mahaifin wancan yaron Dr Abdullahi gwaram ne, babban likitan da ake ji dashi a kaf faɗin jahar nan, ƙwararren likita ne da aka yarda da kwarewar sa wajen aiki wanda hakan ya jawo manya-manyan asibitotan jahohin ƙasar nan ke ruguguwar sa don jagorantar wasu ayyukan tiyata da suka gagare su, wannan baiwar da Allah ya yi masa tasa yake da matukar jin kai da kuma izza ya dauki aikin nasa ba abakin komai ba, don yana da wahala yayi aiki ba'a dace ba, ana haka shekaru biyar da suka wuce yayi aiki a babbar asibitin garin nan na wani patient dake fama da matsalar ruɓewar rabin hanjinsa za'a yi masa dashe, bayan sun shiga tiyata yana kan aiki aka kirasa a waya sai ya tsaya yayi picking Call which is not allowed, to sai wata nurse a wajen tayi kokarin lurar da shi cewa hakan kuskure ne kuma ganganci ne da rayuwar marasa lafiya, daga nan sai ya taso mata da faɗa akan shi zata gwadawa aikinsa to bazai karasa aikin ba sai yaga wanda zai sashi, haka aka taru ana convincing ɗinsa yai hakuri sai dai kafin lokacin marar lafiyar ya mutu, to shine wannan ma'aikaciyar ta taimakawa patient relatives din aka sa ƙararsa a kotun mu, a lokacin an samu kwararrin hujjoji har da na waya da suka tabbatar da ganganci ne don an naɗi bayanan komai acikin waya tunda yanzu zamani ya zo da hatta tiyata akan iya saita Camera a waya a naɗe bayanan yadda aka yi ta, to tanan aka samu hujjar data tabbatar da gangancin da yai wajen rasa rayuwar mara lafiyarsa, nan take kotu ta yanke masa hukuncin rai da rai a tsarin dokar penal code, sannan hukumar su ta medical and dental council tayi punishment dinsa ta hanyar Striking-off dinsa a (sashe na 16 na medical and dental practitioner  Act, cap M8 LFN 2004) wato haramta masa yin aiki a Nigeria aka karɓee license ɗinsa kenan, bayan hakan ma iyalan mamacin sun sake kai ƙara a kotun farar hula wato civil liability aka yanke masa hukuncin biyan diya wanda hakan bazai soke wancan hukuncin na penal code da aka yanke masa ba na rai da rai tunda dai-dai yake da criminal case, kin san idan aka ce wani babba kake a ƙasa kuma kana da daurin gindi komai na iya faruwa, a lokacin babu cin hanci da basu bani ba tare da barazana kala-kala akan na sassauta hukuncin rai da rai dana yanke masa a matsayina na Chief judge a High Court din jahar nan amma naƙi, wannan ya haddasa gaba da tsana mai girma tsakaninsa dani, sai suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙasa da yake yana da masu ɗaurin gindi a can sai alkalin CJN ya yanke masa hukuncin biyan diya ga iyalan mamacin da kuma tabbatar dana hukumarsa ta lafiya na karɓe license ɗinsa (Striking-off) wato hanasa aiki a Nigeria aka jaye na kashesa, wannan dalilin yasa ya koma ƙasar waje yana ci gaba da aikinsa, nasan kin tuna hakan ko tunda a lokacin ban ɓoye miki komai ba". Ba tare da momy ta ɗago ta kallesa ba ta ce, "Na tuna amma meye hadin wannan labarin da case ɗin ɗana". "Baki ji me nace ba? Wannan Dr ɗin shi ne mahaifin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login